Sashe 23
Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta had'u da jajurtattu ne. A wasu kujeru suka zauna kafin su shiga tattauna abinda ya had'asu a gurin. Da yake ta sheda fuskarta a tv da jarida yasa suna shiga ta sheda ta, fuskarta a sake take musu lale marhabun tana nuna musu gurin zama, Uwale ba dai karrama mutane ba. Nabila ce kadai take amsawa, ita kuwa kamar kurma! uffan ba tace ba ta nemi kujera ta zauna tana bin falon da kallo, komai akwai tamkar falon shahararan mutumin daya amsa sunansa. hotonansa dake kafe falon sune suka dauki hankalinsa, uku ne d'aya yana sanye da inform wanda yayi masa bala'in kyau! biyun kuma kayan farauta ne rakwacam! a jikinsa hannunsa rike da wata gora mai lankwasa! kansa nannad'e da wani bakin yadi, gabad'aya jikinsa babu masaka tsinke damtsen hannuwansa daddaure da wasu igiyoyi! hoton ya dauki hankalinta mutuka sai kawai ta tsinci kanta da tunanin rayuwarsu a daji! tsigar jikinta gabadaya ta tashi sa'ilin data tuna sassanyar muryarsa a lokacin da yake rarrashinta idan wata masifa ta sameta, lumshe idonta tayi na minti biyu ta bude still hoton ta cigaba da kallo gabanta na wani irin fad'uwa!. Har Hamra'u ta shigo falon tana can gurin kallon hotonsa, gaisheta take amma inaa! hankalinta gabadaya na can wani guri, Hamra'u ranta ya b'aci wata kibiyar kishi mai mugun tsini tazo ta tsaya mata a wuya!! kusa da Uwale ta zauna tana jin takaicin abun a ranta. Maganar Uwale ce ta dawo da hankalinta, da sauri ta janye idonta daga kan hoton tana kokarin saisaita tunaninta ta kalleta da fadin" Kowa lafiya insha Allah gobe nake sa ran had'uwa dasu." Cikin kulawa tace."To masha Allah, don Allah idan kin isa gidan lafiya ki mika gaisuwarmu gare su, Allah ya kiyaye gaba." Ciki-ciki ta amsa da "Ameen." Ta dora idonta kan Hamra'u dake ciccin magani! kallon 'yar 'kauye tayi mata kafin taja tsaki a fili tace." Stupid girl!." Uwale ce kawai bata fahimci komai ba, Nabila da Hamra'u sunji lokacin da tayi zagin sai suka rasa da wanda take a cikinsu! Hamra'u tafi tsarguwa cewa da ita take, ba tace komai ba ta tashi domin barin gurin, ta kalleta a yatsine kafin tace." Ugly!!." (Mummuna!) da yake ta danyi karatu ta fahimci maganar, amma bata tanka ba, tayi saurin bude dakinta ta shige tana mugun mamakin al'amarin! Ita kuwa Nabila duk wannan abun dake faruwa ba sabon abu bane a gurinta ta riga ta san hali shiyasa uffan ba tace mata ba, har ta k'araci iskancinta ta gama, Uwale dai ba jin turanci take ballanatana ta fahinceta, tas taci musu mutunci cikin turanci ba tare da wata shakka ba! Yace."Kamar yanda muka tattauna maganar a kwanakin baya yanzu ma zan sake dawo mana da ita domin samun solution." Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya cigaba da cewa." Ka san da cewar duk abunda yake faruwa Commissioner of police baya gari yaje taron k'arawa juna sani dashi da ta kwarorinsa, sai dai duk abunda yake faruwa yana da labarinsa, ya san labarinka kuma yana da cikakken labarin irin muhimmiyar rawar da ka taka, sai dai kuma a lokacin da ya samu labarin cewa ka fara gudanar da aiki, sai ya nuna rashin goyon bayansa akan hakan, A cewarsa lallai sai kaje kayi training domin haka dokar aiki take, banyi masa gaddamar hakan ba saboda na san yana da hujjah mai kyau! amma na sheda masa cewa umarnin mai girma governor ne hakan, duk da hakan ya nuna rashin goyon bayansa da fadin shi zai zauna da governor din domin su tattauna maganar, shine nayi maka maganar a cikin kwana biyar da suka wuce, yanzu ma ina maimaita maka, gobe insha Allah muke sanya ran zai sauka, babu shakka na san cewa zai nemi zama da kai, ina so ka kula dashi da kyau!domin shi din wani irin bahagon mutum ne mai raina tunanin mutane, a tsarinsa bai yarda da cewa wani ya fishi ta kowanne fanni ba, kullum shine wanda ya iya, sannan baya kar'bar kuskure a tsarinsa, wannan kadan kenan daga cikin halinsa, ina so ka kiyayi mu'amula dashi." Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace." Asp tun lokacin da kayi min maganarsa ban ji wani tsoro! ko fargaba! ba (bahaushe yace fad'uwar gaba asarar namiji!!) Ni na fi so ma naje nayi training din domin nagoge! maganar halinsa kuma wannan bai dameni ba, abinda na sani shine ba zan yarda da rashin gaskiya ba! ba zan aminci a hada baki dani a cuci 'kasata ba! ba zan yarda a cutar da wani ba! ba kuma zan yarda da cin hanci da rashawa ba."! Cikin jaddada gaskiyarsa yake maganar. Asp yaji dadin furucinsa Yace."Naji dadi sosai da wannan alkawarin naka, ina rokon Allah ya tabbatar damu akan hanya ma daidaiciya." Ya amsa da "Ameeen ya Allah." Tare suka mike tsaye, Asp din yace." Idan babu damuwa inaso mu gaisa da Hajiyan." Cike da jin dadi yace." A haba babu damuwa mutumina muje kawai." Tare suka jera domin shiga gidan suna sake tattauna maganar. *Free pege zai kare a pege 40 kuyi payment domin karanta labarin cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, idan da akwai bukata Sadauki Omar 1k za'a tura domin samun damar karanta littafi biyu wato Goje (Sadauki Omar return) mu nesanta kanmu da haram! duk kankantarta! hakkin wani bala'i ne! kada ganin 'kyashi- hassada mugunta ya hanaki biyan kudin littafi ki jira na sata ki karanta! ki dauki nauyi kin dorawa kanki! abunda ba zai zama dole ba, idan baki da ikon biya babu lallai babu dole akan ki dauki hakkin wani gwara ki hakura!!!!* *Wa'inda zasu sayi littafin nake da bukata, idan kin san ba siya zaki ba don Allah kada ki dauki number ta kiyi min magana *#500 via....0542382124.....Binta Umar gtbank, idan kati zaki tura kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.......07084653262....Mutanan Nijar ku tuntubi wannan number.... 22796074090....Dala dari katin airtal ko mov* 1/25/22, 11:27 - Buhainat: *GOJE!! _(SADAUKI OMAR RETURN *BINTA UMAR ABBALE *MANAZARTA WRITER'S* *ASSOCIATION ____________________ *37&38* Da yake ta sheda fuskarsa suna shiga ta ganeshi, cike da farin ciki take masa barka da zuwa, ta nuna masa gurin zama da fadin." Ashe tare kake da yaran naka sannu da zuwa ga guri zo zauna." Asp ya zauna kusa da ita yana amsawa ya dora da fadin." Tare muke tafe dasu ai nace su zo su gaisheki sannan kuma ita ZINATU tayi miki bankwana domin gobe idan Allah ya nufa zamuje mu kaita gida da yardar Allah." Tace."Eh ta sheda min hakan har na bada sakon gaisuwata ga manyan nata, ina fatan Allah ya kai ku lafiya ya kuma dawo daku lafiya." Gabad'aya suka amsa da ameeen ya Allah. Falon yayi shuru na minti biyu kafin tace."Duk ya iyalin naka ina fatan kowa lafiya." ? Yace."Kowa lafiya lou insha Allah gabadaya zasu zo su gaisheki." Cike da jin dadi tace."To shikkenan ina nan jina jiran zuwansu." Tun shigowarsu shida Asp din yake a tsaye a gefen kujerar da take zaune, be kalleta ba ballantana ya fahimci yanayin da take ciki wanda tsayuwarsa a kanta ya janyo mata, k'amshin turaran jikinsa ne yake fizgarta take jin wani irin azababben feelings! ta rasa wace irin masifa ce wannan duk sanda zai kusanceta hankalinta ya kan tashi, gabadaya jikinta ya mutu ta dinga matse 'kafafunta wani irin sanyi ta keji a cikin jikinta, cikin zuciyarta take wasu irin tunane-tunane marasa kan gado............Gyaran murya yayi gabadaya suka kalleshi amma banda ita, Ya dubi Uwale da fadin.'' Ina Hamra'u ne."? Tace."Yanzu-yanzu ta shiga daki watakila ko tana wani uzuri ne." Ya kalli Asp da d'an murmushi a fuskarsa yace." Yana da kyau kafin ka wuce ku gaisa da matata da yardar Allah." Jin abinda yace yasa Asp din yin 'yar dariya ya bashi hannu suka tafa da fadin'' Gaskiya ne abokina hakan yayi ya kamata ta fito mu gaisa." Murmushi kawai yayi ba tare da yace komai ba ya nufi dakin nata. Cikin tsantsar fad'uwar gabada gami da jin wani abu mai bala'in d'aci a wuya ta bishi da kallo a lokacin da yake kokarin bude dakin, ba ta janye idonta daga kansa ba har sai daya shiga dakin, sannan ta sauke wata zazzafar ajiyar zuciya wacce ta janyo hankalinsu kanta, sunkuyar da kanta tayi 'kasa tana 'kokarin saisaita yanayin da take ciki, halin da ta shiga a lokacin da yake maganar ta kasa fassara shi shin wai me hakan yake nufi? Cikin yanayi na damuwa ya sameta, ya kira sunanta ta dago kai tana kallonsa , nan ya hango b'acin rai cikin 'kwayar idonta, cike da kulawa yace."Menene yake damunki."? da yake a kusa take kuma kishi yana cin zuciyarta, sai kawai ta fashe da kuka harda shashsheka! Hankalinsa ya tashi ya zauna kusa da ita yana rarrashinta, da kyar tayi shuru sai ajiyar zuciya take saukewa, ya rike hannunta da fadin." Waye ya ta'ba min ke."? shuru tayi ba tace komai ba, yace." Ba zaki fad'a min ba ko baki da lafiya."? Kai ta girgiza alamun a'a. Yace."Babu daya daga ciki amma kike kuka gaskiya ban yarda ba kada ki boye min abinda ke damunki kinji my dear." Zuciyarta ta sake karyewa kawai sai ta tsinci kanta da fadin." Yanana don Allah Menene tsakaninka da ita."? Yayi jim yana kallonta kafin yace." Wa kenan."? Ta kalleshi hawaye na karakaina a saman fuskarta, hannu yasa yana goge mata tare da girgiza kai alamun ta daina. Cikin shashshekar kuka tace." Kada ka gujeni na riga na makance akan sonka ba zan iya rayuwa da kowa ba idan ba kai ba, zuciyata tana wasiwahsi cewa zaka maye gurbina da wacce 'yar sarkin daka taimaka wannan shine dalilin daya sani zubar da hawaye." Da murmushi a fuskarsa yake girgiza kansa har yanzu hannunta na cikin nasa yace." Babu wata alaka da take tsakanina da ita, ki cire faruwar hakan a cikin ranki, bani da matar aure sai ke, domin duk kin tara abunda nake da bukata, insha Allahu kece uwar 'ya'yana." Wani sanyi ya ratsa zuciyarta, cikin tsantsar farin ciki ta kalleshi da fadin." Nagode masoyina ina fatan Allah ya tabbatar da alkairin da yake tsakaninmu." Ya amsa da "ameen ya Allah." A 'kalla ya kai minti ashirin da shiga dakin shiru bai fito ba, shi kansa Asp din ya 'kosa ballanatana ita