Sashe 39
Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
DA IKON ALLAH NA 'DAUKI HUTUN KWANA BIYU A CIKIN SATI DAYA, INA GODIYA A GARE KU *Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya ba kema keda Allah!* *#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE* 2/7/22, 09:01 - Binta: *G-J-S-U-R* *57&58* 'Daure da towel mai dan girma wanda ya sauko mata har kasan gwiwa ta fito daga toilet din har yanzu akwai sauran damuwar a tattare da ita sai kace wacce ta jima tana kuka idonta yayi wani ja bayan 'kan'kancewar da sukayi wannan shine dalilin da ya sanya Baraka baiwar ta dake aikin jera mata tufafinta a wardrobe ta fara lallaminta saboda duk wani abunda yake faruwa suna da labarinsa. Rarrashinta take sosai tana kara 'kwantar mata da hankali tare da bata shawarwari masu kyau wanda idan ta dauk'esu to tabbas za taci riba anan a gaba. A 'kalla Baraka za ta iya shekaru talatin da biyu a duniya, ta girmeta da wasu shekarun shiyasa take da sinkaye da hangen nesa, kuma dai itama haka kawai take sha'awar uwar dakin nata tayi zaman aure kamar yanda sauran 'yan uwanta suke zaune a dakinsu lafiya, sau daya ta ta'ba ganin mijin nata a zahiri amma duk iya bin k'wa'kwkwafin ta bata hango wani nakasu a tattare dashi ba, namiji ne na nunawa sa'a irin mazan da suke da wahalar samu, 'yan mata da yawa ire-iren ta gasu nan birjik duk a zaune babu mijin aure, wannan dalilin ne yasa take mamakin wasu 'yan matan idan dadi yayi musu yawa suke tsula tsiya iri-iri, ita dai kam ba taga abun gudu a cikin auran mutumin ba domin ya tara duk abunda ake da bukata. Jiki a sanyaye ta zauna kujerar mudubi tana dan goge guntun hawayen da suka sauka a fuskarta, maganganun Baraka sun kashe mata jiki mutuka, ta rasa mai mutane suke hango mata a tattare da zamanta da mutumin nan, duk wanda zai bude baki sai yace mata shine alkairinta, ba ta'ba gani ko jin wanda ya soki al'amarin ba, sai mutum daya wato Sakina kawarta amma tun daga kan family nata har zuwa kan bayin dake cikin masarautarsu dukkaninsu farin ciki da al'amarin suke, ita da Sakina su kadai ne suke nuna adawarsu a fili, tana ganin dai mutumin bai zauna haka ba sai da ya nemi jama'a domin gabadaya ya siye zuciyoyin duk wanda ya shafe ta. Tana shirya jikinta tana auna maganganun Baraka a zuciyarta da kuma tunanin yanda za tayi zaman aure da mutumin bayan har yanzu ya kasa fuskantar alkibula ma'ana ya kasa fahintar abunda take so da wanda ba ta so. Tazo ta gurfana a gabanta da fadin." Ranki ya dade na kammala komai akwai bukatar wani abu."? Ta kalleta cikin rashin walwala tace." Babu bukatar komai a yanzu, sai ko zuwa anjima kina jina ko."? Da sauri tace."Eh ranka ina jinki." Tace."Kada na kuskura naji kin sake yi mib magana makamanciyar wannan, ki kiyaye ki kuma zauna a matsayinki." Baraka jikinta yayi sanyi cikin bin umarni tace."Allah ya huci zuciyar Gimbiyar mata insha Allah zan kiyaye ba zan kuma." Ba tare da tace komai ba ta nuna mata hanya da hannu, ta mike cikin rashin kuzari ta kama hanyar fita tana zanc an zucci, itama mantawa tayi da halin uwar dakin nata ta san ta da gwale mutum, amma meye laifinta anan don ta nuna mata hanyar gaskiya, shikkenan ai daga yau zata kiyaye harshen ta ko don ta tsira da girma da mutuncinta. Kacibus sukayi da Markisiyya ta gama shirya daining zata shiga ta sheda mata. Ta kalleta da fadin." Ya naga kin fito da jiki a sabule."? Girgiza kai tayi kafin tace." Marakissiya kin san halin mutuniyar sai ana kai zuciya nesa shiyasa kwata-kwata ban so dani a cikin wannan tafiyar ba. Tace."Nima haka wallahi kin san bamu da ikon da zamu nuna rashin yardar mu akan haka to kinga dole muyi hakuri kuma mu kiyaye zama da ita." Tace." K'warai hakane maganarki ki shiga ki sheda mata kin kammala ina jiran ki anan." Tace."To shikkenan jira ni na fito. Zubewa tayi kasan gwiwa ta gaisheta kafin ta sheda mata cewa ta kammala shirya gurin cin abinci. Ta kalleta da fadin." Me ki kayi.'? Ta shiga lissafo mata abinci har kala uku. Sosai ta rufe ta da fad'a da fadin taje ta kwashe kayan abincinta bata bukatar cin abinci mai nauyi da safe, tayi maza ta soya mata k'wai da indomee da kuma ruwan tea, Cike da bin umarni ta amsa kafin tai saurin fita daga dakin.. Ita da Barakan suka fita suna munufurcinta da irin munanan halayen ta marasa kyau. Bayan fitarsu da 'yan mintina Uwale ta shiga hannunta rike da kwando wanda yake dauke da kayan abinci. Ta kai tsayin minti goma tana sallama, ta naji ba ta amsa ba ballanatana ta fito. Ta jima a tsaye tana shawarwari da zuciyarta kafin ta yanke shawarar shiga uwar dakin jikinta yana bata cewar ko babu lafiya. Tana tura kofar dakin kawai ta sameta a hakimce a kan kujera tana latsa wayarta, kamar bata so ta amsa sallamar still hankalinta gabadaya yana kan waya bata dago ta kalleta ba, ballanatana taga da me ta shigo. Uwale ta samu gefe ta ajiye kwandon kayan abincin da 'yar fara'a ta tattare da ita tace." Yarinyar arziki ina fata kin wayi gari lafiya ya kwanan bakunta kuma."? Shuru tay mata still dai hankalinta na kan wayarta. Tace." Ga abinci nan nayi miki da kaina na shiga kicin, funkaso ne da miyar taushe da kuma kunun gyada da 'kosai nasan zakiyi sha'awar ci, bayan haka kuma dazu UMARU yayi waya yake cewa wannan kayan masarufin da ki kazo dashi da kuma atampopin duk yace a bayar dasu ga mabukata shine nace lallai sai naji hukuncin da ki ka yanke." Kamar ba taso ta kalleta kafin tace." Bani da damuwa da duk abunda kukayi da kayan, na kune duk wanda kuke so zaku bawa bani da matsala." Tace." To masha Allah mungode sosai Gimbiyar mata ga abinci nan a jiye duk sanda kika kammala sai kici kada ki zauna da yunwa." Ta kalleta a karo na biyu tana yaba k'okarinta, koda yake dole tayi duk wani kokari a kanta tunda tana kwad'ayin ta zauna da jikanta. Girgiza kai tayi kamar tace mata fita da kayan ki bana bukata, sai dai kawai tayi mata shuru har ta fita daga dakin ba tanka mata ba ballanatana tayi mata godiya. Asp ne ya kira ta suka gaisa cikin sakewa yana tsokanarta tana amsawa sama-sama, kafin yace" bari na baki kawarki ku gaisa ko."? Tace" Bata wayar daman yanzu nake tunanin kiranta." Yace." Kin dai yar da Madam bayan da tsohowar zuma ake magani baki kyauta ba." Aunty Zeey dake zaune a kusa dashi ta dinga zabga masa harara. Ita ya ambaci sunan matar ma bata so saboda tsananin kishinta. Daga daya bangaran Zinat din tace." Aa ba haka bane wallahi Mommy uwa ce a gareni kuma har yanzu ban mance alkairinta ba, sannan ka tambayeta ai muna waya sa'i da lokaci muna gaisawa har da Nabila." Yaji dadin hakan a ranshi yace." Masha Allah naji dadin haka ki dauka cewa da Madam da ita Zainab din duk 'yan uwanki ne.'' Tace."Dama ai haka na daukesu a cikin raina.'' Ya mikewa Zeey wayar ta kar'ba tana jin haushinsa, da ya lura da hakan sai kawai yayi murmushi yana girgixa kansa, ya rasa mai yasa ta zafafa akan al'amarin uwargidanta. Ba suyi wata hirar kirki ba a tsakaninsu, dalili Asp din yana gurin shiyasa Aunty Zeey din ta katse hirar da fadin.'' Zan kira ki an jima idan na sallami Oga zai tafi gurin aiki." Tace."Okey to babu damuwa." Sallama sukai kafin kowa ya kashe wayarsa. Da ido kawai ta kalli funkason da miyarsa ta tabbatar da cewa zai yi dadi, duk da cewa bata cin abinci mai nauyi da safe, ganin funkason shar da miyarsa da take tashin kamshi yasa yawun bakinta tsinkewa, ta bude fulas din kunun gyadan shima yay kyau fari tas dashi sai k'amshi yake, dama can tana son kunun gyada da k'osai saboda haka ta kansu ta fara, tana kurbar kunun tana had'awa da kosan, zuciyarta cike da mamakin yanda tsohowar ta iya girki dad'i gaske, wani irin gardin dadi kunun keyi mata, kamar kunnanta ya tsinke. Saboda tasha kunun da yawa funkason biyu kacal ta ci, ba don ta hak'ura ba, sai an jima za ta zauna taci a tsanake idan cikinta ya samu sassauci. Koda Marakisiyya ta shigo ta sheda mata cewa ta kammala aikinta, sai kawai tace taje dashi suci bata bukata har da ta nuna mata kwandon abinci Uwale da fadin." Ita ta samu wani wanda ya gamsar da ita. Marakisiyya taji ciwon abunda tai mata, amma ba yanda za tayi haka tayi godiya tabi umarni ta fita ta kwashe tarin abincin da tayi ha'kilon dafawa ita da Baraka sukaci wanda zasu iya kafin su fita da sauran su kaiwa 'yan uwansu maza da suka zo tare. Ta kira wayar Sakina ya kai sau biyar amma sai ace da ita busy, tsaki taja tare da mi'kewa tsaye, falo ta nufa gabadaya babu kuzari a tattare da ita, dole tana bukatar wanda zai dan d'ebe mata kewa, amma bata tsammanin sauraran boyyayan masoyin nata a kusa duba da irin abinda yay aikata mata saboda kawai ya samu fuska a gurinta, dole ne ta nuna masa kuskuransa. Aikuwa tana tsaka da wannan tunanin kiran sa ya shigo wayarta, tana kallo har wayar ta katse bata daga ba. Ya kira ya kai sau biyar bata dauka ba. Text ya tura mata cewa ta daga wayarsa yana so yayi magana da ita. Ta mayar masa da amsa kamar haka. _" Saboda kawai ka samu fuska shine zaka turo min hotonan banza ko an fada cewa ni din 'yar iska ce."?_ Murmushi yay lokacin da ya karanta text din ya mayar mata da amsa kamar haka. _"My love kiyi hakuri ba zan sake ba tunda bakya so amma ki daga waya ta ina bukatar jin muryarki."_ Share shi tayi bata bashi amsa ba, koda ya sake kira ma tana kallon wayar taki dagawa. Yaji dadin hakan a ranshi amma duk