← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 97

Sashe 79

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sani ba tun dazu nake tambayarta tayi shuru sai share hawaye take wai *'Kafur!* za ta tafi." Ya kalleta da fadin." Wane irin *'Kafur* kuma? ai na dau'ka ko sati uku baki da zuwa ba, ko wani ne ya mutu a can."? Tace." Umaru zama a tare da kai bashi da amfani tunda ban isa na saka ba kuma ban isa na ha naka ba, to zanyi tafiya ta k'auye zamana a can yafi alkairi." Yace." Me nayi miki wanda ya janyo wannan maganar." Tace." Akan abunda kake Umaru shin ko ka samu ta'bin hankali ne."? Yace." Lafiyata lau na san dai duk kina wannan maganganun akan Zinatu, gabadaya ni yanzu bana ra'ayin zama da ita. Tace." Shine dalilin da yasa ka koreta dada gidanka.? Babu wata damuwa a tare dashi yace." Aa ni ban kore ta ba, ita ta kori kanta." Tace." To shikkenan tunda kace haka mutukar kana bukatar zama tare dani kaje kayi bikon matarka." Yace." Uwale ni yanzu muhimiyyar tafiya ce a gabana gobe insha Allah, sai dai idan na dawo." Shuru tayi kafin tace." Umaru baka kyauta ba wallahi jiya abokinka yazo gidan nan hankalinsa a tashe, a bakinsa na samu labari cewa yarinyar bata gidan. Yace." Kina nufin Asp yazo gidan nan bayan na fita."? Tace." Eh yazo kuma yayi min cikakken bayani akan abunda yake faruwa tsakaninka da matarka, gabadaya kaine baka da gaskiya Umaru me yasa ba zaka tausaya mata ba duba da juna biyun da take tare dashi." Yayi shuru zuciyarsa nayi masa wani irin zafi! Asp ya samu damar da har yake shigo masa gida ba tare da izininsa ba, har ya samu damar da zai dinga bibiyar abunda ya shafi iyalinsa, shi ai ba yayi masa wannan katsalandan din, ya kamata a wannan karan ya nuna masa kuskuransa. Hamra'u ta had'a masa ruwan wanka yayi ya samu sassauci amma kadan domin shi kadai ya san irin bakin cikin dake cin zuciyarsa. Ya sanya jallabiya da gajeran wando ya fito falo fuskar nan a murtuke! Ita kuwa Amarya ta rangad'a ado sai kamshin turare take mai dad'i da tayar da sha'awa. Yana zama gurin cin abinci ta isa gurin cikin kwarkwasa da karairaya ta hada masa abincin ta zauna kujerar dake fuskantarsa tana murmushi take bashi labarai irin na jan hankali. Shi dai uffan bece ba abincinsa kawai yake ci, abinda ya dame shi ne a gabansa. A gabanta ya kira wayar Zinatu. koda ta duba taga shine sai ta ajiye wayar........Lokacin mahaifiyarta ta shiga dakin ta samu kiran ya sake shigowa a karo na biyu. Ta kalleta cikin tausayi da jin kai irin na uwa, tace." Ki daga wayar mana." Murya a dashe! tace." Shine fa." Tace." To sai me? ki daga kiji abinda yake tafe dashi." Kamar ba taso ta daga wayar tasa a kunne can kasan makoshi tayi sallama! Gyaran murya yayi kafin yace." Na dawo na samu labarin kin tafi gidanku shin me kike nufi da aikata hakan."? Shuru tayi ta gaza furta komai. Yace." Ke nake sauraro ko kin gaji kamar yanda nima na gaji."? Hanci taja kafin tace." Bani da lokacin tsayawa na saurarin wannan mayaudariyar muryartaka duk hukuncin daka yanke dai-dai ne a guri na." Kawai ta katse wayar ta ajiye. wasu zafafan! hawaye suka kwace mata! ya cuceta ya dirka mata ciki yana mata iskancin da ransa yake so. Uwar ma kamar ta fashe da kuka saboda da takaici. kaf rayuwar yarinyar kwatankwacin rayuwarta ne! tausayinta duk ya isheta, ta sassauta murya da fadin." Kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki insha Allah zamu tattauna maganar da mahaifinki idan auran ba zai yuwu ba a rabu shi yafi alkairi." Da sauri tace."Mammah ni kaina nafi bukatar rabuwar, babban takaici na wannan cikin da nake dauke dashi." Tace." Wannan kuma sai ki barwa Allah, domin shi ya barwa kansa sanin abinda yake boye, kawai kiyi fatan rabuwa dashi lafiya." Kasa magana tayi kawai ta sunkuyar da kanta sai so take ta tsayar da hawayen dake zuba amma ya gagara! zubar hawayen shine samun zaman lafiyarta. Zazzafar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta girgiza kai ta kama hanyar fita zuciyarta cike da tunanin neman mafita. Kishingide ta sameshi a dakin hutawarsa. A nutse ta zauna kusa dashi kafin tace." Barka da hutu ranka ya dade." Ya amsa da "Barka kadai Gimbiyar mata ya gida ina 'yar uwar taki.''? ya tambayeta Safara'u saboda ya san abinda ya kawo ta gurinsa bayan ba girkinta bane tabbas itama Safara'un tana tafe. Tana kokarin magana Safah din tayi sallama, jikinta nannade da lifaya kwantankwancin ta jikin Aysha. Suka gaisa cikin girma da mutunta juna. Zamansa ya gyara yana kallonsu daya bayan daya kafin yace." Labarin gizo a tambayi koki tun kafin kuyi min bayanin abinda yake tafe daku na karanci hakan a fuskokinku. to ina jiran shigowar Magajin sarki ne domin shi nakeso ya kira mijin yarinyar muji daga bakinsa." Gimbiyar tasha kunu da fadin." Ranka ya dad'e wannan al'amarin fa bana wasa bane ya za'ayi a matsayinka na mahaifin yarinyar nan ka wakilta wani ai sai ya kara rainawa mutane hankali saboda haka kai ya cancanta kayi magana dashi." Yace."Aysha ko bayan raina Abdullahi shine Magaji na, wannan dalilin ya sanya nasa shi a cikin maganar domin yayi wa 'yar uwarsa wakilci, ita tazo da magana to amma yana da kyau shima mijin nata aji daga bakinsa. Tace." Wannan yaro fa bashi da kirki! ranka ya dade in banda wulakanci da ciki zai kori yarinya me tayi masa haka da zafi."? Yace." Ashe har kin manta halinta kenan? Aysha idan ke kin manta wacece Zinatu ni ban mance ba, kada ki manta irin d'auki ba dadin da muka dinga yi da ita kafin ta amince da auran, ko shakka ba nayi matsalar daga gurinta take. Safah ta katse shi ta hanyar fadin." Kada kayi gaggawar yanke hukunci ranka ya dad'e! yanda yarinyar nan ta zabge lokaci guda shine zai nuna mana cewa akwai matsalar da take faruwa a tsakaninsu kuma taura d'aya bata taunuwa, bahaushe yace idan anbi ta b'arawo to abi ta mabi sawu, dole shima nasa laifin saboda haka yana da kyau yazo gabanka ku tattauna domin magana ta waya ba zata gamsar ba." Yace." Wannan shawarar taki tayi Safara'u abinda za'ayi kenan. Insha Allah komai zai warware. Magajin Sarki ne ya shigo da sallama a bakinsa. Gabad'aya suka amsa. ya samu guri ya zauna kafin ya fara gaishe su......Maimartaba yace." Ka kira Umaru mijin Zinatu kace masa ina san ganinsa idan ya samu dama." Ya fito da waya domin bin umarni. Daf da zata katse ya daga wayar............bai ma duba suna ba, sai da yayi masa bayanin kansa sannan yace." Magaji afuwa don Allah ya mutan gida ina fatan kuna lafiya." Yace." Kowa Lafiya lau dama Maimartaba ne ya bukaci ganinka idan ka samu dama." Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace." Magaji ayi min afuwa ina da uzuri aiki zai kani Zamfara sai dai idan na dawo.'' Ransa ya baci da jin abinda yake fada.......Yace." Okey to idan babu damuwa inaso na san dalilin da ya sanya Zinatu zuwa gida." Yayi jim yana nazarin maganar kafin yace." Babu wani 'kwakw'kwaran dalili nima kawai na dawo gida na samu bata nan." Yace." No! akwai dalili Goje sai dai idan ba zaka fada ba." Murmushi yayi kafin yace."Ka tambaye mana ni dai na san lafiya lau muke zaune amma ina tunanin kishi ne dalilin da ya sanya ta yanke wannan hukuncin." Yace."Kishi kuma."? Yace." Eh 'kwarai kuwa na 'kara aure kwana uku da suka wuce wannan shine abinda nake tunani." Yayi murmushi da fadin." Ni a ganina wannan kadai ba zai janyo har tazo gida ba ko ka manta da lalurar da take tare da ita."? A dan kausashe! yayi maganar. Shima ya fusata! yace." Magaji yarinyar nan fa bani na koreta ba, ita ta kori kanta, kuma saboda ita ba zan fasa abinda nayi niyya ba, nasan kasan mata hudu Allah ya halasta min to akan wata ba zan tauye rayuwata ba." Ya girgiza kansa da fadin." Okey to babu damuwa Allah ya sanya alkairi ya bada zaman lafiya. Ya amsa da "Ameen ya Allah." Cikin rashin dadi sukayi sallama da juna. Da yake hands free yasa wayar duk suna jin abunda suka tattauna. Yana kishingide bai ce komai ba.....Gimbiya Aysha kuwa sai fad'a take da fadin." Wannan auran warwareshi shi yafi alkairi dama can ita al'amarin be kwanta mata ba, auran jahili wanda yayi rayuwa a daji! bashi da fa'idah mutumin kauye akwai karancin ilimi ta tare dashi babu abunda ba zai aikata ba." Duk yana jin sababin da take bai ce komai ba har sai da ta gama tukkuna ya gyara zamanshi kafin ya fara magana kamar haka. *Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number* *07084653262* *BINTA UMAR ABBALE* 3/22/22, 21:16 - Binta: _Akwai ingantaccan maganin gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ *117&118* "Aysha duk wannan maganganun da kike basu da tushe ballantana makama, wannan dalilin kad'ai ba zai sanya mu kashewa yarinya aure ba, ba hujja bace, dole mu jirayi zuwansa kamar yanda ya fada yana da uzuri to zamu saurare shi zuwa lokacin da zai kawo kansa." 'Bacin rai ya hana ta
Chapter 79 · 0% Book details