Sashe 57
Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
jin yunwa, ya dai daure ne kawai har gari ya waye. Yaji dadin yanda ya samu nutsuwa da ita, amma abunda tayi a yanzu ya 'bata masa rai mutu'ka! sam baya so wani sa'bani mai muni ya shiga tsakaninsu shiyasa yake bin komai a sannu a hankali. Tsabar yunwar da yake ji ta ha nashi aikata komai, sai kawai ya dauki waya ya kira Hamra'u tare da sheda mata cewa zai turo direba yanzu ta had'a masa abinci. Cike da annushuwa ta amsa tare dayi masa fatan alkairi." Ya kashe wayar yana jin wani iri a tare dashi, kwata-kwata bai so hakan ba sai dan babu yanda zai yi. Baraka ta gurfana a gabanta tare da mika mata key din dake hannunta tace."Ranki ya dade na kammala aikin." Ta kar'bi key din da fadin." Kin sa turare a dakin ko."? Tace."Eh nasa ranki ya dade." Tace."Shikkenan ki tashi kije kawai." Godiya tai kafin ta tashi ta fita. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta dauki wayarta dake ajiye a gefanta. Kiran wayarsa tayi, lokacin yana cin abinci yaga kiran nata kamar baya so ya daga.............Ta dan sassauta murya da fadin." Ina kwana." Babu yabo babu fallasa ya amsa. da "Lafiya lau." ta dan ja numfashi kafin tace." Ya aikin ? dama cewa nayi ko zaka turo direba ya daukar maka abinci na kammala." Da karsashi! da kwarin gwiwa take maganar. Yana tauna abincin dake bakinsa yace." lokaci ya k'ure miki sai da kiyi hakuri domin yanzu haka abinci ne a gabana nake ci idan kina bukatar naci abincinki sai kiyi himma idan Allah ya kai mu gobe." Tace." A ina ka samu abinci."? Kai tsaye yace." Gurin Hamra'u." Gabanta yayi wani irin faduwa! Ta maimata maganar. "Gurin Hamra'u fa kace."? Yace." Eh kina mamaki ne."? Wani kuttun takaici ya tokare mata a wuya!! Kashe wayar kawai tayi wani mugun kishi da b'acin rai! ya turnuke ta. "Hamra'u! Hamra'u! Hamra'u!!! wannan yarinya ta zame mata kadangaran bakin tulu! Ta dinga tunanin irin cin zarafin da za tayi wa yarinyar domin ta huce ba'kin cikin da take kuntuka mata! Shin wai meye ruwanta da mijinta ne.? Falo ta fito ta zauna kan kujera kafin ta 'kwalawa Marakisiyya kira. Da sauri ta fito daga kicin tana amsawa, tace." Je ki sashen masu gidan kice Hamra'u tazo ina neman ta." Da sauri ta amsa kafin ta kama hanyar fita. Sosai Hamra'un tayi mamakin kiran da take mata, Uwale tace." Ki tashi kije mana kada zuciyarki ta raya miki sharri! Tace."Uwale bana bukatar wata mu'amula ta shiga tsakanina da matar nan saboda bata da kirki wallahi albarkacin Yaya na kawai nake saurara mata." Uwale tai murmushi kafin tace." Kin kyauta ai tashin hankali bashi da amfani ki tashi kije watakila sulhu take nema dake. Tayi jim tana nazari kafin ta yanke shawarar zuwa. Ta same hakimce a kan kujera, sai da taji wani abu ya dan ta'ba zuciyarta, kallon fuskarta tayi suka hada ido, bata hangi komai ba, domin ita gimbiyar ta boye b'acin ranta. Da hannu ta nuna mata gurin zama. A nutse ta zauna kafin tace." Kin tashi lafiya ."? Ta amsa da "Lafiya ya kuka tashi? ya Jikin Uwale."? Tace." Taji sau'ki." Falon yayi shuru na 'yan mintina kafin tace."Kin san kiran da nake miki kuwa."? Tace."Aa sai sheda min." Murmushi tayi kafin tace." Ni da kaina na ha naki hidima da mijina saboda wasu dalilai na, kiyi hakuri yanzu na amince miki cewa ki cigaba da ayyukanki nagode sosai wannan shine dalilin kiran, kada kiji komai na yarje miki cigaba da kula da d'an uwanki." Ba ta kawo komai a ranta ba tace." To shikkenan idan maganar kenan ni zan tafi." Ba tare da tace komai ba ta nuna mata hanya da hannu. Ta tashi ta fita tana jin wani irin dadi domin ita a tunaninta Umar din ne ya nunawa gimbiyar muhimmamcinta shiyasa ta nemi sulhu da ita dama ita tasan Umar yana sonta saboda haka zata sake zage damtse gurin kulawa dashi har tasha gaban duk wata 'ya mace a gurinsa... *Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number* *07084653262* *BINTA UMAR ABBALE* 2/28/22, 09:20 - Binta: *LOVE! *83&84* Ita kad'ai ta bar wa zuciyarta abinda ta kudurta, malam ba haushe yace (wanda ya'ki sharar masallaci yayi ta kasuwa) yamma likis ya dawo gidan da tarin gajiya a tattare dashi. Tsaye ta mike tana masa barka da zuwa. Tun daga sama har kasa yake kallonta, gabadaya yaji gwiwarsa tayi sanyi yarinyar na da wani irin diri da zubin jiki mai kyau! Tana sanye da 'kananun kaya wanda suka matse ta riga da wando tight! hattar da shatin nipples dinta sai da suka fito, wandon ya manne a jikinta ya fito da sharp din jikinta wanda yake mutukar masifar so da 'kwakwa! sosai da sosai Kwalliyar ta tafi da imanin sa. Ya sauke zazzafar ajiyar zuciya kafin ya janye idonshi daga kanta, ko'karin wuce ta yake, da sauri taje ta rike hannunshi, kanta ta d'ora saman kafadarshi.......Be iya ce mata komai ba kawai yasa hannunshi guda ya rike kwankwasonta a haka suka shiga dakin taba langwabe a jikinsa. Tare suka zauna bakin gado ya fara kokarin cire safar kafarsa, 'kasa ta sauka ta kama kafar tana kokarin cire masa.......sai ya mayar da hannushi wuyansa yana cire botiran rigar dake jikinsa, ya ajiye saman gado. Kallonshi tai tana dan lumshe idonta.....Yayi saurin janye idonsa daga kanta jin yanayin jikinsa yana sauyawa. K'afar sa ya dan janye jin kamar tana masa tafiyar tsutsa! Ta tsurawa yatsun kafar ido gashin da yake kwance kan yatsun take ja a hankali. Ya sake janye kafar a karo na biyu, yace." Me ya hakane."? Murmushi kawai tai kafin ta koma ta zauna kusa dashi tana nanuk'arsa! Cikin zuciyarsa yace."kalankasa sai san jiki da fitinar tsiya! Hannu ta dora saman kirjinsa tare dan jan nipple dinshi d'aya Da sauri ya cire hannun yana d'an harararta, ya riga ya fahimci abunda take so, kawai sai ya zame kafad'arsa wanda kanta yake kwance ya mike da sauri toilet ya nufa. Jiki a mace ta dauke kayan da ya cire ta ajiye a in da aka tanada.....gefan bed din ta zauna tare da tsirawa toilet din ido, wani lokacin har mamakin kanta take ganin yanda ta damu rayuwarta a kansa wai har tana kishinsa, koda wasa ba tayi tunanin hakan na iya faruwa ba. A gurguje ya fito daga toilet din kasancewar lokacin sallah ya gabato yana kimtsa jikinsa tana aikin kallonsa, kafin tace." Abinci yana jiran ka a daining." Ya dan juyo yana kallonta kafin yace." Da gaske."? Kai ta d'aga masa.....'Karamin murmushi yayi kafin yace." Nagode sosai na kuma ji dadin hakan amma sai na fito daga massalaci tukkuna." Ba tace komai ba ta mike kai tsaye gurin da yake ta nufa. Yana kokarin fesa turaran ta kar'ba daga hannunsa. Ya zuba mata gajiyayyun idanuwansa da suke kokarin tona asirin da yake boyewa. Cikin nutsuwa take fesa masa turaran, shi kuma yana ta aikin kallonta da mamakin abinda take, sam bai tsammaci cewar hakan zata faru ba, duba da irin rabuwar da sukayi da safe, bayan haka kuma ta kira waya yaki dauka, yayi tunanin daya shigo gidan rigima zata 'balle sai yaga akasin hakan. Ta ajiye turaran saman mirror tana kallonsa, har yanzu idonsa k'uri a kanta da alamar tambaya a tattare dashi. Karamin yatsanta ta kai saman idonsa, yay saurin motsa kwayar idon kafin ya dawo hankalinsa, tace." Ka tafi massalaci kada ka rasa jam'i ." Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya dauki cazbaha dake saman mirror din, ya kalleta da sakakkiyar fuska "Allah yay miki albarka." Da farin ciki ta amsa da "Ameen my husband." Murmushi kawai yayi ya juya da niyyar fita. Ta bishi da kallon so da k'auna tare da ayyana abubuwa masu kyau a tare dashi......Yanda ta daukeshi ba haka yake ba yana da kyawun zuciya. Sosai yayi mata adduar shiriya da fatan dorewar zaman lafiyarsu, yanda yake jin ta a cikin ransa yana ganin zai iya kare rayuwarsa tare da ita kad'ai mutukar zata cigaba da kyautata masa tare da bin iyakokin da Allah ya ajiye. Sai da ya gabatar da isha'i tukkuna ya koma gidan. Gurin su Uwale ya nufa domin baya tsammanin idan ya shiga sashensa zai sake fitowa yafi bukatar ya zauna tare da gimbiyar tasa yana kallon ado da kwalliyar ta. Wai akace kowacce mace da irin kissa da kisisinar ta, duk yanda Hamra'u tayi domin ta janye hankalinsa abun ya gagara! domin dai gabadaya kaf hankalinsa da tunaninsa na kan matarsa magana yake amma tunaninsa na gurin ta. Tayi- tayi! ta buga dashi kan yaci abinci fafur! ya'ki, jikinta yayi mugun sanyi dan ba tayi tsammanin faruwar hakan ba, domin tunaninta yana nuna mata cewar sulhu da Gimbiyar ta nema ya samo asali ne ta dalilin jajurcewarsa ashe hasashe kawai take ba haka abun yake ba......Kuka ne kawai ba tayi ba don ganin ha'kanta bai cimma ruwa ba. Yayi musu sallama ya tafi babu wani 'kulli a zuciyarsa........Ita kam kasa daurewa tayi ta shiga dakinta taci kuka ta koshi! gaskiya ta gaji da wannan game din dole tasan matsayinta ta gaji da zama ba tare da ta san meye makomarta..........To itama dai Uwale tunanin da take kenan tana so idan Allah ya kai su 'Kauyen *Kafur!* su samu zama da iyayen yarinyar domin su tsayar da magana. Duk da abincin bai masa yanda yake so ba, haka nan ya daure yaci domin ya 'karfafa mata gwiwa domin duk a tunaninsa itace tayi, tissue yake kokarin yaga, ta rigashi ba jira komai ba ta fara goge masa baki, fuskarsa a sake yace." Ashe amaryar tawa gwana ce a kowane bangare." Murmushi kawai tayi ta gyara zamanta kan kujera kamar gaske tace." Na iya girki ko."? Yace." Sosai kuwa! yayi dadi amma ko dan gaba ki kiyaye bana san yaji sosai a abinci." Tace." To zan kiyaye insha Allah." Shuru gurin ya dauka na 'yan mintina kafin ya kalleta da fadin." Kwana nawa abun yake kafin ya tafi."? Ta kalleshi da nazarin