Sashe 34
Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
'karasa kusa da ita ta tsira mata ido na minti biyu kafin tace." Sai yanzu ki ka tashi kenan."? Kai ta daga a raunane tace." Aunty an d'aura auran ne."? Girgiza kai tayi da fadin." Sai goma da rabi tukkuna, na shigo ne domin naga ko kin gyara jikinki ashe ke kina ma kwance." Kai ta dafe da fadin." Jiya ban samu bacci ba sai gefin asubah, shiyasa ban tashi da wuri ba ko sallah fa banyi ba." Tace." Zinat ba zaki sanyayawa ranki ba ko? me yasa kike so ki jefe kanki cikin wani hali, iyayenki fa ba zasu ta'ba cutarki ba." Tace."Aunt Hassana don Allah mu bar wannan maganar domin ni ba wannan ne dalilin ya hana ni bacci ba, ai na hakura na barwa Allah." Tace."Okey to idan hakane ki tashi ki gyara jikinki kiyi kwalliya sosai tunda kinqi yarda da ayi miki kitso da kunshi (lalle) irin na amare kada dai ki yarda mu da muke 'yan gayya mu fiki kyau zakiji kunya. Murmushin takaici tayi tana kokarin saukowa daga gadon tace." Bana ra'ayi ne kawai, amma ban ha naku kuyi kwalliyarki ku ba, ban damu ba idan kun fini kyau." Hanyar toilet ta nufa jikinta duk a sanyaye........Aunty Hassanar ta bita da kallo tana girgiza kanta, ta rasa wane irin hali ne da ita gabadaya a baud'e take. Wani dan'kareran les ta fito mata dashi kudinsa ya kai dubu dari da wani abu rigar bubu ne anyi ado da wani irin net bayan stones din dake jikin les din an kuma baza wani stones din masu walwali a jiki, c-green ne, color shi tayi kyau sosai. Duk wani abu da ta san za tayi amfani dashi sai da ta fito mata dashi ta ajiye mata. Tana kokarin fita daga dakin, kira waya ya katse mata hanzari. Ta dawo ta dauki wayar tana dubawa, sunan ba'kauye ne yake yawo kan fuskar wayar. Cike da mamaki take duba wayar, waye wannan kuma? toilet din ta kalla, ta san halinta tun tana yarinya take da nawa bata da zafin nama haka take idan ta shiga wanka sai an manta da ita. Yanke shawarar daga wayar tayi a nutse tai sallama. Jin sabuwar murya cikin nutsuwa yasa shima ya amsa a nutse da fadin." UMARU ne." Da sauri tace." Angon ne ashe kayi hakuri tana bandaki sai dai idan ta fito ko." Yace."Babu damuwa idan ba matsala ina so na san da wa nake magana." Murmushi tai kafin tace."Hassana ce yayar amaryar taka. Yai murmushi da fadin." Ai kinga tambayar tayi amfani Auntynmu ya hidima da jama'a."? Tace."Alhamdulillhi wallahi, Allah dai ya sanya alkairi ya baku zaman lafiya UMARU kayi hakuri da yarinyar nan daban take a cikinmu tana da wani irin hali, amma kuma idan ka'iya zama da ita tana da sauki kai da iya mu'amula." Yace." Kada ki damu aunty insha Allah zan rike amanarku zan iyakar bakin kokarina." Tace." To mungode sosai Allah ya baku zaman lafiya." Ya amsa da ameen ya Allah ya dora da fadin "bari na bari zuwa an jima zan sake kira." Tace."To shikkenan babu damuwa." Sallama sukayi ta zauna zaman jiran fitowarta. Ido suka hada lokacin data fito daga toliet din tace."Wai dama kina zaune har yanzu." Tace."Nazo fita ba k'auye ya kira wayarki." Saurin kallonta tayi suka hada ido ta girgiza kanta rai a bace tace." Kin ji kunya ko."? Girgiza kai tayi tana dan tabe baki tace."Wane irin kunya kuma." Gaban dressing mirror ta wuce tana ya mutse fuskarta. Aunty Hassanar tace."Kullum kina nuna mana cewa kin saduda ashe ba haka bane, a zuciyarki don iskanci ki rasa da wane suna za kiyi serving number sa sai da ba k'auye wai shin ma dame ki ka fishi kin san dai baki fishi kyau ba." Tana 'yar dariya tace."Aunty Hassana ai sunan da ya dace dashi kenan, d'an k'auye ne dashi da family sa, kinga kuwa babu laifi don an kira shi da wannan sunan ba kauye bagidaje." Ta girgiza kai cikin takaici tace." ki cire wannan sunan bai dace ba, gwara kisa masa sunansa na Asali hakan shi yafi mutunci." Saboda bata san suyi ta ja'in ja yasa tace."To shikkenan aunty zanyi yanda ki kace din, amma da ya kira me yace miki."? Tana kokarin mikewa tace." Be ce komai ba zai dai sake kiran ki abinda fada kenan. Ta'be baki tai ta cigaba da shafa mai a fatar jikinta. Aunty Hassanar tana kokarin fita daga dakin ta dakatar da ita da fadin." Aunty Hassana ya maganar mutanan da aka tura su shirya min daki." Tace."Ai babu wannan maganar domin mijin naki ya shedawa Maimartaba cewa ke kadai yake bukata akwai komai na bukata a gurin da zaki zauna wannan dalilin yasa aka rushe wacan maganar. Ta girgiza kai da fadin." Wannan ai zubar da kima da mutunci ne, Aunty Hassana cikinku wa aka ta'ba yiwa haka? ai na dauka kowacce sai da aka cika mata daki uku da kaya amma ni saboda ba'a sona za bar ni haka, to wallahi babu wanda ya isa na dogara dashi da kayansa. Hannu ta daga mata da fadin." Wannan maganar Maimartaba zaki samu ki fada masa bani da kika raina ba, Zinatu kije ki samu mahaifinki ki nuna masa cewa baki yarda da hukuncinsa ba, wannan shine zai tabbatar mana da cewa kin fita zakkah a cikinmu." Tana gama maganar ta bude dakin ta fita ranta a mugun 'bace! addua ce kawai zata shiryar musu da ita. Hawaye masu zafi suka dina sauka a saman fuskarta, wannan tozarci dame yay kama? kamar ita 'yar gata gaba da baya amma a kaita gidan aure babu kaya sai kayan miji wanda ta raina bata daukashi a bakin komai ba, kwata-kwata ba'ayi mata adalci ba. Kiran wayarsa ne ya katse tunaninta, da sauri ta dauki wayar tasa a kunne sai ajiyar zuciya ta saukewa cikin kuka tace." Bana bukatar komai naka a gurin da zan zauna, ka kwashe komatsanka zanzo da nawa baka isa na dogara da kai da abunka ba." Tun wayewar gari ya tsinci kansa cikin walwala da farin ciki, wanda shi kansa ya kasa gane dalilin.............Wannan shine dalilin yasa maganganunta ba suyi masa zafi ba, yay murmushi irin wanda ya saba kafin yace." To ke meye na damuwa bayan baki da niyyar zaman auran, ai zuwa da kayan daki zai miki wahala shiyasa na hutashsheki, bayan haka kuma nima haka na samu gidan cike da kayan more rayuwa gwamnati ta zuba min, kada ki damu sashenki daban sai kin so zaki ga wani kuma baki da matsalar komai, wannan dalilin yasa na shedawa Maimartaba cewa ke kadai nake da bukata." hanci taja kamar za tayi magana sai kuma taja bakinta ta tsuke kokarin kashe wayar take yayi saurin fadin." 'Karfe nawa ma za'a daura auran."? A kufule! tace."Ban sani ba."!! Kashe wayar tayi tana tsaki sai numfarfashi take na takaici da 'bacin rai! Dariya yay mai yawa kafin ya ajiye wayar ya nufi toilet cikin wani irin farin ciki wanda ya jima be tsinci kansa a ciki ba. *'DAURIN AURAN* Ya samu halartar manyan mutane sarakai 'yan kasuwa da manyan 'yan siyasa daga kowace jaha, daurin auran yayi albarka da yawa daga cikin mutanan da suka halarci daurin auran sunyi mamakin rashin halartar angon, sai dai Asp beyi kasa a gwiwa ba gurin sheda musu halin da ake ciki, hakan yasa wa'inda ba su sheda da UMAR din ba suka sheda dashi da jamurtarsa amma mafi akasari jama'a sun san shi a hoto da kuma gidajen television................ Asp bai samu kansa ba sai da ya tabbatar da cewa yasa jama'ar da suka samu damar hallatar daurin a auran a mota, da yawa daga cikinsu 'yan uwan UMAR din ne da suka dinga turereniya gurin zuwa daurin auran. wanda aka daura a garin KANO a fadar maimartaba Sarkin gari.. *Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya ba kema keda Allah!* *#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE* 2/2/22, 18:21 - Buhainat: _Ina muku tallan group dina mai suna_ *MAR'ATUSSALIHA* *Wanda na bude shi wata shida da suka wuce a lokacin 1k ne kudin register, yanzu saboda yanayi na rayuwa yasa na mayar dashi #500 za kiyi register domin kasancewarki cikin group din, matan aure da zawarawan dake shirin aure da 'yan mata masu shirin aure ku nake da bukatar kuyi rigstar domin k'aruwarmu baki d'aya, akwai sirri da amana a tsakaninmu, duk wata matsalar dake damunki ki sameni ta pravite insha Allah zan baki shawarwari wanda zasu taimaka miki domin gyara kanki da zamantakewar auranki, 'yar uwa kiyi register da group din MAR'ATUSSALIHA Insha Allah zaki samu mafita.......ga duk wacce take da bukatar biyan kudin 0542382124....Binta umar gtbank sai ki tura kudin ta wannan account din ki tura min sheda ta wannan number... 07084653262* *51&52* Fitowarsa daga wanka yayi dai-dai da shigowar kira a wayarsa, koda ya dauki wayar ya duba sai yay murmushi domin ganin sunan wanda yake tsammani a fuskar wayar Yasa wayar a kunnanshi tare da sallama a bakinsa. Daga daya bangaran Asp ya sauke ajiyar zuciya da fadin."Alhamdulillhi komai ya kammala an daura aure cikin farin ciki da mutunta juna kowa ya kasance cikin walwala da farin ciki, bayan haka daurin auran ya samu halartar manya mutane daga kowane sassah na kasar nan, anyi taro an tashi lafiya duk jama'ar da suka samu damar halartar daurin auran daga b'angaran ka kama daga 'yan uwa da abokan arziki da kuma yaran ka yanzu haka suna kan hanyarsu ta komawa gidajensu da ikon Allah, muna rokon Allah ya bada zaman lafiya a cikin wannan auran sannan ya mayar da kowa gidansa lafiya." Numfashi ya sauke bayan k'are maganar Asp din yace." Na rasa da wane baki zan mika godiya ta a gare ka, hakika ka cika mutum wanda ya tara duk wasu abubuwan da ake da bukatar mutumin 'kwarai ya kasance, wallahi wayewar yau haka kawai na tsinci kaina wani irin farin ciki wanda na kasa tantance ko na menene? bana gari ina wata uwa duniya ka tsaya min akan muhimmin al'amarin da cancanta ace ni nake tsaye a kansa, Asp da izinin Allah ba zan baka kunya ba, yanda ka tsaya kai da