Sashe 5
Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kukan na kara kusanto inda take yasa ta kurma ihu! sai ta fara jan gwiwa tana waiwayenta bayanta. Jin ihunta ya tashi hankalinsa da saurin gaske yasa bakin kokon dake hannunsa ya kamfaci ruwan dake gudana ya juyo da saurin gaske, me zai gani ita ya hango a gigice! tana rarrafe tare da d'aga masa hannu, haushi ta bashi, bega abun gudu a gurin ba, tuntuni sun saba yada zango a gurin, babu wata dabbah mai cutarwa da ke zuwa gurin. saboda su kansu dabbobin sun gane gurin, basa tunkarar zuwa sun san idan sun shiga basa fitowa cikin dadin rai. Koda ya k'arasa inda take sai kawai ta rike masa kafafu tana karkwarar jiki, "Allah yasa tsakanina daku azzalimai macuta." Kalmomin da suka futo daga bakinta kenan ta nayi tana dukan gwiwarsa harda cizo. Gabadaya ta kanainayeshi, tana dukansa, kuka take sosai! bece mata komai ba har sai da ta gaji da kukan ta cikashi, ta daga kai tana kallonsa, ya cije baki kamar yanda ya saba idan zaiyi magana "Na fahimci duk gidan da ki kaka fito babu tarbiya, bana shiri da mara kunya ba kuma na san raini! meye laifina anan? ina iya kokarina akanki kina zagina saboda kina takama da mulki da sarauta ko."? Hannu ta daga masa da fadin." Kaga malam ya isa haka kawai ni ka daukeni ka bar gurin nan dani." Ya girgiza kansa kamar koda yaushe idan zaiyi magana yace."Ba zaki samu hakan ba, yanda kika rarrafo da gwiwarki hakanan zaki biyo bayana." yana gama maganarsa ya fizge kafafunsa ya barta a gurin. Da kyar tayi yunkurin tashi tsaye, ta daga masa hannu da fadin." Don Allah kada ka tafi kayi hakuri ka dawo kafafuna sunyi tsami ba zan iya tafiya mai tsayi dasu ba." Yana jin maganarta be juyo ba ya cigaba da tafiyarsa, yana so ya fara koya mata hankali tunda ya fuskanci bata da mutunci. Takawa take tana ciccije baki, hawaye kuwa sai karakaina yake a fuskata, abubuwa da yawa sunyi mata dabaibayi, ciwo! tsananin fargaba da tashin hankali bakar azaba da yunwa ta rasa da wane bala'i za taji. Tun tana hangensa har ta daina, ta dinga tafiya cikin ciyayi tana jin saukar kwarika a kafafunta, ta riga ta saduda ta barwa Allah da wannan masifar da take ciki gwara wata dabbar ta cinyeta. Ya kai minti ashirin da isa amma shuru babu labarinta, a jikinsa yaji akwai wani abu tunda babu wata tazara mai tsayi tsakaninsu da bakin kogin. Bayanta yabi yana haske fitilar hannunsa, yaci tuntube da ita, kwance kafafunta sun rufta cikin wani rami da alama na wasu dabbobin ne, sai kici-kici take tana kuka, hannunsa ya mika mata, ta rike da kyau! yasa karfi ya fizgota! Ajiyar zuciya suka sauke a tare, be jira komai ba, ya sunkuya tare da juya mata baya, kafira! bakin rashin kunya ya mutu, tana zazzare ido ta haye bayansa ya mike tsaye da ita, hannunta tasa sosai ta matseshi, sai ajiyar zuciya take, shi kam cakumar da take masa ta sanyashi shiga tashin hankali wanda sai yayi shekaru be shiga irinsa ba, huci kawai yake yana cizan lips dinsa, cikin mawuyacin hali suka isa gurin, Yayi gaggawar sauketa, tayi kwance a gurin tana fitar da numfashin wahala, shi kam can gefe ya matsa tare da juya mata baya, matsalarshi guda a yanzu halin da ya shiga, shigarsa a wahala amma fitarsa nada wuya yakan yi kwana da kwanaki kafin yanayin ya bar jikinshi. *Ga wa'inda basu samu damar karanta Sadauki Omar ba, zasu biya 1k domin samun damar karanta littafi biyu* *#500 via 0543282124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....* *22796074090* katin Mov ko airtal 1/12/22, 20:32 - Buhainat: *GOJE!* _(SADAUKI OMAR RETURN *BINTA UMAR ABBALE *_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION _____________________ FREE PEGE _Ina mika sa'kon ta'aziyya ta ga al'ummar musulman duniya baki daya, Na babban rashin da mukayi, hakika ba zuri'ar Malam kadai ne sukayi rashi ba duk duniya ne, muna rokon Allah ya jikin Malam Ahamad B.u.k (Bamba) Ya sanyashi cikin Aljanna madawwamiya Allah ya kyauta namu zuwan bayan tasu *9&10* Ya jima yana kokarin kawar da yanayin daya yake ciki amma abun ya gagara! yakan zama sakarai mara dubara a duk sanda irin wannan yanayin zai shiga jikinsa, gabadaya wayo da dubararsa nemarsu yake ya rasa, jikinsa ya takure guri daya, yana jin wani irin sanyi tare da tashin tsigar jiki. Ba da son rasa ba ya juya kanta, yaga tana wanke fuskarta da ruwan daya ajiye, Asuwaki ya mika mata tabi asuwakin da kallon banza kafin tasa hannu a wulakance ta karba, duk da asuwakin sabo ne sai da ta wankeshi sannan tasa a bakinta, dauke kansa yayi yana girgiza kai ya lura da yarinyar kyankyaminsa take, a tunaninta ko yasa asuwakin a bakinsa. Wani buhu ya janyo ya dauko wasu mangwaro masu nuna manya guda uku, ya wanke tas karamar wuka ya zaro daga jikinsa ya mika mata mangwaron da hade da wukar. Hannu na rawa ta kar'ba yawunta na tsinkewa, bala'in yunwa takeji dama. Kafin tayi amfani da wukar sai data tasa ruwa ta wanke duk da tana ganin acikin gidanta ya fito da ita amma bata yarda da tsabtar duk wani abu da zai fito daga jikinsa ba. Inda Allah ya taimkashi, kayan dake jikinsa masu kauri ne wannan dalilin ya hana girmanshi fitowa amma a zahiri gabanshi yana tsaye kyam! sama da awa daya da rabi yaki kwanciya duk da 'yan dabarun da yayi abun yaci tura, sa'i da lokaci yana shiga irin halin amma na yau yafi muni. Itacuwa ya had'a ya kunna wuta ya zauna yana gasa jikinsa duk a kokarinsa na ganin ya kawar da abunda ke damunsa. Ita da take zaune ba tsirara ba ba kuma mai suttura ba, ta yun'kura ta mike da kyar take tafiya har ta cimma inda yake jin zaune. Zata zauna ya daga mata hannu, ba tare da ya kalleta ba yace."Ki koma ki zauna a inda kike ko kina bukatar wani abu ne."? Hararsa tayi tana murguda baki kafin tace."Naga kana shan dumi kai kadai shiyasa nazo nima ina bukata. Tana maganar tana kokarin zama kusa dashi. Tun daga sama har kasa yake bin ta da kallo, har ta samu guri ta zauna tana kara hannuwanta a jikin wutar, yanayin zaman da tayi yayi masifar jefashi cikin tashin hankali, inda ita kuma a wautar ta bata kawo komai ba tana ganin ai da tun farko yayi niyyar lalata da ita to da yayi amma ta lura sam ba wannan ne a gabanshi ba. Ya dinga kokarin dauke kansa da kanta amma Shaidan yana kara 'kawata masa suffarta, gaza dauke idanuwansa yayi daga kanta, ya cigaba da satar kallon wasu guraran da suka bashi sha'awa a jikinta, amma be yarda ta fahimci halin da yake ciki ba. Sun jima a haka babu wanda yayi magana a cikinsu, kafin suji bushe-bushe na kusanto inda suke da alama yaranshi ne suka dawo daga farauta. Ta kalleshi a lokacin da ya tsirawa shara'ban kafarta ido. Tayi saurin gyara kafafunta tana watsa masa harara. Ya sauke ajiyar zuciya tare da sake tamke fuskarsa cike da bada umarni yace."Ki tashi ki bar gurin nan." Yanda yayi maganar babu wasa yasa ta tashi tsaye, yayi saurin dauke kansa, kawai sai taja masa tsaki ta wuce! Abin ya bashi mamaki mutuka! ya girgiza kai tare da nazari da tunanin matakin da zai dauka a kanta Gurin gabad'aya ya rikice da gangi da bushe-bushe duk a sakamakon dawowarsu, hannu tasa ta toshe kunnuwanta takaici kamar ya kasheta, da yake da akwai hasken wutar daya kunna tana kallo suka dinga firfito da matattun macizai da mesa tare da sauran dabbobin da suka farauto, Abun ya dinga bata mamaki ganin sun daga wani lafcecan maciji sun sanya wuka mai kaifi sun rabashi gida biyu, suka tsire shi a jikin wani itace kafin su barbada masa gishiri da wani abu ja da alamar manja ne sannan suka sanyashi a wuta suna gasawa. Hankalinta yayi bala'in tashi, karni da wari duk ya cika gurin zuciyarta ta dinga hantsilawa saboda tsabar kyankyamin abunda suke. Tana nan zaune tana kallon ikon Allah suka gama gasa maciji nan wanda bai sani ba sai yace bushashshan kifi ne suka fara yankarsa da wuka suna ci hankalinsu a kwance. A gurin ta dinga kyalaya amai duk sai da ta amayo mangwaron data sha, taja gefe guda tare da toshe hancinta. Sai da dare ya tsala sosai sannan kowa ya nemi makwanci, yana sanya kafarsa yaji ya taka abu cabal! yayi saurin kunna fitilar hannunsa yana dubawa, aman da tayi ne duk ya bata kan shimfidar, tana rakube a gefe guda bacci ya dauketa. Yaji takaicin bata mai shinfida da tayi yaja tsaki tare da samun ruwa ya wanke kafarsa ya dawo yana tunanin inda zai sanya hakarkarinsa ya kwanta ba don bacci ba. Kusa da ita ne kadai babu kazanta kuma baya so ya kusanceta gudun abinda ka iya zuwa ya dawo, domin har yanzu yanayin be bar jikinsa ba. Kawai sai ya yanke shawarar zuwa gurin yaranshi domin samun matsuguni, tsakaninsu babu wata tazara mai tsayi kuma yana da tabbacin babu abunda zai sameta, rigar jikinsa ya cire ya rufa mata a jikinta sannan ya bar gurin. Da yake baccin ya dauketa a cikin tsoro da fargaba yasa ta dinga munanan mafarkai da namun daji sun biyo ta zasu cinyeta sai ta farka a gigice! tana kwalla ihu! da fadin." Kura ce! kana inaaaa! *GOJE!!* zata cinyeni."! Gabadaya suka tashi tsaye da shirin ko ta kwana, amma ba subi bayansa ba, shine ya cimma inda take tsaye sai rawar dari take a tsaye. Yana zuwa ta rungumeshi, tsam! tsam! tana wani irin kuka da fadin." Kura ce ta biyo ni."!!! Ya dinga nanata mata addua a kunnuwanta har ta samu nutsuwa, ya zaunar da ita, amma fafur taki zama wai dole sai sun zauna tare. ta rike masa hannu katamau! Shi kam taushin hannunta da dumin da yake shine yayi masifar sanyayyar masa da jiki, Babu zato babu tsammani ta janyoshi duk karfinsa, sai ya tsinci kansa a zaune a kusa da ita, yayi mamakin hakan mutuka A maimakon ta saki hannunsa, tunda yana