← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 97

Sashe 96

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da magana dashi. Jakada ya sheda mata cewa Sarkin yace sai daddare ta sameshi gurin hutawarsa. Ta zauna tasa takardar a gabanta ta dinga rusa kuka wiwi! ******** Aunty Zeey dai ta shiga ta fita ta rusa auran da Asp yake nema. Yana zaune a ofis yarinyar ta kira shi a waya take sheda masa cewa ta fasa auransa domin taji cikakken labari cewa shi din mijin tace ne a gidansa, saboda haka ba zata aureshi ba tayi zaman takaici. Asp ransa ya baci mutuka yaso ya fahimtar da ita amma fafur! taki sauraransa domin ta tsorata da yanda ta samu labarin abinda yake gudana a gidansa wannan dalilin yasa ta yanke shawarar rabuwa dashi domin ita babban burinta tayi aure a inda zata samu nutsuwa da kwanciyar hankali. Umar ne ya shiga ofis din ya sameshi ransa a bace nan yake tambayarsa, ya shiga sheda masa abinda ke faruwa. Yaja tsaki da fadin." To meye abin damuwa da daga hankali? tunda kaga Allah yayi haka to babu alkairi a tsakaninka da yarinyar, saboda haka kada ka wani damu ka kwantar da hankalinka a nutse sai ka duba wacce ta dace tunda gasu nan budurwa bazawara duk wacce kakeso, wallahi ni kaina auran nakeso na kara da wata bazawara yarinyar ta kwanta min a rai sosai ina nan ina binkice a kanta." Asp yaji sassauci sakamakon shawarwari daga abokinsa, nan ya manta da maganar suka shiga wata wacce ta shafi aikinsu. *BAYAN SHEKARA DAYA* Junior wato mai sunan Asp yayi wayo har ana shirin yi masa k'ani Zinat haihuwa ko yau ko gobe itama Hamra'un laulayi take, lokacin cikin wata biyu da sati biyu, duka suka zame masa hoto kowacce da yaje gurinta da matsalarsa zata lanjare ta fara wayyo-wayyo abinda ya tsana kenan a rayuwarsa, kawai sai ya kyalesu ya mayar da hankalinsa gurin neman auran da ya sanya a gaba domin Allah ya hallata masa yana kuma da iko to babu abinda zai sanya ya tauye rayuwarsa. Sai dai mutum yana tashi Allah na tasa, a zahirin gaskiya yaso ya auri bazawararsa amma sakamakon abinda Allah ya kaddarata yasa ya rufawa abokinsa asiri......Abinda ya faru shine. An gama shirye-shiryen komai na bikin Nabila an sanya ranar daurin aure daga kowanne bangare sun amince saura kwana uku d'aurin aure binkice ya tabbatar da cewa Sulaiman wato mijin da Nabilan zata aura dan 419 damfara ne. Turkashi d'an damfara a gidan commissioner 'yan sanda yazo neman auran 'yarsa ya akayi duk iyakar binkicen da yayi akansa bai hasashi hakan ba. Ya sanya rundunar 'yan sanda domin suyi masa tara-tara! inaa! Malam Sule tuni ya fece kasar ma gabadaya ya bari..........Wannan badakalar dake faruwa su kansu iyayensa basu sani ba, Ashe dama duk iyayen kudin da dan nasu yake samu na sata ne. Mahaifinsa har gida yaje gurin Asp din yana bashi hakuri harda hawayensa. dattijon ya bashi tausayi sosai ya rarrasheshi tare da sanya direba ya mayar dashi gida tare da tabbatar masa da cewa babu komai magana ta wuce a gurinsa. Washe gari gurin aiki abokin nasa, yaje masa da maganar da ta girgiza shi sai kawai ya zuba masa ido yana kallo ya gaza furta komai tsabar maganar ta doke shi... *Wai me yake shirin faruwa ne *Kada ki karanta min littafi idan baki biya, kada ki siya ki fita dashi, 'Yar uwa kada ki ganshi a group kiyi shearing domin hakkina ne, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne.....0542382124...Binta umar gtbank. idan kati zaki turo sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number* *07084653262* *BINTA UMAR ABBALE* 6/27/22, 13:36 - Buhainat: _Akwai ingantaccan maganin gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ _*Mafi akasari masu bibiyar littatafan BINTA mutane ne masu mutunci da karamci da kuma dogon tsinkaye! babu yanda za'ayi suci zarafi na ko su gaya min mara dadi koda kuwa kuskure nayi cikin hikima zasu tunasar dani domin na gyara, amma abin mamaki wasu cima zaune da ban san da zamansu ba, sune suke cin zarafi na bayan sun karanta littafina har suna kirana da wasu kalmomin da basu cancanta ba, NAGODE bahaushe yace anayi da kai gwara ba'ayi da kai matakin NASARA ne, da yawa masu tsinkaye sun fahimci inda na nufa a cikin wannan littafin nawa mai suna GOJE! Alhamdulillhi naji dadi masoya da kuka bani goyon baya har Allah yasa na kammala isar da sakon dana dauko. Kunyi da aljihunku kana kuma kunyi da muryoyinku, Littafin GOJE! yazo da sabon salo kowa ya sheda hakan, ina rokon Allah ya bani rai da lafiyar da zan cigaba da nishad'antar daku tare da wa'azantarwa. daga karshe nake baku hakuri sakamakon tsaikon da littafin ya dinga samu bayan ya dauko gangara! kuyi hakuri insha Allah hakan ba zata sake faruwa ba *GOJE* *(SADAUKI OMAR RETURN*) *END *ALHAMDULILLHI* *134* Ya kalleshi cikin jadadda aniyarsa yace." Da gaske nake magana ba wai da wasa ba inaso ka bani auran yarinyar nan domin hakan shine maslaha a gare mu bakidaya." Shuru yayi na minti biyu kafin ya cigaba da cewa.'' Kasancewar mun riga mun sanar da jama'a ranar daurin aure a yanzu abune mai wahala gami da jin nauyi mu sake sanarwa mutane cewa lamarin auran ya lalace duk da cewar ba daga bangaranmu aka samu matsala ba amma da kunya, wannan dalilin yasa naji sha'awar auran yarinyar a cikin raina nasan daga 'bangaran ka ba zan samu matsala ba sai dai daga ita yarinyar idan da hali ka sheda mata al'amarin idan ta amince Alhamdulillhi." Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace." Ban yi mamakin faruwar wannan al'amarin ba Umaru, nasan komai yana tafiya ne cikin kudirar ubangiji, wani baya auran matar wani haka zalika wani baya haihuwar dan wani, tabbas daga 'bangarena baka da matsala, zanfi kowa farin cikin kasancewar hakan, sai dai akwai gagarimar matsalar da nake hangowa mutukar al'amarin nan ya tabbata." Murmushi yayi a nutse yace." Ka kyautata zaton alkairi abokina wannan al'amari da zai faru insha Allah alkairi ne, matsalar dai bai wuce ace rashin amincewa daga 'bangaran iyalina ba, kada ka damu da wannan, a yanzu akwai kyakykyawar fahimta a tsakaninmu, insha Allah zan zaunar dasu na fahimtar dasu yanda al'amarin ya kasance, burina shine ita yarinyar ta amince shikkenan sai komai yazo cikin sauki." Yace." Hakane Allah ya tabbatar da alkairi maganar Nabila kuma zan zauna da ita a yau da ikon Allah komai zai zo da sauki za kuma mu tattauna da mahaifiyarta." Cikin farin ciki ya mika masa hannu sukayi musabaha da juna kafin yayi masa sallama ya kama hanyar fita. Asp din ya bishi da kallon mamaki! hakane kowane mutum da akwai ranarsa, dama fargabarsa jin kunyar jama'ar daya gayyata ace kamarshi commissioner 'yan sanda ya gaza gano wanda yazo gidansa da niyyar auran 'yarsa, wannan shine babban takaicinsa, amma cikin ikon Allah abokinsa ya rufa masa asiri a lokacin da yake cikin tararrabi, tabbas zuciyarsa tayi na'am da abokin nasa, baya fargabar bashi auran 'yarsa, domin shi yafi kowa sanin halinsa. Tana cikin k'unci da damuwa sakamakon yaudarar da Sulaiman yayi mata, sai gashi Ubangiji yayi mata tagomashi da samun nagartaccan namiji, koda mahaifin nata ya sheda mata niyyar abokinsa a kanta, babu jayayya ta amince, domin dama can tun fil-azal mutumin yana burgeta da kyawawan dabi'unsa, gashi d'an gayu kyakykyawa kuma jajurtaccan namiji, babu ruwanta da matansa, tunda shi ya bukaci auranta ta amince Allah ya sanya alkairi, to itama Madam tayi farin cikin faruwar hakan, domin dama tana cikin halin damuwa da takaici sai gashi Allah ya share musu hawaye ya maye musu gurbi da namijin da yake da wahalar samu a wannan zamanin, tayi addua sosai tare da fatan zaman lafiya madawwamiya. To da yake a gidan Zeey yake bayan sun gama tattauna maganar sai yayi musu sallama ya tafi, koda yaje can din ma kasa shuru yayi dole itama tana da hakki ta san abunda yake faruwa a matsayinta na matarsa, nan ya sheda mata duk abunda yake faruwa. Ko a jikinta dan bata nuna wata damuwa ba ko farin ciki ba, sai dai a can kasan zuciyarta taji dadin kasancewar hakan, yanzu ai dole ita Zinat din ta san wacece Madam da makircinta. Washe gari Asp din yana fita ta dauki waya domin kiran Zinat din. Lokacin suna tare da maigidan yana shirin fita gurin aiki. Ta daga wayar suka gaisa kamar gaske, can kuma sai Aunty Zeey din ta fashe da wata mahaukaciyar dariya kamar sabuwar kamu. Shi kansa Umar din dake can gefe a zaune sai da yaji taratsin dariyar. Tace." Aunty Zeey me yake faruwa ne nifa matsala ta dake kenan." Ta tsagaita dariyar da fadin." Murna na kira nayi miki" Tace." Wace irin murna kuma."? "Au zaki nake ni kenan." cikin zaurance tayi maganar. Tace." Bangane hausarki ba don Allah kiyi magana ta fahimta mu gama na sallami mijina zai fita gurin aiki." Cike da mamaki tace." Sannu da kokari gaskiya na jinjina bajintarki amma ina zargin munafikin mijin naki bai sheda miki cin amanar da suka kulla miki ba." Gabanta ya yanke fadi, da sauri ta kalli gefan da yake, yayi saurin dauke kansa yana sake tamke fuskarsa, cigaba yayi da daura blet dinshi. A sanyaye tace." Don Allah kiyi min bayani. Tace." Oh!oh! wa'ka a bakin mai ita tafi dadi nasan dai komai nisan jifa kasa zai fado amma dai ki zauna cikin shiri nan da kwana uku zakiji bud'a! "Ayyiriririri!!!!." kawai sai
Chapter 96 · 0% Book details