← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 97

Sashe 94

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ga b'acewar motar daga layin gidan nasa sannan yayi addua a zuciyarsa ya kama hanyar massalaci kamar yanda ya dauki niyya. Sai da ya hau titi sosai sannan ya lalubi wayarsa dan ya gaza hakuri yana tokin motar ya kira wayarta. Ta daga da sallama , a bakinta. Muryarsa ya raunata da fadin." Kina so zuciyata ta bindiga ko."? Tai masa shuru ba tace komai ba. "Kin mayar dani shakatafi kina min yawo da hankali so kike na kwana a kan kwalta ina galantoyin neman in da kike." Zumbura baki tai da fadin." Na maka fa ina gidan Aunty Hassanata'' Ya fesar da wani zazzafar huci! cikin kunar zuciya yace." Daga can nake kuma Alhaji Sa'idu ya tabbatar min da cewa bakya nan okey tunda kina so na shiga tsakiyar motoci su bugeni shikkenan bukatarki sai ta biya." Da sauri ya kara karfin motar ya figeta da mugun gudu! yana sane yayi hakan. Aikuwa hankalinta ya tashi jin k'ugin motoci da iska a kunnanta. Kashe wayarsa yayi ya Ajiye ya saisaita tafiyar da motar. Gaza hakuri tayi ta fito daga daki hankalinta duk a tashe take shedawa Asp abinda yake shirin faruwa. Yace." Rabu dashi duk barazana ce kada ki kuskura ki sheda masa kina gidana." Maganar sam bata gamsheta ba, gabadaya ma hankalinta ya karkata kansa. Ta dauki waya ta kira shi sai da ta kusa katsewa ya daga, bai saurari maganarta ba yace." Sha biyu dai-dai na dare za'a kawo muku gawata." Gabanta yana faduwa tace." Wace irin magana ce wannan ka daina don Allah." Yace." Allah idan baki fada min inda kike ba to ba zan dawo gidan da lafiya ba, gani ma zaune a mota cikin wani daji." A sanyaye tace." Amma dai kasan abinda kayi baka kyauta ba ko." "Na sani kuma na baki hakuri ai kowane dan adam yana laifi mai zai sanya ba zaki yafe min ba." Sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke a hankali tace." Na yafe maka amma don Allah kada ka kara zargina da wani abu bana jin dadin hakan Hamra'u da 'ya'yanta bani da nufin cutar dasu. Ya sake jin wani sabon so da kaunarta na ruruwa a zuciyarsa......."Zinatu baki da matsala dani na amince dake dari bisa dari na kuma tabbatar da cewa ke alkairi ce a tare dani abinda ya faru tsakaninmu sharrin shadain ne amma da izinin Allah hakan ba zai sake faruwa ba. Ta sauke ajiyar zuciya da fadin." Ameen ya Allah yanzu kana ina."? Ya gyara zamansa kan kujerar motar da fadin." Ina hanya insha Allah nan da lokaci kankani zan iso ina fatan nazo na sameki a gidana." Tace." Insha Allahu dama banyi nisa ba, ina gidan abokinka." Cike da mamaki yace." Wa kenan."? Jim tayi kafin tace." Wa kake dashi bayan Asp ina gidanshi." Murmushin takaici yayi yace." Dama sai da na zargi hakan a zuciya wato hada baki kukayi domin ku wahalshe ni ko ."? Murmushi tayi ba ta iya cewa komai ba. Yace." Zan kashe waya amma ki tabbatar da cewa na sameki a gida." Tace." Kada ka damu kai dai kayi draving a nutse." Yace." Insha Allah." Kashe wayar tayi tare da tunanin yanda za'ayi ta iya fita daga gidan, tana jin kunyar Asp sosai amma dole tabi umarnin mijinta tunda ya gane kuransa yanzu ta tabbatar da cewar tana da muhimmanci a rayuwarsa. Allah ya taimaka Asp din a gidan Zeey yake, taji dadin hakan sosai, amma kuma boy yaronta yana gurin Nabila dan tunda suka zo gidan take dawainiya dashi nono ne kawai yake kawoshi gurinta. Wata shawara ta yanke a zuciyarta, hijab dinta tasa ta fito falon babu kowa duk suna daki da sauri ta kama hanyar fita shawarar data yanke kenan daga baya an kawo mata yaron. Kai tsaye Side dinsu ta nufa, da yake bracck din akwai haske bata samu matsala ba, sai dai haushin karnuka da suka cika mata kunne.........Kai tsaye sashenta ta nufa zuciyarta cike da tunane-tunane masu kyau da marasa kyau. *Kada ki karanta min littafi idan baki biya, kada ki siya ki fita dashi, 'Yar uwa kada ki ganshi a group kiyi shearing domin hakkina ne, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne.....0542382124...Binta umar gtbank. idan kati zaki turo sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number* *07084653262* *BINTA UMAR ABBALE* 5/16/22, 21:20 - Binta: _Akwai ingantaccan maganin gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ *132* Asp yasha mamaki lokacin da Madam ke sheda masa cewa Zinat bata gidan, koda ya kira wayarta domin ta bashi tabbacin inda take, sai ta hau inda-inda, da yake mutumin yana kusa da ita shi ya k'arbi wayar yayi gyaran murya Asp yaji muryarsa ta doki kunnunsa, shuru yayi yana mamakin al'amarin. Yace." Gata nan a kusa dani wahala ta ta k'are ai na fad'a maka dama ba'a shiga tsakanin masoya." Maganar ta bashi dariya yayi kadan kafin yace." Dama ni na isa na shiga tsakaninku? kawai dai nayi hakan ne domin na nuna maka kuskuranka amma banyi da wata manufa." Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." To daka kai har ita abinda ku kayi min sai Allah ya saka min." Cike da mamaki yace." Yanzu dai Kana so mu nemi gafararka kenan? Yace." Kwarai kuwa shine samun nutsuwarku domin Allah ne kadai yasa da sauran kwana na a gaba da tuni sai dai labari na." Asp ya fashe da dariya da fadin." Ai na kara tabbatar da cewar duk wata burga da kake da fuffuka k'arya ce wannan yarinya itace rayuwarka gabadaya kwana biyu kacal duk ka susuce kamar ba jarumin namiji ba." Ya shafa gemunsa yana mata wani sihirtaccan kallo hannunta ya sake rintsiwa a cikin nasa yace." Asp sanin abinda ke zuciyar mutum sai Allah sai kuma shi wanda zuciyar take jikinsa amma kana hasaso gaskiyar abinda ke cikin zuciyata wannan shine gaskiyar magana.'' Ajiyar zuciya ya sauke da fadin." Alhamdulillhi abokina nayi farin cikin hakan, kuma ina rokon Allah yasa wannan abunda ya faru a tsakaninku ya zama karshen matsalarku, Allah ya kore fitina a tsakaninku." Cikin farin ciki da jin dadi ya amsa da "Ameen suma ameen mutumin kirki na gode kwarai da kokarinka a kaina da kuma iyalina, ina rokon Allah ya bani ikon kyautata maka." Ya amsa da ameen ya rabbi kafin suyi sallama cikin karamci da mutunta juna. ***** To alhamdulillhi bayan faruwar wannan matsala wani abu mara kyau ko tashin hankali bai sake faruwa ba a tsakaninsu, duk wasu tunane-tunane da yake marasa kyau a da ya ajiye ya daina, yana kokarin kyautatawa iyalinsa shi kansa sai yanzu ya gane cewa zaman lafiyar da suke shine kwanciyar hankalinsa. **** Kowa ya san dai abinda commissioner ya aikata ya sa'bawa dokar 'kasa wannan dalilin yasa bayan ya warware aka gurfanan dashi a gaban mai sharia, ba tare da jayayya ba ya amsa laifinsa, wannan dalilin yasa mai sharia ya sasauta masa, amma tabbas hukuncin kisa ne a sauka a kanshi, saukakawa sharia da yayi baiyi jayayya ba yasa mai sharia ya yanke hukuncin cewa a kai shi can gidan kaso (prison) na tsayin shekaru biyar kafin a kashe shi. To ya za'ayi, bahaushe yace." Son zuciya 'bacin ta, zuciya mugun nama idan kabi ra'ayinta ta kai ka ta baro, Allah kasa mufi karfin zuciyoyinmu. A ranar da aka tasa 'keyar Commissioner of Police gidan kaso (prison) a ranar aka mayar da Asp kujerarsa wato shugaban 'yan sanda abokinsa Umaru GOJE ya maye tashi kujerar mai taken kakakin rundunar 'yan sandar jahar KATSINA. haka abokan suka wanzu cikin hidimtawa al'umma da kare 'kasa tare da abinda ke cikinta. **** "Aunty Maijidda miliyan biyar nakeso ki bani aro." Kai tsaye ya fadi maganar idonsa 'kuri a kanta. Ta kalleshi ta sake kallo takaicinsa duk ya cika mata zuciya tace." Sadiq ashe baka hankali don ubanka me za kayi da miliyan biyar."? Ya 'bata rai da fadin ." Kinga aunty Maijidda babu ruwanki da abinda zanyi da ita kawai ki bani bana bukatar surutu." Tace." Bani dashi ka tashi kuma ka fice min daga gida mara mutumci'' Cikin fusata ya buga hannun kujera ya mike tsaye yana huci! da numfarfashi yace." Ni kike kira mara hankali "? Tace." Eh kai ne mara hankali Sadiq ko zaka dake ni ne."? Ya zabura! kamar zai kai mata mari! tayi saurin gocewa gabanta na faduwa take kallonsa. Ya cize baki yana hura hanci da fadin " Zaki gane baki da wayo sai na tona miki asiri." A gaggauce ya kama hanyar fita. Da karfi ta kira sunansa "Sadiq." ko juyowa bai yi ba ya bude kofa ya fita kai tsaye fadar sarki ya nufa da yake safiya ce fadar sarkin cike take da jama'a 'yan uwa da abokanan arziki da kuma masu zuwa sulhu da sasanci. Cikin rashin kintsi ya shiga fadar, gabadaya ido yayi caa! a kansa. Guri ya samu ya zauna ya tsirawa sarkin ido tamkar wanda yake binsa bashi. Sarkin jikinsa yayi sanyi haka kawai yake tausayawa yaron, rayuwarsa ta gurbata gurin shaye-shaye da rashin kintsi da kamun kai. wannan dalilin yasa duk abinda yaron ya bukata daga gurinsa yake tallafa masa. Gyaran murya yayi a nutse ya kira sunansa. Ya amsa yana me sunkuyar da kansa kasa Yace." Kana bukatar wani abu daga gurina. Yayi shuru yana dawurwura! har yanzu idon jama'ar dake gurin na kansa. Sarkin ya kalli shamaki dake kusa dashi yace.'' Wannan yaron ga dukkan alamu akwai abinda ke tafe dashi a
Chapter 94 · 0% Book details