← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 97

Sashe 95

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kawo min shi kusa dani domin naji daga gareshi.'' Shamaki ya kamo hannunsa ya tsuganar dashi gaban Sarkin kafin yace." Yaro kada kaji tsoro ka fadi abinda ke tafe da kai, ni ina magana ne da yawun sarkin dake gabanka a halin yanzu. Sadiq wani irin gumi ya fara yanko masa. Wai shin ma ya akayi ya kawo kanshi gurin nan? Idan ya tonawa 'yar uwarsa asiri ai tare suka had'u suka shirya sharrin tilas shima ya fuskanci hukunci . Cikinsa ya duri ruwa ya dinga wani irin k'ugi kai Allah ya tsinewa (kamru uwar laifi) sai yanzu ta sake shi ya gane wautar da yake kokarin tafkawa. Alamun rashin gaskiya ya bayyana a tare dashi sai gumi yake sharcewa ya kasa cewa uffan sai magana ake masa. Sarki a jikinsa yake ji akwai matsala dan rashin gaskiyar dake tare da yaron yafi komai daga masa hankali, addua yake akan Allah yasa ba zuwa yayi ya kashe rai ba. Ba zato ba tsammani! Sadiq yaji saukar tsabga a bayansa. Ya gantsare tare da kurma uban ihu! idonsa akan dogarin dake tsaye a kansa da murtukekiyar bulala a hannunsa sai zare masa ido yake. Cikin hargagi! yace." Hattara 'yan samari nan ba gurin harigido bane ba gurin gardama da jayayya bane yi kokari ka fadi abinda ya kawo ka Sarki yana sauraranka." Bulalar ya daga da niyyar sake zabga masa Sarkin ya dakatar dashi. Ya sauke hannunsa da fadin." Gyara kintsi! Allah ya 'karawa sarki lafiya." Fadar tayi shuru na 'yan mintina, kafin a nutse Sarki ya kalleshi da fadin." Abubakar Sadiq ni abinda nake hasashe shine kaje ka dauko magana a cikin gari kazo ka gurfana a gabana domin na zame maka garkuwa to ka sani cewa ni UMARU ba zan lamunci zalinci ba duk irin hukuncin da ya cancanta da abunda ka aikata shi za'a yanke maka." Ai kawai sai ya fashe da kuka! ya rike kafafunsa da fadin." Ranka ya dade ka gafarce ni wallahi ba laifi na bane duk abunda ya faru Aunty Maijidda ce ta bamu umarni." Jin ya ambaci sunan amaryarsa yasa ya tsira masa ido da mamaki a tare dashi. Daga farko har karshe ya warware yanda akayi suka shirya sharrin amma beyi tasiri ba, tunda wacce sukayi niyyar sabautawa rayuwa addua iyaye na tasiri a kanta, tana dakin mijinta a halin yanzu har da zuria a tsakani. *Kada ki karanta min littafi idan baki biya, kada ki siya ki fita dashi, 'Yar uwa kada ki ganshi a group kiyi shearing domin hakkina ne, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne.....0542382124...Binta umar gtbank. idan kati zaki turo sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number* *07084653262* *BINTA UMAR ABBALE* 6/27/22, 13:36 - Buhainat: _Akwai ingantaccan maganin gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ *133* Shuru fadar ta d'auka bayan k'are jawabin da ya hargitsa tunanin duk wanda yake zaune a gurin. Bahaushe yayi gaskiya da yake fadin da d'an gari akan ci gari, ashe dama da sanya hannun Maijidda gurin faruwar al'amarin da ya tashi hankalin masarauta da duk wanda ke cikinta, tunaninsa bai taba kawo masa cewa Maijidda za taci amanarsa ba, ashe duk abunda take akan iyalinsa na ganin idone dama Aysha ta jima tana jadadda masa cewa ba mutuniyar arziki bace amma baya yarda da maganarta, cikin ikon Allah sai gashi yau ya tabbatar da maganarta. Ya kalli Sadiq dake gurfane a gabansa yana zabga wani irin gumi! ya zubar da hawayen har ya gaji fargaba da tashin hankali duk sun dabaibaiye shi. Ga mamakin duk wanda ke zaune a gurin sai kawai sukaji yace ." Ka tashi kaje Allah ya shiryeka tare da masu irin halinka." Galadima ya kalleshi da fadin." Allah ya baka nasara iyakar hukuncin kenan."? Murmushin takaici yayi kafin yace." Galadima wannan shine hukuncin da nake ganin zan iya dauka akan zuriar Malam Buba, sun ci albarkacinsa abinda suka niyyata ya faru Allah ya takaita, ita yarinyar yanzu haka tana dakinta zaune kalau wannan shine babbar nasarar da muka samu." Gabadaya fadar ta cika da kabbara "Allahu akbar"! an gaishe da adalin sarkin mai aiki da ilimi da sanin ya kamata, adalin sarki ne wanda za kayi masa laifi shi ya saka maka da alkairi UMARUL-FARUK kenan, haka duk masu irin sunan suke akwai tausayi da kyauta kulawa da sadaukarwa hakuri juriya cikin ko wane hali. Gabjejan dogarin dake tsaye a bakin kofa ya bugawa Sadiq din tsawa tare da nuna masa hanyar fita." Ganin yanda jikin dogarin ke rawa yasa ya tsorata da sauri ya mike takalmi a hannu ya kama hanyar fita daga masarautar yana godewa Allah da ya takaita masa wahala. Ya jima yana tunanin ta yanda zai tunkari Gimbiyar tashi da maganar saboda sanin halinta amma ya zama dole ya sanar da ita domin tana da hakki akan hakan. Ya gama yi mata bayanin komai tana sauraransa amma ba taji irin hukuncin da ya yankewa Maijidan ba. Tace." Yanzu ita Maijiddar wane hukunci ka yanke a kanta kasan dai wannan abunda ta aikata dole a dauki mataki saboda gaba." Shuru yayi yana nazari. Tace." Nasan dama wannan matar ai ta gama da kai babu wani mataki da zaka dauka a kanta, shikkenan ni zan dauki mataki idan kai ba zaka dauka ba." Ya kalleta da fadin." Wane irin mataki zaki dauka wannan maganar fa na fada miki ne saboda a fita hakkinki amma daukar mataki ba'a hannunki yake ba. Ta fusata! da fadin." Idan ban dauki mataki akan Maijidda ba kace ni ba 'yar halak bace."! Ya zuba mata ido yana kallo da bacin ran maganarta a tare dashi. Safah ta shigo ta same su suna kallon juna sai kace zakaru! kowanne ransa a 'bace! Guri ta nema ta zauna a nutse tace." Allah ya kori shaidan din da yake kokarin ratsa tsakaninku. Ta kalleta da bacin rai a tattare da ita ta shiga sheda mata abunda ke faruwa. Itama rai a bace tace." 'Yar uwa bake kadai zaki dauki mataki ba nima zan dauki mataki akan Maijidda domin wannan abunda ta aikata bai kamata a zuba mata ido ba." Ganin sun hada kai yasa ya sassauta yana so su saurareshi. Fafur! suka ki sauraransa ko wacce na kawo masa hujjojinta. Yace." To yanzu ya kuke so nayi? Aysha ke kin san irin taimakon da Malam Buba mahaifinta yayi min ya kuma yi miki a lokacin da yake raye to mai zai sanya bayan ransa na wukalanta bayansa Tace." Malam Buba daban Maijidda daban ai ganin hakan yasa take duk abinda takeso to wannan karon ba zata kai labari ba. Safah tace." Nifa zama da ita na gama ranka ya dade Safara'u ko Maijidda wannan shine hukuncin dana yankewa kaina. Yace." Abinda kuka shirya kenan."? Itama Ayshan tace." Kwarai kuwa ko ka saki Maijidda ko kuma mu tattara mu barka da ita.'' Yanda suke jadadda maganar yasa jikinsa duk yayi sanyi, shi yanzu ina zai iya rayuwa idan babu su. Itama Maijiddan ya mahaifinta ne ya bashi kyauta kafin ya rasu shiyasa yake mutunta ta amma tilas yayi wani abu akan al'amarin. Yace." Idan na saki Maijidda bawai daku biyu kawai zan dawwama ba ina da damar karo biyu akai saboda haka kuyi hakuri ku cigaba da cud'awa da ita, kuna mata adduar shiriya." Safah tafi d'aukar zafi duk hakurinta a ranar rufe ido tayi ta dinga zazzaga masa bala'i kamar wani sa'anta! Dashi da Ayshan mamakinta kawai suke. "Ranka ya dade baka da hujja! domin duk wanda yaji wannan al'amarin ya san kaine baka da gaskiya! Maijidda tayi garkuwa da 'yar cikinka domin cikar burinta Allah ya kare, to ina mai tabbatar maka da cewa watarana dani ko 'yar uwata za tayi garkuwa tunda zuciyarta babu alkairi saboda haka ni kam ba zan zauna ba, tunda ka zabi zama da Maijidda Allah yasa haka shi yafi alkairi." Hanyar fita ta nufa fuskarta babu annuri ko kadan. Sunanta ya kira tare da bata dawowa ta zauna. Taje ta zauna tana dauke kai. Ya jima yana mamakinta, tunda suke bata ta'ba yi masa figala irin wannan ba, Safah tafi masa Maijidda sau miliyan. Yace." Shikkenan tunda dai kun hade kanku bakwa kaunar Maijidda a gidan nan zan duba maganarku da safe kowa zai ji matsayinsa. Safah ta bude baki za tayi magana, Aysha ta dakatar da ita. "Ki bari tunda yace sai da safe kowa zai ji matsayinsa shikkenan kada ki sake cewa komai." Aikuwa sai taja bakinta tayi shuru. Al'amarin da yayi masifar bashi mamaki! har yanzu ya gaza gane cewa Aysha ce ke auran Safah ko kuma shi, tsayin shekaru masu yawa haka al'amarin yake tafiya a tsakaninsu. Ya kallesu babu walwala a tare dashi yace." Ku tashi ku bani guri." Suka tashi a tare suka kama hanyar fita babu nadama a tare dasu. Kallo ya bisu dashi yana mamakin yanda suke gudanar da al'amarinsu, yana ganin ko ya rabu da Maijidda ya kawo wata cikinsu wahala zasu bata gwara ya hakura ya zauna dasu da halinsu. Wannan shine karshen turka-turkar! Saki daya kacal ya rubutawa Maijidda ba tare da cikkenan bayani ba. Ayshan ce ta karbi takardar da kanta ta shiga har sashen Maijiddan ta bata takardar tare da gogar zana dan bata fayyace mata komai ba. Maijidda dai ta duba abinda ke takardar cikinta ne ya rud'e sai da ta shiga bandaki ta fito hankali a masifar tashe ta tura jakada can fadar sarkin cewa tana
Chapter 95 · 0% Book details