Sashe 51
Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
abokina bari na kira Madam a waya yanzu na sheda mata." Yace." Godiya nake mutumin kirki Allah ya saka da alkairi." Yana 'yar dariya yace." Umaru bana san yawan godiyar da kake min ai tuntuni na fada maka cewa ni da kai mun zama daya saboda haka don Allah ka daina yawan yi min godiya idan wani abu ya ratsa a tsakaninmu." Murmushi kawai yayi yana girgiza kai tare da mamakin mutunci da dattakon mutumin tabbas irinsu na da wahalar samu a duniyar nan. Sashen ta ya nufa a karo na biyu, ya sameta tana waya da Aunty Zeey sai kyalkyala dariya take, aunty zeey din take bata labarin wani maganin mata da tayi amfani dashi wai Asp din kuka ya dinga yi wurjajan! harda majina!! shine fa abun ya bata dariya tace." Nima ina so akawo min irins.........Shigowarsa ta katse maganarta, ta gyara fuskarta da fadin." 'Kawata zan kira ki idan an jima." Tayi saurin kashe wayar domin bata so ya fahimci abinda suke tattaunawa. Ido suka had'a tayi kasa da kanta tare da dan zumb'ura baki. Yace." Ke da waye kuke waya haka."? Cikin shan 'kamshi tace." 'Kawata ce." Yace." Amma dai tana da matsayi babba duba da irin walwalar da ki keyi." Shuru tai masa ba tace komai ba. Yace." Munyi waya da Asp insha Allah za'a kawo miki abunda ki ke bukata daga gidanshi." Ci kanka ba tace ba, yay jim yana kallonta koda za tayi magana. Ganin tsayuwarsa a dakin tana nema ta haifar mata da matsala yasa ta kalleshi da fadin." To kayi tafiyarka mana." Juyawa yayi da nufin fita ta tsirawa bayansa ido! yanayin kayan dake sanye a jikinsa sun ja hankalinta sosai har ta dinga jin bakon abu na ziryar tar gangar jikinta.......Zazzafar ajiyar zuciya ta sauke bayan fitarsa ta kwanta saman kujera da waya a hannunta. Boyayyan masoyinta ta lalubo text tai masa zuciyarta sai harbawa take ita a kankin kanta tasan abunda take ba daidai bane amma ya za tayi, a halin da ake ciki a yanzu tana bukatar kulawa da rarrashi da kuma soyayya. Koda ya duba text din murmushi kawai yayi.....Gaisuwa ce kawai da fatan alkairi ba wani abu da tayi wanda ya wuce gona da iri. Whas'App a shiga ya tura masa sabbin sticks masu hargitsa lissafi mussaman yasa Adewale ya turo masa saboda plan dinshi a kanta. Bayan ya tura mata sticks din sai ya rubuta magana kamar haka........... _"Wai shin yaushe ki ka shirya had'uwar mu ne, my love ina cikin tsananin bukatarki na san dai kema kina da wannan bukatar ki shirya had'uwarmu a shirye nake dana gamsar dake zan gwada miki soyayyar da baki ta'ba tsammani ba."_ Tashin hankali kenan, ai ganin zafafan sticks din ya jefa ta cikin mawuyacin hali, gabadaya jikinta ya dinya kyarma tsigar jikinta duk ta tashi wani irin sha'awar namiji take, tana duba sticks din tana lumshe ido 'kasan ta sai wani irin abu yake, pant dinta kam ya riga ya gama ji'kewa. Lamo tayi kan kujera mararta na wani irin ciwo mara misali still ruwan kasan ta dake fita har yanzu be daina ba. Idonta ya ciko da ruwan hawaye, wai shin ya za tayi da wannan masifar ne? anya kuwa FARUK mutumin arziki ne? idan ba haka ba mai zai sanya ya dinga turo mata hotonan iskanci yana tayar mata da hankali, kwanakin baya ta gargade shi amma ya be bari ba, tana ganin dole tai wa tufkar hanci tun kafin ya jefeta a wani hali. Koda Nabila ta shiga ta sameta cikin wani irin yanayi sai hankalinta ya tashi, ta ajiye kayan abincin a gefe, ta karasa har inda take kwance tana kiran sunanta. Ta kalleta da jan ido kafin tace." Yaushe ki ka shigo."? Kusa da ita ta zauna cikin kulawa tace." Tun dazu nake sallama a falo shuru sai can mai aikin ki ta fito daga kicin take sheda min kina cikin daki to na shigo ina ta sallama baki amsa ba anya kuwa aunty Zinatu ko baki da lafiya ne."? Zaune tayi yunkurin tashi tana dan cije baki tace "Bana jin dadi wallahi mara na ke ciwo." Tace." Ayya ko lokaci ne yayi."? Girgiza kanta kawai tai ba ta iya magana ba. Tace." Ko asibiti za muje idan kinci abincin bari na kira Uncle a waya." Tana nufin Umaru domin da Uncle take kiransa kuma ita duk a tunaninta yana gurin aiki. Da sauri tace." Aa kada ki kira shi rabu dashi kawai zan sha magani." Jiki a sanyaye ta sauke wayar daga kunnanta, wanda a lokacin ma kiran har ya shiga basu sani ba. Ganin wayar ta katse ne yasa yabi layin domun sanin wanda ke kiransa. Ta duba wayar da fadin." Kinga ya ma kira." Tsaki! taja da fadin." Baki ji abinda nace ba kenan? cewa nayi fa ki kyaleshi shin waye ma ya baki number shi."? Da yake tuntuni ta san halinta sai tayi murmushi tare da kokarin mayar da al'amarin 'karami tace." Na fara kiran shi na katse saboda abunda ki kace ashe ta shiga ina ganin shine dalilin da yasa ya kira domin yaji waye." Shuru tai tana wani ya mutse fuska. Ya sake kira a karo na biyu domin wancan da yayi ya katse bata daga ba. Jin muryar mace a kunnansa yasa shi mamaki. Yace." Wacece ne."? Tace." Uncle Fadila ce ina kwana."? Ita kad'ai ce take kiransa da wannan sunan, shiyasa lokaci guda ya gane ta, ya saki fuska da fadin." Daughter ya kike ina Madam ina fata kuna lafiya."? Tace."Duk muna lafiya lau Uncle, Nazo kawowa aunty Zinatu abinci ne." Cike da jin dadi yace." Nagode sosai daughter bari na shigo mu gaisa." Tace." To Uncle sai ka shigo." Kashe wayar yayi itama ta kashe tata wayar babu wani abu a zuciyarta tace." Aunty ko na zuba miki abincin ne."? Kallonta tayi ta watsar taja tsaki ta mike tare da kama hanyar toilet tana wasu tunane-tunane a ranta. Murmushi tayi tare da bin bayanta da kallo, ita kam ta rasa! wane irin hali ne da ita, duk yanda za kayi don ka kyautata mata sai ta gwasale! bata ta'ba mu'amula da mutum mai irin halinta ba. Jikinta ta gyara, ta cire pant (wando) ta sauya wani ta fito cike da rashin kuzari a tattare da ita. Koda ya shigo dakin kallo daya yayi mata ya sheda cewa akwai wani abu dake damunta......Koda yake ya san dole abunda zai faru kenan, shi kansa kallon sticks din ya jefe shi a cikin wani yanayi don dai kawai yana iya sarrafa kansa ne. Ta dauke kanta daga garesu bakin gado ta zauna tana jinsu suna sake gaisawa sai godiya yake mata. Tace." Uncle babu komai ai an zama daya ka daina godiya." Murmushi yayi ya dan kalli gefen da take zaune kamar hankalinta ba'a kansu yake ba, amma kuma duk maganganunsu ta naji tana kuma aunasu akan sikeli, har yanzu ba suyi abunda ya wuce gona da iri ba, sai dai tana mamakin yanda akayi yarinyar take da number wayarsa, koda yake hakan ba abun mamaki bane idan akayi duba da irin sha'kuwar dake tsakaninsa da mahaifinta watakila a gurinsa ta samu number. Ta mike tsaye tare da gyara zaman hijab din dake wuyanta, tace." Uncle ni zan tafi gida, Aunty Zinatu Allah ya kara sauk'i." bakinta ne ya sub'ce da fadin hakan shaf ta manta maganarsu. Uffan ba tace ba ballantana tayi mata godiyar hidimar da akayi mata, tana dai jin sa yana mata godiya tare da bada sakon gaisuwarsa ga Mahaifiyarta . Bayan fitar Fadilan ya k'arasa kusa da ita da fadin." Kin ci abincin ko."? Girgiza kai tayi alamun A'a." Yace." Saboda me ki dubi time fa ace har yanzu baki karya ba me yasa kike san zama da yunwa."? Lumshe ido tayi tare da jin tsunkuli a mararta ta dan ya mutse fuska da fadin." Ba na jin zan iya cin wani abu yanzu." Yayi jim yana kallonta kafin yace." Me yake damunki domin alamu ya nuna baki jin dadi." Kallonsa tayi da lumsassun idanuwanta da suke buge da muguwar sha'awa. Magana take so tayi amma rashin abunda za tace yasa ta mayar da kanta kasa kawai taja bakinta tayi shuru. Murmushi yayi a cikin zuciyarsa yake ayyana wani abu, wato yanzu ya gama gane lagonta abinda yake saurin ladabtar da ita kenan, bata da juria ko kadan, a cikin kwayoyin idanuwanta kadai zaka fahimci hakan. Ya zauna kusa da ita sosai kafadarsu ta had'u ba tayi yun'kurin matsawa ba, sai ma wani irin ajiyar zuciya data sauke, burinta kawai taji ta a kwance a faffadan kirjinsa dake mutukar gigita ta. Ya dan kwantar da murya irin yanda ya saba rarrashinta......"Ki daure ki ci ni zanyi miki maganin matsalarki." Yanda yake maganar a tausashe yana mata wani irin kallo yasa gabadaya gabobin jikinta suka saki, ta sake shiga wani yanayin, a dan raunane ta kalleshi kafin tace." Ni na fada mata ina da matsala."? Ya dan kashe idonsa still yana kallonta yace." A cikin kwayar idonki na gani." Ido ta tsira masa dan so ta tabbatar da maganarsa, a ganinta tayi kokarin ganin ta boye abunda yake damunta ashe hakan bata samu ba. Ganin ta kasa magana yasa da kanshi ya janyo kwandon abincin ya fito dasu ya dauko plate ya zuba mata funkason uku ya zuba miya a kai, da ido kadai ka kalli funkason da miyarsa sai kayi sha'awa tun kafin kasa a bakinka, kamshin miyar ya cika dakin. Ya d'ora plate din a cinyarsa kafin yasa hannu ya gutsira tare miyar kai tsaye bakinta ya nufa da fadin." Bude bakin." Wai! abun nema ya samu sai ta wani susuce! ta dinga yi masa wani irin kallo tana mamakinsa, ashe dai yana da wayewar kai har haka, ada kallon bagidaje take masa amma yanzu ganin abunda yake irin na goggun 'yan duniya yasa ta 'karyata zarginta. Da 'kyar ta iya bude bakinta yasa mata funkason da ya jike da miya nan da nan ta cinye yasa mata wani, haka suka dinga yi har sai da ya tabbatar ta k'oshi sannan ya bude mata lemo tare da kokarin sanya mata a baki, girgiza kanta tayi ta nuna masa ruwa.........Ruwan ya dauko ya tsiyaya mata a cup ta kar'ba tana sha tana