← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 97

Sashe 38

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tsoron ka shiga hannunsa ba za kaji dadi ba._ Murmushi yay lokacin da ya karanta sa'kon ya gyara kwaciyarsa kafin ya bata amsa kamar haka. _"Na san da haka my love bana tsoron had'uwa dashi ballanatana naji tsoron gwabzawa dashi ina mai tabbatar miki da cewa a kanki babu abunda ba zanyi ba, zan iya fansar da raina akan soyayyarki ina so ki cire tsoro a cikin zuciyarki, ki cigaba da kokarin ganin kin rabu dashi kizo gare ni muyi aure, ni nayi alkawarin baki dukkanin kulawar da kike bukata."_ _Cikin jin dadin maganarsa tace."Nagode sosai wannan manganun naka sun kashe min jiki wallahi na rasa abinda zance maka nagode sosai da kulawarka kuma nayi maka alkawari cewa zanyi kokarin ganin mun hadu da juna, kada ka damu bukatarmu ta zata biya da izinin Allah."_ _Yace." Nagode my love yanzu me kike bukata nayi miki wanda zai faranta ranki."?_ Shuru tayi bata iya ce masa komai ba, gabadaya ya gama kashe mata jiki da salon soyayyarsa. Ganin tayi shuru ba tace masa komai ba kuma yana ganinta a online bata sauka kawai ba tare damuwar komai ba ya tura mata sticks masu tayar da hankali gami da tayar da sha'awa mussaman yasa Adewale ya tura masa su, a cewarsa shima zai turawa matarsa domin taga irin style din da yake so tayi dinga yi masa idan ya dawo gari. Adewale abun nema ya samu a take ya tura masa kala-kala wanda har sai ya rintse ido gurin kallon wasu daga ciki, don dai ma yana da kok'arin danne sha'awarsa amma da anyi katari da mara hakuri ganin sticks din zai sanya shi aikata aiki mara kyau. Yana tura mata ya sauka daga layin ya dauki daya wayar tasa kai tsaye what'sApp din ya shiga tana online har yanzu. Sai kawai yay mata magana. _"Me kike a online? karfe goma sha biyu da rabi."_ Ganin shigowar sakonshi yasa gabanta mugun faduwa!. Koda ta duba sai ta kasa magana, baki da jikinta gabadaya sun mutu in banda faduwa babu abunda gabanta keyi a dabarbace ta kashe wayar ta kwanta lamo kan gado ganin sticks din ya sanya ruwan ni'imar da ya saba zuba a jikinta yin 'karfi, gabadaya pant din ya jike ta dinga takure jikinta guri guda yanayin yana sake shiga jikinta sakamakon tashi da tsigar jikinta keyi nipples dinta basu ta bayi mata 'kai'kaiyi irin na ranar ba. Haka ta kasance cikin mawuyacin hali har asubah bata rintsa ba sakamakon ciwo da cikinta ke mata. Da 'kyar tayi sallah ta koma ta kwanta lamo kan daddumar ..........dole taja masa kunne kan cewa kada ya sake turo mata da hotonan iskanci. Misalin bakawai da rabi na safe, Baraka wato daya daga cikin hadimanta tayi knocking din kofar dakin. Ta mike zaune da kyar da fadin." Waye."? Cikin girmamawa tace." Baraka ce ranki shi dade." Sai da ta dauki kusan minti biyar sannan ta tashi taje ta bude mata kofar. Tana shigowa ta zube gwiwa biyu tana gaisheta. Da kyar ta amsa ta nemi saman sofa ta zauna yanayinta kadai shi zai nuna maka cewa akawai abinda ke damunta. Ta kalleta da kulawa tace."Ranki ya dade ko bakya jin dadi ne? domin naga alamun haka." Girgixa mata kai tayi da fadin."Lafiya ta lau ina Marakissiya."? tana nufin 'yar uwarta da suka zo tare. Da sauri tace."Tana kicin domin had'a miki abin kari." Tace."Okey ki hada min ruwan wanka, sannan ki shirya min kayana cikin wardrobe ki ajiye komai a muhallinsa." Cike da bin umarni ta amsa da "an gama Gimbiya." Mikewa tayi da sauri ta kama hanyar toilet din sai ta dakatar da ita da fadin." Ruwan da d'umi sosai zaki had'a min kinji ko." Ta amsa da "To ranki ya dade." Toilet din ta nufa cikin bin umarni. Bayan ta hada ruwan ta fito sheda mata sannan ta fara sauke akwatinan kayan domin gabatar da aikinta na gaba. Ta dauki kusan minti goma a zaune kafin ta yunkura ta tashi domin shirin wankan, kira ya shigo wayarta dake can kan daddumar da tayi sallah. Kafin ma ta bata umarni taje ta dauko mata wayar, ta karba a yatsine tana dubawa. *BA 'KYAUE* sunan dake yawo kan fuskar wayar kenan. Tsaki taja da fadin.'' Da sassafe ya kira waya kamar wanda yake bin bashi.....Daf da zata tsinke ta daga tasa a kunne. A maimakon tai masa sallama sai kawai ta sauke masa ajiyar zuciya a kunne, tai shuru da bakinta. Shi yay mata sallamar ta amsa kamar bata so, yace."Kin tashi lafiya ya kwanan ba'kunta."? A takaice tace."Alhamdulillh." Ya dan ja fasali kafin yace."Jiya na gan ki a online misalin daya na dare ke da waye."? Cikin sigar zargi da tuhuma yake mata tambayar. Gabadaya duk sai ta daburce! tana so ta tonawa kanta asiri........."Wac....Wace irin tambaya ce wannan.''? Yace."Alamu sun nuna baki da gaskiya ga yanayin yanda kike magana a daburce! okey duk wani abu da za kiyi ina ji a jikina domin bani kadai bane akwai masu sheda min halin da kike ciki saboda haka ki shirya dawowata sati biyu masu zuwa." Da kyar ta iya saisaita muryarta amma inaa! sautin muryarta rawa yake yaki saisaituwa duk ta tsure jin yace bashi kadai bane dama tun haduwarsu a daji ya ta'ba fada mata cewa yana da aljanu tana jin tsoron kada su sheda masa halin da take ciki, Ta daure da 'kyar tace." Bana neman tashin hankali ko wata 'bakar magana zargin da kake min ba zan ha naka ba ka cigaba sannan duk sharrin da aljanunka za suyi min sun jima ba suyi ba, dai kai dasu duk baku dame ni ba." Tana gama maganarta ta kashe wayarta ba ta jira amsarsa ba. Shi kam dariya ma ta bashi ya tsaya ya dara yana jin dadin yanda game din yake tafiya a tsakaninsu, Hamra'u ya kira suka gaisa ganin zata jashi da hira alhalin fita zai yi yasa a tausashe yace." Kanwata yi hakuri yanzu ba lokacin hira bane lokacin aiki ne idan na dawo na samu nutsuwa zan kira ki muyi hirar soyayya, yanzu ki bani Uwale idan tana kusa mu gaisa domin na kira wayarta bata shiga ba." Taji ciwon hakan a cikin ranta amma sai ta danne a sanyaye tace" Bari na kai mata wayar tana kicin.? Cikin mamaki yace."Kicin kuma me takeyi? Hamra'u keyi menene amfaninki."? Da sauri tace."Aa nima ba laifina bane domin babu yanda banyi da ita ba akan ta zauna ta huta ni zanyi mana komai kamar yanda na saba tace ita lallai sai ta shiga kicin da kanta tayi wa amaryarka girki." Ya dinga girgiza kai yana mamakin rigima irinta kakar tasa, yace." Yanzu je ki kai mata wayar za muyi magana." Ta amsa da "to" kafin ta je ta kai mata wayar. Tana kicin taa dage sai soya funkaso take gefe guda kuma had'addiyar miyar taushe ce wacce taji nama da gyada da alayyahu sai turiri take tana tayar da kamshi mai dadi. Tace."Uwale yayana yana son magana dake." Da farin ciki ta karbi wayar tasa a kunnuwanta da fadin." UMARU ina kwana.''? Ya amsa da "Lafiya lou Uwale kun tashi lafiya ya kuma hidima da jama'a."? Tana 'yar dariya tace." Alhamdulillhi an yi taro lafiya jama'a kowa ya koma gidansa lafiya " Yace."To alhamdulillhi haka akeso nima insha Allahu sati biyu masu zuwa na kammala komai na dawo gida." Tace."Alhamdullhi, Allah abin godiya UMARU Allah ya dawo da kai lafiya ya kuma cigaba da baka nasara akan duk abunda kasa a gaba." Ya amsa da "Ameen ya Allah." Ya dora da fadin." Yanzu Hamra'u take sheda min cewa kina kicin kina aiki Uwale me yasa ba zaki zauna ki huta ba sai kin wahalar da kanki Hamra'un za tayi duk abinda ya dace." Tace."Hakane maganarka UMARU bahaushe yace YABA KYAUTA TUKWICI yarinyar nan 'yar babban gida ce wannan shine dalilin da yasa nake dawainiya da ita ba wai don naga gazawar ita Hamra'un ba." Yace."Duk da haka dai ki samawa kanki lafiya domin ba na so kina aikin wahala saboda shekaru sun ja miki, idan ya kama na dauko masu hidima a gidana ina da ikon yin hakan, domin itama Hamra'un ba ita take da alhakin haka ba tunda dai ba auranta nake ba." Tace." To yanzu dai nayi laifi kenan don na nuna kulawa a kan matarka."? Ya girgiza kai da fadin." Ba kiyi laifi ba Uwale cewa nayi ki zauna ki huta ita Hamra'u ta cigaba da aikinta kafin na dawo gari." Tace."Ai shikkenan tunda kai baka san gwaninta ba sai anjima." Sallama tayi masa ta mikawa Hamra'u wayar tana mita akan abunda yay mata. Yace." Hamra'u bata wayar da sauran magana dani da ita. K'in kar'ba tayi yana jinta tana fadin." Oho!oho! ai ka gama magana UMARU har da zan nuna kulawa kan matarka ka gwasale ni." 'Yar dariya yay ya daga murya yanda za taji sosai yace." Yanzu dai mu bar wannan maganar haka Uwale kina ji na ko."? Shuru tai masa ta cigaba da soya funkasonta.....Ya cigaba da cewa." Wannan kayan abincin da aka jibge a store ba na bukatar na dawo na samesu, ki tara 'yan uwa da abokanan arziki da kuma yara na ina nufin su Alba kenan duk ki raba musu, ni a bar min kadan sun isa." Tace."Kana da hurumin hakan amma sai an shedawa ita GIMBIYAR domin itama tana da hakki." Ya jima yana mamakin maganar kafin yace." To shikkenan ki sheda mata cewa Umarni na ne nace rabawa mabukata kayan masarufin da tazo dasu sannan kuma nagode da hidima." Tace." UMARU ba haka sharad'in kayan gara suke ba, kana da hakki tana da hakki, saboda haka ni sai naji hukuncin da ta yanke idan bakinku yazo daya shikkenan sai ayi yanda kace." Takaici ya ishe shi, kawai ya kashe wayarsa ba tare da yayi mata sallama. aljihu yasa wayar, ya janyo takalmansa ya fara kokarin sanya wa a kafafuwansa dake cikin safa, yana ganin idan an jima kadan, ya samu sukuni zai kira yarinyar ya sheda mata hukuncin da ya yanke, bawai don baya bukatar kayan masarufin ba, kawai dai yana so ya tsira da mutuncinsa domin ganin tsarin yarinyar watarana zata iya yi masa gori akan wani abu daya dangance ta. *SAI RANAR MONDAY ZA MU CIGABA
Chapter 38 · 0% Book details