Sashe 63
Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
taso masa yace.'' Jiya bayan rabuwarmu ina shiga gidan.......duk ya kwashe komai ya fada masa. Ya dinga girgiza kansa yana mamakin al'amarin yace." Yanzu Zinatu da hankalinta ta aikata wannan d'anyan hukunci. koda yake ko shakka ba nayi da sanya hannun Zainab domin yini sukayi a tare wa yasan irin abunda suka shirya. Ya girgixa kansa da fadin." Kada ka zargi kowa domin yarinyar abunda yafi haka ma zata aikata, na shiga dakina na samu ta tarwatsa min ko'ina wannan shine dalilin da ya sanya na samu rauni a kafata. Yace." To wai shin ma me ya had'a ku ne har hakan ta faru."? Tsaki yaja kafin yace." Bak'in kishi ne da jahilcin dake damunta, tana zargi na dan haka zuciyarta take raya mata, amma ni nasan abunda na aikata ba haram bane domin da niyyar taimako nayi kuma ko'ina hakan na iya faruwa ballanatana a cikin gidana, Asp mutukar naga abunda zai cutar da wani musulmi dan uwana mace ko namiji sai inda karfi na ya kare." Yace." Maganar kake a du'kun'kune ka fayyace min makasudin abunda ya janyo matsalar." Kallonsa yayi na second biyu kafin ya fara warware masa abunda ya faru. Yace." Gaskiya ne baka aikata haramci ba kamar yanda take zarginka, kayi hakan ne da niyyar taimako amma kasan mata idonsa yakan rufe akan kishi basa tunani akan kowa sai a kansu amma meye laifinka dan ka dauki Hamra'u kasa a mota shin so take ka bari ta mutu ko yaya."? Yace." Nima dai haka na gani meye laifina anan? wallahi banyi hakan da wata manufa ba sai da niyyar taimakon musulunci." Yace." Umaru wallahi kwata-kwata bana k'aunar alakar Zainab da Zinatu domin dukkaninsu basu da kirki! maganar dai guda daya ce akwai sanya hannun Zeey dangane da faruwar hakan kuma zanje gidan na sameta." Yace." Aa kada ka yanke hukunci cikin fushi! na fada maka fa cewa..... ..Koda babu Zainab a cikin rayuwar *ZINA* to zata iya aikata abunda yafi haka wannan shine dalilin da yasa tun kafin muyi aure nake da shakku akanta saboda gudun faruwar matsala irin wannan......Ban auri Hamra'u ba haka tana faruwa to inaga kuma na aure ta."? Yace." Kai dai zaka zage damtse ka tsaya a matsayinka na namiji ka nuna mata bambanci sosai amma naga duk ka wani susuce! wai shin ko tsoronta kakeji ne."? Murmushin takaici yayi kafin yace." Asp mu rufe maganar nan dan Allah! muyi abunda zai yuwu domin ina so na tafi gida na kwanta na huta." Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke kafin yace." Ai shikkenan tunda ka fadi haka amma ni kam dole na tauna tsakuwa domin aya taji tsoro." Shuru kawai yayi masa yana jin wani irin takaici a ransa.........Wai yana tsoron yarinyar, wannan maganar ta sosa masa rai mutu'ka! shin akwai wata mace da zai ji tsoro a fadin duniya, Uwarsa ce kuma bata raye. Takardun dake hannunsa yake bud'ewa, wata doguwar takarda ya fito da ita da hoto kati daya, mika masa yayi kafin yace." Ka duba hoton sosai ka kuma duba rahoton dake jikin takardar. Saman takardar kawai ya duba yaga an sanya *AMINIYA GIDAN JARIDA KANO STATE* Ya kalleshi da fadin." Wani abu ne yake faruwa a jahar *KANO."?* Yace." Duba dai amma ka fara nazarin hoton mutumin dake hannunka." Ya 'kurawa hoton ido yana ta so ya hasaso kowaye.....ya girgiza kansa da fadin." Bangane waye ba wallahi." Asp din ya kar'bi hoton da fadin........ *UBAN DABA NE."!* A zabure! ya kar'bi hoton yana sake dubawa, kafin kice kwabo gumi ya fara tsatstsafowa a saman goshinsa. Tabbas idan ba wanda yayi masa farin sani ba ba zai ganeshi ba domin duk kammaninsa sun sauya......duk babu wannan 'kasumbar! yana sanye da kayan hausawa riga da wando harda hula sai dai jikinsa lullube yake da wani farin mayafi irin na maza wannan shi ya hana bayyanar nakasar dake tare dashi .........Tabbas shine domin k'wayar idonsa basu sanja ba suna nan yanda suke gwala-gwala masu tsananin ja! kamar garwashin wuta! Ya kalli Asp din da fadin." Ya akayi yanzu meye abin yi."? Asp din yace." Nafiso ka karanta rahotannin kafin mu tsaya a matsaya ana bincike ne a kansa da yaransa da suka sauka a garin. Ya mayar da hankalinsa kan takardar yana karantawa. Rahoto ne daga gidan jaridar *AMINIYA* cewa wasu 'yan gudun hijira da suka samu masauki a k'auye *KUYAN TA INNAH* ana zarginsu da ta'addanci tare da yiwa k'ananun yara fyad'e........Ana dai binkice a kansu domin tabbatar da gaskiya magana. Ya share zufar saman goshinsa, ya kalli Asp din da fadin." Ko shakka ba nayi zasu aikata abunda yafi haka, babu wani maganar binkice! wai shin me yasa jami'an tsaron *KANO!* suke da sakaci ne? to ni da kaina zan shiga Kanon domin a gudanar da binkicen dani idan ba haka ba zasu iya kyaleshi ya cigaba da ta'addanci tare da kashe rayukan da basu ji basu gani ba." Murmushi Asp din yayi kafin yace." Kai ka fiye gaggawa! yanzu idan akayi wani yun'kuri zasu ankara su samu damar tserewa.....wannan rahoton babu wanda ya san dashi sai ni da kai sai kuma Commissioner.......Domin Abokina *Wali Nasiru* dake *KANO* tare da sauran abokan aikinsa ne suka shiga 'kauyen suna binkice akan matsaltsalun dake faruwa.....nan suka samu cikakkaken bayani daga bakin wani dattijo cewa tsayin shekara dari da wani abu wata gagarimar matsala bata ta'ba faruwa ba a 'kauyen sai dalilin zuwan 'yan gudun hijirar.......Dalilin da yasa kenan suka tsananta binkice akansu domin gano gaskiyar lamari.......Kasan abokina ne sosai tare mu kayi karatu to yana bani labarin abunda ke faruwa sai na bukaci da ya turo min rahoton domin ni kaina sai da na zargin wani abu, saboda haka muyi hakuri kada muyi gaggawa domin hakan zai zaburar dasu, su gudu! a nutse zamu kamasu. ina kuma kara tabbatar maka da cewar babu wanda ya san wannan rahoton daga ni sai kai sai kuma mai gayya mai aiki don bana tsammanin ma gwamnati tasan da abunda ke faruwa domin yanzu muka gama tattaunawa commissioner din akan hakan." Dogon tsaki! yaja ransa duk a dagule! wane irin aikin gaggawa ai a ganinsa jinkiri shi zai cutar dasu, ya ga dama sun samu amma za suyi wasa da ita! ya dinga jan tsaki! kansa ya cigaba da sarawa! tabbas da ba dan a karkashin gwamnati yake aiki ba to da babu shakka yau zai yiwa garin *KANO* dirar mikiya duk inda *UBAN DABA!* Da yaransa suke sai ya lalubo su domin gwabzawa! Asp din yace." Ya kamata kaje gida ka huta idan zai yuwu ma gobe ka zauna ka sake jin 'kwarin jikin ka Allah ya sawwake." Ya amsa da "Ameen yana duba agogon dake daure a hannunsa, uku da rabi na yamma....Asp din ya mike da niyyar fita shima mikewar yayi, ya dauki gilas dinsa ya sakaye idonshi kafin yabi bayan Asp din da niyyar zuwa gida ya sha magani ya kwanta ya huta. 'Bangaranta kuwa tunda ya fita ta kasa samun nutsuwa, tana ji kamar ta kira shi a waya tana kuma tunanin kada ta zubar da ajinta.....Haka ta dinga juye-juye a saman gado sa'i da lokaci tana share hawayen takaici! ita kanta ba'a son ranta ta aikata masa hakan ba, kawai ya b'ata mata rai ne. Kafin ya shiga gidan sai da ya gabatar da sallar la'asar tukkuna.........Ya duba gurin su Uwale domin ya tabbatar da cewa sun fito daga asibitin saboda a d'azu da safen Likitan yake tabbatar masa da cewa zai sallamesu zai kuma sanya direba ya kai su gida. Sosai yayi farin cikin ganinsu A falo suna hira har ita Hamra'u domin ta wartsake kamar ba ita ba, hakan duk ya faru ne dalilin kwantar mata da hankali da Uwale keyi ta tabbatar mata da cewa suna zuwa k'auye manya zasu tsayar da maganar daurin auransu, wannan ne dalilin da yasa ta samu nutsuwa ta kuma kwantar da hankalinta. Gabadaya suka dinga bin sa da kallo har ya samu guri ya zauna.......Uwale ce ta magantu, cikin damuwa tace." UMARU mai ya samu 'kafar ka."? Shuru yayi na minti biyu kafin yace." Na d'an taka k'usa ne kin san tana da dafi! shine dalilin da yasa kafar ta kumbura! Sosai tayi mamaki kafin tace." Cikin wannan uban takalmin da kake sanyawa har kusa ta iya huda maka 'kafa UMARU anya kuwa."? Murmushi yayi da fadin." Uwale ki bar tsautsayi kawai! Allah ne kawai ya takaita min wahala 'kusar bata shiga sosai ba ku cigaba da yi min addua." Tace."To Allah ya kiyaye ya tsare gabanka da bayanka." Ya amsa da "Ameen ya rabbi kafin ya kalli Hamra'u da tunda suka fara maganar ba tace komai ba. Ya dan saki fuskarsa da fadin." Ya jikin naki."? Tace." Da sauki Yaya na, kai ma ya jikin naka? Allah kiyaye gaba." Ya amsa da "Ameen ya rabbi nagode sosai amma kin dai ji abunda likita yace miki ko? ki rage tunani dasa damuwa a ranki." Tace." To Yaya na insha Allah zan kiyaye nagode Allah ya saka da alkairi." Bece komai ba ya kalli Uwale da fadin." Uwale a dan bani abinci zanci kafin nasha magani." Ko kafin Uwalen ma tace komai zumbur ta mike ta kama hanyar kicin......Gabadaya suka bita da kallo suna girgiza kai, tausayi take basu. Yaci abincin sosai yayi godiya ga Allah kafin ya wuce sashensa dan beyi niyyar shiga gurinta ba gudun b'acin rai! abunda baya bukata kenan. Marakisiyya dake shanya kayan data wanke a harabar gurin ita taga wuce war sa, ta dur'kusa har kasa tana gaisheshi ya amsa ba tare da ya kalleta ba, ya wuce ya bar ta a gurin. Ita din ke shedawa uwar dakin nata dawowar mijin nata.........Tace mata ta ganshi ya fito daga sashen masu gidan ko za'a kai masa abinci." Ranta ya 'baci! ta kalli Marakisiyyar ta watsar kafin ta buga mata tsawa! had'e da nuna mata hanyar fita. Da sauri ta mike ta kama hanyar fita gabanta na faduwa! sam ba tayi tsammanin cewar maganarta zata fusata! Uwar dakin nata ba, a ganinta kamar gwaninta tayi. Ita kuwa har Marakisiyyar ta fita ba daina hararar hanyar data bi ba.......Wani irin kishi ne yake damunta. wannan ai abun kunya ne mijinta ya dawo amma ace mai'aikinta ce ke sheda mata, bayan haka kuma tana jin haushin abunda ya kai