Sashe 82
Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dawo da ita ba tare da izinina ba, bana gari kana zurga-zurga a cikin gidana, akan me ba zanyi zarginka ba." "Ya isa haka."!! Da karfi yayi maganar jikinsa na wani irin karkawa. Ya cigaba da cewa." Wallahi ban ta'ba tunanin da'kiki! bane kai sai yau! dole kayi wannan tunanin saboda jahilcin da yake damunka, ka jima kana mummunan furuci a kaina har kana danganta ni da matarka ta sunnah. to bari kaji kwata-kwata kai baka dace da wannan yarinyar ba, wallahi dana san haka halinka yake da ba zan shige maka gaba har ka samu nasarar auranta ba, babu damuwa kayi kuskuran sakinta ni kuma zan baka mamaki."! Bai jirayi amsarsa ba kawai ya kashe wayarsa. Wayar ya tsirawa ido yana kallo hankalinsa a tashe! wannan shine a dake ka a kuma hana ka kuka, Asp ya shiga huriminsa amma saboda tsabar rashin tsoron Allah yana nad'e tabarmar kunya da hauka. A daran kasa rintsawa yayi koda yake dama can ba wani baccin arziki suke ba, kullum suna tsakanin border suna kai kawo amma dai wani lokacin idan baccin yazo yi suke ba tare da saninsu ba, domin shi bacci daban yake a cikin abinda Allah ya hallata mara sa rai. Yana kallon wasu daga cikin abokan tafiyarsa suna bingirewa bacci na kwasar su, bai hanasu ba kwai ya kyalesu su sarara shima ya samu damar nazari da tunanin hanyar warware matsalarsa......Sai dai a gurin tunanin baccin dai da yake gudu yazo ya sace shi ba tare da yayi tsammani ba. Cikin baccin yayi mafarki da wani dattijon mutum da fararan kaya a jikinsa kansa nade da farin rawani farin gemunsa ya kusa ta'ba kasa akwai wani zabgegen carbi a hannunsa. suffar mutumin dai gashinan ba mutum ba ba kuma aljan ba. Sunansa ya kira." UMARU." Ya amsa da "Na'am." Yace." Ni ne abokinka ina tare da kai tun kana cikin uwarka nima sunana UMARU ni musulmi ne ina kuma taimakon bil'adam mussaman musulmai. ban ta'ba bayyana a gare ka ba sai yau duba da ganin yanda al'amuranka suka lalace! me yasa kake sakaci da addua? a can baya baka da wasa amma yanzu ka bari har ma'kiya sunyi tasiri a kanka." Shuru kawai yayi yana kallon Dattijon. Yace." Rufe idonka. Kallonsa yayi nan ya hango k'wayoyin idon dattijon sunyi kama dana *ZAKI!* Ya zabura! da sauri ya rufe idonsa. Kamar al'amara ya ganshi gurfane bakin kwatami (kwata mara kyau) yana hake kasar gurin. yana fito da layar! a zabure! ya bude idonsa yana duba hannunsa yaga layar sai ya fara dube-dube a gurin, babu dattijon babu dalilinsa. Ya dinga kiran sunan Allah yana tu'ajibun Al'amarin shin waye wannan dattijon daya ziyarceshi.? Ya sake duba layar dake rintse a hannunsa tunanin a inda ya ciro ta yake.....Kofar gidan Malam Shafi'i." Zuciyarsa take tuna masa. Tabbas hakane shin me hakan yake nufi? surkulle akayi maka aka shiga tsakaninka da iyalinka. wannan karon ma zuciyarsa ta sake tunasar masa. Sai kawai abubuwan da suka wuce suka dinga dawo masa daki-daki! jikinsa ya jike sharkaf da gumi tsabar fargaba da tashin hankali. Haka ya wayi gari cikin rashin karsashi da kwarin jiki, duk abunda yake daurewa kawai yake ya rasa ma tunanin da zai yi. Ya kira wayar Asp din sau curin masaki amma yaki dauka domin ya dauki fushi! dashi mai tsanani. Ya kira Hamra'u da fadin.'' Lallai ta kai wa Zinatu wayar yana so yayi magana da ita, dalili ya kira wayarta itama taki dauka. Rasa abinda yake damunta tayi ba dan ranta yaso ba ta kai wa Zinat din wayar ta sheda mata abunda yake da akwai. Tace." Kinga Hamra'u fita dan Allah bana san b'acin rai! kinzo da rawar jikinki watakila ba alkairi bane a kiran nasa, saboda haka kije kawai bana bukata. Jikinta babu kwari ta fita da wayar a hannunta tana tunanin irin masifar da zai mata. Aikuwa dai rufeta yayi da bala'i yana nema ya d'ora mata laifi! takaici yasa kawai ta fashe da kuka ta kashe wayar ba tare da ta cigaba da sauraransa ba kwanciya tayi ta dinga kuka tana tunanin ya rayuwarta zata kasance a gidan, dan taga kamar hankalinsa ya dawo kan matarsa watakila ita za ta zame musu 'yar aiki, gashinan sai walagigi suke da rayuwarta shi ya kyareta! ya hantare! ta ita kuma ta aike ta shin wannan wane irin aurene mara 'yanci. *Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number* *07084653262* *BINTA UMAR ABBALE* 3/24/22, 19:24 - Binta: _Akwai ingantaccan maganin gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ *121* Ya kira wayar Asp yafi a 'kirga amma bai saurareshi ba, kawai sai ya yanke shawarar rabuwa dashi ya mayar da hankalinsa guri daya amma can kasan zuciyarsa akwai tarin fargaba da tashin hankali a dan'kare! domin duk abubuwan da suka faru a baya yana tunaninsu yana kuma nazarin ya akayi hakan ta kasance. babu shakka yanzu ya fara hangen gaskiya akan mafarkin da yayi cewa da akwai sanya hannun iyayen Hamra'u gurin 'bacewar tunaninsa, idan ba haka ba ya akayi al'amura suka sauya, da hankalinsa da tunaninsa ba zai manta lokacin da yanke hukuncin wata shida kafin a daura musu aure ba, amma ya akayi al'amura suka sauya, babban abinda yafi damunsa yanda suka samu matsala da amininsa ya rasa dalilin da ya janyo hakan, burinsa ace Asp din ya d'aga wayarsa sun tattauna maganar, amma ga dukkan alamu yayi fushi dashi irin wanda bai ta faruwa a tsakaninsu ba. Damuwar da yake ciki ta sanya masa rashin karsashi! da 'kwarin jiki duk abinda yake 'kok'ari kawai yake amma gabadaya hankalinsa yana gida gurin iyalinsa mussaman ita Zinat din da take tare da lalura. Wani irin tashin hankali ne ya faru a daran ranar da suka gama shirye-shiryen tafiya gida. Abinda ya faru shine, tun bayan zuwansu garin. 'yan ta'addan da suka damu garin ta'addanci suka sauya dubara! domin tuntuni suna da labarinsa da irin jazaba da baiwar da Allah yayi masa, sai duk suka watse suka sauya ma'boya, amma suna da labarin duk abinda yake faruwa a garin. Iya bakin kokari da binkice sunyi a garin basu kama wani mai laifi ba. wannan dalilin yasa suka shirya tafiya domin hakan ma nasara ce, ace zuwansu garin ya tsorata masu laifin sun gudu saboda rashin yarda da kai. Ashe lamfo sukayi. a daran ranar suka saka musu bom! gurin da suke ya kama da wuta!.........Mutum shida suka kone kurmus! wasu suka jikkata! tashin hankali kenan! wannan al'amarin ya dunguzuma shi! shima bom din wurgi yayi dashi can wata nahiya. Cikin mawuyacin hali yake lalube da hannunsa so yake ya tashi zaune amma inaa! jikinsa yayi nauyi wasu guraran duk sun 'kone! ya kira sunanan Allah da k'arfin gaske! kafin yayi kalmar shahada! ya zabura! ya mike tsaye! yana wani irin ihu!!! da gurnani!! Abinda ya tsorata su kenan dama sunyi lamfo a ma'boyarsu! duk sai suka gigice! suka fara fitowa wasu na gudu wasu kuma na harbinsa da bindiga. Basu samu nasarar samunsa ba, saboda yafiso da dabaru!! Shi din dai Allah ya bawa nasara ya harbe kafafun mutum biyar sukayi kwance a gurin suna jan jiki da ihu!! Sauran suka ranta a na kare! duk da haka bai fasa sakar musu bullet ba, sai da ya sake samun mutum biyu suka zube a gurin. Hayaki! da zafin wuta ne kawai yake tashi a gurin. Jini da sassan jikin dan Adam dole ya firgita wanda bai saba gani ba. Ya dinga bin 'yan uwansa yana dubawa wasu da rai wasu babu wasu sunyi daga-daga! naman jikinsu ya tarwatse! Kuka ya dinga yi da hawaye yana kiran sunan Allah! a fili. wannan wane irin tashin hankali ne! Wannan al'amarin da ya faru ya tashi hankali kowa ba mazauna garin ba kawai duk wani mai kishin musulunci da kishin 'kasa dole ya jajantawa kansa zubar jini a Najeria ya zama kamar zubar ruwan famfo. A galabaice aka nufi asibiti dashi da sauran wa'inda suke raye. 'Yan jarida mane ma labarai basu samu cikakken bayanin da suke bukata ba, dalili shi wanda zai musu bayanin baya hayyacinsa, sai dai sun d'auki rahoton gurin da abin ya faru, kuma sun samu nasarar daukar hotonsa a lokacin da ake kokarin sanyashi a cikin motar asibiti, sannan suka kutsa suka dauki hotonan masu laifin da aka samu nasara a kansu. To kafin kice kwabo labari ya cika 'kasa baki d'aya *GOJE!* wannan mafaraucin mutumin da ya kasance Jami'in tsaron dake garin katsina ya samu nasara akan 'yan ta'addan da suka addabi garin Zamfara! sai dai yana da muhimmanci mutanan Zamfara da 'kasa gabadaya su dage da addua akan Allah ya tashi kad'arsa! saboda yana cikin tsaka mai wuya dashi da abokanan tafiyarsa dalilin tashin bom da 'yan ta'addan sukayi ya k'ona wasu daga cikinsu kuma sun rigamu gidan gaskiya, yanzu haka dai *UMARU wanda kuka fi Sani GOJE!* Yana kwance a babban asibitin garin Zamfara domin ceto rayuwarsa." wannan rahotanin da ke yawo gidajen television redio tare da wayoyin mutane . Tashin hankalin da Asp ya shiga yafi gaban a kwantatashi! kaf headquarter 'yan sandan suna cikin tsananin tashin hankali da damuwa sakamakon abinda ya faru da ma'aikatansu mussaman shi Umar din da suke alfahari dashi........mutum