Sashe 84
Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da fatan samun sauki da ramgwame. Har suka shirya tafiya bai tashi ba, Sarkin yace a kyaleshi kada a tashe shi tunda sun dubashi a haka babu matsala. Har bakin mota Asp ya rakasu yana godiya cikin girma da mutunta juna suka rabu. Sarkin da kansa ya sanya Magaji ya kira masa Zinat a waya. Koda suka gaisa sai ya shiga shaida mata abinda yake da akwai. Kasa hakuri tayi hawayen da take dannewa suka subce tace." Ranka ya dade ya jikin nasa ina fatan ya tashi kun gaisa da juna."? Yace." Alhamdullhi yaji sauki ki kwantar da hankali ki kuma kiyi masa addua domin adduarki tana da muhimmanci a tare dashi. Tasa hannu ta share hawayen dake zuba tace." Bana iya bacci kullum addua nake masa Allah ya tashi kafadarsa nace ina san zuwa domin na dubashi Asp ya hana." Yace." Zinatu kada ki janyowa kanki wata matsalar, kinga kema ba cikakkiyar lafiya gareki ba. ki barwa Allah al'amarin sannan kuma zuwanki bashi zai bashi lafiya ba, watakila akwai abinda yake nufi da hakan dan haka ki samu nutsuwa ki kuma tsananta da yiwa mijinki addua." A sanyaye tace." To insha Allahu Na gode a gaishe min dasu Mommy. " Yace." Za suji da kyau." wayar ya kashe zuciyarsa cike da tausayin yarinyar. Koda ya tashi daga baccin Asp yake sheda masa zuwa surukin nasa sai duk yaji rashin dadi. Yace." Me yasa baka tasheni ba naso mu gaisa na nemi afuwar abubuwan da suka faru. Yace." Shi da kansa ya hana a tasheka sosai ya dubaka ya kuma jajanta al'amarin, dattijon yayi adduo'i masu muhimmanci a garemu baki daya." Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace." Ranka ya dade wallahi har kunyar na hada ido nake dakai saboda irin abubuwa marasa kyau da suka faru tsakanina da kai wallahi duk abunda ya faru bana hayyacina don Allah kayi hakuri ka gafarceni." Murmushi yayi da fadin." Umaru abubuwan da suka faru tsakanina da kai ban daukesu wata tsiya ba, domin dana k'ullace ka da ba zanzo inda kake har na kula da kai ba, ni kaina sai da na zargin hakan saboda nafi kowa sanin halinka, wasu abubuwan da aikata akwai alamun tambaya a ciki to amma Alhamdullhi tunda ka gane gaskiya kuma dawo nutsuwarka wannan shine farin cikinmu." Yace." Na gode abokina Allah ya bar abota domin Allah, amma ina zargin wani abu dangane da al'amarin sai dai na kasa yarda da hakan." Yace." Me kake tunani."? Ya sauke ajiyar zuciya kafin yace." Idan ban manta ba kwanakin da suka wuce da kaina na sheda maka cewa wata shida na tsayar domin daurin aurena da Hamra'u." Yace." Eh kwarai kuwa hakane amma nayi mamakin yanda akayi ka sauya shawara akayi abun cikin gaggawa." Murmushin takaici yayi kafin yace."Iyayen yarinyar basu da kirki sun jefe ni sun juyar min da hankali domin biyan bukatarsu na rasa abinda suke nufi da hakan, ko da ba suyi surkulle a kaina ba ni na amince cewar zan auri 'yarsu to wane irin rashin Imani ne zasu juyar min da tunanina su mayar dani kamar zautacce." Yace ." Gaskiya basu kyauta ba wallahi ban san me yasa wasu mutanan suka yarda da asiri ba, to meye amfanin hakan da sukayi tunda gashi tun ba'aje ko'ina ba aikin da sukayi ya lalace." Ya girgiza kai da fadin." Cikin mafarki da taimakon wani bawan Allah naje na lalata aikin. Ya dinga kallonsa yana mamakin maganarsa......Murmushi yayi ya bagarar da maganar ta hanyar fadin .'' Tunda na warware sosai sai ka kira min matata mu gaisa ko hankalinta ya kwanta." Yace." Kasan kuwa ta dameni kullum sai ta kira waya yafi sau biyar har kuka takeyi. Tsigar jikinsa ta tashi, ido ya lumshe da fadin." Nima kukan zucci nake tsayin wata da wasu kwanakin ban sata a idona ba mun rabu babu jituwa wallahi hankalina gabadaya yana kanta. Asp din yana laluben number yace." Kamar ita kadai ka ajiye a gidan ko ka manta su biyu ne ga Uwale ma babbar uwar gida." Murmushi yayi bai iya cewa komai ba, hannu ya mika masa domin ya bashi wayar. Yasa wayar a kunnanshi yayi dai-dai da maganarta......"Assalamu alaikum." Idonsa ya lumshe wani irin yanayi na ziyartashi. Gyaran murya yayi a nutse yace." Wa'alaikissalam Sirrina marufar asiri na." Jin muryarsa a kunnanta ya sanya ta sauke sanyayyar ajiyar zuciya a hankali tace." Alhamdullihi jin muryarka a yanzu ya tabbatar min da cewa sauki ya samu a gareka ina rokon Allah ya baka lafiya tare da sauran wa'inda suke kwance." Ya amsa da "Ameen ya rabbi ya kike ya babyna dake tare dake."? Hannu ta dora saman cikin da yayi wani irin girma tace.'' Babynka yana kewarka shima kullum sai yayi kukan rashinka a kusa dashi." Yace." Ki bashi hakuri kinji ko insha Allah ina nan zuwa gare ku baki d'aya sannan ina neman afuwarki akan abubuwan da suka faru a baya. Tayi dan murmushi da fadin." Na yafe maka nima ka yafe min." Yace." Baki min komai ba my love ni ne mai laifi a gurinki amma naji dadi da ki kayi min afuwa zan dawo mu cigaba da rayuwa mai kyau." Tace." Allah ya yafe mana baki daya. Ya amsa da Ameen kafin yace." Ina Uwale ki bata wayar mu gaisa." Tace." Gata a kusa dani tare da Hamra'u." Shuru yayi bece komai ba . Ta mikawa Uwale wayar suka gaisa sosai tana jajanta masa. Yace." Uwale ku kwantar da hankalinku na samu lafiya insha Allan zan dawo da kafafuna. Tace." To Alhamdulillhi Allah ne abin godiya mutanan *Kafur!* ma duk sun ce ayi maka sannu da jiki sai ka dawo gida zasu zo dubaka." Yace." Na gode sosai Allah ya saka da alkairi." Wayar ta mikawa Zinat din fuskarta yawalce da fara'a da jin dadin samuwar lafiyar jikinta nata. Ta mikawa Hamra'u wayar dake zaune tayi jugum! A sanyaye tace." Yaya na sannu ya jikin."? Babu yabo babu fallasa ya amsa, iyayen yarinyar sun janyo mata tsana a gurinsa. Daga haka babu wata kalma mai dadi kawai ya kashe wayarsa. Idonta ya ciko da ruwan hawaye! tana so itama ya dinga gwada mata soyayya koda bata kai irin wacce yake gwadawa Zinat din ba. A sanyaye ta mika mata wayar jikinta babu kwari ta tashi ta shige daki ta kwanta abin duniya ya isheta. Zinat da Uwale kuwa yinin walwala da farin ciki sukayi sakamakon amsa adduarsu da Ubangiji yayi babu shakka Allah maji rokon bawansa ne. To bahaushe yace ." Rana dubu ta 'barawo rana guda ta me kaya. *UBAN DABA!* ya samu nasarar shiga asibitin cikin shigar Dr Shu'aib likitan dake tsaye a kan Umar din! Yayi basaja sosai da yake Dr Shu'aib din gajere ne mai 'kiba shiyasa babu wanda yayi tunanin cewa bashi bane, abinka da dare duk da akwai fitilu a asibitin hakan bai sa an ganeshi ba,kai tsaye ya nufi d'akin da Umar din yake kwance! A hankali ya mayar da kofar ya rufe.....Asp dake kwance a can saman kujera ya bude idonsa sakamon jin motsin a dakin Dama can bashi da nauyin bacci. Ganinshi yasa ya koma ya kwanta dan beyi tunanin cewa wani ne daban ba. baccin ya sake fizgarsa. Da har ya tsorata amma ganin ya koma ya kwanta yasa ya sauke ajiyar zuciya. Kai tsaye gadon da yake kwance ya nufa. Isarsa ke da wuya ya b'ude idonsa!! 'Kwayar idonsa kawai ya kalla ya sheda waye a gabansa. A zabure! yayi nufin tashi.......shi kuma da gaggawa ya rike masa wuya da kyau!! Wata shegiyar igiya mai wasu k'ananun kososhi masu tsini! ya ciro daga can kasan aljihun wandon dake jikinsa. Kokarin d'aure masa wuya yake da igiyar abun ya gagara! domin dambe! suke sosai! duk da ya sha'ke masa wuya! amma bai samu nasara a kansa ba. Naushi! ya kaiwa hancinsa a take ya fashe ya fara zubar da jini. ya sake kawai fuskarka wawan naushi! yayi tagaga! zai fadi! amma saboda taurin zuciya bai sakar masa wuya ba. Gurnani! ya dinga yi yana buge-buge! da kyar yake janyo numfashi! ya galabaita sosai! saboda dama can jikin babu 'kwari! Kamar a mafarki ya dinga jin wani irin abu. Ya bude ido da saurin gaske. Abinda ya gani ya tayar masa da hankali shin mai yake faruwa a tsakaninsu. Da sauri ya nufi gurin da fadin." Dr me yake faruwa ne."n Juyowar da zai yi suka had'a ido! nan ya sheda ko waye! jikinsa ya shiga tsuma! ya zabura! zai fita. kawai ya d'aga igiyar dake hannunsa ya kai masa duka da ita a fuska! aikam duk ta yanke masa fuskarsa har kan idonsa ya rufe! idon jini ya 'bata fuska........Da kyau! yayi ihu!! da fadin." Babu lafiya a daki mai lamba 21." Kafin kice me hankalin kowa ya tashi duk likitocin dake aikin kwana suka fito tare da masu gadi. Kai tsaye d'akin suka nufa.....Lokacin ana buga damben Maza! tsakanin mutum biyu. Asp na kasa a kwance yana matagugu! rai a hannun Allah. Sosai suke dambe!! irin na k'wanji da 'kwanji *UBAN DABA!* hannu guda gareshi amma ya san makwantan mugunta! Shi kuma da yake da rauni a jikinsa hakan bai sanya yayi rauni ba, ganin Asp a kwance! ya tayar masa da hankali babu shakka yau sai yaga karshen mutumin nan mutu'kar yayi sanadin abokinsa. Ganin abinda yake faruwa ya tayar musu da hankali. Duk yawansu aka rasa wanda ya iya zuwa gurin domin bada taimakonsa. Su kansu sucurity din abun yafi 'karfinsu! Gabadaya ya manta da wanda yake gogayya! shine fa mutumin nan da wu'ka! bata aiki a kansa! amma ya dage yana wahalar da kansa sai kai masa sara da kaifaffar wukar dake hannunsa burinsa kawai ya illatashi. Ganin haka yasa yayi kwankwance ya murd'e! masa hannu ya kwace wu'kar! Bai kuma jirayi komai ba ya soka masa ita wuyansa!! A take ya fadi a gurin yana wani irin gurnani! jini ya dinga tsartuwa! Zubewa a kusa dashi da wu'kar a hannunsa da karfi yace *." Ashahadu Allah ila ha'illalahu -wa ashshahadu Anna Muhammadur-rasulullah.* fad'ar hakan keda wuya ya mi'ke cikin zafin nama yaje ya fizgo k'aramar bindigar dake jikin rigar Asp dake rataye bai jira komai ba ya sai ta a wuyansa. *Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba,