Sashe 41
Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya fada cewar kece za'bin sa, sai gashi kuma Allah ya kawo masa wata bayan ke, bamu san alkairin da yake tattare da al'amarin ba, sannan kuma idan kin kwantar da hankalinki kema idan da rabo zai aureki tunda yana sonki, amma ki daina fito da kishinki a fili akan wannan al'amarin.' Duk cikin maganganun Uwale babu na son zuciya gaskiya ce amma ita kuma sai ta kasa fahintar hakan, ta juya al'amarin wata siga daban, ta kuma 'kullaci Uwalan a cikin ranta a ganinta kamar itace bata so UMAR din ya aureta. Hawayen fuskarta ta goge ta nufi dakinta mayafi ta yafo a jikinta, kicin din ta nufa ta dauki kwandon abincin kai tsaye sashen Zinat d'in ta nufa. Ta same ta zaune a falo cikin shiga ta alfarma, Alkyabba 'yar gasken, gold yaji a ko'ina har a yatsun kafa, falon ban da k'amshi na mussaman babu abunda yake, kallo daya tayi mata taji gwiwarta tai sanyi, Gimbiyar tana da wani irin k'warjini na mussaman wanda Allah ya huwace mata. Jin motsi yasa ta dago kanta tana kallon bakin kofar, lokacin ita Hamra'un ta juya tana rufe kofa, bata dauke idonta ba har sai da ta juyo suka had'a ido.....Wani irin kallo ta kai mata wanda gabadaya ya kashe mata jiki, daman abinda ta guda kenan. Ta daure tayi mata sallama tare da k'arasawa kusa da ita da kwandon abincin a hannunta. "Auntyna barka da asubah fatan kin tashi lafiya."? Cikin nutsuwa take gaisheta. Kafin ta amsa sai da ta mula tukkuna! Ta d'an janyo kwandon abincin da fadin." Ga kayan kari kummalo nan Uwale tace a kawo miki." A d'age tace." Tsakanin ke da ita wacece tayi girkin."? Kai tsaye tace." Ni ce nayi saboda Yayana ya bada Umarnin hakan cewa ita Uwalan ta zauna ta huta, ni na gabatar da komai kafin ya dawo." Ta jima tana kallonta gami da auna maganarta tace." Shin kece kika fada masa cewa kakarsa tana min hidima."? Shuru tayi ba tace komai ba. Ta ta'be bakinta da fadin." Okey shurun ki ya bani amsa, ki tashi ki bani guri tare da wannan tarkacan k'azantar da ki ka shigo min dashi bana bukata." Ba tace mata komai ba, ta yun'kura ta tashi tsaye, kwandon abincin ta d'auka ta kama hanyar fita, zuciyarta cike da takaici da haushinta. Kallon banza tabi dashi, cikin zuciyarta tana raya wasu abubuwa akan yarinyar, tabbas akwai alamun munafurci a tare da ita. Gabad'aya ta riga ta saki jiki tana jiran abinci mai dadi da gamsarwa irin na jiya, wannan shine dalilin da yasa koda Marakissiya ta tambayata abunda take bukata ta dakatar da ita da cewar taje kawai tayi musu nasu, ita tana jiran wanda za'a kawo mata daga cikin gidan, sai kuma yanzu taga a kasin haka, tsaki taja mai tsayi, sam bata tsammanin zata iya cin abincin yarinyar domin bata yarda da tsabtarta ta ba. Shigowar Uwale ne ya katse tunaninta, wannan karon a d'an sake ta amsa sallamarta, bata kuma dauke idon ta ba har sai da ta k'araso inda take zaune. Cikin damuwa tace." Zinatu me ya faru ne? Hamra'u ta kawo miki abinci kin kore ta dashi." Numfashi ta sauke kafin tace." Babu komai kawai bana bukatar nata, nafi bukatar naki domin wanda ki kawo min jiya yay min dadi sosai." Ta 'bangale baki tana dariyar farin ciki tace."Shine dalili kenan to kada ki damu idan kinfi bukatar nawa nayi miki alkawarin yi miki duk irin wanda kike so." Murmushi tayi da fadin." Nagode sosai, me zaki min yanzu? amma dai ina bukatar kunun gyada irin na jiya." Tace." To kada ki damu yanzu zan je na dama miki bayan shi sai me kuma."? Kallonta tayi cikin zuciyarta tana yaba kokarinta, a rayuwarta tana son mai sonta, lokaci guda taji tsohowar ta kwanta mata a rai." A sake tace." duk abunda ki kayi ina bukata, Ina yaba kokarin ki sosai koda yake dama girkin tsaffi akwai dadi da gamsarwa." Ta kyalkyala dariya da fadin." 'Kwarai haka maganarki take, ai mutanan da bamu da 'kyiwa da ganda muna zama mu gyara abinci yanda zai gamsar, mijinki ma Umaru haka yake min irin wannan sambatun." Murmushi kawai tayi, bata iya cewa komai ba, har Uwalen ta fita daga falon, Ta girgiza kai da fadin." Kakar sa mai kyawun hali, shi kam halinsa daban da sauran mutane. Ganin Uwalan ta shigo cikin farin ciki da walwala ya sanya ta mamaki, ta bita da kallo a lokacin da ta kama hanyar kicin, sai ta shiga nazari da tunanin abinda ya sanyata walwala da farin ciki irin haka, dalili duk lokacin da zata shiga sashen Gimbiyar to babu shakka zata fito da bacin rai amma yau sai aka samu sauyi. Tana nan zaune tana saka wasikar jaki tsayin mintina arba'in Uwale ta fito daga kicin ta kammala komai hannunta rike da kwandon abincin. Ta dinga yi mata kallon mamaki! kafin ta bude baki da niyyar magana Uwalan ta riga ta da fadin." Hamra'u kada kiyi wa al'amarin nan mummunan fahinta, domin ni dake da Zinatu duk daya na dauke ku a zuciyata, bayan na shiga gurinta take sheda min cewa tafi bukatar ni nayi mata abinda za taci saboda taji dadin wanda nayi mata jiya, don haka kada ki sanya a ranki cewa domin ta tozartaki ta 'kyamaci abincinki." Kasa magana tayi tsabar bacin rai da yanda zuciyarta take tururin zafi, zuwan gimbiyar gidan yana barazana da rayuwarta domin abubuwan da Uwale take mata zasu iya sanyawa zuciyarta ta buga......Tana can tana tunani Uwalen ta fita motsin kofa ne ya dawo da ita nutsuwarta. Ajiyar zuciya mai zafi ta sauke kafin ta mike ta nufi dakinta. Tana shiga ta zauna gefan gado tare da daukar wayarta, kai tsaye number wayarsa nemo, a wannan ga'bar dole itama tayi wani k'okorin domin samun cikar muradin ta, bata iya k'arya ba amma tana ganin yau zata fara saboda abubuwan da Uwale da ita Gimbiyar suke mata a gidan sun isheta. Murya na rawa kamar me shirin fashewa da kuka duk ta sheda masa abunda yake faruwa bata tsaya a haka ba, sai da ta kara gishiri kamar yanda ta tsara hakan a ranta. Yace." Hamra'u banyi mamakin jin wannan al'amarin ba, domin duk abinda akace min yarinyar ta aikata ba zan karyata ba, saboda dama can bata da tarbiya, to amma duk abinda za tayi ya tsaya iyakacin kaina domin ni na ajiye ta a gidan, ba zan lamunci taci zarafin wata daga cikinku ba, Mussaman Uwale da bani da kamarta a duniya , saboda haka kiyi hakuri idan na dawo zanyi wa tufkar hanci, na roki alfarma a gurinki cewa duk irin rashin arzikin da za tayi miki kada ki biye mata, ai kin fita nutsuwa da hankali da kuma ilimin addini, banda jahili babu wanda yake da ta'kidin cin zarafin dan adam wanda Ubangiji ya karrama shi a cikin hallita, mulki! izzah! iko! sune suke damunta da sannu ni zan sauke mata duk wani abu dake kanta." Sassauta murya tayi cikin kissa gami da kokarin kar yaga laifinta tace." Insha Allahu zan kiyaye duk abunda za tayi min koda zata zagi iyayena ne to ba zan tanka mata ba, zan bari ne har ka dawo." Yace." Yawwa nagode sosai my lov dina, maganar hidimar da Uwale take mata kada ki kara magana akai ki kyaleta tunda tana ganin zata iya idan na dawo dole ta ajiye aikin ta zauna ta huta." Tace." To shikkenan Yaya na Allah ya dawo da kai lafiya." Ya amsa da ameen ya Allah, kafin suyi sallama da juna. ****** Bayan kwana biyar da faruwar al'amarin, Asp ya kira ta a waya suka gaisa da juna ya tambayata ko tana da matsala tace babu, sai yace." To masha Allah haka ake so, ai mutumin naki yana kan hanya gobe mybe iwar haka ya sauka, ko da yake ma ai nasan ya fada miki dawowar tasa. Gabanta yana d'an faduwa Tace." Aa ni bai fada min ba." Kawai ta tsinci kanta da fadin." Yaushe rabon ma da ya kira ni a waya." Asp din ya shiga mamaki mutuka, kafin yace." Kinga kullum kuwa muna waya dashi kuma idan na tambayashi cewa kuna waya sai yace min Eh amma kiyi hakuri kada ki damu mybe aiki ne yay masa yawa. Ta danne bacin ran dake taso mata tace." Ranka ya dade abokinka mak'aryaci ne, kuma bashi da kirki wallahi, ai ya san abinda ya aikata dole ya kare kansa a gurinka. Yace." ZINATU ki daina jifan sa da irin wannan kalaman mijinki ne fa a koda yaushe ya zama magana mai kyau ce zata fito daga bakinki. "Humm kawai ta iya cewa ranta idan yayi dubu ya baci Tace." Ba ka tambayi dalilin komai ba ka nema ka dora min laifi idan nace maka kana tsoronsa sai kace ba haka bane." Yar dariya yayi yace." Ai na san labarin gizo ba zai wuce na koki ba, shiyasa ban tambayi dalili ba, amma dai ki fada min laifin da yay miki ina sauraranki." Tace."Gabad'aya ya sanya an fita da kayan masarufin da masarautar mahaifina ta bashi, a cewarsa yafi karfin komai baya bukatar taimakon wani, shine ni kuma nai mamakin hakan nace har yaushe yayi arzikin da zai dinga yiwa mutane tutiya shin wai nawa ne ma albashinsa a wata."? Asp din ya dinga jinjina maganar a ransa, ba tun yau ba yasan da cewar yarinyar ga'buwa ce zata iya farfada masa wannan maganganun. Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Aa kece dai ki ka fahimceshi a bai-bai amma ba nufinsa kenan ba, domin mun jima da yin wannan maganar in da yake sheda min cewa akwashe kayan a rabawa mabukata, ba wai don baya bukata ba, tunda akwai wa'inda suka fishi bukata a raba musu sai a bar masa kadan, ni kaina yayi min kyautar wasu, nace A'a saboda nima Allah ya rufa min asiri, wannan shine dalilinsa, amma ina fatan bakiyi masa rashin kunya ba." Shuru tayi masa domin shi kansa a yanzu haushinsa takeji ganin har yanzu yaki hango laifin abokin nasa . Jin tayi shuru yasa ya gazgata zarginsa, yace." shikkenan shurunki ya bani amsa ba, kinga kuwa duk wani abu da yay miki a yanzu ke kika janyo amma bari zan kira