← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 97

Sashe 28

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gurin wasan makaho bane, sam-sam! ba zata yarda wannan karan ya samu nasara a kanta ba, babu ruwanta da jarumtarsa! tunda a zahiri ta fishi komai, to dole shi zai rusana mata!!!! *TURKASHI!!* *Tofah! yanzu za'a fara wasan ko ya zaman auran nasu zai kasance oho? ni ban san ma me zance muku ba, amma dai muje zuwa..............!* *Wa'inda zasu sayi littafin nake da bukata, don darajar Allah da Annabi idan kin san ba siya za kiyi ba kada ki dauki number ta kiyi min magana *#500 via....0542382124.....Binta Umar gtbank, idan kati zaki tura kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.......07084653262....Mutanan Nijar ku tuntubi wannan number.... 22796074090....Dala dari katin airtal ko mov* 1/31/22, 07:31 - Buhainat: *41&42* Shigowar mahaifyarta d'akin ne ya katse tunaninta, cikin mutuwar jiki ta tashi zaune ta tana kallonta har ta k'araso ta zaune gefen gado babu walwala a fuskarta. A d'an raunane tace."Mamnah barka dare." Tana nazarinta ta amsa da fadin." Barka dai me yake damunki ne baki fito kin ci abinci ba."? Kamar me jiran kiris sai kawai ta fara share hawaye murya a sarke tace."Mammah ya za'ayi na iya cin abinci a irin wannan halin, gabadaya kun kasa fahintata kuna nema ku jefa rayuwata a cikin masifa, yanzu tsakani da Allah a gidan nan wa aka ta'ba yiwa auran dole acikin 'yan uwana, kowacce fa wanda takeso aka aura mata amma ni an d'auke ni kyauta an bawa wani wanda bashi da cikakken asali wallahi ba'ayi min adalci ba." Ta dinga kallonta tana tunano wani lamari daya shud'e shekaru masu yawa, Ajiyar zuciya ta sauke kafin tace." Yanzu Ke a ganinki hakan da akayi miki rashin adalci ne." ? shuru tayi ba tace komai ba, ta cigaba da cewa." Ke ba kiji kunyar fadin wannan maganar ba? shin wai to ya kike so ayi miki da har kike fadin ba'ayi miki adalci ba, ai na dauka sai da aka baki lokaci domin fita hakkinki me yasa baki fitar da mijin aure ba, ko kuma kin fiso kiyi ta zama a haka babu aure mutane na zarginki."? Girgiza kai tayi da fadin" Mammah sati biyu yayi kadan, har yaushe na dawo na samu nutsuwa komai fa yana bukatar nutsuwa da kwanciyar hankali, amma sai kawai a yanke min hukuncin da bai cancanta ba, gaskiya ni ba'ayi min adalci ba don banga abunda zanyi da wannan ba'kauyen mutumin ba." Murmushi mai ciwo tayi kafin tace." Wannan ba'kauyen da ki ka raina shine marufar asirinki domin a halin yanzu idan bashi din ba babu wanda zai aureki ki samu zaman lafiya saboda haka ki kiyaye ni wallahi, kada na kara jin kin furta wata mummunar kalma akan wannan al'amari, idan ban da butulci ma irin naki wannan yaron ai bai cancanci haka daga gurinki ba." Hawaye ta goge da fadin." Ni dai kawai bana son shi ne ko kadan a raina domin ba tsaran aura ne bane, amma shikkenan tunda kun gaji da zama dani zan aure shi kamar yanda kuke so sai duk abunda ya biyo baya kada kuyi kuka dani." Cike da mamaki! take kallonta kafin tace." Zaki caka masa wuka ya mutu kenan."? Girgixa kai tayi tana share hawayen dake zuba a saman fuskarta. Taja dogon tsaki da fadin "Karshen k'iyayye dai ki caka masa wuka a mak'oshi! ko kuma ki zuba masa guba a abinci ya mutu! to idan baki fasa aikata daya daga cikin wannan ba bakya kaunar Allah da Annabi, wallahi ki ka kashe shi kema sai an kashe ki! kina ta'kamar gata ko? ubanki yana da kudi da mulki idan kin kashe rai yana da abunda zai fanshe ki, to bari kiji wallahi nayi miki rantsuwa da Allah ki ka kashe rai! sai na tsaya kai da fata kema kin fuskanci hukunci dai-dai da abunda ki ka aikata! idan wannan ne kud'irinki akan UMARU to kada ki fasa." Tana gama k'are maganar ta tashi ta fita daga dakin ranta a b'ace! al'amarin yarinyar yanzu tsoro yake bata, dole ta tsananta da addua akan al'amarin. Bayan fitar ta daga dakin komawa tayi ta kwanta hawaye na bin gefen fuskarta, ita ba nufin ta kenan ba, kawai ta fadi abinda yake cikin zuciyarta ne, bata fatan kashe kiyashi ballantana wani dan adam. Bacci rabi da rabi tayi saboda tsabar damuwa. Da asubar fari ta kira wayar Asp dama duk tana da numbers su. A lokacin data kira wayar dawowarsa kenan daga massallaci, ganin sabuwar number besa shi mamaki ba, wayar yasa a kunnansa da sallama a bakinsa. Murya a dashe ta amsa kafin ta gaisheshi. Sai ya shiga tunanin inda ya san muryar don dashewar ta sanya ya kasa tantance muryarta. "Wacece ne bangane mai magana ba."? Hanci taja ta dan sake bude muryar da fadin." ZINAT ce." Gabansa ya fadi kadan, yace." Zinatu kece ashe ina fatan dai lafiya."? "Numfashi ta sauke kafin tace."Ai kai ma tunda kaga wannan kiran kasan ba lafiya ba." Tafad'a cikin dusashewar murya. Lokaci guda ya harbo jirgin, gefen gado ya zaune da wayar a makale a kunnansa yace." To menene kiyi min bayani Ina jinki." "Asp me yasa za'a hada baki da kai a cuci rayuwata."? cikin sigar tuhuma take tambayarsa Yace." Bangane maganarki ba." Ajiyar zuciya ta sauke da fadin." Ba zaka gane ba tunda bakinku daya amma ina so ka sheda masa cewa ni ba tsaran auransa bace idan yana farin ciki da dariya to ya dena domin aure na zai zame masa tashin hankali." Da sauri yace."Subahanallahi! Zinatu duk me ya janyo wannan maganar."? Tayi saurin tare shi da fadin."Ni dai sako na baka, ka fada masa cewa bakin rijiya ba gurin wasan makaho bane." Maganar sai ta bashi dariya, ya d'an dara kafin yace." Aa ni wannan maganar bana cikinta amma bari na baki number sa sai ki fada masa baki da baki." Tace."Ai ba tsoronsa nake ba turo min number. " Yace."Yanzu kuwa.'' Kashe wayar yayi yana mamakin al'amarin, gaskiya akwai matsala babba. Kafin ya tura mata number sai da ya kira shi ya sheda masa abunda ke faruwa yace." Don Allah kada ki biye mata ku lalace gabadaya na fahimci rarrashi take bukata, ka rarrasheta kada ka kara mata wani takaicin." Dariya kawai yayi kafin ya amsa masa da "to shikkenan zanyi yanda kace din." Yaji dadin hakan sosai domin shi haka kawai yake so yaga tabbatuwar auran. Yana tsaka da shiryawa ta kira wayar, da yake Asp ya bashi numberta koda ya duba yaga itace sai ya share yaki dagawa. Sai da ta kira sau uku sannan ya daga babu wargi yayi sallama. Ba tare da ta amsa ba cikin gadara da fitsara! tace. Kana jina ko."? Shuru bece komai ba, taja dogon tsaki! da fadin." Nasan a halin yanzu kana nan cikin murna da farin ciki da samun abunda ba kayi tsammani ba, to bari kaji wani abu farin cikin ka zai zama bakin ciki! haka zalika dariyarka zata zama kuka domin daga ranar da akace an d'aura mana aure zaka gane cewa kayi tsaurin ido! na bawa abokinka sako yace sai da ya bani number ka, nace ya bani domin bana tsoron sheda maka abunda yake zuciyata." Ta'kare maganar tana numfarfashi! A nutse yace." Kin san macen da ake kira da (Matar ladan noma."?) shuru tayi tana nazarin sunan. Yace."Tunda baki gane ba bari na ganar dake, mahaifinki ya bani kyautarki sadaki kawai zan bayar, ban ta'ba jin sonki a raina ba, domin baki ma da abinda zaki ja ra'ayi na, ina da wacce nakeso yarinya mai kyau mai hankali nutsuwa da tarbiya ke kam (Matar ladan noma ce) banyi noma ba, amma taimakon da nayi miki yasa mahaifinki ya bani ke ni kuma na kar'ba saboda kada na watsa masa k'asa a ido, zan zauna zaman aure dake ba don ina sonki ba."ya kare maganar hankalinsa kwance. Bakinta ne ya mutu murus! bata tsammaci ya iya cin mutunci haka ba, ta kasa ce masa komai sai wata irin zazzafar ajiyar zuciya da take sauke masa a kunne. Cikin rashin damuwa Yace."Zan kashe waya idan baki da magana." Da 'kayar ta iya danne kukan bakin cikin da yake kokarin kufce mata tace." K'azami bagidaje ba'kauye kawai."! Tayi saurin kashe wayar ta jefar saman gado, zaman 'yan bori tayi kasan kafet taci kukanta ta koshi. kalmar ce kawai take mata amsa kuwwa a kunne *Matar ladan noma!* lallai in baki ya san abinda zai fada to be san abunda za'a mayar masa ba. Sam maganganunta basu bata masa rai ba, hankalinsa a kwance ya cigaba da shirye-shiryensa, besa damuwarta a ransa ba tunda ya riga ya san dole hakan zata faru, yasan cewa akwai jan aiki a gabansa, amma hakan be daga masa hankali ba ya riga ya shirya ya kuma tanadi hanyoyin da zai bi cikin ruwan sanyi yayi maganinta. Tafi sati biyu tana jinyar kanta, tare da bakin cikin ba'kaken maganganunsa! duk sanda zata tuna sunan daya kira ta dashi sai tayi kukan takaici (Matar ladan noma) wannan sunan yakan sanya duk wani alkadari nata ya karye duk shirin da tayi a kansa daga zarar ta tuna cin mutuncinsa sai jikinta ya mutu! gabadaya ta rasa yanda za tayi da rayuwarta gashi ta kasa gane kan mahaifiyarta fushi take da ita sosai! hakan ya k'ara daga mata hankali mutuka, dole haka ta sanyawa zuciyarta dangana ta aro walwala da farin cikin tasa a cikin ranta ta nuna sadudarta a zahiri. sannan har dakinta taje ta nemi afuwarta akan furucin da tayi a kwanakin da suka wuce. Ganin yanda ta saki ranta tana walwala da farin ciki sai itama ta sakar mata fuska ta fara janta a jiki tana yi mata nasiha tare da nuna mata yanda rayuwa take gefe guda kuma tana gyara mata jiki da magungunan mata masu kyau da inganci. Hakuri kawai tayi ta daure zuciyarta take amfani da kayan matan, duk dan ta nuna mata cewa ta hakura da auran kuma babu wani mummunan kudiri a cikin zuciyarta. .........Hakan da tayi sai tasa 'Yan uwanta farin ciki dama kullum adduarsu Allah ya shiryi ta ta gane hanya me kyau. Tun ranar data kira shi a waya yaci mutuncinta bata sake kuskuran 'kara kiran sa ba saboda tana gudun ya kuma dan'kara mata wata mummunar maganar. A nasa bangaran shima be
Chapter 28 · 0% Book details