Sashe 76
Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ne......0542382124....Binta umar gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number* *07084653262* *BINTA UMAR ABBALE* 3/18/22, 20:30 - Buhainat: _Akwai ingantaccan maganin gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ *111&112* A kwance ya sameta bacci na shirin d'aukarta, ya zauna kusa da ita da fadin." Ki tashi ga abinci na san akwai yunwa a tare dake." Ta d'an muskuta da niyyar gyara kwanciyarta a ta'kaice tace." Bana jin yunwa." Yayi kasa'ke yana kallonta kafin yace." Ban yarda ba kwayar idonki ta tabbatar min da cewa akwai abinda ke damunki ko bayan haka ma ai ba ke kadai ce kike rayuwa ba, akwai wanda yake bukatar kici abinci shima ya samu rabonsa. Shuru kawai tayi masa ba ta da niyyar tashi ballanatana taci abincin. Ya 'bata ransa da fadin." Na lura kina so mu sanya kafar wando guda, me yasa ki ke min haka ne? ko dan kin ga na damu dake." Uffan ba tace masa ba, asali ma idonta yana rufe sama-sama take jin sa. Cikin zafin zuciya ya janye bargon dake rufe a jikinta murya a sama ya kira sunanta "Zinatu." Ta bude ido tana kallonsa fuskarta babu fara'a ko kadan. Yace." Na gaji da wasa da hankalin da kike min ki fito fili kiyi min bayanin dalilin da yasa kike wannan abun ai ba haka muka rabu ba da juna ba. Zaune ta mike tana kallonsa duk ya wani firgice! har gumi yake kamar babu Ac a dakin. Zum'bura baki tayi ba tace komai ba ta fara kokarin komawa ta kwanta, da sauri ya rike kafadarta ya hana ta kwanciyar in ban da rawa babu abunda jikinsa keyi, da alama baya son b'acin ranta. "Kina so ki jefa ni cikin damuwa ko? shin ko dai wani abu 'yan uwana sukayi miki wanda kike hukuntani dashi." Ta kalleshi tare da girgiza kanta kafin tace." Ko daya ni 'yan uwanka ba suyi min komai ba sai alkairi saboda haka ba wannan ce matsala ta ba." Da sauri yace." Menene matsalarki ki fada min zanyi miki magani." Cikin ranta ta ayyana wani abu, ta kalleshi ba tare da ta auna maganar ba tace." Ka janye maganar auran Hamra'u." Ya tsira mata idanuwansa da suke a rikice! alamun rashin gaskiya ya bayyana a tare dashi, yace." Wacece Hamra'u."? Kallon mamaki take masa "Wacece Hamra'u."? wai tambayarta yake saboda ya raina mata hankali. Ganin tana masa kallon zargi yasa ya daburce kafin yace." Waye ya fad'a miki zan aure ta da har kike wannan maganar."? Tsaki taja kafin tace." Ba ka da gaskiya wallahi kuma ban san cewa kai munafiki bane sai yau wato har ni kake tambaya wacece Hamra'u? yarinyar da kowa ya sanka da ita a gari shine zaka raina min hankali. Maganganunta sun 'bata masa rai mutuka! ya fusata! tare da nuna ta da hannu "Kin ga saurara kada kiyi min rashin kunya ni kike kira da munafiki."? Tace." Kana nad'e tabarmar kunya da hauka meye dan ka fada min dalilin zuwanka garin cewa maganar auranka zaku tattauna har ka bada sadaki kun tsayar da magana to sai me don kayi aure ko ka d'auka zan damu kaina a kan hakan namijin da ake so shi ake kishi a kansa." Yaji wani mugun bakin ciki da jin kausasan kalamanta! ya dinga fesar da wani irin huci! yana kallonta idonsa yayi jajawur! magana daya da tayi itace take sa hankakinsa ya tashi, (Namijin da ake so shi ake kishi a kansa) wato wannan yana nuna masa cewar duk abinda zai yi yaje yayi bata sonsa. Ya tashi ya fita ya bar mata dakin domin zamansa zai iya haifar da kowace irin matsala mara kyau. Ba ta wani damu da yanayin da ya shiga ba, bacci tayi sosai babu wata damuwa a tare da ita, ta riga ta san duk abinda yake raragefe ne da kame-kame. Washe gari bai saurareta ba ya shirya ya fita da tarin bacin rai a tare dashi. Wanda har sai da abokinsa ya fahimci cewa yana da damuwa domin kallo daya yayi masa ya sheda hakan, abota ce ta gaskiya wannan dalilin yasa dukkaninsu suka fahimci junansu. Ya kalleshi da fadin." UMARU kana da damuwa domin na ganta a cikin idanuwanka." Ajiyar zuciya ya sauke ya kalleshi da fadin." Zinatu ce damuwa ta Asp yarinyar nan idan ta burkice na kan rasa gane kanta." Asp din yace." Wani abu ne ya faru."? Yace." Ta samu labarin tabbatuwar aurena da Hamra'u shikkenan take fushi jiya da k'yar na rintsa wallahi." Yace." Sai hakuri, amma dole ka fuskanci wannan matsalar, kai dai kawai kabi hanyoyi masu kyau da zaka rarrasheta mussaman yanzu da take da juna biyu dole sai an bi komai sannu a hankali." Yace." Kana nufin nayi ta bin kanta ta nayi min yanda takeso, bana tsammanin yin hakan." Yace." Aa ba haka nake nufi ba abinda nakeso ka fahinta shine kada ta dauki zafi kaima ka dauka, ka kai zuciyarka nesa ka rarrasheta kada ka biye mata idan ka kwantar da kai ina mai tabbatar maka da cewa fushin ba zai yi nisa ba." Shuru kawai yayi yana nazarin maganar.......Wani sa'in shi kansa mamakin kansa yake idan yana wani abu akan yarinyar ya rasa dalilin da ya sanya yake gudun bacin ranta, amma baya so ya sakankance ta gane lagonshi ta raina shi. shi yasa wasu lokutan yake mata jan ido. Da tarin yunwa da damuwa ya isa gidan. jiri da ciwon kai sun addaba masa! kai tsaye gurin Uwale ya nufa ya samu abinci yaci ya kwanta yana hutawa. Uwalen da kanta ta fuskanci bashi da lafiya....Tace." Ai ba kwanciya ya dace kayi ba asibiti za kaje a dubaka shine abinda ya dace." Idonsa a rufe yace." Kada ki damu ina so na huta tukkuna muna da likitoci na mussaman zan kira daya daga ciki ya dubani." Tace." To hakan shine dai-dai ai matar taka ma ai ta jima anan muna hira sai bayan la'asar ta shiga gurinta. Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Uwale me yasa kika shedawa yarinyar nan abunda yake faruwa."? Tace." Me yasa ba zan sheda mata ba Umaru ko kafiso mu tafi a haka ta samu labari a duniya tayi mana kallon mutanan banza." Yace." Ba nufina kenan ba, nafiso duk abinda zai faru a bari ta haihu tukkuna kinga tun bayan dawowarmu babu kwanciyar hankali, na san kuma dalilin jin wannan maganar ne." Tace." Umaru dole ne fa kayi hakuri da duk abunda zai biyo baya domin lusarin namiji baya ta'ba iya zama da mace biyu uku ko hudu, ka zama jarumi jajurtacce! akan duk abinda zai faru, bayan haka kuma ya zama dole ka jawa Hamra'u kunne ta kiyaye ta kuma sauya munanan d'abi'un da take yi kishi ai ba hauka bane." Ya kalleta da fadin." Me tayi Hamr'un."? Girgiza kanta tayi da fadin." Aa ni ba zan fada maka komai ba, amma lallai ka ja mata kunne akan abubuwan da take aikatawa." Ransa ya 'baci! idan ya fahimci maganar wato Hamra'u ta samu hanyar cin mutuncin matarsa saboda tana da tabbacin cewa ta kusa zama dai-dai da ita, wannan shine tunanin da yake, Hamra'u taki dawowa saboda akwai wani abu da tasan ta aikata na rashin kyautawa. sosai yayi mamakin al'amarin beyi tsammanin cewa zai samu matsala da yarinyar ba, saboda yana da tabbacin nutsuwa da hankalinta. Sai wajejan goma da wani abu ya shiga gurinta, lokacin ma ita har taci abinci tayi shirin kwanciya ba ta dai kwanta ba wayarta take dubawa. Yayi sallama ya shiga dakin kamar mara laka a jikinsa. Babu yabo babu fallasa ta amsa tana kallonsa har ya zauna kusa da ita.......Tace." Sannu ka dawo lafiya."? Wani sanyi ya sauka a zuciyarsa, sam bai tsammaci haka da gurinta ba. Da kwarin gwiwa yace." Lafiya ya kika wuni ya babyna."? Tayi shuru ba tace komai ba. Ya sake matsawa jikinta yana nanik'arta. ba tace komai ba, amma gabadaya tsigar jikinta ta tashi jinsa a kusa da ita yana nema ya haifar mata da matsala. Ya sassauta murya da fadin." My love ki kalleni za muyi magana ta fahimta." Ta jim na minti biyu kafin ta kalleshi. ya dinga sarrafa kwayoyin idonsa a kanta, gabadaya jikinta ya mutu, dama abinda ya keso kenan. Ya sauke sanyayyar ajiyar zuciya kafin ya lalubi hannunta ya rike cikin nashi, a hankali yace." Hamra'u bake taci mutunci ba, ni taciwa mutunci kuma dole na nuna mata muhimmancinki kiyi hakuri kinji ko." Murmushin takaici tayi kafin tace." Waye yace maka Hamra'u taci mutunci na."? Yace." Uwale ta sheda min abinda ya faru a tsakaninku kuma raina ya 'baci sosai wannan dalilin yasa na yanke shawarar kiran wayarta a gabana ta baki hakuri." Ta kalleshi tana so ta gazgata maganarsa, kamar gaske dai gashi nan yana mata dadin baki. Ya fito da wayarsa ya nemi number Hamra'un.....cikin ikon Allah wayar ta shiga ba'a samu matsalar network ba. Bai wani saki fuska ba ya amsa gaisuwarta kafin ya dora da fadin." Hamra'u abinda ki kayi ban ji dadi ba, kuma ba Gimbiya ki ka tozarta ba ni Umaru ki ka wulakanta sanin kanki ne cewa mutanan garin *Kafur!* muna da karrama bako da mutuntashi me zai sanya ki wulakanta min mata saboda kin ganta a mahaifarki." Murya na rawa ta fara rantse-rantse da fadin." Ya saurara tayi masa bayani.....'Kin sauraranta yayi yace." Mutukar kina so mu shirya da juna dole ki bata hakuri akan abinda