← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 97

Sashe 35

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fata kaga tabbatuwar al'amarin nan, to nima nayi maka alkawari zanyi iyakar bakin kokarina gurin ganin na zauna lafiya da yarinyar nan, kafi karfin komai a gurina, duk irin kin al'amarin nan da nake tunda ka shiga cikinsa dole nayi mubaya da kai da abunda kake so nagode sosai da sosai Allah ya saka da alkairi ya bar mana zumunci." Murmushi yay da fadin." Haba babu komai wannan ba wani abun damuwa bane, dama ni fatana ka yarda ka amince dari bisa dari da wannan auran, domin haka kawai nake maka sha'awar auran yarinyar duk da a zahiri kai ka nuna cewa ba irinta kake da bukata ba, wannan dalilin ba zai ha naka nan gaba ka auri wacce zuciyarka take so ba tunda kana da damar hakan, nagode sosai da yanda kake mutuntani kana kar'bar shawarwarina daga karshe nake sake yi maka fatan alkairi da samun zuria dayyiba." Cikin jin dadi ya amsa da ameeen ya rabbi Allah ya saka da alkairi mutumina." Cikin zolaya yace."Yanzu zan shiga cikin gidan domin samun dauko maka hoton amaryar taka ko baka da bukatar hakan."? Hannu yasa ya dan sosa sumar kanshi kafin yayi dan murmushi irin wanda ya saba, yace." Ina da bukata mana, ba kaji bahaushe yace."Amarya ko tabuzuzu ce tana rike da kambutan sarauta ba to ballantana ita wannan *GIMBIYA* ce mai lasisi wallahi haka kawai naji ina so nayi tozali da ita." Asp ya kyalkyala da dariya da fadin." Allah mutumina ai dama ni na san duk wannan abun da kake iya fatar baki ne kana son yarinyar nan kawai ba zaka fito fili ka nuna ba." Shima yana dariyar yace."Haka dai kake hasashe amma ni yar hanzu bana jin sonta a cikin zuciyata." Yace."Okey to shikkenan mu bar wannan maganar amma ni na san akwai ranar da tarihi zai maimaita kansa." Shuru yay bece komai ba har yanzu da kyakykyawan murmushi a fuskarsa sai wani sosa sumar kanshi yake kamar wani mara gaskiya. Asp din yace."Zan kashe waya zuwa an jima zaka ji ni." Yace."Okey to shikkenan babu damuwa sai na jika din." Sallama sukayi da juna kafin kowa ya kashe wayarsa. To a can gidan Uwale kuwa hayaniya ce kawai take tashi tun bayan dawowar mazan daga gurin daurin aure suka taru a gidan tare da sauran 'yan uwansu mata kowa na fadin albarkacin bakinsa. Da yawa daga cikinsu sun ji dadin kasancewar al'amarin, amma kuma akwai wa'inda suke ganin kamar hakan cin fuska ne da kuma rashin adalci idan akayi duba da irin halarcin da Hamra'u tayi masa bai cancanta ace saboda yayi arziki ya samu duniya ya juya mata baya ba, ita ya kamata ace ya fara aure kafin wata mace. Uwale da yake tana da hankali da tsinkaye ta dinga nusar dasu domin su fahimci cewa shi UMAR din bashi da laifi domin yarinyar bashi akayi ba wai don yayi arziki zai guji auran ita Hamra'un ba, kuma ya tabbatar mata da cewar zai auri ita Hamraun a matsayin matarsa ta biyu...........Duk da wannan bayanin da tayi musu hakan besa hankalinsu ya kwanta ba domin ita mahaifiyar Hamra'un ma kasa zama tayi a gidan rai a bace ta tattara 'ya'yanta suka tafi........'Bangaran Ita Hamra'un, abun babu dadi domin tun waye war garin ranar take kuka duk ta tsangwami kanta da kanta gani take kamar bukatarta ba zata biya ba , haka kawai take tsoron hada kishi da 'yar sarautar tun ganin farko da tayi mata jikinta yay sanyi! 'Kawarta Zabbah da tazo ta sake rikirkita ta da cewar had'a kishi da 'ya'yan sarauta bala'i ne domin basa barin kishiyarsu ta zauna lafiya babu wanda be san gidan sarauta da asire-asire ba, saboda haka dole itama sai ta tashi a tsaye mutukar tana so bukatarta ta biya. 'Bangaran uwar Hamra'un ma maganar da suke tattaunawa kenan da yar uwanta, inda suke zuga ta kan cewa lallai dole ta tashi a tsaye domin ganin 'yarta ta auri UMARU idan ya kama tabi malamai a kansa ba damuwa bace tunda duk wani abu da akayi masa shi ya janyo dalilin rashin adalcin da yayi musu, idan ba haka ba mai zai sanya yaje ya auri wata bayan kowa ya san abinda yake tsakaninsa da Hamra'u, ta bauta masa sosai ta kori duk masu neman auranta akansa, ta zauna zaman jiransa, rana tsaka saboda yayi arziki zai je ya auri 'yar sarauta, ya wulakanta yarinyar da tayi masa halarci, wannan dalilin yasa suke zugata kan cewa lallai ta nemi taimako a gurin malamai domin janyo hankalinsa, idan kuma ta zauna to tana ganin daula da jin dadi zasu wuce 'yarta wacce akayi gwagwarmar tare da ita. Sosai Dayyiba mahaifiyar Hamra'u ta dauki hudubar 'yan uwanta tasa a zuciyarta cewa gobe zakara ne zai bata sa'a yo ita da take a cikin garin Katsina to me zai gagareta, akwai malamai iri-iri wa'inda zasu taimaka mata, duk asirin da ake fadi cewa gidan sarauta suna dashi, to ita ta dauki alwashin bugawa dasu. Tofah!!! ***** Yayi ta tsumayin Asp din shuru be turo masa hotonan ba, agogon dake daure a hannunsa ya duba awa biyu kenan da wayarsu, ko wane irin hoto ne yaci ace an dauka ya turo masa haka kawai ya 'kagauta ya kalli kwalliyar amaryar tasa. Number sa ya nemo ya kira cike daso ya daga wayar, sai duk 'kagautarsa bai samu abunda yake so ba, domin wayar haka ta k'araci 'burari Asp din be daga ba. 'Karamin tsaki yaja tare da dan ya mutse fuskarsa, ya ga alama fa zuciyarsa ta nema ta takura masa. Ajiya wayar yayi, ya dauki d'ayar dake saman drowar yana kunnawa ya shiga WhatsApp number tace kawai data Asp a layin. Ya duba status Asp ya dora hotonan daurin auran........Jama'a birjik babu masaka tsinke harabar gidan sarautar cike da jama'a, murmushi kawai yake yana cigaba da duba status din.......... Kowa ya halarci daurin auran a cikin abokan aikinsa da 'yan uwansa da kuma yaransa su Alba da sauransu. hoton karshe shine Maimartaba Omar tare da maigirma Governor katsina wato Nasiru Alkanawi dashi Asp din da kuma mutuminshi abokin fad'ansa wato Commissioner of police wato Murtala Kabiru, serving din hoton yay a ajiye a gallery hoton yayi masa kyau sosai. Yana k'okarin sauka sak'on ta ya shigo, da sauri ya shiga yana dubawa hotonta ne kusan goma ta turo masa. Ya dinga duba hotonan d'aya bayan d'aya yana jin wani bala'in kishi na sukan zuciyarsa. A zahiri dai shi ta turowa hotonan, amma a cikin rashin sanin ta, sai kawai ya tsinci kansa da jin haushin kansa da kuma kishin kansa da kansa. A zahiri shi ya kamata ace ta turowa hotonan a matsayinsa na miji a gareta. amma ta turawa wani wanda bata da tabbas a kansa, wannan ya nuna masa cewa zata iya aikata komai bayan da auransa a kanta. Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya dauki daya daga cikin hoton nan data turo masa yay magana a kansa. "Wannan hoton yayi kyau sosai my love kallonki a yanzu ya jefe ni cikin wani hali mai wuyar fassaruwa, gabadaya kin gama kashe min jikina ina jin sha'awar kasancewa dake a halin yanzu, my lov ina kishin wannan mijin naki kada ki bari ya kusanceki ballantana wata mu'amula ta shiga tsakaninku, ki rike min amanar kanki." Koda ya tura mata sakon be sauka ba har sai data ta duba, ba tace masa komai ba sai emoji data tura masa mai dauke da alamar kuka da ban hakuri.....Daga haka sai kawai ta sauka, Cikin jin haushin abinda tayi ya kashe wayar ya ajiye yana nazari da tunani akan al'amarinta. Kiran sallar la'asar ne ya katse tunaninshi, da sauri ya tashi ya nufi toliet domin daura alwala. koda ya fito daga bandakin kai tsaye masjid ya nufa wanda yake cikin barrack din da suke zaune........Da yawa daga cikinsu arna ne musulman cikinsu kadan ne, amma duk da hakan akwai kyakykyawar alaka a tsakaninsu domin tsayin kwanakin da yayi tare dasu bai ta'ba samun matsala da kowa ba. Bayan fitowarsu daga masjid din Adewale abokin aikinsa wanda ta su tazo daya ya tsare shi da hira, hakan ya zauna ya biye masa yana ta bashi labarin ban dariya cikin harshan turanci yake magana domin hausar tashi bata fita sosai. Kwanakin da yayi a cikinsu gami fa cud'anyarsa dasu yasa kwakwalwarsa ta kara bud'ewa dama can sama-sama yana jin turacin amma ba kamar yanzu ba, ya na ji sosai kuma idan ta kama yana sauya harshe yayi magana tamkar wanda ya jima a cikinsa. Adewale mutum ne mai barkwanci shiyasa tasu tazo d'aya duk sanda basu da aiki sukan zauna guri daya yay ta sauraran shiremansa yay ta kyalkyala dariya kamar bashi ba. Kiran Asp ne ya shigo wayarsa yasa a kunne tare da sallama Asp din yace. "Ka duba tuntuni na tura maka sakon." Yace."Okey to ina godiya sosai naje sallah shine dalili." Yace."Ba damuwa yanzu Ina shirye-shiryen d'auko hanya amma ina tsammanin jirgi zamu bi." Yace." Saboda me? zaku bi jirgi ina Kano ina Katsina ? da har sai kun shiga jirgi." Yace." Wannan amaryar tamu ai daban take da sauran mata, idan da akwai abunda yafi jirgi to a ciki zan kawo maka ita har Katsina." Yayi yar dariya da fadin." Kana d'aurewa karya gindi wallahi, amarya babu ango a kusa ina tausaya mata kwanan kad'aici." Asp din yay dariya sosai kafin yace."Ka fara tausayawa kanka kafin ka tausaya mata dukkaninku ababan tausayi ne." 'Yar dariya yay irin wacce ya saba da fadin'' Na yarda da maganarka amma ka mi'ka min sak'on gaisuwata a gurinta ka sheda mata cewa daga yau ta fara lissafin dawowata." Yace."Wannan kuma aikin ka ne, domin saura kadan na kammala nawa, sauran kuma ya rage naka." Kokarin magana yake Asp din ya kashe wayar Ya cire wayar daga kunnansa yana murmushin da har yanzu ya rasa na menene. Yana duba hoton nan Adewale ya leko da kansa. Da sauri ya janye wayar don haka kawai yake jin kishin wani ya ga kwalliyarta.........duk da hakan sai da ya hangota, ya kyakyala da dariya yana sake le'ka kansa da fadin."Oga wannan yarinyar fa tana da kyau sosai ina san 'bakar mace domin tana da wani sirri na daban." Wani irin kallo yay masa mai kama da harara
Chapter 35 · 0% Book details