Sashe 33
Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
a gurina wallahi jinka nake tamkar wanda muka fito ciki d'aya Allah ya kawar da idon makiya a tsakanimu." Ya amsa da "Ameen ya Allah, kafin suyi sallama da juna. ***** To a daran ranar da sukayi wannan tattaunawar da Asp din ya yanke wata shawara wacce yake ganin zata taimaka masa gurin tantance nagarta da kamun kan yarinyar........ da yake yana amfani da layin waya biyu sai yayi amfani da d'aya layin da ba kowa ya san shi dashi ba, wata irin rikitacciyar wasika ya tura mata mai dauke da zafafan kalaman soyayya da tsuma zuciya, sosai yayi amfani da hikima gurin shirya kalaman wanda yake da tabbacin cewa dole su rikirkita mata lissafi, bai fayyace mata kansa ba asali ma babu suna a wasikar yana tura mata ta in box ya cire sim card din ajiyeshi cikin cover shi sai an kwana biyu zai mayar. Kamar yanda yayi tsammani hakan ne ya faru, domin tunda ta karanta wannan text din gabadaya ta rikice ta rasa abinda yake mata dad'i a duniya, macace mai bala'in son soyayya da kulawa shiyasa kullum cikin kallon indian film take amma irin na soyayya, tana bala'in san wanda kullum zai dinga kasheta da kalamai yana rarrashinta ita kuma tana masa shagwaba da sangarta irin yanda take so, kasa hakuri tayi tabi layin da kira, sai dai ta kisa sau goma ana ce mata layin baya aiki a halin yanzu, hawaye masu zafi ta share tana tunanin daga wace duniya sakon wasikar yazo gareta? wanene wannan wanda yake da kalamai irin haka? shin a ina ma ya samu number ta, hakika zata so ganin sa ido duk talaucinsa zata iya zama dashi mutukar zai dinga lallabata yana bata abincin zuciya irin wanda take bukata. Hanci taja tasa hannu ta goge hawayen dake karakaina a saman fuskarta, me za tayi da wancan ba 'kauyen mutumin da be iya komai ba sai 'bakar maganar magana, tunda take dashi bai ta'ba yi mata kalami mai dadi ba, ko a lokacin zaman su a daji ta lura kan dole yake rarrashinta idan wata masiba ta sameta, a halin yanzu ya kamata ace ya kwantar mata da hankali domin samun soyayyarta amma saboda girman kai ya kasa duk sanda zaiyi mata magana cikin gadara! da isa! shi ba kowa ba sai iko yake nuna mata ita kam ba zata yarda da wannan ba, tunda dai a zahiri tana ganin ta fishi da komai ba zata yarda ya mulke ta ba har yanzu tana nan akan bakanta ko auran sukayi. Kullum sai ta gwada kiran layin sai ace mata baya aiki, duk ta susuce! tunaninta ya kammanin mutumin yake? ba abunda take so taji sai muryarsa. A na gobe daurin auran da daddare kowa yai bacci ta gwada kiran layin, jin yana shiga yasa ta tashi zaune da saurin gaske farin ciki gabadaya ya cika mata zuciya burinta kawai ya daga wayar taji sautin muryarsa..... *Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya kema keda Allah!* *#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE* 2/2/22, 18:21 - Buhainat: *49&50* Cikin wata murya mai sanyi da ita kanta bata san tana da ita ba tayi sallama kafin ta dan lumshe idonta tare da sauke ajiyar zuciya tace." ina so na san da wanda nake magana a halin yanzu." Shuru yayi bece uffan ba, gabad'aya mamaki ya gama kashe shi jin irin salon da take masa magana ashe ta iya tausa murya haka. Shuru be ce mata komai sai saukar numfashinsa da takeji a kunnawanta. sai gabadaya jikinta ya sake rikicewa, haka kawai Allah ya jarabce da son wanda bata ta'ba gani ba. Cikin 'yar shagwaba tace." Please don Allah waye ne? kwana biyu da suka wuce naga text dinka shine dalilin da yasa ma na kira ka domin san kowaye kai ." Idonsa a lumshe yayi d'an gyaran murya kamar zai yi magana sai kuma yaja bakinsa yay shuru, gabadaya ta gama kashe masa jiki da salon da take masa magana yana masifar son shagwabbiyar mace. Jin yayi shuru ta sake narkar da murya dan a zahiri saura kadan ta fashe da kuka tace." Ba za kayi min magana ba ko? ka san kuwa halin da ka jefa zuciyata."? Zaune ya tashi yana sake rike wayar a kunnunsa, kafin ya aro wata murya da duk bin diddigin mutum ba zai gane muryarsa bace yace." Wani bawan Allah ne yazo da kokan baran shi a k'urataccan lokaci." Jikinta ya 'kara saki jin sanyayyiyar muryarsa ya jefa ta cikin wani yanayi mai wuyar fassaruwa, tace." Kayi min bayanin kanka daga ina kake kuma ina ka samu number ta."? Dan murmushi yay kafin yace." Sunana FARUK ni dan asalin hajar katsina ne." Gabanta yay fadi jin ya ambaci garinsu ma'kiyinta. Jin tayi shuru ba tace komai ba ya cigaba da cewa." Na tsinci hotonki a social media gurin wani biki sai kawai Allah ya jarabceni da tsananin sonki da kaunarki, talaka ne ni amma ina da zuciyar nema, duk da na san cewa ke ba tsaran aure na bace, hakan bai sa na saduda ba sai da nayi fafutukar samun number ki, amma wanda ya bani number ya sheda min cewa aure za kiyi hakan be firgitani ba, tunda dai ba'a daura auran ba zan fito na nuna miki tawa soyayyar da take gudana a cikin jikina." Tun sanda ya fara maganar take share hawaye, tayi duk yanda za tayi ta tsayar da kukan abun ya fassakara, tana kukan tace." Kazo a 'kurataccen lokaci bawan Allah, sosai nake son mai sona kuma ina alfahari da soyayyarka, hakika da kazo a kan ga'bar da iyayena suka yanke min hukunci to babu shakka kai zan nuna musu a matsayin mijin aure, babu ruwana da talaucinka mutukar zaka bani abincin zuciyata bani da damuwa, yanzu maganar da nake maka gobe za'a daura min aure da wani wanda bana ra'ayinsa." Cikin wani irin kuka mara sauti takarashe maganar. Jikinsa ne ya mutu jin kukanta yake har tsakiyar kansa, Cikin taushin murya da sigar rarrashi yace." Yi shuru ki daina kuka kinji ko wannan kukan da ki ke yana ta'ba min zuciyata ina jin kamar nazo inda kike na rarrasheki bana son zubar hawayenki. Hannu tasa ta goge hawayen amma ba tace komai ba. Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace." Yanzu ya za kiyi dani da soyayyata Gimbiyata bana jin zan iya rabuwa dake fa.'' A sanyaye tace." Nima bana tunanin hakan a zuciyata, ka bari a kwana biyu zan yanke shawara akan soyayyarmu." Murmushin takaici yay kafin yace." Okey na fahimta yanzu zamu cigaba da gaisawa ne ta waya babu matsala hakan."? Shuru tai na minti biyu kafin tace." Babu matsala amma ka bari ni zan dinga kiran ka" 'Yar dariya yay da fadin." Shikkenan my love yanda ki ke so hakan za'ayi amma inaso muna gaisawa koda ta charting ne." Ba tare da damuwar komai tace."Wannan babu damuwa zanyi serving number naka yanzu." Yace."To ina godiya my princess bari na barki ki kwanta ki huta ko, amma ina tabbatar miki da cewa yau ba zan iya rintsawa ba." Da sauri tace."Saboda me."? Cikin tausayawa kansaYace. " Saboda gobe za'a daura miki aure da wani." 'Karamin tsaki taja kafin tace." Ka kwanta kayi barcin ka, kada kasa damuwar komai a ranka domin wanda za'a daura min aure dashi, bashi da wani muhimmanci a zuciyata, bana sonsa bana ra'ayinsa, da auransa da babu duk daya suke a gurina, ka kwantar da hankalinka nayi maka alkawari kai zaka mallake ni, domin da kai zuciyata ta aminta duk da ban ta'ba ganinka ba ina hasaso fuskarka a idona, ina sonka a duk yanda kake, zanyi mana duk wani kokari da zai tabbatar mana da biyan bukatarmu." Yaji haushi da takaicin maganarta amma sai ya danne a zahiri ya nuna mata farin cikinsa, sallama yay mata da jin zafin maganganunta a zuciyarsa ya kashe wayar yana tsaki da fadin." Sakarai mara wayo kawai." Kwanciya yay yana tunaninta, gabadaya ma ya raina wayonta da dubararta, koda yake macace mai rauni zata iya yin abinda yafi haka. Agogon ya d'an duba, yanzu minti talatin kenan da wayarsu, ya kama sha daya dai-dai na dare, yanzu da Asalin number shi ya kira ta. Sai da ta kusa katsewa sannan ta dauka tana cin magani, wayar tasa a kunne amma ba tace komai ba. Yay mata sallama cikin asalin muryarsa mai cike da amo!! Ciki-ciki ta amsa tana ya mutse fuska. Yace." Tun dazu nake kiran wayarki sai ace dani busy shin dawa kike waya a cikin wannan daran."? Cikin tsiwa da gadara irin yanda take masa magana tace." Ina ruwanka da wanda nake waye? ko kana da damuwa da hakan ne."? Daurewa yay yace." Ni nake da damuwa da hakan kuwa, dalilina kuwa nasan baki nutsuwa da kamun kai zaki iya raba dare da wani namijin a waya saboda rashin kintsi." Zuciyarta ta dinga wani irin zafi da tukukin bakin ciki! Abinda yake had'ata dashi kenan bakar magana, kwata-kwata be iya rarrashin mace ba, haka kawai zai tayar mata da hankali tana zaman zaman ta. Murya na rawa kamar me shirin fashewa da kuka tace." Bagidaje kawai kana da matsala wallahi, haka kawai zaka shiga rayuwata cikin daran nan to ta Allah bata ka ba" Yay dariyar cusa takaici yace." Naji bagidajen ne dole kuma a zauna dani a haka na kuma bada umarni ayi ko ana so ko ba'a so."! Tsaki mai tsayi taja irin wanda ta san baya so tace." Wahalalle kawai bani da lokacinka." Da sauri ta kashe wayarta domin bata so ta sake jin sautin muryarsa! Bacci k'auracewa idonta yay ta dinga zubar da hawaye tana tunanin boyayyan masoyinta daya bayyana mata kansa a yau..........Shin wai ya za tayi da wannan takad'irin mutumin da ake kokarin aura mata bayan be tara duk abunda take da bukata ba. Haka ta kasance cikin tsananin damuwa gami da juye-juye sai gefin asubah bacci mai nauyi ya d'aukata. Shigar aunty Hassana dakin yayi daidai da bude idonta gari ya waye tarwai. Zaune ta mike tana dan ya mutse fuska! wani irin ciwo kanta yake ba komai ya janyo mata hakan ba illah kwanan kuka da tunanin da tayi. A nutse ta