← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 97

Sashe 47

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

take dasu tun bayan saukarsu a gidan. Shima Umar din yaji dadin hakan, domin da babu ita to tabbas za'a ji kunya idan akayi duba da irin kalar matar gidan, wanda a tunaninsa nauyin kula da 'yan uwansa yana wuyanta. Sashensa ya nufa domin barin su suka karya a tsanake. Dama bai tsammaci samunta a sashen ba, ya kalli agogon dake kafe a dakin tara saura na safe.......Jalliyar jikinsa ya cire ya zauna gefan gado daga shi sai gajeran wando. Wayoyinsa dake ajiye kan bedside ya dauka duka ya kunnasu..............tarin messages da suke kan wayar ya fara dubawa, kafin yaji shigowar wani messenge din a daya wayar. Da sauri ya dauka domin yana tsammanin message din daga gurin ta ne dalili number ta ce kawai akan wayar sai ta Asp Aikuwa itace take bashi amsar text din sa na jiya. _" FARUK Kayi hakuri tun jiya ka turo min sako babu replay sai yanzu, kada ka samu damuwa nayi maka alkawarin kare maka kaina, kuma duk rintsi ba zan bari wani abu ya ratsa a tsakaninmu ba ni taka ce har abada."_ Ya karanta text din ya kai sau biyar, yana nazari da tunanin kalamanta........Murmushi kawai yay yana mamakin al'amarin, ba zata bari wani abu ya ratsa tsakaninsu ba, amma mai yasa jiya ta kasa sarrafa kanta sai yanda yayi da ita, aka ce wai maza sun fi iya yaudara to yau ya 'karyata wannan magana domin ga yaudara nan kiri-kiri yana gani, be yarda da soyayyar da takewa boyayyan masoyin nata ba.....Ba tare da ya bata amsa ba ya ajiye wayar, ya cigaba da duba mai muhimmancin. A nutse ta shigo da sallama a bakinta, shuru falon, da alama yana daki, saman daninig ta ajiye kwandon abincin dake hannuna. Tayi jim! tana dan tunani kafin ta yanke shawarar buga kofar dakin nasa. Yana jin bugun ya tsammaci yarinyar ce, be so hakan ba, saboda yana gujewa abunda ka iya zuwa ya dawo. Jallabiyarsa yasa kafin ya bude mata kofar. Ya dan saki fuskarsa tare da kiran sunanta. Farin cikin ganinsa ya cika mata zuciya, wani irin kallo tai masa kafin ta amsa da fadin." Barka da asubah Farin cikin zuciyata." Ya amsa da "Barka dai fatan kin tashi lafiya."? Ta dan girgiza kai da fadin." Lafiya lau amma kwana nayi ina mafarkin ka." Murmushi yayi yana mata wani irin duba, kafin bakinsa ya subce gurin fadin." Nima haka da kyar na iya rintsawa saboda tunaninki." Taji wani irin sanyin dadi a ranta, tace." Nagode sosai masoyina ga abun kari na kawo maka, sannan ina so na gyara maka dakin ka." Yace." Okey to godiya nake my love Allah yay miki albarka." Ta amsa da "Ameen tana kokarin shiga dakin ya bata hanya yana bin bayanta da kallo, yarinyar tausayi take bashi mutuka, ta jima tana dawainiya dashi da kakarsa babu shakka idan bai aureta ba yayi butulci, nagartaciyyar macace irin wacce take da wahalar samu, dole ya cika muradin zuciyarsa. Tana tsaka da karkad'e bedshirt din breziyya ta fad'o kasan kafafunta.........Gabanta ne yayi mugun fad'uwa, lokaci guda kafafunta suka shiga karkarwa! Jiki a mace ta tsirawa breziyyar ido tana tunanin wani abu..............Wato daga dawowarsa har wata mu'amula ta shiga tsakaninsu? shin ina 'kiyayyar da sukewa junansu take? wasu zafafan hawaye ne suka k'wace mata tana gogewa wasu na zubowa, wani mugun kishi ne ya dinga yun'kuro mata, ta dinga ji kamar ta dora hannu aka ta dinga zabga ihu! ko ta taji sassaucin abinda take ji a cikin ranta. Sosai take kuka sai kace wacce uwarta ta mutu! mugun haushin gimbiyar take idan akwai wacce ta tsana a duniya to itace. Ta gama gyara dakin cikin halin ni 'yasu kafin ta kama hanyar toilet tana had'a hanya kamar wata 'yar maye, Wai UMAR din ta masoyinta shine ya fara mu'amula da wata mace ba ita ba. Tana shiga toilet din taci tuntunbe da pant a k'asan ties, da sauri ta janye kafarta, gabanta ne ya tsananta fad'uwa, ta jingina jikin bango(garu) idonta kuri kan pant din tana ayyanawa abubuwa da yawa a cikin ranta Da tasan mugun ganin da za tayi kenan da ba tayi sha'awar shigowa dakin ba. Wani nannauyen abu yazo ya tsaya mata a wuya, ganin pant da breziyya ya gama kashe karsashinta, al'amarin ya bata mamaki mutuk'a sam bata kawo cewa wani abu zai shiga tsakaninsu a kusa ba. Kafarta tasa ta ture pant din, cikin rashin kuzari da kunar zuciya ta gyara toilet din ta fito zuciyarta dankare da kishin gimbiyar ji take kamar taje ta shake mata wuya saboda yanda take jin wani bala'in haushinta a cikin ranta. Tana fitowa suka hada ido yana zaune a daining yana karyawa, kallonta yake yana mamakin yanda idonta yayi ja! da alamun kuka a tare da ita Kasa had'a ido tayi dashi ba tare da tace masa komai ba ta kama hanyar fita. Cokalin dake hannunsa ya ajiye ya kira sunanta. Tsayawa tayi amma bata juyo ba. Yace."Me ya sami idonki sunyi jawur! domin ba haka kika shigo." Kamar me jiran kiris sai kawai ta fashe da kuka kariris! al'amarin ya bashi mamaki mutuka gaya! ya mike da niyyar zuwa inda take, a gaggauce ta bude kofa ta fita tana share hawaye. Sai kawai yayi tsaye a tsakiyar falon yana mamakin al'amarin. Da yake sun shagala da hira a tsakaninsu babu wanda ya lura da shigowarta sai Ladidi wacce ta kasance 'yar uwa Dayyiba wato mahaifiyarta.............Itace ta lura da shigowarta. Sai kawai ta tashi ta bi bayanta dakin, ta sameta tana kuka! Zama tayi kusa da ita tana tambayarta, sai kawai ta rungumeta cikin kuka tace." Ladidi na rasa ya zanyi da rayuwata Umaru yana wahalar da zuciyata gani nake kamar yaudarata yake tunda ya auri 'yar sarauta ba zai aureni ba. Hannu tasa tana share mata hawaye tace." Hamra'u mu ma tunanin da muke kenan, muna ganin kamar wannan yaro wasa yake mana da hankali domin idan da wacce ya kamata ya aura kece duba da irin hallacin da ki kayi masa, amma saboda rashin adalci lokaci guda muka samu labarin auransa da 'yar sarki, da muka fito muna magana kakarsa ta goya masa baya cewa ai bashi yarinyar akayi ba a son ranshi ba ya aureta ba idan gaskiya ne al'amarin me yasa ba'a had'a auran a lokaci daya ba, kakarsa Uwale ba taso ya aureki ba domin da taso ya aureki da tuntuni anyi angama idan ma haihuwa ce da tuni kin haihu, amma babu komai, akwai hanyoyin da zamu bi domin biyan bukatarmu domin ba zamu bar wannan daular ta wuce mu ba." Tana sauke ajiyar zuciya tace." Ladidi wannan al'amarin dole sai an nemi taimako don ganin tabbatuwarsa ki shed'awa Inna ta duk abunda yake faruwa domin a yanzu babban burina naga na mallaki Umar a matsayin mijina uban 'ya'yana." Tace." Kada ki damu daga zarar mun isa gida zanje na sheda mata duk abunda yake faruwa dole sai ta tashi a tsaye domin idan lamari irin wannan ya tunkari mutum ba zama zai yi ba sai ya tashi ya nemi taimako daga gurin Malamai." *(Subahanallahi Allah kasa mufi karfin zukatanmu, Allah kada kasa mu gaza gurin neman biyan bukata a gurinka, Allah ka sanya mana imani a zuciyarmu*) Yana kokarin fitowa daga part din shi Asp ya kira shi, ya sanya wayar a kunnanshi da sallama a bakinsa, Asp ya amsa yana 'yar dariya shima dariyar yay kafin su gaisa cikin girmama juna, Yace." Ya kwanan amarya."? Murmushi yayi tare da d'an sosa gemunsa yace." Ta nan lafiya yanzu zan shiga gurinta yanzu." Yace ." A'a ban gane ba, kana nufin kace min ba tare kuka kwana ba"? Yace." Tare muka kwana da asubah ta gudu." 'Yar dariya yay da fadin." Taji maza kenan shiyasa ta tsere kai kuma ai kayi gaggawa." Dariya yay kafin yace." Kai fa kake min fada na gyara kuskurana kuma nayi mata kalamai na soyayya ta bada kai a garin hakan na kasa daurewa kawai na ragewa kaina zafi." Cike da jin dadin faruwar al'amarin yace." Alhamdulillhi nayi farin ciki da jin hakan, wannan shine mataki na farko da zai sa ku sasanta kanku, Allah ya baku zaman lafiya da zuria dayyiba." Ya amsa da "ameen suma ameen mutumin kirki nagode kwarai da karamci." Yace." Babu komai Umar mun riga mun zama daya da juna idan ka shiga ka mika min gaisuwa gurin amaryar." Yace." Za taji insha Allah." Sallama sukayi cikin mutunci da mutuntawa. *Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya ba kema keda Allah!* *#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE* 2/16/22, 16:16 - Binta: *69&70* Tun lokacin da Kawu Ado ya fara magana yake girgiza kai yana mamakin al'amarin, koda yake ba abin mamaki bane idan akayi duba da irin rashin tarbiyar yarinyar, zagi da cin mutumcin d'an adam abune mai sauki a gurinta, sosai ransa ya 'baci da irin tozarcin da tayi wa 'yan uwansa dama abinda yake gudu kenan, yana k'aunar family nasa gaba da baya duk talaucinsu da rashin wayewar su shi ba zai k'yamace su ba tunda sune k'ashin bayan samar dashi, sannan tare dasu yayi rayuwa saboda haka ba zai zama wani abu a duniya ya wofintar dasu ba, dole ya nuna mata muhimmancin 'yan uwansa domin a gaba ta kiyaye. Kawu Ado ya sauke numfashi da fadin." Saboda haka Umaru mu ba zamu ce ka rabu da yarinyar nan ba, taci albarkacin mahaifinta, amma tilas ka auri wacce tasan kima da mutunci da darajar mu, ina nufin yarinyar nan Hamra'u itace wacce ya dace ka aura tun kafin zuwan wannan al'amari, saboda haka wannan ba shawara nake baka ba umarni ne a matsayina na wanda ya isa ya fada maka magana kaji, idan kuma ban isa ba to sai na cire hannuna daga kanka." Ajiyar zuciya mai zafi ya sauke kafin yace." Kawu ka isa ka zartar da ko wane irin hukunci a kaina domin a yanzu bani da kowa sai kai sai kuma Uwale tare da sauran 'yan uwana ina alfahari daku mutuka, kuma ya zama dole na sanya kafar wando guda ga duk wanda yayi nufin tozarta ku, kamar yanda ka bani umarnin auran Hamra'u dama da wannan
Chapter 47 · 0% Book details