Sashe 91
Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yayi sanyi kuma ta tausayawa Hamra'un. Suna tsaka da hira Madam da Nabila sukayi sallama. Cikin sakin fuska ta amsa ta mike domin girmamawa. gurun zama take nuna mata, ita kuwa aunty Zeey din kamar wacce aka aikowa da mutuwar iyayenta, muraran ta fito da bacin ranta da kishinta. Madam wayayyar macace mai ilimi da sanin ya kamata, ta kalleta da fadin." Zainab kina nan kenan."? Ta dauke kai da fadin." Aikuwa." Murmushi tayi kafin ta juya tana amsa gaisuwar da Zinat ke mata, a mutunce suka gaisa Madam tayi mata gaisuwa daman abinda ya kawota gidan kenan. Aunty baki a tabe ta kalli Nabila da fadin." Ke kuma kin isa kenan babu wanda yake da mutuncin samun gaisuwarki a cikinmu. Tace." Haba dai Aunty Wallahi ina ta gaisheki ba kiji ba sai nace bari ku gama gaishe-gaishe sai mu gaisa a nutse. K'aramin tsaki taja ta kawar da kanta. Itama Nabilan taji takaicin abinda tayi mata amma sai ta daure ta sake gaisheta, ta amsa kamar bata so. Ta juya ta gaishe da Zinat din tare dayi mata gaisuwa. ta amsa a sake da nunawa kulawa. Ba su wani zauna ba suka suka tashi da niyyar tafiya, har bakin kofa ta rakasu tana godiya. Tana juyowa suka hada ido da Zeey sai harararta take, taja tsaki mai karfi kafin tace." Wannan matar kike wa ladabi matsiyaciya sumu-sumu macijin sari ka noke. Ta zauna kujerar dake fuskantarta tace." Aunty zeey me yasa kike zagin Madam ne? wallahi ni duk laifinta da kike fadi ba tayi min komai ba. Tace." Dama yaushe za tayi miki tunda baku hada miji ba, matsiyaciya ai gashinan tana zaune da god'amemiyar 'yarta taki auruwa, babu mashinshini." Cike da mamaki tace." Aa kamar an sa ranar auranta. Tsaki taja da fadin." A bakin wa ki kaji babu wani mai so bakin jinine da ita. Yar dariya tayi kafin tace." A bakin maigidana naji cewar dashi aka karbi kudin auranta an sanya shekara guda. Aunty Zeey jikinta yayi sanyi ta zuba mata ido da mamaki a tare da ita. Tace." Wallahi kuwa kin san abinda yayi Asp shi yayi mijina shiyasa na samu labari. Tace." Aikin banza to meye abin rufa-rufa dan ya fito ya fada min wani abune mtwwws! ni na rasa me yake damun Asp wallahi matar nan gabad'aya ta shanye shi sai abinda tace masa..... *Kada ki karanta min littafi idan baki biya, kada ki siya ki fita dashi, 'Yar uwa kada ki ganshi a group kiyi shearing domin hakkina ne, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne.....0542382124...Binta umar gtbank. idan kati zaki turo sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number* *07084653262* *BINTA UMAR ABBALE* 5/10/22, 13:59 - Binta: _Akwai ingantaccan maganin gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ _*(Uwace ita a gurina kuma 'Yar uwa ce, ina jin ita din kamar 'yar uwa ta ta jini, ta damu da damuwata ta kasance kullum mai min addua da fatan alkairi, na rasa a wane matsayi zan ajiyata a zuciyata, tana kira na da Mamana, ni kuma ina kiranta da Daughter, dalilin rubutuna muka hadu, tsayin shekaru hudu muna tare abin farin cikin kuma muna gari d'aya, Daughter ZAINAB KHABIR ISHAK koda nisan in da kike ya kai birnin sin sai nayi fatan Ubangiji Allah ya sadamu da juna, to ballanatana muna cikin gari daya, wannan zumuncin zai cigaba da wanzuwa da ikon ALLAH. na jinjina miki k'warai Allah ya saka da alkairi *129* Cikin nazari take kallonta tana auna maganganunta, ba tun yau ba ta lura da cewar tana da masifar kishi irin wanda ba a so, to idan ba hakaba meye laifin Madam mace mai mutunci da sanin ya kamata, a ganinta idan haka duk kishiyoyi suke to babu shakka za'a samu maslaha a zamantakewa, amma Zeey ta tsawwala da yawa, tunda suke da Madam bata ta'ba zagin Zeey ko ta fadi wata mummunar kalma a kanta ba, amma ita a koda yaushe cikin zagin matar take. Ajiyar zuciya ta sauke tace." Zeey ki sanyawa zuciyarki salama don Allah kiyi tsaftataccen kishi, ba wai ina goyan bayan Madam bane amma a ganina kamar bata da matsala da zakiyi hakuri to babu shakka zaku zauna lafiya." Tsaki taja da fadin." Na lura dai tsakaninmu babu amana fuska biyu gareki Zinat idan ba haka ba mai zai sanya a gabana kina goyan bayan mutsiyaciyar matar nan da kowa ya san da cewa mutuniyar banza ce wacce babu abinda tasa a gaba sai bin bokaye da zinace-zinace duk domin biyan bukatarta." cikin masifa da kumfar baki take maganar. Ita dai tsabar mamaki kasa cewa komai tayi, kawai ta dinga kallonta tana jimanta al'amarin. Tana cigaba da zagin Madam din ta lalubi mayafinta ta yafa, ta mike da fadin." Ni nayi nan ai yau na fahimci inda kika nufa kuma." Ta mike da fadin." wallahi Zeey baki da fahimta itafa rayuwa gabadaya hakuri ake da ita, amma duk kin bi kin tayar da hankalinki sai zage-zage kike akan kishiya wacce bata damu dake ba, ta mayar dake shashasha wallahi kiyi gaggawar gyarawa." Ta watsa mata kallo mai muni kafin taja wani dogon tsaki fuuuuu! ta kama hanyar fita tana surutai marasa ma'ana. Baki a bud'e ta bita da kallo har ta fita daga falon, girgiza kai tayi tana mamakin al'amarin, tabbas an san kishi halak ne amma a ganinta irin nasu aunty Zeey din ya sa'bawa sharia domin kuwa zuciya za ta sanya su aikata abinda ba shikkenan ba. Ita dai zata cigaba da hakurin zama da Hamra'u tunda dai Allah yasa yarinyar ta gane gaskiya to sai suyi hakurin zama da juna. *BAYAN WATA UKU* Zaman lafiya da daidaito yake wanzuwa a gidan tun bayan dawowar Hamra'u babu wata matsala data sake faruwa, kowacce na kokarin kyautatawa 'yar uwarta hakan yayi wa Uwale dadi, sai dai kuma shi daga b'angaran uban gayyar babu wanda ya san abinda yake cikin zuciyarsa sai Allah sai kuma shi, amma yana bala'in jin haushin had'e masa kai da sukayi, idan Zinatu tayi magana a gidan to ta zauna, duk yanda yaso ya ruguza alakarsu ya kasa, a yanzu Hamra'u tafi jin maganar Zinatu a kan tashi maganar, babban takaicinsa kenan, zai bada umarni ayi abu amma idan ya dawo gidan sai ya tarar ba'ayi ba. Hamra'u cikinta wata bakwai ta gaza komai ta lanjare abinka da mara jiki, cikin har rinjayarta yake saboda girmansa, anyi scanning an tabbatar da cewa twins 'yan biyu ne duk mata, wannan dalilin yasa likita ya kafa mata dokoki, wannan bai dameta ba tunda akwai kyakykyawar fahimta a tsakaninsu, gabadaya ta tattara mijin ta barshi a gurin Zinatu......Hakan yayi masa dadi mutuka, amma bai nuna ba, sai ma ya fara wasu irin zantuka domin neman magana da tada zaune tsaye. Cike da mamaki ta kalleshi bayan ya gama maganganunsa. "Ta nan ka bullo kuma."? Ta fada tana masa kallo na rashin fahimta. Yace." Eh kwarai kuwa ai gaskiya ce, gabadaya kin tattara komai kina zalintar 'yar mutane duk abinda ki kace shi za'ayi idan kina tursasa Hamra'u to ni baki isa ba."! Cike da karsashi da kwarin gwiwa yake maganar. Ta danne bacin ranta dalili ba taso suyi hayaniya hakan babu amfani, amma ta lura kwana biyu neman masifa yake da ita. "Kai yanzu dan Allah ba kaji kunyar fadin wannan maganar ba."? Shuru yay mata yana duba wayarsa. Ta girgiza kai cikin 'kunar zuciya tace." Ka tashi ka tafi dakin nata ai ba rike maka kafafu nayi ba, domin bani na gayyatoka ba." "Ba za'a tashi ba." ya fada yana watsa mata harara! Ta daga masa hannu da fadin." To tunda abun ya kasance haka kaje can ku yanke shawara da matarka, amma kada ka kara shigo min daki ranar girkinta." "Kin riga kin lalata min ita yaushe zanyi magana taji ta saurara." Ta dinga kallonsa da mamakin furucinsa ta rasa wane irin hali ne dashi kwana biyu ya d'ora mata karan tsana masifar yau daban ta gobe daban. Tashi tayi ta fita daga dakin ta barshi, shi kad'ai ya gama duk wasu uzurinsa ya fito cikin milk din jallabiya, tana zaune a falo tare da Marakisiyya suna kallo yazo ya fita yana baza 'kamshin turare, bayanshi tabi da kallo tana ayyana wasu abubuwa a kanshi gabadaya ya sauya halaye sai tsiro musu da abubuwa yake marasa dadi. Babu kunya a daran ya lallabo da bukatarsa, aikuwa ta furje tace." Tunda yana zarginta da zalinci to yaje can gurin matar tasa ya biya bukatarsa itama ta daina yarda tunda abun arziki yana zama sharri Yayi-yayi da ita ta'ki, sai ya shiga kwantar da kai yana yi mata dadin baki tai masa banza ta cigaba da gyarawa yaronta shimfida. Kallonta yake yana lumshe idonsa lokacin tana sanye da karamar riga iya gwiwa mai santsi duk ta kwanta a jikinta komai yana gani a idonshi, hallitarsa ta sanja wata irin jaraba ce take cinsa. ya dinga wani micincina ido yana shafa gemunsa. Ta gama komai ta nemi guri ta kwanta duk yana kallonta. Kallonsa tayi da fadin." Idan zaka fita ka kashe min fitila. Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke kafin yace ." Kina tunanin kinfi karfina ko."? Da sauri tace." Me za kayi min to ko ka danne ni kayi ta karfi babu abunda zaka samu." "Haka ki kace."? Shareshi tayi, ta gyara kwanciyarta tare da rufe jikinta da bargo. Ya tashi yaje ya kashe fitila ya dawo gaba gadi gadon