← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 97

Sashe 40

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da haka ba zai kyaleta ba zai cigaba da gwadata domin ya tabbatar da nagartar ta. **** Sai bayan isha'i ya samu kansa dan gabadaya yau a tsaye suka wuni, yayi wanka ya fito cikin k'ananun kaya t- shart da 3Qutar masu haske kai tsaye falo ya nufa ya samu Adewale yana kallo ga plate din abinci nan a gabansa. Kusa dashi ya zauna yana kiran sunan Allah, hannu yasa ya dafe kanshi da fadin." Ba haushe yace Aski idan yazo gaban goshi yafi zafi Adewale kwana Biyu nan wallahi a gajiye nake gashi bana samun bacci isasshe." Cokali cike da abinci ya kai bakinsa yana taunawa yace." Oga aikin nan namu ai sai mai juriya akwai tarin kalubale wanda ba kowa ne zai gane ba sai wanda ya san ya al'amarin yake, ni kaina na matsu na koma gida domin dukan yayi yawa ban ta'ba kwana uku babu sex ba sai da nazo garin nan, shiyasa wani sa'in nake fita na rage zafi." Yana girgiza kansa yace."Adewale baka da magana sai ta sex kai kenan kalle-kallen blue film ko gajiya ba kayi wallahi ka kiyaye kuma kai hattara kada garin son zuciyarka kaje ka dauko ciwo neman mata bashi da fa'idah." Shiru yay na minti biyu kafin yace." Oga ina kiyayewa fa bana yarda na kwanta da mace ba tare da kariya ba, bani da juriya akan wannan al'amarin Oga haka Allah ya hallice ni, kai kam ai ina ganin k'okarin ka don ban ta'ba ganinka da wata mace ba." Yace." Kariyar banza, ai duk wayonku ba zaku hana Allah zartar da ikonsa ba, wallahi ka kiyaye domin inganta rayuwarka data 'ya'yanka." Yana 'yar dariya yace." Oga kullum aka zauna da kai sai ka kashewa mutum jiki da nasiha, duniyar nan fa ita kenan to me zai sa mutum ba zai ji dadinsa ba." Ya kai hannu ya janyo plate din abinci dake rufe ya bude da fadin." Kayi nisa Adewale sai dai kawai na taya ka da adduar shiriya." Ya mike tsaye yana kyalkyala dariya da fadin." Yanda yau muka yini a tsaye da zaka bani hadin kai da na kawo maka wacce zaka sauke gajiyarka." Shuru yay masa be iya ce masa komai ba, domin al'amarin mutumin yana nema yafi k'arfinsa. Ya cigaba da subararsa yana jinsa uffan bece masa ba, abincinsa kawai yake ci yana nema masa shiriya a gurin Allah. Gajiya yay da surutun ya kama hanya ya fita da niyyar zuwa ya samu wacce zai sauke gajiyarsa a kanta. A nutse ya kammala cin abincin ya yagi tissue ya goge bakinsa, hamdala yay ga Allah, kafin ya kishingida kan kujerar ya dauki wayarsa yana dubawa. Ya kai mintina goma yana duba wayar kafin ya lalubi number abokiyar rigimar tashi. Daf da zata katse ta daga wayar, wannan karon ma a maimakon tai masa sallama sai kawai ta shiga sauke masa ajiyar zuciya a kunne. Lumshe idonsa yay ya janye wayar daga kunnansa yana jin wani irin yanayi na shiga jikinsa, ya ci ya 'koshi ga gajiya jikinsa yayi tu'bus! ta bakin Adewale san samu ya samu wacce zai sauke gajiyarsa, cikin wannan yanayin ita kuma tazo tana masa numfarfashi a kunne sai kace wacce take cikin wani yanayi. Jin shuru bece komai ba yasa ta cire wayar tana dubawa, har yanzu yana kan layin bai kashe ba. Zum'bura baki tayi ta ya mutse fuska da fadin.'' Ina jinka ka kira waya kuma kayi shuru" Gyaran murya yayi ya saisaita yanayin sa da fadin." Ya kike ina fatan kin wuni lafiya."? A takaice tace." Lafiya." Yace." Masha Allah haka ake so menene labari."? Tai masa banza tana jin kamar ta kashe wayarta. Yace." Baki da labari me dadi wanda zaki bani."? "Umm." tace tana jin wani irin haushinsa a zuciyarta. Yace." Okey d'azu da safe munyi waya da Uwale ina fatan ta sheda miki hukuncin dana yanke akan wannan kayan garan da ki kazo dashi." Tace." To ni me ya dame ni da wannan, al'adah ce ta masarauta cewa duk yarinyar da za'ayi wa aure sai an had'a da kayan masarufi da turaman atamfofi da sauransu, kai akayi wa hidima da sauran family naka duk yanda kukayi dai-dai ne." Yace." Eh na fahimta bana bukata ne shiyasa nace a bayar dasu kafin na dawo Uwalen take sheda min cewa lallai sai an fada miki kin yanke hukuncii tukkuna." Tace." Kai har kafi 'karfin wani abu kenan."? Yace." Ban fi k'arfi ba kawai bana bukata ne." Ranta yay masifar baci tace." Nawa kake dashi? me ka ajiye a banki? shin yaushe ma ka zama mutum! ka samu sutturar sanyawa da har za ayi maka kyauta kace baka so, shin wanene kai a cikin mutane da har zaka nuna cewa kai kafi karfin wani abu."!? Cikin daga murya take maganar." Yace." A'm human being ni mutum ne kamar kowa nace bana bukata idan da akwai wanda ya isa ya sauya min ra'ayi ina jiran sa." Taja wani mugun tsaki irin wanda ta san baya so a kufule! tace." Nonsense kawai." Kashe wayarta tayi zuciyarta na wani irin turiri, sosai taji ciwon abinda yayi, shi din har waye da mahaifinta zai masa kyauta ya k'yama ta, yaushe har ya zama mutum yayi arziki gami da sutturar sanyawa da har zai nunawa duniya cewa shi yafi karfin a taimaka masa, wannan abun yayi mata ciwo sosai! a ganinta hakan kamar tozarci ne.... *Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya ba kema keda Allah!* *#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE* 2/8/22, 09:42 - Binta: *59&60* Da tsananin bacin rai ya kwana ya kuma tashi dashi, a cikin ranshi yana raya irin tsauraran matakan da zai dauka akan yarinyar mutukar ya koma gidan tazo masa hauka da rashin hankali makamancin wanda take masa a yanzu, wanda yayi imani da cewa don baya kusa da ita ne amma da ba don haka ba da kudi a kace ta zage shi ko taci masa fuska ba zata iya ba. Yana tsaka da shiryawa Hamra'u ta kira shi a waya. beyi a kasa a gwiwa ba ya d'auka tare da gyaran murya kafin ya ambaci sunanta." Hamra'u." Ta amsa da 'yar dariya a tare da ita tace." amma bana son wannan sunan nafi bukatar da ka kira ni da my love din ka kamar yanda ka saba kira na." Murmushi yayi tare da kokarin kawar da damuwarsa yace." Ashe nayi laifi don na kira ki da sunanki na hakika okey to My love dina haka kike so ko."? Ta shiga kyalkyala dariya farin ciki duk ya cika mata zuciyarta tace."Ina son wannan sunan a bakin ka yaya na."? Murmushi kawai yayi, yana k'ok'arin d'aura takalminsa tace." Na san dai yanzu kana shirin fita ko."? Yace." K'warai kuwa kiran wayarki ne ya dakatar dani, ina fata dai kun tashi lafiya? idan Uwale na kusa bani ita mu gaisa." Tace." Yau ma tana kicin tana aiki." Shuru yayi ransa ya b'aci sosai, shin wai mai yasa Uwale ba zata zauna ta hutar da kanta ba. Yace." Kema kina da laifi Hamra'u me yasa ba zaki kar'be ta ba." Tace."Wallahi babu yanda ban yi da ita ba akan cewa ta bari amma taki amma dai bari naje kicin din na same ta." Yace." Yawwa kiyi min wannan k'okarin kafin na dawo kema zaki zauna ki huta tunda baki da hakki akan hakan na ma fasa daukar masu aiki, ita matar gidan da kanta zata shiga kicin tayi ayyukanta, babu ruwana da wani mulkinta." Farin ciki kamar ya kasheta tace." To shikkenan Yaya na Allah ya dawo da kai lafiya." Ya amsa da "Ameen kafin ya kashe wayar, ya cigaba da shiryawa. To da kyar dai Hamra'u ta shawo kan Uwale ta fita daga kicin din, ita kuma ta d'ora a inda ta tsaya, amma inaa! sai da hannu ya bambamta girkin tsaffi ya fita daban. Ta kammala ta tsaf ta shirya wanda za'a akai wa Zinat din a kwando ta fito ta sheda mata cewa ga abincin can a kicin. Tace." Ai sai ki 'karasa ladan ki, ina nufin ki d'auka abincin ki kai mata, dama naga baki ta'ba shiga kun gaisa da juna ba." Tace." Uwale nifa bana san shiga sabgar matar nan tunda naga bata da kirki wallahi yanzu ma kawai umarnin yaya na ne, amma ba don haka ba wallahi ba zanyi mata bauta ba, kuma kina maganar na shiga gurinta domin mu gaisa ai ita ya kamata ta fara zuwa inda muke tunda mu ta zo ta samu a gidan." Tace."Hamra'u duk na gane inda kika dosa, kada kice zaki fito da kishin ki a fili har yarinyar nan ta gane akwai wata ala'ka a tsakaninki da mijinta, ina so kibi komai a sannu a hankali." Cike da jin haushin maganarta tace." To ni ina ruwa na don ta fahimci da akwai soyayya a tsakanina da mijinta, dama abunda nake so ta sani kenan cewa akwai alkawarin aure a tsakaninmu, bayan haka kuma Uwale naga kamar kin fi k'aunar ta a kaina, to bari na tuna miki idan kin manta nice taki kafin ki nuna kulawa da kauna akan wata a kaina ya kamata ki nuna." Ta ri'ke baki da mamakin maganganunta tace." Hamra'u rashin kunya zaki min daga fada miki gaskiya shine zaki gaya min magana." Fashewa tayi da kuka da fadin." A'a ni ba nufi na kenan ba, kawai dai naga abunda kike bai dace ba shiyasa nai miki magana domin ki gyara dan gaskiya ba zan boye miki ba ina jin takaicin halin ko'in kulan da kike nuna min wallahi da kin so da tuni UMARU ya aure ni amma kin mayar da abun wasan yara." Tana kuka sosai take maganar. Uwalen hankalinta ya tashi domin tunda take da yarinyar bata ta'ba yi mata rashin kunya irin na yau ba, kuma tabbas ta sheda cewa yarinyar 'yar halak ce." Tace."Kiyi hakuri ki daina kukan hakan, idan da wacce nafiso Umaru ya aura to kece ta farko, sai dai kuma kin san komai nufi ne na Allah, duk yanda muka so ki auri UMARU idan Allah bai nufa babu yanda za muyi, wannan auran kuma da yayi daga Allah yake domin shima da bakinsa
Chapter 40 · 0% Book details