Sashe 67
Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
asarar namiji! dashi da *UBAN DABA!* Yanzu aka fara! har sai yaga abunda ya turewa buzu nadi........a zuciyarsa yake wannan maganar, a zahiri kuwa ganin yanda duk hankalinta ya tashi yasa ya sassauta muryarsa yana rarrashinta, sai ya kasance suna rarrashin juna ita dai burinta yay mata alkawari cewa ya bar harkar *TAURI!* Kuma bai zai tunkari *UBAN DABA!* ba. Alkawarin gaibu yayi mata domin ta samu nutsuwa! amma baya tsammanin zai janye kudirinsa! harkar *Tauri* kuwa wannan a jinin jikinsa take. Yayi mata alkawarin ya bari, amma abun mamaki taji yana waya da babban yaronsa *ALBA* yace lallai - lallai gobe ya kawo masa maciji yana bukatarsa. Cikin faduwar gaba take kallonsa har ya 'kare wayar ya ajiye a gefansa.......Ta 'bata rai da fadin." A'a ina za'a kawo maciji kuma me za kayi dashi."? Yace." Ina bukatarsa ne babu ruwanki dashi." A raunane! tace." Yanzu fa kayi alkawari ka daina wannan harkar, me yasa duk ga dabbobi ne wanda Allah ya hallata ba zaka ci ba sai maciji me kukeji a jikinsa."? Ya d'aga mata hannu da fadin." Kinga *ZINA* kada ki dameni dan Allah ba fa zaki ha nani aikata abunda na taso dashi tsayin shekaru da yawa ba, saboda haka ki cire kanki daga wannan sabgar." Rai a b'ace! ta kama hanya ta fice daga d'akin, tana Allah wadai da al'amarin. Tsayin sati suna 'yar tsama a tsakaninsu domin tun ranar da ta fita daga dakinsa bata sake shiga ba, kowa a dakinsa yake rayuwa, shima bai nemata ba sai da ya tabbatar da cewar ya cinye miyar macijinsa sannan ya nemi in da take da bukatarsa domin dauriya kawai yake a tsayin kwanakin. Tace bata san wannan ba, domin data kalleshi zata dinga hasaso shi yana cin maciji sai zuciyarta ta tashi, takai ta kawo ma duk sanda yayi yunkurin sumbatar bakinta sai ta kwara amai na bam mamaki! Al'amarin ya dinga dugunzuma masa zuciya yana bala'in jin haushi yaje da bukatarsa ta dinga gudunsa gashi sam baya son ya dinga gwada mata k'arfi! yafiso suyi komai cikin walwala da farin ciki. Yau dai shiri na mussaman yayi kafin ya tunkari inda take sai da yayi wanka da turaruka bakinsa sai kamshi yake fitarwa shigar da yayi ma ta mussaman ce, domin wasu kayan bacci yasa masu kyau da daukar hankali. Tana kwance kan gado abun duniya ya isheta kwana biyu ta kasa gane kanta, komai na duniya yayi mata zafi ta rasa yanda za tayi da rayuwarta.............Yawan tashin zuciyar da take yana damunta. Shigowarsa dakin yasa da sauri ta juyar da kanta, sam bata san Kallon fuskarsa. Cikin bargon da take ciki ya shiga yana lumshe mata ido, kokarin janyota yake tayi sauri tashi tana yamutse fuskarta........Yawu ne ya taru a bakinta ta sauka daga gadon toilet ta nufa ta zubar da yawun ta dawo. Abun ya bashi haushi mutuka! ya rufeta da fada ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba. Hannu ta daga masa da fadin." Don Allah ka kyaleni haka, ni wallahi gabadaya yanzu bana san damuwa, kai kuma na lura duk sanda ka shigo dakin nan sai ka 'bata min rai! kawai ka daina shigo min daki." Ya mike zaune yana mata wani irin kallo kafin yace." Iskancin banza da wofi! meye abun k'yama a jikina da har kike tara yawu! na dauka yau kwana takwas rabon da ki bani hakkina na aure ina ruwanki da tsarin rayuwata maciji ni naci abina mai zai dameki kuma." Tace." Ni fa ba maganar maciji nake maka ba, kai din ne kawai bana son gani." da gaskiyarta take maganar. Takaici da bacin rai sukayi masa katutu! ya daina jin tausayinta kuma duk abunda za tayi sai ya biya bukatarsa. A daran bai saurara mata ba ya turmusheta ya zage dukkakin karfinsa a kanta, ya galabaitar da ita sosai domin dama yakan dade kafin ya kawo haka hallitarsa take da nisa. Aikuwa da ciwo ta tashi dan rasa gane kanta yayi.....babu shiri ya kira likiti domin ya duba masa ita. Kallon farko likitan ya gane abunda ke da akwai amma bai tabbatar ba sai da ya auna fitsarinta.....nan ya tabbatar da zarginsa, ciki ne sati bakwai da kwanaki. Sai ya rasa ina zai sanya ransa yaji dadi, kawai ya shiga godewa likitan kamar shi yayi masa kyautar cikin, kudi ya fito dasu daga aljihu ya bawa likitan yana godiya. A ranar sai bayan azuhur yaje gurin aiki, yana tare da ita yana rarrashinta da kalamai na so da k'auna, ita dai jinsa kawai take tana mamakin al'amarin, dama jikinta sai da ya b'ata cewa hakan na iya faruwa aikuwa gashi hakan ta kasance.....ita kam bata shirya haihuwa yanzu ba, tunda beyi k'wari ba tasan yanda za tayi ta zubar dashi. Koda ya dawo daga gurin aiki sashenta ya nufa domin dubata, ya same ta fes da ita domin duk jin jikin da take bata fasa ado da kwalliya ba hakan kamar ya zame mata jiki. Ya zauna kusa da ita yana nanikar jikinta, shi yana bala'in san kamshin ta ita kuma tana gudunsa, ba komai ne ya janyo hakan ba, sai d'an tayin cikin dake kwance a kasan mararta. Be damu da yanda take kauce-kauce ba, ya dinga sumbatar fuskarta yana ta so ya hada bakinsa da nata tana kaucewa.......da kyar ya samu nasara! tunda ya kama harshen be saki ba sai da ya gamsu tukkuna. Idonta ya ciko da ruwan hawaye harara kawai take zabga masa ta rasa wane irin mara zuciya ne shi. Ido jawur! yace." Ya jikin ina fatan kin wuni lafiya tare da babyna." Shuru tai masa tana dauke kanta. Ya sauke zazzafar ajiyar zuciya tare da kallon agogon dake daure a hannunsa, magariba ta gabato, tsaye ya mike ya dan kalleta tana ta yamutse - yamutse! huci ya fesar! kafin ya kama hanyar fita, tabi shi da kallo tana zum'bura bakinta. Kasa daurewa yayi ya bar maganar a ransa a daran ya shedawa Uwale, farin ciki kamar ya kasheta, tace." Lallai kace da kwarin gwiwarmu za mu shiga k'auyen *K'afur!* ai wannan abun alkairi ne da ya kamata ace yan uwa sun sani. Murmushi kawai yayi da fadin." Saura kwana nawa bikin ne."? Tace." Ashe baka lissafi ai yau saura kwana uku mu tafi dan duk wasu shirye-shirye mun kammala." Yace." To Allah ya kaimu amma ni ina tsammanin a ranar zan dawo bayan an daura aure.'' Tace." To babu damuwa amma ita matar taka sai ka bar ta tare damu domin 'yan uwa su kara sanin ta." Yace." Shikkenan haka za'ayi insha Allah." Sallama sukayi da juna kai tsaye da ya fito sashen Gimbiyar ya nufa cike da farin cikin kasantuwa da ita. *Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number* *07084653262* *BINTA UMAR ABBALE* 3/8/22, 18:59 - Binta: _Akwai ingantaccan maganin gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ *97&98* Wani irin bacci sukayi mara dad'i sakamakon damuwar da suke ciki. da yake namiji ne shi yakan iya danne damuwarsa ita kam ta kasa dannewa domin gabadaya jin kanta take a takure! ita akan kin kanta tasan yun'kurin da tayi ba mai kyau ba ne, shiyasa take bala'in jin kunyar hada id'o dashi! Kwance ya sameta saman gado tun bayan sallar asubahi ta kwanta tana k'okarin gayyatar bacci yaki zuwa babu shi ma gabad'aya a idonta tunani yafi yawa a tare da ita. Ido ta tsira masa har ya k'araso bakin gadon, ya shirya tsaf da niyyar fita gurin aiki. Babu yabo babu fallasa ya kalleta da fadin." kin tashi lafiya."? A hankali ta amsa tana dan lumshe idonta. Kallonta yake yana ayyana abubuwa da yawa a kanta, yanayin ta ya nuna kamar mara lafiya. Ya daure zuciyarsa yace." Ko kina da damuwa ne."? Zuciyarta ta karye hawaye naso ya zubo tana mayar dashi bata bukatar tayi masa kuka tunda yana kiranta da shagwababbiya. Shuru tayi ba tace masa komai ba. sai da ya sake maimata maganar sannan tace." Lafiya na kalau." Ya kalli agogon dake daure a hannunsa da fadin" Okey haka nake so ni zan fita amma idan kinji wani guri nai miki ciwo ki kira ni a waya." Ta kalleshi k'auna da sonsa na kara nunkuwa a zuciyarta, a jiyar zuciya ta sauke a hankali tace " To." Ya kama hanyar fita jikinsa duk babu dadi, yarinyar ta tsaye masa a rai. "Haka zaka fita ba kayi breakfast ba."? Maganarta ta katse masa hanzari. juyowa yayi yana kallonta. Ta sunkuyar da kanta domin bata jurewa kallon kwayar idonsa. " Kada ki damu zan samu abunda zan ci buri na ki tashi ki nemi abinci kici ko dan abunda ke cikin ki idan kinyi min haka kin gama min komai." Ta yun'kura ta tashi tana d'an ya mutse fuskarta. Saurin kawar da kansa yayi sakamakon ganin zahirinta kayan bacci ne a jikinta wanda suka fitar da wasu sassan na jikinta. Yay gaggawar bude kofar dakin ya fita yana jin yanda jarumarsa ke motsi har ta fara yun'kuri! al'amarin ya bashi mamaki mutuka! koda yake ba'a abun mamaki bane idan anyi la'akari da kwanakin da ya dauka rabon da ya hada shinfida da ita. Yana zama a ofis kiran wayar Maimartabar ya same shi. Suka gaisa cikin mutunci da