Sashe 85
Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number* *07084653262* *BINTA UMAR ABBALE* 3/28/22, 21:25 - Binta: _Akwai ingantaccan maganin gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ *123* Asp ya hangi abinda yake shirin faruwa! cikin 'karaji! yace." Umaru kada ka harbi kan domin hakan ba hujjah bane." 'Dakin yayi tsit! tsananin tashin hankali ya hana su aikata komai! Asp yaja jiki da rarrafe ya iske gurin da yake tsaye har yanzu bindigar na wuyansa. Ya rike kafafunsa jikinsa na wani irin karkawa yace." Na fada maka kada ka harbi kanka Umaru zaka mutu kafuri domin abunda ka aikata a yanzu ba haram bane jahadi kayi kuma kayi dai-dai domin karshensa kenan a kashe shi kamar yanda ka kasheshi saboda haka ka cire bindigar nan daga wuyanka." Dr Salihu dake tsaye jiki a sanyaye yace." Wannan magana haka take ranka ya dade kada ka aikata aikin daka sani kayi hakuri mu jin dadin abinda kayi a yanzu kuma muna alfahari da hakan." Gabad'aya hayaniyarsu ta cika dakin kowa yana fadin albarkacin bakinsa. Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke ya juya yana kallon gawar a kwance tayi muni! fuskar ta kara 'baki babu alamun rahama a tare da gawar! Dr Salihu ya iso gurin a hankali ya cire bindigar daga hannunsa, ajiyar zuciya ya sauke da sauri ya matsa daga gurin, fita yayi yaje adana bindigar ya dawo dakin. Lokocin likitocin sun rufu kan Asp suna bashi taimakon gaggawa! Umar din ya tsugune gaban Gawar! yana dubata. Dr Salihu ya tsuguna da kayan aiki a tare dashi. Binkicen gawar yayi sosai nan ya tabbatar da cewa ya mutu mintina ashirin da suka wuce. Ya kalleshi da fadin." Abin mamaki da al'ajabi ko ya akayi wannan takadirin ya samu nasarar shigowa asibitin nan."? Murmushin takaici yayi kafin yace." Idan nace Najeria babu tsaro sai a musanta! handama! babakere! cin hanci! zamba! cikin aminci cin amanar 'kasa! zalinci! duk ya tattara a wannan 'kasa shuwagabbani kuma suna kallo. Dr Salihu ko shakka ba nayi wannan d'an ta'addan dake gabanmu yana da d,caurin gindin shuwagabbani." Dr ya sauke zazzafar ajiyar zuciya da fadin." Yau dai karya ta kare wai bori ya kar boka gashinan a kwance ka alkadarinsa wannan babbar nasara ce a gareka amma a ina zamu samu cikakken bayani. Shuru yayi na minti biyu kafin yace." Akwai sanya hannun Dr Shu'aib ina zarginsa." Dr Salihu ya jima yana kallonsa kafin a sanyaye yace." Amma ban ta'ba tunanin cewa Dr Sha'aib zai ci amanar aikinsa ba tsayin shekaru goma yana aiki ba'a ta'ba kamashi da wani laifi mai muni ba sai a wannan lokacin yana da kyau dai ayi binkice sosai. Yaja dogon tsaki da fadin." Idan babu sanya hannunsa babu yanda za'ayi wannan dan iskan ya san in da nake, bari na sheda maka cewa kai tsaye da nufin kisa ya shigo dakin sai kuma yayi rashin sa'a! ni na kasheshi babban burina kenan naga gawarsa a kwance a gabana." Cikin karsashi da kwarin gwiwa yayi maganar! Dr Salihu dai gabadaya jikinsa yayi la'asar tausayin Abokinsa ya cika masa zuciya, wannan shi ake kira da mugun ji! ko mugun gani! ba shakka azal! ce ta ritsa da abokinsa amma kaf tarihin rayuwarsa bashi da wani tabo Dr Shu'aib mutumin kirki ne kowa ya sheda hakan. Washe garin ranar da al'amarin ya faru gari ya d'auka Asibitin ya cika da mutune da kuma 'yan jarida babban burinsu a bar su su shiga domin su dauki hoton gawar sannan kuma su samu zantawa da Jarumin da ya kawo karshen d'an fashin daya Addabi kasa. Labari har fadar shugaban k'asa cewa a daran jiya *GOJE! ya samu nasarar kashe UBAN DABA!* wanda ya addabi 'kasa da ta'addanci sai dai kafin ya samu nasara a kansa sai da sukayi dauki ba dad'i! anan ya samu nasarar galabaitar da kakakin rundunar 'yan sanda Jahar katsina wato Asp Musa Baharu yanzu haka dai yana kwance ana bashi taimakon gaggawa." Mai girma shugaban kasa yayi farin cikin faruwan hakan, ba kuma tare da bata lokaci ba ya tura wakilansa domin zuwa su tabbatar da al'amarin kana kuma suyi jinjina tare da mik'a gaisuwa da godiya da yawunsa. Comissinoner ya kasa zaune ya kasa tsaye! jikinsa sai rawa yake bakinsa ya bushe tsabar fargaba da tashin hankali sun ha nashi sakat! sa'i da lokaci gabansa sai ya yanke ya fad'i! watakila ya tattara kayansa ya gudu shine kawai kwanciyar hankalinsa. Umaru shi da kansa ya bada Umarnin d'aure Dr Sha'aib a cewarsa a gurinsa za'a samu duk wasu bayanan da ake bukata. Da farko dai gardama ya fara, sai suka cire imani da tausayi suka fara laftarsa! babban mutum da girma da iyali sukayi masa tik! suna masa tujara! duka ko ta inaa!.......Yana kuka da hawaye da majina ya daga hannuwasa da fadin" Ku saurara zanyi bayani." Suka saurara da dukan da suke masa. wasu zafafan hawaye masu zafi suka fara tsare a saman fuskarsa. A daddaure! aka shiga dashi dakin. Sun kai su ashirin a tsaye a kansa! Asp dake kwance a hankali ya tashi yana kallonsa sosai yake mamakinsa! fuskar salihai gareshi ba za kayi tsammanin zai aikata wani mugun aiki ba. Umaru kuwa yana tsaye ya goya hannuwansa a baya. shima mamakin Dr Shu'aib din yake, wai dashi aka hada baki domin ganin bayansa. 'Yan jarida biyu maza da mace daya suka shigo dakin da kayan aiki a tare dasu. Ganin shigowarsu yasa kai tsaye ya nufi gurin da Dr Shu'aib din yake gurfane! gumi yayi masa dabaibaiyi. *(Allah mugun ji da mugun gani Allah ka karemu)* Ya tsuguna gabansa a nutse ya kira sunanshi. Cikin tararrabi da damuwa ya kalleshi bakinsa ya bushe tsabar wahala! Zuciyar musulci gabadaya sai tausayinsa ya rufeshi, amma bai nuna a zahiri ba, ya sha kunu da fadin." Dr kayi mana cikakken bayani gamu gabad:aya ga kuma manema labarai shin ya akayi *Uban daba!* ya samu damar shigowa asibitin nan da mummunan kudiri, ya shigo dakin da nake kwance jikinsa sanye da kayan aikinka yanayin hallita ya sanya da yawa mutane basu sheda waye ba saboda basaja! shin ya akayi hakan ya faru."? Ya jima kansa ya sunkuye yana dawurwura! kafin da kyar yace." Umaru kaddara ce ba halina bane wallahi azal ce ta afka min." Yace." Duk na yarda da maganarka amma kasan cewa idan da kaddara tabbas akwai son zuciya a ciki akwai sanya hannun shugabbani a tunani sunyi maka alkawarin makudan kudi shin ko ba haka bane."? Maganar a kan hanya take, wannan ne dalilin da ya sanya ya kasa furta kalma guda. tabbas hakane. Yace." Shurun ka na nufin maganata a kan hanya take." Ya kalleshi idonshi jawur! ya tara 'kwallah! yace." Umaru babu ruwan shuwagabbani a cikin wannan al'amarin. abunda na sani shine mai girma Commissioner naku shi yayi tattaki ya sameni har cikin gidana da mummunan kudirinsa. Cin amana ba halina bane. ba a shedar kai amma tunda nake ban ta'ba yunkurin cin amanar aikina ba sai a wannan lokacin. nayi mamaki mutuka lokaci guda na amince da manufarsa. a take yayi min alkawarin miliyan goma bayanshi wani babban dan kasuwa Alhaji Mutari mai zinare yayi min alkawarin miliyan ashirin mutukar na amince da manufarsu. Nan na tambayesu dalilin da yasa suke bukatar ganin bayanka. Dukkaninsu suka tabbatar min da manufarsu....Commissioner yana adawa da yanda Allah yayi maka d'aukaka! yayi maka baiwa! ya daga darajarka! duniya ta sanka manyan mutane suke alfahari da kai! a cewarsa yana ji a jikinsa watarana zaka iya gadar kujerarsa ko kuma ka iya mulkar kasar baki daya. to wannan dalilin yasa yake jin haushinka yake bukatar ganin bayanka a doron duniya. Alhaji Muktari mai zinare ya tabbatar min da cewa. kai ne kayi sanadiyar tattalin arzikinsa, wannan dalilin yasa ya sanya ido akanka har ya samu nasarar samun labarin asibitin da kake kwance. A take suka had'u shi da Commissioner suka sauya min ra'ayi! suka rinjaye ni na amincewa bukatarsu. Wannan shine abunda ya faru." Cikin rauni da rashin confidence ya 'karasa maganar. Asp ya kalleshi da fadin." Dr Shu'aib kaci amanar aikinka! bayan haka kuma kaci amanar k'asa! kwanakin da suka wuce na dauka tare da kai muke jajanta yanda al'amura suke faruwa. rashin tsaro ha'inci da cin hanci! ashe ta ciki na ciki zuciyarka babu alkairi! akan miliyan talatin ka yarda kaci amanar Allah har ka bada goyon baya kashe rai! shin ka dauka kai cewa zaka zauna a duniya ba zaka mutu ba? haba Malam yanzu kana maganar kaddara! akwai ta amma kuma son zuciya yafi yawa a ciki saboda haka dole ka fuskanci hukunci daga hukuma! A raunane! yace." Asp na amince da kowane irin hukuncin da za'a yanke a kaina! kamar yanda na sheda muku da farko wallahi ba halina bane tsautsayi da kadd.........Umaru ya katseshi ta hanyar buga masa tsawa. "Ya isa haka."! shuru yayi yana kallonsa. Ya kalli jami'an tsaron dake tsaye a kansa umarni ya basu cewa a fita dashi. Suka mikar dashi tsaye. damar da 'yan jaridar suka samu kenan suka dinga daukar hotonsa suna masa vedio sai sunkuyar da kansa yake abin duniya ya dameshi! basu fasa d'aukar hotonsa ba har sai dai aka shige dashi mota tukkuna. Kaf ya tattara bayanai da hujjoji da suka cancanta! da kansa ya kira kakakin rundunar 'yan