← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 97

Sashe 74

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mai hankali ya auna maganar ya san habaici ne. Tana daga cikin daki duk ta na jin abinda yake faruwa....Uwalen na share hawaye tace." Shafi'i na gode da cin mutunci matarka ta zuga ka kazo har gida kaci mutuncina cikinmu daya da kai, baka duba furfurata ba, ka tsaya a kaina kana fada min magana babu komai na gode." Yace." Ai gaskiya na fada miki Uwale ki gyara kuskuranki, kafin ki k'aunaci kowa Hamra'u ya kamata ki nunawa kauna da kulawa, amma a karon banza kin watsar da zumunci saboda kwadayi kin kama wata mara tarbiya kina mata ladabi a gabanki ta fitar da hannu ta tsinkawa yarinya mari ki kasa daukar mataki, karshe ma ki ka mayar da laifin kanta, wannan ba adalci bane." Ta sanya gefan zani ta goge ragowar hawayen da ya rage tace." Tabbas da na san wannan bacin ran zan samu da nayi zamana banzo ba, Shafi'i ban ta'ba tunanin akwai ranar da za tazo ka tsaya a gabana ka nayi min rashin kunya ba." Yace." Duk abinda nayi miki ke kika janyo idan kina son zumuncinmu ya cigaba da gudana to kiyi gaggawar sanya albarka a cikin auran Umaru da Hamra'u! domin da kin so da tuni Umaru ya auri yarinyar nan idan da rabo a kusa ma da tuni ta haihu." Tayi shuru ta kasa magana tsabar bacin rai! Shi kuwa rigarsa ya buge ya fita daga gidan ransa a bace. Tana daga cikin dakin take jin sautin kukanta, tausayinta ya rufeta,duk akan ta nuna kulawa da ita ne yasa aka zo har gida aka sanya ta zubar da hawaye......ita kuwa zata bawa mara da kunya. taji wani kwarin gwiwa a tare da ita. A nutse ta zauna a kusa da ita tare da dafa kafad'arta. Ta kalleta a sanyaye da fadin." Kiyi hakuri abinda akayi miki kinji ko." Girgiza kanta tayi da guntun murmushi a fuskarta tace." Uwale ke zan bawa hakuri nasan dalilina dan uwanki yazo har gida yaci miki mutunci iya son ransa, kuma cikin maganganunsa na fahimci abunda yake nufi. Ban hana Umar Auran Hamra'u ba, nima kaddara ce ta had'a ni dashi ashe shine uban 'ya'yana ban sani ba, Amma wallahi kaf tunanina bai ta'ba kawowa cewa zan aureshi ba ballantana har na fuskanci matsala irin wannan, wallahi na amince ya auri yarinyar nan mutukar shine kwanciyar hankalinku gabadaya. Uwalan ta dinga kallonta tana mamakin furucinta, sam ba tayi tsammanin cewa tana da sauki kai irin haka ba, yarinyar nada nagarta sai mu'amula ta had'aku sannan zaka fahimta. **** Washe gari da sassafe ta fita wajen gidan domin samun network......Lokacin jama'a basu fara kai kawo ba, ta kira shi yana shirin fita. Cike da farin ciki ya daga wayar ''Farin ciki na kin tashi lafiya."? Ta amsa babu yabo babu fallasa kafin ta d'ora da fadin." Za kazo yau din."? Yace." Eh insha Allah, ina fatan lafiya.''? ba tace masa komai ba, kawai ta kashe wayarta ta koma gidan. Ta samu Uwale ta fito da shirin shiga gidan Tasallah........Tace." Na fita ne nayi waya da maigidanki yace yana kan hanya insha Allah." Tace."Allah ya kawoshi lafiya da dai nayi niyyar mu zauna mu kwana biyu amma saboda abubuwan da suke faruwa na rashin dadi gwara mu tafi shi yafi alkairi." Murmushi tayi wanda ya tsaya iyakacin fatar bakinta, tace." Wancan kayan dake cikin baggo na tsaraba ne ya kamata tunda zaki shiga cikin jama'a ki tafi dasu." Tace." Kina nufin akwai wasu kayan da ki kazo dasu."? Tace." Eh suna can dakin." tafada tana nuna dakin Umar din da yake dake rufe. Uwale kasa magana tayi saboda mamakin mutunci da karamcin yarinyar, tana da kyawun zuciya tana kuma da kyauta da alkairi hakan kamar a jinin jikinta yake.....Ta kalleta da fadin." Sannu da kokari, Allah ya saka da alkairi amma yana da kyau muje tare dake sai ki basu da hannunki. Tayi jim tana nazarin maganar kafin ta girgiza kai da fadin." Babu komai Uwale ni dake duk daya ne kawai ki basu a matsayin kece ki ka kawo musu babu komai." Tace." Aa ba za'ayi haka ba, idan ma ba za kije ba babu damuwa amma tabbas da sunanki zan bada kayan." Tayi murmushi da fadin." To hakan ma yayi ni zan shiga na kwanta Allah ya sanya alkairi." Ta amsa da ameen tana kokarin bude dakin Umar din domin fito da kayan. *Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number* *07084653262* *BINTA UMAR ABBALE* 3/18/22, 20:29 - Buhainat: _Akwai ingantaccan maganin gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ *109&110* Gidan ya rage saura ita kadai, sai ta shiga tunanin abubuwan da suke faruwa, jiya da daddare kafin su kwanta Uwale tayi mata cikakken bayanin abunda yake tsakanin mijinta da yarinyar da tuntuni ta d'ora zargi a kanta, tabbas koda Uwale ba tayi mata bayanin komai ba dama tuntuni ta fahimci wani abu, duk da dai shi bai fad'a mata cewa akwai al'kawarin aure a tsakaninsa da yarinyar ba, to ita yarinyar ta nuna mata alamu tun farkon fara had'uwarsu...Ba zata ha nashi aure ba, domin a yanda Uwalen ke sheda mata yanda yarinyar tayi wahala a kansa hakan ya sanya taji tausayinta, bayan haka kuma ta san duk daran dadewa bai zama lallai ta zauna ita kadai ba, wannan ne dalilin da yasa ta tausayawa yarinar. wai akace son maso wani koshin wagala! amma babu shakka ba zata lamunci munafurci da kumbiya-kumbiya ba. domin tafiso duk abinda za'ayi a fada mata kada a munafurce ta, abu na karshe kuwa dole ya jawa yarinyar kunne ta kiyayi shiga gonarta ko kuma yi mata rashin kunya anan ne za'a samu matsala! domin mutukar yarinyar tace zata raina mata hankali to abu ne mai sauki a gurinta ta cire blet ta zane mata jiki dashi, sai dai duk abunda zai faru ya faru. To can gidan biki kuwa ya kacame! da hayaniya mata sun fi ashirin akan Uwale dake rabon turaman atamfofi da mayafai da sabulai na wanka da wanki. Da yawa wasu basu samu zanin ba, saboda yawansu, wasu kuma mayafai suka samu da sabulai, duk wanda ta mik'awa sai tayi masa bayani cewa daga matar Umaru ne. A cikin wa'inda suka samu kayan har da mutanan Dayyiba......sai suka silale suka nufi gidanta domin kai mata rahoto. Wasu kuwa gidan Uwalen suka nufa domin mika godiyarsu da kuma jin dadin alkairin da akayi musu. Hayaniyar shigowarsu gidan ya katse tunanin da take. Ta fito tsakar gidan ta gan su da yawa a tsaye....ikon Allah har da masu durkusa mata, ta jingina jikin bango (garu) tana amsa gaisuwarsu da fadin." Ku daina godiya haka babu komai an zama daya. D'aya daga cikinsu tace." Dole muyi godiya yarinyar kirki! domin bamu tsammaci haka daga gurinki ba, dalili mun samu labari a bakin wasu daga cikin 'yan uwanmu cewa baki da kirki mutuniyar banza ce ke da dai sauransu, sai gashi kinyi mana bazata mun gode sosai." Murmushi kawai tayi kafin tace." Ba komai kun san mutum tara yake bai cika cif ba, kowa yana kuskure a rayuwa, wa'inda na 'batawa rai a cikinku su yafe min tunda har Allah yasa na shiga cikinku ai mun zama daya dama rashin sabo da juna ne." Matar tace." Kwarai kuwa Gimbiya to mu dai muna bayanki insha Allah domin dai Dayyiba bata da alkibula mai kyau! mu mutanan *KAFUR* muna sonki da kaunarki dan haka ki cire kokwanto a ranki." Tace." To na gode sosai Allah ya saka da alkairi." Gabadaya suka amsa da ameen. kafin suyi mata sallama su fita....Itama cike da farin ciki da jin dadi ta koma dakin ta kwanta, cikin zuciyarta take adduar Allah ya bata hakurin zama dasu, tunda tana son mijinta babu abinda ba za tayi ba. Dayyiba da labari ya iske ta kamar ta kurma ihu saboda bakin ciki, idonta ya ciko da ruwan hawayen bakin ciki ta kalli Taburni da fadin." Amma dai kinji kunya wallahi Ashe amincin da yake tsakaninmu na 'karya ne."? Taburni tace." Kamar yaya ban gane ba."? Ta zabga mata harara da fadin.'' Meye amfanin zuwa ki kar'bi turmin atamafa kamar baki ta'ba daura zani ba." Ta daga mata hannu da fadin." Kinga Dayyiba saurara! kawai saboda gudun bacin ranki ina kallon alkairi sai na bar shi, kema kin san ba zai yuwu ba, zani da sabulai na samu ke ko dake ko babu ke dole ina da rabo saboda matar Kawunsa ce to meye abin damuwa." Dayyiba ta sanya gefan zani ta share guntun hawayen daya fara fitowa tace." Taburni ban san ya zanyi ba akan wannan al'amari, wallahi idan Hamra'u ta samu shiga gidan Umaru buri na bai wuce ace ta zama mowa ba, amma na san hakan ba zai yuwu ba sai na taka muhimiyyar rawa. gashi bani da kudi a hannuna ballanatana naje a taimaka min." Tace." Yanzu dai abu na farko da za fara shine janyo hankalinsa kan 'yarki, ma'ana ya daina ganin kowa a gabansa sai ita, kafin ace ta shiga gidansa, sai kuma ayi musu farraku da Uwargidansa. Tace." Taburni bani da kudi wallahi, kuma kin san wannan harkar sai an ajiye kudi dole a zubar da jini." Taja tsaki da fadin." Ashe wasa ki ka
Chapter 74 · 0% Book details