Sashe 93
Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
daga hannunsa. Ya kalleshi da fadin." Tace babu damuwa amma dai kaji da kunnanka albarkaci na ne." Bai damu ba yace." Eh ai kai din babban mutum ne shiyasa na kama kafa da kai." Maganar ta bashi dariya sai da yayi kafin ya mike da fadin.'' Bari na shiga toilet na fito." Be ce masa komai yana can tunanin irin kalaman da zai yi mata zuciyarta tayi rauni ta dawo gareshi. Ajiyar zuciya mai sanyi ya sauke a lokacin da ta daga wayar. Cikin nutsuwa ta gaishe shi, ya amsa yana mamakinta, ta dora da tambayarsa mutan gidan, yace." duk suna lafiya sai dai kewarki.' Shuru tai masa ba tace komai ba. Ya raunana muryarsa kamar mummuni yace." Ke yanzu abinda ki kayi a ganinki shine dai-dai.''? Tace." Me nayi."? Kaskantar da muryar ya sakeyi yace." Saboda kawai sa'bani ya gifta a tsakaninmu sai ki tafi gida kin san halin da kika jefa mu a ciki kuwa ."? 'Karamin tsaki taja kafin tace." Kaga Umaru bana san wasu maganganu yanzu ina jiran takarda ta."! Ba ta jirayi amsa ba ta kashe wayarta. Aikuwa gigicewa yayi hannunsa na wani irin rawa yake sake kiran wayar, tana kallo taki d'auka. Ya mike tsaye yana kai kawo a falo! Cikin wannan halin Asp ya fito ya sameshi. Ya kalleshi kamar ya dora hannu aka ya kurma ihu!! Shi kansa Asp din bai ta'ba ganin ya shiga tashin hankali irin haka ba. Hankalinsa a kwance ya zauna kan kujera da fadin." Ya kukayi da ita."? Ya sharce gumin goshinsa da jan kafa ya samu kujera ya zauna kafin yace." Asp yarinyar nan bata da hankali wallahi! da kamar da arziki muka gaisa a mutumce har ina murna amma budar bakinta tana jiran takarda wannan maganar ta 'bata min rai wallahi." Yace." Allah ya kyauta to kadai yi kokarin ganin kayi gaggawar gyarawa tun kafin al'amarin ya lalace'' Yace." Wai kai da gaske kake ba zakayi min jagoranci ba." Ya kishingida da fadin." Zancen kake so ai na yanke magana babu ruwana a cikin al'amarin dan ina so na tsira da sauran mutuncina a idon mahaifiyar yarinyar shiyasa na cire kaina daga sabgar." Da karfi ya buga! hannun kujarar da yake zaune! ya mike tsaye! jijiyar kansa ta tashi idonsa yayi jawur!! ita da take daki a kwance sai da taji hargowarsa yana saukewa Asp din ashafa kamar wani ubansa. "Dole da kai a cikin sabgar tunda tun farko kai kayi ruwa kayi tsaki al'amarin ya tabbata, mahaukaci kuke so ku mayar dani! ita tana dankara min duk maganar da tayi ra'ayi kaima kana farfad'a min abinda ranka yake so, to baka isa ka kashe min aure ba, idan ma kaine kake zugata duk zanyi maganinku." Tamkar mahaukaci sabon kamu haka ya tubure!! Yana kishingide yana kallonsa har ya kare cin mutuncin bai ce masa uffan ba, ya kama hanyar futa yana wani irin huci! Fitarsa keda wuya Madam ta fito ta zauna kusa da mijin nata suna sake tattauna maganar. Wayarsa ya dauka ya kira Zinat din ta fito ta samesu a zaune. Tace." Duk ina jin hargagin da yake ka rabu dashi kawai domin mai hali baya fasa halinsa wallahi ranka ya dade dan dai kawai ka hana ni tafiya gida ne amma da tuni na tafi dan zaman nawa bashi da amfani." Yace." Akwai dalilina na aiwatar da hakan, shi kuma ki kyale ni dashi idan da sabo na saba da halinsa." To a daran dai bai iya rintsawa ba, asubar fari ya dauki hanyar KANO zuciyarsa cike da tararrabi da Alhinin 'bacin ran da zai je ya tarar.... *Kada ki karanta min littafi idan baki biya, kada ki siya ki fita dashi, 'Yar uwa kada ki ganshi a group kiyi shearing domin hakkina ne, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne.....0542382124...Binta umar gtbank. idan kati zaki turo sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number* *07084653262* *BINTA UMAR ABBALE* 5/14/22, 22:04 - Binta: _Akwai ingantaccan maganin gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ *131* Cikin girma da dattako aka saukeshi, yanda ake karramashi da mutuntashi ya sanyayar masa da jiki, anya kuwa zancan zucci yake shida zuciyarsa. Gama cin abincinsa ke da wuya magajin sarki ya shigo, cikin sakin fuska da wasa da dariya suka sake gaisawa kafin ya isar da sakon da yake tafe dashi cewa maimartaba na bukatar ganinshi. Duk kwarin kansa da jarumtarsa sai da gabansa ya fadi jin cewa maimartaba na bukatar su tattauna, ko babu wannan dalilin haka kawai mutumin yake masa kwarjini! Yayi kokarin danne fargabarsa ya mike tare da aro jarumta yabi bayan magajin sarkin dan amsa kiran da ake masa. Yaji dadin ganin sarkin shi kadai, ya cire takalmansa a nutse ya shiga fadar da sallama a bakinsa. Shima ya amsa fuskarsa a sake hakan zai nuna maka cewar yana farin ciki da zuwan Umar din. Ya zauna kusa dashi daga kasan kafafunsa irin zaman rakuma yayi kai a kasa yake mika gaisuwarsa. Cike da annushuwa ya amsa yana tambayarsa hanya tare da iyali.'' Ya amsa da "Kowa lafiya lou ranka ya dade duk suna gaisheku" Yace."Muna amsawa da kyau Umaru naji dadin zuwanka ina fatan dai babu wata matsala dake faruwa tsakaninka da iyalinka, domin ni babban burina a duniya ace yara na suna zaune a dakin mazajensu da dadi babu dadi ayi hakuri da juna domin shi aure ibadah ne, kuma jin dadinsa kadan ne don haka ayi hakuri da juna ana kai zuciya nesa." Yayi kwatakes da jin nasihar da sarkin yake masa, wannan ya tabbatar masa da cewa yarinyar bata gidan, dan haka da sauri yace." Insha Allahu zamu kiyaye za kuma muyi iyakacin bakin kokarinmu gurin kwatanta adalci sai dai dan adam tara yake bai cika goma ba, ranka ya dade ina neman afuwa dangane da abubuwa na rashin dadi da suka dinga faruwa a can baya sharrin shadain ne, yanzu alhamdulillhi muna zaman lafiya da juna babu wata matsala da ikon Allah. Yace." Alhamdulillhi Umaru babu wani bawa da zai kasance a duniya ba tare da kuskure ba, saboda haka kada ka damu dangane abunda kake tafe dashi, na amince da kai dari bisa dari, shine dalilin da yasa na dauki 'yata na baka aure, saboda haka magana tuntuni ta wuce a gurina, Allah ya kiyaye gaba." Cike da kwarin gwiwa ya amsa da "Ameen.'' yana jin sanyi a zuciyarsa yanzu ya kashe matsalar yana da tabbacin cewa ko zuwa tayi ta kawo k'ararsa mahaifin nata ba zai saurareta ba. Ya wani risinar da kai cikin sigar girmamawa yake ta godiya da irin alkairin da akayi masa Wannan abunda yake ya kara kankaro masa daraja da mutunci a idon sarkin. Tun a mota ya kira wayar Asp yake sheda masa abinda ke faruwa. Asp din yace." Ikon Allah ni kuma kaga yanzu muka gama waya da ita ta bani tabbacin cewa tana KANO din gidan Hassana 'yar uwarta. Dogon tsaki yaja ya girgiza kansa dake bala'in sara masa yace." Kaga ni yanzu na wucr bichi na kusa isowa gida amma t ilas na juya baya tunda ka tabbatar min da gaskiya. Sam bai bashi tausayi ba, yace." Eh hakan shine maslaha amma ka fara sheda mata zuwanka ta waya bayan haka kuma ka tanadi kalaman da zasu tausasa mata zuciya." Ya hadiye wani kuttun takaicin da ya tokare masa a wuya, wai shin da Asp yake wannan maganar shi yafishi sanin abinda zaiyi, gabadaya ma haushin Asp din ya kamashi ya kashe wayar ba tare da yayi masa sallama ba. A kalar motar ya juya da tunanin abinda zai faru idan suka hadu [5/14, 6:44 PM] Matar 'Dan Aljannah: Sai bayan isha'i ya shiga unguwar tarauni a cikin unguwar gidan Hassanan yake, gidan bai bace masa ba duk kuwa da cewa zuwanshi daya. Parking dinsa keda wuya mijin Hassanar ya fito daga gidan da cazbaha a hannunsa da alama massalaci zai shiga. Ya karasa bakin motar yana mamakin maganinsa. Akwai sabo a tsakaninsu duk da ba'a gari daya suke ba amma sa'i da lokaci suna gaisawa a waya. Ya mika masa hannu suka gaisa cikin girmama juna. Alhaji Sa'ido yace." Allah dai yasa lafiya Umaru na ganka cikin dare wallahi ba kaji yanda jikina yay sanyi ba. Jin abinda yace ya sanya shima jikinsa mutuwar yace." Alhaji Zinatu ba ta gidanka kenan."? Ya gyada kansa da fadin." Eh ai ni rabon da in sanya Zinatu a idona har na manta sai dai wani sa'in muna gaisawa a waya a duk lokacin da suke waya da 'yar uwata na kan bukaci ta bani ita mu gaisa." Wani zazzafan gumi ya karyo masa, gabadaya ya rasa yawu a bakinsa kafafunsa ne ma suke rawa gabadaya ya rasa yanda zai bullowa al'amarin, kawai sai ya shiga kici-kicin bude mota ya shiga. Alhaji Sa'ido yace." Umaru akwai matsalar da take faruwa tsakaninka da iyalinka ka nutsu ka tsaya mu tattauna sha'anin mata sai hakuri." Ya shiga motar ya zauna yana kokarin tayar da ita yace." Alhaji afuwa kayi min hakuri tabbas hasashenka gaskiya ne sai dai a halin yanzu bani da nutsuwar da zan tsaya nayi wata doguwar magana saboda wani dalili don Allah idan ka shiga gidan ka mika min gaisuwata." Jiki a sanyaye yace." To shikkenan Allah yayi mana magani, Allah ya kiyaye hanya." Ya amsa da "Ameen ya rabbi Alhaji na gode kwarai." Alhaji Sa'ido bai gusa da gurin ba har sai da ya