Sashe 92
Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya nufa. Da sauri ta tashi zaune tana kallonshi yana kokarin cire rigar jikinsa. Kamar ya san abinda take shirin aikatawa yayi gaggawar rike hannunta rikon tsauri yayi mata ya fara gudanar da abinda yake ganin shine mafita a rayuwarsa. To da yake sun riga sun zama daya ya gama gane lagonta duk turjiyar da take masa abu daya yayi mata ta bada kai bori ya hau, dan har sai da ta fishi ficewa daga hayyaci! ita dashi a wannan fagen ba'a cewa komai ***** To har yanzu dai Commissioner yana kwance a asibiti tare da kyakykywar kulawa daga manya likitoci hakan ba yana nufin komai ya wuce ba, Aa ana so ya warware ma'ana ya samu sauki a yanke masa hukuncin da ya dace da abinda ya aikata a matsayinsa na wanda yayi rantsuwa da Allah cewa ya dauki amanar kula da k'asa da kuma al'ummar dake cikinta, iyalinsa na cikin tsantsar tashin hankali duk da cewa basu rasa komai ba na rayuwa amma tabbas suna da tabbacin cewa hukuncin da za'a yanke masa mai tsauri ne, dalilin gagarimin laifin da ya aikata na cin amanar k'asa. ****** Haihuwar Hamra'u tazo da tangard'a, wannan dalilin yasa babu shiri aka shiga da ita dakin fid'a domin ceto ranta da abinda ke kwance a cikin nata. Anyi cikin nasara an ciro tagwayen mata kyawawa farare tas masu kama da ita lafiyarsu lau, itama kuma alhamdulillhi, ta tashi da hankalinta an kuma kira sunanta ta amsa. Wannan ya sanya hankalinsu duk ya kwanta ganin yanda Allah ya takaita wahala komai anyi cikin nasara da amincewar ubangiji. Allah kenan kana taka yana tasa, a daran Hassanar ta mutu ta bar Husainar, likita ya tsananta binkice gurin gano dalilin mutuwar yarinyar bai ga komai ba dan Ubangiji bai so ya gani ba, kawai dai ya kar'bi abarsa ne bayan ta nuna kamanni. Ban ta'ba ganin kukan Umaru ba sai a ranar ya dinga share hawaye yana kallon Usainar yaso Allah ya hada duka ya bar masa domin da haihuwar yaran Allah ya jarabceshi da masifar son su. Hakanan sukayi hakuri suka barwa Allah ikonsa. Kwananta goma sha hudu sati biyu kenan aka sallamesu suka koma gida lokacin ta warware sosai tana iya komai da kanta sai dai wasu abubuwan Zinat din ke mata ko kuma ta sanya daya daga cikin hadimanta suyi mata. Kwana arba'in da biyu da haihuwar jini ya 'balle mata, hankali a masifar tashe suka nufi asibiti aka fara bata taimakon gaggawa! Sai da kwana ta biyar a kwance a asibiti sannan ta samu sassauci, likita ya kafa sharudai da dokoki kafin ya sallameta suka koma gida. Ba batun bin ba'asi ya shigo dakinta ya rufe ta da masifa ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, a ganinsa Ita take cutar yarinyar har hawan jini yake so ya kamata. Wannan al'amarin yayi bala'in 'bata mata rai! da yake shad'ain yana kusa! abinda yake so kenan! sai ya kara rura wutar rikicin suka dinga masifa yana fada tana fada karshe dai 'bacin rai yasa yace ta fitar masa daga gida, ita kuma tayi rantsuwa ita din 'yar halak ce sai ta fitar masa daga gida kamar yanda ya bukata. amma kafin hakan dole ta in da aka hau ta nan ake sauka. Wayar Asp ta kira domin sheda masa halin da ake ciki... 5/12/22, 07:44 - Binta: _Akwai ingantaccan maganin gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ _*Sanin hali ya fi sanin kama, AYSHA BAGUDO wanda bai san ki ba shi zai miki mummunan zato d'an adam tara yake bai cika goma ba, alkairinki yafi sharrinki yawa, Aysha tarayya ta dake alkairi ne, ina jin dadin amincin dake wanzuwa a tsakaninmu, ALLAH ya hada fuskokinmu da alkairi*_ *130* Lokacin yana gidan Madam bama ya jin dadi zazzabi na damunsa, sai kawai yace tazo gidan ta sameshi su tattauna amma ta janye kudirin tafiya gida hakan ba hukunci bane. Koda taje gidan ta zube masa magana da duk abinda yake faruwa ransa ya 'baci sosai shi kansa ya kan rasa gane kan abokin nasa wataran. Yace." Kiyi hakuri Zinat kin san kowane bawa akwai irin hali da d'abi'arsa, mafi akasari maza suna da wannan halin, idan sun ga iyalinsu na zaman lafiya da juna sai su dinga zargin wani abu amma ki bar ni dashi zan nuna masa kuskuransa." Ta goge hawayen dake karakaina a saman fuskarta tace." Ranka ya dade ni kam nagaji wallahi a halin yanzu ina bukatar nutsuwa zuciyata ta samu sauki tunda yace na fitar masa a gida to zaman me zanyi duk sanda ya bukaci cigaba da zama dani sai na dawo, idan kuma karshen auran ne yazo Allah yasa haka shi yafi alkairi." Ya girgiza kai da fadin." Ba za'ayi haka ba, komai yayi tsanani maganinsa Allah, dazu mu kayi waya dashi yana gurin aiki nima abinda yasa ban fita ba zazzabi ke damuna, amma tabbas zai shigo idan ya dawo zamu tattaunar maganar kada ki damu ki tashi ki koma dakinki." Ta girgiza kai da fadin." Babu fa inda zan koma ai tunda kace zai shigo ina nan sai ayi wacce za'ayi idan ya gaji sai ya sawwake min. Ya dafe kansa yana girgisa kansa, al'amarin ma'auranta yana nema ya jefashi cikin matsala kullum cikin sulhu har yanzu sunqi girma suyi hakuri da juna, laifin kuma ba na kowa bane na abokin nasa ne, shine mara hakuri amma babu komai ya san abinda zai masa. Tunda suka gama hayaniyar ya fita bai sake tuna da matsala a gidansa ba, domin koda wasa bai yi tsammanin cewa zata yanke hukuncin tafiya ba, kawai barazana yayi mata tunda sun saba irin wannan rikicin da wanda ya fishi ya kuma dawo gidan ya sameta. To wannan ne dalilin da yasa da ya dawo ya ga bata gidan hankalinsa ya tashi ainun! koda ya tambayi Hamra'u tace itama wallahi bata sani ba domin tana bacci lokacin data fita. Jiki a sanyaye ya gudanar da uzururrukansa kafin ya nufi gurin Uwale kamar wani mara laka a jikinsa, shi kansa ya san da cewa yarinyar itace jin dadin rayuwarsa. Ta kalleshi cikin nazari tace." Umaru kana da damuwa ga dukkan alamu." Ya dan mutsika fatar goshinsa da fadin." Uwale ba zan boye miki komai ba sa'bani muka samu da Zinat shine ta bar gidan. Uwale ta dinga kallonsa da bacin rai a tare da ita tace." Ni ba zan saurareka ba Umaru domin ko shakka ba nayi laifin naka ne yarinyar tana iyakacin bakin kokarinta a gidan nan, amma kai baka gani da idona nake kallon wasu abubuwan na rashin kyautawa da kake mata, amma tunda nake da ita bata ta'ba zuwa gurina ta kawo karar kayi mata laifi ba, saboda haka ni babu ruwana a cikin wannan al'amari." Da gama maganarta ta tashi ta shige daki ta bar shi a zaune yana sakawa da kwancewa. Ganin zaman bashi da fa'idah yasa ya nufi gurin Hamra'u, nan yace ta kira wayar Zinat din ta tambayeta. Tace." Ai yanzu muka gama waya da ita take sheda min cewa tana KANO." Gabadaya yaji yawun bakinsa ya d'auke! tsabar fargaba da rashin sanin takameman abinda zai fadawa iyayenta. Gabadaya ya rasa abinda ke masa dadi babu karsashi a jikinsa ya fita daga dakin. **** Kwana uku da faruwar al'amarin ya galabaita yayi wani zuru-zuru! dole ya tunkari ASP domin warware matsalar dan baya tunanin tunkarar mahaifin yarinyar shi kadai tilas Asp din zai zame masa garkuwa. Aikuwa yana zuwar masa da maganar yace." Sai dai ka nemi wani ya shege maka gaba, ni ina da Uzuri." Ya zuba masa ido da mamakin maganarsa. Asp ya murtuke fuska babu alamun wasa a tattare dashi. Ya girgiza kai da fadin." Ka san dai da kunya na tunkari mutumin nan da wata magana Asp ni kaina na sheda abinda nayi ban kyauta ba, amma me yasa za kayi min haka bayan kasan cewa kaine wakilin yarinyar nan ai maganar babu ruwanka bata tashi ba." Yace." Eh kwarai ni ne wakilinta, kuma ni na shige maka gaba har komai ya tabbata amma ka mayar dani mutumin banza wannan dalilin yasa nace na daina shiga cikin al'amarin kaje ka gyara kwa'barka." Ya sharce gumin saman goshinsa! cikin damuwa yace." Zahirin gaskiya ban san ta inda zan fara ba wallahi, gabadaya ma kunyar hada ido nake da yarinyar gashi na kira wayarta ya kai sau ashirin taki d'auka da alama har yanzu bata huce ba. Yace." Ga hanyoyi nan da yawa idan bata dauki wayarka ba, ai kana da kafa ka taka kaje can ka sameta ku warware matsalarku." Yace." Shi yasa nace kayi min jagora tunda tana ganin mutuncinka." Ya girgiza kai yana kara gyara fuskarsa, yace." Na fada maka fa wannan karan babu wani abu da zanyi maka kai da kanka zaka gyara kuskuranka." Ya gaza furta komai domin gabadaya kansa ya kulle ga Asp din ya taurare masa ya kasa shanyo kansa. Hannu na rawa ya dauko wayarsa number ta ya kira ya mika masa wayar da fadin." Taimakon daya za kayi min kace da ita ta daga waya ta." Ya jim yana kallonsa kafin yace." Bari kawai na kira ta da waya ta." Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke yana jin wata irin damuwa a tare dashi. Jin muryarta ya sanya jikinsa mutuwa wata irin kasala ta dabaibaye shi, ya tsirawa Asp ido a lokacin da suke wayar ji yake kamar ya kwace