← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 97

Sashe 83

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

daya ne zuciyarsa babu alkairi domin shi bai so al'amarin ya tsaya a haka ba, amma a zahiri ya jajanta kuma shine ya jagorancesu tafiyar zuwa can garin domin duba marasa lafiyan. Idan kuka ga yanda hankalin iyalinsa ya tashi sai kun tausaya musu. Zinatu tsayuwa ta gagareta! kafafunta sai karkarwa suke! tun lokacin da taga mijin nata a tv an nuna shi kan wani gado irin na asibiti kamar matacce hankalinta ya tashi, kuka ta fashe dashi tana kiran innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!! shikkenan mun zama marayu! Kuka gabadaya gidan aka rasa mai rarrashin wani dan Uwale ma kasa daurewa tayi abunka da mutan k'auye sai sambatu takeyi tana share hawaye. Zinat kasa zaman gidan tayi tasa hijab ta fice. kai tsaye gidan Asp ta nufa. Lokacin bai jima da dawowa ba wanka ya shiga domin shiryawa tafiya. Kukan da yaji a falon ne yasa cikin gaggawa ya fito. Ya sameta sai rusa kuka take Madam ta rungumeta tana rarrashi itama Nabila dake zaune a gefe hawaye take sharewa. Ya sassauta murya da fadin." Kuyi hakuri addua za kuyi musu Allah ya basu lafiya. Jage-jage da hawaye a fuskarta take kallonsa da k'yar ta iya cewa." Ranka ya dade kuna 'boye mana wani abu amma a jikina nake ji mijina ya mutu." Ya girgiza kai da fadin" Zinat da mijinki ya mutu da yanzu gawarsa ta iso gida yana nan a raye amma ba zan boye miki ba yana bukatar adduarki." Tana shashshekar kuka tace." Don Allah kayi hakuri ka tafi dani gurinsa inaso na ganshi mu yafewa junanmu." Tausayinta ya rufeshi yace." Insha Allah zai dawo gida da rai da lafiya ku cigaba da rayuwa. kiyi hakuri tafiya dake ba zai yuwu ba tunda bani kadai bane amma insha Allahu idan mun isa zan kira ki a waya ki dubashi. A sanyaye tace." Rayuwata ta kare idan na rasa mijina ina sonshi bana so ya mutu barni amma mutuwa dole ce."!! Wasu hawaye masu zafi suka zubo a fuskar Madam dauriyarta ta k'are sakamakon tausayin yarinyar. Shima zuciyarsa ce ta karye kawai sai yayi gaggawar shigewa daki yana kiran sunan Allah a zuciyarsa, a gurguje ya shirya ya fita ta can kofar waje domin baya so yazo fita tausayin yarinyar ya sashi zubar da hawaye. Isar su keda wuya Allah ya kar'bi rayuwar mutum biyu daga cikin wa'inda suke kwance! Asp dai kasa hakuri yayi ya fara share hawaye ganin tashin hankali da masifa mutuwa dole ce amma irin wannan akwai tausayi da tayar da hankali. Gawarwakin aka had'a guri guda kafin asa a motar da zata kaisu gida. A daran suka juya amma banda Asp domin cewa yayi ba zai tafi ba tukkuna sai yaga abinda hali yayi, gabadaya ya cire tsammani da samuwar abokin nasa. Commissioner bai ce masa komai ba kawai ya rabu dashi amma akwai abinda ya kud'ire a ransa! Da asubah bayan ya idar da sallah yaje ya zauna kusa dashi yana kallonshi cikin zuciyarsa yake masa adduar samun sassauci. Likita ya shigo dakin, suka gaisa kafin ya k'arasa bakin gadon yana dubashi. Ya kalli Asp din da fadin ." Insha Allah yau din za'ayi masa aikin wannan 'kunar dake kafafuwansa za'a cire fatar gabad'aya a wanke gurin. kana a sanya magani." Yace." Dr amma bayan wannan babu wata matsala ko ina nufin babu wani abu daya nakasa a tare dashi. Yace." Bana tsammanin hakan gaskiya tension ne yayi masa yawa da kuma fargaba amma insha Allah zai tashi da tunaninsa wannan shine iyakar binkicen da mukayi a kansa. Yace." To Alhamdullhi Allah ya bashi lafiya, su kuma wanda suka rasu Allah ya yafe musu ya kuma kar'bi shahadarsu." Likitan ya amsa da Ameen ya rabbi kafin ya gama duddubashi ya fita daga dakin. Misalin tara da rabi Governor garin katsina tare da mu'karrabansa suka sauka a gidan gomnatin garin. Tare da governor Zamfara suka isa asibitin domin duba marasa lafiyan. Lokacin ya tashi kuma cikin hayaccinsa kamar yanda Likitan ya fad'a! sai dai ya gaza furta kalma daya sakamakon nazari da tunanin abunda ya faru. Shi kansa Asp din gajiya yayi da magana yayi shuru da bakinsa farin cikinsa dai ya tashi cikin nutsuwa babu buge-buge! Shigar su keda wuya ya bisu da wani irin kallo yana girgiza kansa gabad'aya haushinsu yake ji Malam me za'ayi da mulki bala'i ne ga wanda ya san hakan! Asp ya mi'ke tsaye yana musu barka da zuwa. Suka samu kujeru suka zauna hankalinsu gabadaya yana kansa alhini da damuwa ya bayyana a fuskokinsu da alama dai ko a cikin shuwagabbanin suna da imani. Kafin ma wani yayi magana a cikinsu shi ya mangantu....Asp yayi mamakin hakan mutu'ka! "Rashin tsaro da rashin tsoron Allah da son duniya da mulki shine babbar asara! ga duk wani shugaba." Duk suba zuba masa ido jin maganar da yake. Ya cigaba da cewa." Lokacin da kake ya'kin neman za'be! idonka ya rufe ka tara talakawa kayi musu al'kawaririka kan cewa idan sun mara maka baya zaka tallefesu zaka basu aikinyi za kuma ka taimaki k'asa baki daya." "Mulki ya zama abun rububi da kokawa! saboda samun jin dadin duniya, kayi rantsuwa da Allah da al'kur'ani kan cewa zakayi adalci daga bisani idan bukatarka ta biya sai ka mance da komai ka fara gina rayuwarka ka auri kyawawan mata ka ajiye a gida kaci mai kyau! kasha mai kyau! ka kwanta a mai kyau! ka sanya suttura mai kyau! kayi facaka da kudi! ka nemi duk macen da kake bukata ka tura yaranka kasashen waje suyi karatu, ka tara kudi a banki ka sayi gidaje gonaki ka gina gidajen mai kayi duk wata bukatar rayuwarka ka manta da talakawa da nauyinsu yake wuyanka wannan shine al'kawarin daka kayi wa Allah."? D'akin yayi tsit! babu wanda yace uffan. Ya sauke ajiyar zuciya kafin ya cigaba da cewa........."Talauci yayi yawa a duniya saboda zalincin shuwagabbani mai yasa matasa ba zasu shiga wani mummunan hali ba."? "Sace-sace fyad'e harkokin Daba gami da sara suka sun zama ruwan dare shin menene ya jawo hakan? idan akwai son zuciya irin na mutum to akwai sanya hannun gwamnati. Akwai matasan da suke da degree takardunsu sunyi kyau amma ba'a daukesu aiki ba, an dauki wanda yake takardar secondary aiki a halin yanzu sai kana da hanya zaka samu, mahukunta da shuwagabbi basa bin doka kowa kansa ya sani yaya rayuwarsa za tayi kyau ya ingata iyalinsa......Idan haka ake mulki Allah yayi mana tsakani dashi." *Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number* *07084653262* *BINTA UMAR ABBALE* 3/26/22, 06:13 - Binta: _Akwai ingantaccan maganin gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ *122* Governor Nuhu Bamalli ya sauke zazzafar ajiyar zuciya bayan kare maganganun Umar din yace." Umaru ba zamu musanta maganarka ba, domin duk abinda ka fada gaskiya ne, mulki a yanzu ya zama Innalillahi wa'ina wa'ina ilaihi raji'un! amma inaso ka sani cewa ba duka aka taru a ka zama daya ba, da yawa akwai masu gaskiya ma'ana masu kwatantawa mulki irin na Annabi Muhammad SAW da sahabansa, amma mafi akasari dai marasa tsoron Allah a ciki sunfi yawa, sannan kuma bahaushe yace." Idan anbi ta barawo to abi ta mabi sawu! ina nufin ba shuwagabbani kadai suke da laifi ba, har da jama'ar gari! rashin yiwa shugaba addua bai dace ba, kana kuma zagin shugaba da cin mutuncinsa bai kyautu ba, Umaru wata masifar da kanmu muke janyota idan Allah ya jarrabemu da masifa sai kuma mu dauki laifi mu dorawa shuwagabbani. akwai masu aikata manyan laifukan da Allah ya haramta, Zina tayi yawa a duniya uwa uba lud'u da madigo da suka zama gama gari wannan babban masifa ce zata iya janyo mana fushin ubangiji. duk abinda muke aikatawa na rashin gaskiya Allah ya na kallonmu kuma muna cin albarkacin Annabi Muhammad SAW ne da babu albarkasa da tuni Allah ya kifar damu, saboda haka kayi hakuri dole ranka ya baci kuma duk sharhin da kayi mana babu wanda ya bata mana rai, maganarka gaskiya ce, kasan da cewa muna alfahari dakai a Najeria da zamu samu jarumai irinka to babu shakka Najeria zata gyaru za'a samu sauyin rayuwa fiye da yanda muke tunani, kayi hakuri ka cigaba da bada gudumawarka mu bamu isa mu biyaka ba, amma ka ajiye a ranka cewa zakaje lahira ka tarar da aikin alkairin da kayi, Allah ya Ubangiji ya baka lafiya ya kuma kare ka a duk inda zaka shiga, muna rokon Ubangiji Allah ya bamu zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasa baki d'aya." Gabadaya suka amsa da Ameeen ya Allah." To a takaice dai yini guda abinda ya kasance kenan. Manya k'asa 'yan kasuwa da manyan 'yan siyasa masu sarauta suna sauka a garin domin dubashi. Sarki Umaru mahaifin matarsa tare da 'yan uwanshi a washe garin ranar suka sauka a garin. kai tsaye babban asibitin suka nufa domin dubashi. Lokacin da suka isa asibitin yana bacci bayan an gamai masa aikin k'unar jikinsa Asp na kusa dashi a zaune. Maimartaba tare da mukarrabansa suka samu guri suka zauna cikin alhini da damuwa. Ganin Takawaran nasa a kwance magashiyan jiki duk a 'kone ya tayar masa da hankali mutu'ka! ya tausaya masa sosai kana yayi masa addua tare
Chapter 83 · 0% Book details