← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 84

Sashe 9

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

**********
Amina ta dawo daga siyan itace, ta shigo sashinsu taji kawu Bala yana yiwa Inno bayani, wai ranar juma'a Malam Rabi'u zai turo magabatansa, su kuma sun sanya gonar Baba a kasuwa, malam Rabi'u yace zai siyi gonar.
Jiki a sanyaye Amina ta ƙarasa ta ajiye itacen, ya mai da dubansa kan Amina ya ce "Au to faɗuwa ta zo daidai da zama, iyayen mijinki zasu kawo kuɗi ranar juma'a in Allah ya kaimu, kuma zai sai gonar mahaifinki ya siya ya bamu kuɗin mu yi miki kayan ɗaki".

"Amma baffa idan ka siyar da gonar baba, mai zamu dinga nomawa?".

"Rufen baki, mara kunya, ko shi Hassan É—in ubanki bai isa in magana ya ce zai yi jayayya ba, ke kin je 'yan kwangilar yahudawa sun hure miki kunne har zan faÉ—a ki mayar ko? To na yanke hukunci na gama"
Shiru Amina tayi, zuciyarta na wani irin raɗaɗi, har ga Allah bata son a salwantar da 'yar gonar nan ta su, ga uwa uba wannan Auren da bata ƙaunarsa sam.

Bayan tafiyar Kawu Bala, Inno ta ce "Amina yanzu meye abin yi, ta yaya zamu samu mahaifinki balle a sanar masa da halin da a ke ciki?".

Amina ta ce "'Nima ban sani ba"

Inno ta ce "Ni dai bana son a sayar da gonar nan, kuma da idan sun sayar wata uwar arzikin zasu saya miki na kayan ɗakin da sauƙi, amma na san abin da Allah ya nufe su zasu saya miki, sauran su riƙe abun su".

Ita dai Amina ba tace komai ba, saboda takaici ya hanata Magana sam.

**********

Abun duniya ya isheta, duk yadda Ummanta ke nuna jikinta da sauƙi, amma ita hankalinta dai yafi kwanciya da ace sunje Asibiti an duba umman nata sosai, sai dai idan har suka ce za suyi jigilar zuwa Asibiti a dubata, to zasu shiga cikin jarinsu sosai, duk da haka ba yadda Hafsa ba tayi ba, a kan Umman ta amince su tafi Asibiti Allah ya kawo wata hanyar, amma Umman taƙi haka Hafsa ta ƙyaleta.
Hafa na zaune a bakin rariya, tana wankin waken awara, Umma ta kalleta ta ce "Yanzu Hafsa har yanzu shiru ko ba kowa?"

Sarai Hafsa ta gane abin da Umma ke nufi, amma tayi shiru taƙi amsawa.

"Nifa wannan miskilancin naki ne yake ƙular da ni, da ke fa nake Magana".

"Umma to me zance, kema fa kin san ba kowa É—in".

"Ko a gurin sana'ar taki baki haÉ—u da kowa ba?"

"Umma kefa kike cewa in tsare mutuncina, ni da na fita sana'a ina ni ina kule kulen maza?".

"Ba haka nake nufi ba Hafsa, daidai gwargwado kina samun masu sonki, amma kin ƙi ki tsaida hankalinki, kuma ko wannan rashin fara'ar taki da haɗe rai, ya isa ya hana samarin kulaki".

Hafsa ta ce "Aikuwa su sha zamansu, dan ni ba su ne a gabana ba".

"Au haka ma zaki ce? Ai shikenan idan dangin ubanki suka kuma waiwayoki kya shiga hankalinki ai".

"Ai ba su da wani iko da ni, dan haka ba su da damar da zasu É—aga mana hankali, har yanzu ban manta da wahalar da muka sha a hannunsu ba".

"Ki manta ɗin dai shine yafi alkhairi, dan akwai gaɓar da dole a neme su a rayuwarki, mussaman a gurin Aure, dan kin san dai ni ba zan aurar da ke ba ko?".

Shiru Hafsa tayi, dan ko zancen Mutanen nan ba ta ƙaunar ayi sam.

***********
"Daddy" ta faɗa da ƙarfi tana rungume shi, kamar wata 'yar yarinya.

"Fadila ke dai ba kya girma ko? Don't you know, that you are now a big girl?" Mutumin yayi Maganar yana murmushi.

Tura baki Fadila tayi ta ce "Daddy wannan karon ka daÉ—e da yawa, kuma mu kayi waya da kai jiya baka gaya mini zaka dawo ba".

"Eh dama nace bari in yi surprising É—in ku ne kawai"

"Kamar yadda Yaya Khalil yayi mana kenan, sai ganinsa kawai muka yi a gida".

"Eh munyi waya, ya gaya mini yazo, na so in biya in ganshi ma, amma Allah bai nufa ba, ya school É—in, dama Mum É—inku tace mini kin fara zuwa".

"School gata nan so boring and frustrated".

"Da haka duk muka yi karatun, kawai ki maida hankali kiyi abin da ya kai ki, abin da duk baki gane ba, idan da wanda ya fiki ganewa ki zauna ya koya miki".

"Taɓ, salon a rainani ace mini daƙiƙiya, i better Google what ever i dont understand".

"But is not as accurate as what someone will guide and teach you, anyway i wil find someone to be assisting you at home after school" Cewar Alhaji Ahmad.

"A nice idea Daddy, thank you ina Mummy?"

"Nima ita nake jira, tana sashinta go and have some rest" Fadila ta miƙe tare da yasar da jakarta a nan falo ta wuce.

Hajara ce ta shigo tana kwashe kayan da Fadila ta zubar a falon, ta risuna ta gaida Alhaji Ahmad, hannu ya É—aga mata tare da faÉ—in sannu kawai.

Hajiya Zainab ta fito cikin gayu, ta zauna kusa da maigidan nata tana ta kwarkwasa, kamar Amarya.

Fadila ce ta kuma fitowa ranta a ɓace, ta tarar da Hajara na gyaraa falo, cikin faɗa ta fara yiwa Hajara magana "Wace ta gyara mini ɗakina a cikinku?"

Hajara ta ce "Asabe ce"

"Wai wasu irin banzaye ne ku? Kira mini ita, yarinya sai daƙiƙancin tsiya, kira min ita".

Alhaji Ahmad ya ce "Yaya, mai ya faru ne?".

"Daddy na gaji da halin maids É—in nan, sai ka yi ta maimaita musu abu É—aya amma basa ganewa".

Mummy ta ce "Wallahi ni kaina ina mamakin rashin tunanin na yaran nan, kai ta maimaita magana basa ganewa".

Asabe ce ta ƙaraso ta ce "Gani".

"Eh gaki na ganki, wai jahilar ina ce ke? In ta maimaita magana ba kya ganewa, na gaya miki kar ki sake maimaita mini bedsheet, da na tashi a cire shi a wanke, na bar underwear a toilet, kin wanke banɗaki kawai amma baki wanke mini ba, ni kike jira inje School in dawo in wanke? Idan naki ne zaki bar su baki wanke ba? Ko da yake ku dama ƙazanta a jininku take".

Asabe ta duƙa ta ce "dan Allah ki yi haƙuri, Hajiya ce ta samu aiki, ayyukan sun yi yawa yau saboda dawowar Alhaji".

"Shut up I don't care malama, aikina na sani dana saki kiyi mini, idan ba zaki yi ba you can park your load and go back to your useless village, 'yar ƙauye mara ganewa kawai"

Tun É—azu Hajiya Zainab suna falon, suna jin yadda 'yar su ke wannan zazzaga amma ba su tofa ba, sai yanzu Alhaji Ahmad ya ce "Easy Daughter, ai ta baki uzurinta, ke ki je kiyi mata aikin, and ke kuma 1ki daina yiwa mutane shouting haka ba daÉ—i".

"Daddy ni kaina ba jin daÉ—in shouting É—in nan nake ba, suke sani Wallahi".

Haka Asabe ta wuce sashin Fadila ranta a matuƙar ɓace, da jin zafin cin zarafin da Fadila tayi mata.

Da sassafe, bayan kammala ayyukan gidan, iyalan na kan dining suna cin abinci.
Hajara ta tarar da Asabe tana ta haÉ—a kaya.
"Asabe wannan kayan da kike haÉ—awa fa?".

Asabe ta ce "Ƙauyenmu zan koma".

"Saboda me?"

"Ba zan iya jure zama ana cigaba da ci mini mutunci ba, na haƙura da aikin na nemi wani gurin".

"Haba Asabe, yanzu kan ki samu wani gidan aikin fa?".

"Allah ba zai hana ni ba, na gaji da cin mutuncin nan".

Hajara ta ce "Na shiga uku ni Hajara, Asabe idan kika tafi aiki da jarabar mutan gidan nan kashe ni zai a gidan nan".

"Allah ya baki yadda zaki, amma ni ba zan iya ba na gaji, zan iya wankawa yarinyar nan mari".

Asabe ta fito falo da kayanta, ta kuma gaishe da su, Alhaji Ahmad ne ma ya É—an saki jiki ya amsa.

Asabe ta ce "Dama ina so zanje gida ne, ance mahaifiyata babu lafiya, zan je jinyarta bani da tabaccin zan dawo".

Mummy ta ce "To ki gaida gida"

Fadila ta ce "Allah raka taki gona" Asabe jiki a sanyaye ta miƙe, Alhaji Ahmad ya kirata, ya sa hannu a aljijunsa, ya ɗauko kuɗi masu yawa zai miƙawa Asabe.

Mummy ta yi caraf ta ce "Na meye kuma zaka bata wannan uban kuÉ—i haka? Naga an biyata kuÉ—in aikinta, wannan kuma na menene?".

Daddy ya ce "Ai wannan watan ya kai a biyasu, tun da  jibi in Allah ya kaimu zai mutu, kuma ai tayi aikin watan, gara a biyata kuɗin aikinta, kuma a bata na siyan magani, ai ko bakomai an moreta a gidan nan" ba dan Mummy ta so ba, ya bawa Asabe kuɗi kusan dubu sittin ya sallameta.

Hajara kuwa zullumi ta shiga da taradaddi, ta san duk wata wahala da ɗawainiyar gidan nan kanta zata dawo ita kaɗai, ga mutanen gidan da shegen sa aiki su kuma ga son jiki, in an bar 'yar aiki ta huta to fa dare ne yayi, suna su biyun ma da ya suka ƙare, balle yanzu sai ita kaɗai.

*********

"Yawwa Hanne, yau da Yamma Malam Rabi'u zai kawo kuɗin Auren Amina, duk da ina samun labarin yadda kike zigata take masa rashin mutunci, bata saurarsa to ki sani duk wani ƙulle ƙullenki da makircinki ba zai hana Auren nan ba".

Inno ta ce "Ni wani ƙulle ƙulle zan akan auren nan, ni da nake 'yar karere?" Tayi maganar cikin ladabi kuma a sanyaye.

Kawu Bala ya ce "Oho miki dai, kuma anwa gonar Hassan kuÉ—i, dubu É—ari uku, zai kawo kuÉ—in gonar da na Auren, sati biyu kawai za'a saka ba wata bidi'a za a tsaya yi ba".

Amina dake ta ƙoƙarin tuƙa tuwo ta zabura ta ce "Gonar baban ce dubu ɗari uku? Wallahi kawu cutarku zai yi gonar nan tafi haka".

"Zaki rufe mini baki ko sai na zo na danna kanki a murhun nan? Fitsararriya mara kunya ina Magana kin tsoma baki, naga uban da ya isa ya hana a siyar da gonar nan ayi auren nan" Amina ta sunkuyar da kai, ranta na mata ƙuna, Shikenan duk wata kadara da Baba ya mallaka an kaɗar da ita.
Chapter 9 · 0% Book details