← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 84

Sashe 7

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abdul yayi dariya ya ce "Ba zaka ƙare a kai na ba, amma Allah yasa ginin da na ke a Kano ya burge Fadila, wai ni kana ma miƙa mata saƙon gaisuwata kuwa?"

Jikin Khalil ne yayi sanyi amma ya dake ya ce "Malam kawai ka rabu da wannan yarinyar".

"Saboda me? Ko dai ba zaka bani ita bane, saboda ni talaka ne?"

"Kai haba dai, wace irin magana ce wannan, ni ba ruwana ka nemi soyayyarta kawai, zan wuce maka gaba gurin Daddy, yanzu dai ka tashi muje yawo".

"Yawo kuma? Kai zaka mini aikin marking É—in?".

"Kai dalla ka dena takurawa kan ka malam, zo muje Chilling kawai".

"Gaskiya ka hanzarta ka zo ka koma in da ka fito, duk ka addabeni tun lokacin da ka dawo".

"Wallahi sai ka taso"

Abdul ya ce "To Jarababbe ai ka bari in tashi in kintsa ko a haka zan fita?".

"To kintsa mu fita".

Khalil yana jin daɗin abotarsa da Abdul, iyayen Abdul talakawa ne, ƙoƙarin sa da kuma rahamar ubangiji ya sanya ya samu Scholarship, na karatu a Malesia, wanda a nan suka haɗu da Khalil, Mahaifiyar Khalil ba ta son mu'amalarsu Saboda shi ba ɗan masu kuɗi bane, amma Khalil ya nacewa Abdul.
Abdul ya fuskanci Mahaifiyar Khalil ba ta son sa, dan haka ba ya son zuwa gidan sam, Khalil yana da izza irin ta yaran masu kuÉ—i, saboda ko ba komai É—abi'a naso take, amma bai san yana yi ba, kuma sam baya nunawa Abdul Izzar.
Babban abun da yasa yake son Abdul shine, mutum ne mai wadatar zuci, ga girmama mutane, dan idan mahaifin Khalil yana gari, wataran ya kan sai abun da yake da shi, yaje ya gaisheshi, hakan yasa shi kansa mahaifin Khalil yake son Abdul.
Ganin ba yadda Hajiya Zainab ta iya ne, ya sa ta ƙyalesu suke abota, hatta motar da Abdul yake hawa, Khalil ne ya bashi.
Mahaifin Khalil shine ya samarwa da Abdul aikin lecturing, ya yin da nasa É—an ke can Hukumar Land a Abuja.
Abdul ya daɗe yana son Fadila, amma ya kasa gaya mata, saboda yanayin yadda ta ke gudanar da al'amuranta. Hakan ya sanya ya gayawa Khalil yana son ƙanwarsa, Khalil ya ji daɗi, amma ya san ba abune mai yiwuwa ba, saboda yadda ahalin su ke ƙyamar talaka!.

**************
Yau ta kasance ita ce ranar Fadila ta farko a Makarantar Jami'a, sai da aka sha yaƙi da ita, sannan ta tashi ta shirya da safe, tamkar wata ƙanƙanuwar yarinya.
Mummy sai mita take tana in dai haka Fadila zata cigaba, Wannan karatun ba mai yiwuwa bane ba sam.
  Da kanta tayi driving motarta zuwa School, sai dai ta dinga bin 'yan ajin nasu da wani irin kallo mai kama da na ƙasƙanci.
Guri É—aya ta ware, can gefe guda ta yi zamanta, ba tare da ta shiga sabgar kowa ba, sai hura hanci kawai da take yi.
Malamar farko da ta shigo fara yi musu lectures, ta yi musu nasiha sosai a kan mahimmanci mai da hankali a kan karatu, da irin yanayin yadda rayuwar Jami'a ta bambanta da ta sakandare.
Ba laifi malamar ta sha gayu tsaf da ita.
Ajin ya haɗa da waɗanda suna kammala Sakandire suka samu gurbin karatu, da waɗanda suka shafe lokaci a gida ba a samu gurbin karatu ba, a taƙaice dai ajin ya haɗa yara, matasa da kuma dattawa.
Ƙarfe sha biyu, Fadila ta ɗau jakarta ta koma gida, ba dan an gama lectures ɗin ba, sai dan yadda gaba ɗaya zaman makarantar ya ishe ta, ga warin hammata da wasu daga cikin samarin ajin suke yi, duk da wadattaciyar iska da fankoki da suke ajin, amma bai hana wasu idan suka gifta taji ba, wanda hakan ya sa ta fara jin tashin zuciya ta ce ba zata iya zama ba.

***********
Kamar kullum bayan sallar magariba sannan kayan sana'ar Hafsa suka ƙare, ta tattara kayanta ta nufo gida, sai dai tun daga yadda ta ji Mama ta amsa mata sallama ta san jikin Maman babu daɗi.

Cikin azama Hafsa ta shiga É—akin tana faÉ—in "Mama ya naji muryarki haka? Jikin ne?".

Mama dake kwance ta tashi zaune da ƙyar ta ce "A'a lafiyata ƙalau Hafsa har kin dawo" ta yi maganar tana haki.

"Mama gashi kina haki, amma kice mini lafiyarki ƙalau? Bari in ɗauko miki maganinki"

Hafsa ta tashi da sauri ta nufi in da take ajiyewa Mama magungunanta, Mama kuwa bin Hafsa tayi da ido, cike da tausayawa.

Hafasa na duba gurin magungunan babu sai fankon ledar maganin, ta kalli Mama jiki a sanyaye ta ce "Mama dama maganin ya ƙare baki gaya mini ba?"

"Bana son tayar miki da hankali ne, kuma dama kin ce jari yayi ƙasa, bashi yayi yawa, kinga dole a lallaɓa kar mu cinye jarin gaba ɗaya".

"Haba Mama, ai lafiya gaba take da komai, kuɗi kona waye ai gara in taɓa  in sai miki magani, bari im je gurin Magaji, idan yana nan ya zo ya duba jinin naki, sai in taho miki da maganin".

"To Hafsa, kar ki daÉ—e amma, kiyi maza ki dawo ga wani Abinci can na ajiye miki"

Hafsa ta ce "To mama, daga nan ta fice".

Kai tsaye chemist É—in Magaji ta tafi, ta tarar ba kowa a shagon sai shi da wani abokinsa, wanda duk unguwarsu É—aya.

Tayi musu sallama suka amsa mata, ta kalli Magaji ta ce 'Magaji dan Allah so nake a duba mini awon jinin Mama, idan ya hau ne sai a bata maganinta, na dawo na tarar tana haki".

Magaji ya ce "Gaskiya ina da abun yi yanzu".

"Don Allah ka taimaka, bata da lafiya sosai" tayi maganar cikin damuwa.

Magaji ya ce "Ashe alfarma tana da daÉ—i Hafsa? Ai da har gida nake zuwa ina yiwa mahaifiyarki gwajin, amma na nuna ina sonki, ba kunya kika nuna ba kya sona, kuma saboda kina da kunya shine kika kuma dawowa neman alfarma a gurina".

"Ita Alfarma ana nemanta ne a in da ya dace, ana alfarma akan komai amma banda So, ban taɓa keta bulle na na nemi Alfarmar wani ba, saboda gudun ƙasƙanci sai a gurinka, kuma ka nuna mini iyakata, daga yau ka rubuta ka ajiye, idan ni Hafsa na kuma neman Alfarma a gurinka, kai mini duk cin mutuncin da ka ga dama" tana gama faɗin haka ta juya ta bar Chemist ɗin.

Tana tafiya Magaji ya ce "Aikin banza, yarinya ba 'yar uban kowa ba, sai izza da girman kai, tana 'yar talaka futuk, tana suyar awara akan kwalbati, amma zan nuna ina sonta ta wulaƙantani".

Abokin Magaji mai suna Nura ya ce "Nikam burgeni take, ba ruwanta da shirme da rawar kan 'yan matan unguwar nan, a nutse take".

"Kai dalla ware, ba wata nutsuwa, duk buge ce, ni ban ma san tsautsayin da ya kaini cewa ina sonta ba, bayan ma 'yar mace ce, har wata nutsuwa ko tarbiyya ce da 'yar mace?".

Nura ya ce "A'a Magaji, da ta yarda da soyayyarka, ba zaka kirata 'yar mace ba".

Haka Magaji ya cigaba da sukan Hafsa, Nura yana karewa.

Hafsa kuwa ganin kuɗin hannunta ba su da yawa, ta san ba zasu isa ta kai Mama Asibiti ba, haka ta haƙura taje wani Chemist ɗin ta sai mata irin maganinta, duk da akwai buƙatar a sake gwada jinin amma babu yadda ta iya.

Khalil ne ya shigo ya tarar da Fadila tana gayawa Mummy yadda 'yan ajinsu suke, da yadda wasu suke addabar su da warin hammata.
Khalil ya ce "Zaki ga warin hammata, kije ki yi musu hauka suyi miki dukan tsiya, dan ba kowa zai É—au rashin kunya ba".

"Aikuwa da na saka an kulle mini yaro kowaye ubansa a garin nan" Mummy tayi Maganar tana zazzare ido.

Khalil ya girgiza kai ya ce 'To ni dai jibi in Allah ya kai mu zan koma gurin aiki".

Mummy ta ce "Allah ya kiyaye hanya, dama ka takurawa 'ya ta, gashi kuma next week babanku zai shigo gari".

Khalil ya ce "Allah bai yi zamu haÉ—u ba, ma yi waya da shi".

**************
Gaba ɗaya yau Amina ta wuni jikinta babu daɗi, wanda tsabar damuwa da kuka ya haifar mata da ciwon kai, yau 'yan ajinsu suke zana paper ƙarshe babu ita, haka ta sha kukanta ta godewa Allah.
Inno ta tursasa mata cin abincin dare, dan wuni tayi ba ta ci komai ba, sai kwanciya.
Tana tsaka da cin tuwon ne, É—an gidan Baffa Lawan yayi sallama ya ce "Amina kije Malam Rabi'u yana sallama da ke a waje".

Amina ta ce "Ka je kace masa bana nan". Yaron ya juya ya fice.

Inno ta ce "Wato ke dai Amina ba kya gudun magana ko?".

"Inno to ni ya ake so in yi? Ni Wallahi ba zan iya Auren wannan mutumin ba".

Suna cikin Magana Baffa Lawan ya shigo yana hayagaga yana É—aga murya.

"Wato wuyanki ya yi kaurin da za'a ce ana sallama da ke ki ce aje ace ba kya nan? Zaki tashi ki je ko sai na kakkarya ki, sakarya yarinya mara Albarka".

Amina na kuka ta tashi ta Sanya hijjabinta, Baffa Lawan ya cigaba da sababi yana cewa Inno ce ke goya mata baya take rashin mutunci.

"Kuma ki san da saninki, na saka gonar babanki a kasuwa, an samu mai saye gobe za muje mu karɓo kuɗin, ai miki kayan ɗaki ds su, Hassan ko yana nan ko ba ya nan, zamu aurar da ke"

Ƙara fashewa da kuka Amina ta yi, ta nufi hanyar fita tana goge hawaye.

Malam Rabi'u yana tsaye a ƙofar gida, yana ganin Amina ta fito ya fara murmushi, duk da babu wadataccen haske a gurin, amma hakan be hanashi ƙare mata kallo ba.

"Amaryata barka da wannan lokaci, ya Mutanen gidan?".

"Yanzu tsakani da Allah ka yi mini adalci kenan? Dan me zaka takura sai ka Aureni? Nace maka ba zan iya aurenka ba, ana dole ne?".

Malam Rabi'u ya ce "Ai ko ba kya so na ni ina sonki, kuma wan mahaifinki ya ce ya bani ke, kuÉ—in Aure kawai zan kawo wani satin, kuma ba za'a sanya lokaci mai tsawo ba".
Chapter 7 · 0% Book details