Sashe 54
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ai bece muje tare ba"
Fadila ta ce "Ni dai yi sauri ka gama"
Ita kanta har mamakin kanta take yi, yadda yau ta saki jiki da Yazeed, ita gaba ɗaya a rayuwarta bayan 'yan gidansu sai Yusra, sukaɗai ne mutanen da suke bata nishaɗi, dan ita ba shiga harkar mutane take ba, amma Yazid mutum ne mai matuƙar barkwanci, duk haushinsa da kake ji, sai ta fuskanci in ka zauna tare da shi zai baka dariya, sai dai shima ba kowa yake shiga harkarsa ba, balle ka gane tsananin sauƙin kansa, gashi baya fushi abinsa, ga rashin girman kai.
Gaba É—aya ya manta da su Amra da ke jiransa, ya kammala typing ya kalleta ya ce "to muje Cafe a cire, sai a rabawa 'yan group"
"Sai fa kaci Abincin nan"
Ya É—an waro ido "In karya azumin nawa?"
"Ai ba azumi kake yi ba" tayi maganar tana sake tsareshi da ido.
Ta saka shi a gaba, ya ciro pack É—in Abincin, soyayyar doya ce da miya sai uban nama fal a cikin miyar, sai ruwa da lemo.
Ruwan yai bisimillah ya fara sha. Fadila ta ce "Kana malami kana ƙarya, yanzu azumin kenan?"
"Niba malami bane, É—alibi ne, kuma aike kika karya mini Azumin"
"Wata ƙaryar again" tayi maganar tana hararasa.
Bece mata komai ba, ya fara cin doyar da ƙamshin miyar kawai ya sanya yawun bakinsa tsinkewa, Fadila ta juya masa baya tana danna waya, yayin da shi kuma gaba ɗaya ya kasa sakewa, Yazeed yana da matuƙar gudun zuciya da abin da zai sa a masa gori wata rana, ya ci Abincin nan ne kawai dan yana son ganin yayi abin da zai sa Fadila taji daɗi, ba wai dan yunwar da ta addabi cikinsa ba.
Ya kammala ya dinga yi mata Addu'a, har sai da ta haÉ—e rai, saboda godiyar tayi yawa.
Sai da suka fara zuwa Cafe, suka ciro aikin, sannan Fadila ta ce suje wurin Sir Kankiya.
Sai dai da suka je, suka tarar baya nan, suka zauna zaman jiran Kankiya, Yazid ya cewa Fadila ta tafi kawai zai jira shi, amma taƙi, saboda ba ta san me zai cewa Yazid ba.
Ƙarshe Fadila ta gaji da zaman, tayi masa sallama ta tafi, a kan Cewar duk yadda suka yi da shi ya gaya mata. Yazid ji yake kamar yayi tsalle dan murna, saboda kulawar da Fadila ta nuna masa yau, zuciyarsa bata taɓa kamuwa da tsananin son abin da yake kasancewa da shi ba kamar Fadila.
Alhaji Ahmad ya dawo gida, kusan ƙarfe biyar na yamma, sai dai daga yadda suka gaisa da Baba, ya lura kamar akwai damuwa a tare da shi. Alhaji Ahmad yayi parking, tare da kallon sa ya ce "Malam Hassan, lafiya naga kamar kana cikin damuwa?"
Baba ya risuna ya ce "Amina ce haryanzu bata dawo daga Makaranta ba, gashi ban san makarantar tasu ba balle in bi bayanta, nayi wauta yakamata ace tun tuni na san makarantar ta su"
Daddy ya ce "Subhanallah, kwantar da hankalika, bari in je makarantar da kaina"
Baba ya ce "A'a ranka ya daÉ—e, da ka kwatanta mini ni sai inje in duba"
"Haba Malam Hassan, Amina ai 'ya ta ce, idan Fadila ce zan wakilta wani ya nemota ne? Bari inje" yayi reverse ya ja motar ya ya nufi makarantar su Amina.
Alhaji Ahmad kai tsaye cikin makarantar ya shiga, ofishin director ya shiga, suka gaisa, Daddy yake tambayarsa yaji shiru haryanzu Amina bata koma gida ba.
Director yayi murmushi ya ce "Mun tsaresu ne, lesson ake tayi musu, lallai muna son wannan karon branch ɗin Kano, muci comptetions ɗin wannan shekarar, kuma Alhamdilillah Amina akwai basira, duk da ɗazu na zagaya ajin nasu, taƙi mayar da hankali wai ita ta gaji gida zata tafi"
Daddy yayi murmushi ya ce "Dole ta gaji, tun safe fa, kuma gashi in Allah ya kaimu next week, za kuyi resuming makaranta, kaga ita gaba É—aya bata huta ba kenan"
"Haka ne, amma da anyi an gama shikenan, kuma idan Allah yasa tayi nasara, zaku yi alfahari da hakan, tana da ƙwazo sosai"
"Gaskiya ne, yanzu dai a ƙyaleta, tun da tace ta gaji ba ganewa zata yi ba, a turota mu tafi gida"
Director yayi murmushi ya ce "Dama yanzu za a tashe su su tafi, kuma dan wannan ranka ya daÉ—e ai da ko waya kayi, da kaina ma sai in dawo da ita gida ba sai ka zo ba"
"Ba komai, a turo ta mu tafi"
Suka fito daga Office É—in tare da Alhaji Ahmad.
Tunda aka sanarwa da Amina Babanta ya zo É—aukarta, ita zatonta Baba ne, ta san a rina, yadda tayi yammar nan, dole hankalinsa ya tashi ya biyo bayanta.
Sai jefa ƙafa kawai take, idanunta sunyi fuci-fuci sun yi jawur, jakar ma yadda ta saƙalata da gani ta mata nauyi.
Mamaki ne yakamata ganin Daddy a harabar makarantar.
Murmushi yayi mata ya ce "Sannu, sai kace wadda ake bawa training É—in sojoji, duk kin yi wujiga-wujiga".
Aikuwa kamar ƙiris take jira.
Kamar za tayi kuka ta ce "Ni ba zan ƙara zuwa lesson ɗin nan ba, duk anfi wahalar da ni, gashi na gaji ga yunwa nake ji, bayana sai ciwo yake da cikina" tayi maganar a wahale, ƙwallar haushi na taruwa a idonta.
Alhaji Ahmad yayi murmushi ya ce "Eh gaskiya kam basu kyauta miki ba, ace mutum yana jin yunwa, kuma ga mutum rago Sarkin kuka, ace an hana shi tafiya gida dole a sa mutum ya gaji ai, har ya fara kuka" ya ƙarasa maganar yana murmushi.
Amina ta gane tsokanarta ya ke yi, sai kawai ita ma tayi murmushin, sannan ta ce "Ya aka yi ka san makarantar mu?"
"Tunani nayi, zuciyata ta bani nan ce makarantar" É—an shiru tayi tana tunanin ya za ayi haka ya yiwu.
BuÉ—e mata gaban motar yayi ya ce ta shiga.
"Wai gaban motar zan shiga?"
"A'a tayar motar zaki hau". Ya faÉ—a tare da zagayawa mazaunin direba.
Ƙarewa motar kallo take, irinta kusan uku ne a gidan, Alhaji Ahmad ne kawai yake hawansu, baya hawa ƙananun motoci sai manya manya, ko nauyi basa masa wurin tuƙawa. Tayi maganar a zuciyarta.
Sai da tayi bismillah sannan ta hau motar, wani irin sanyi tare da ƙamshi suka ratsa hancinta, abinka da wanda yake a gajiye, ta sake kashingiɗewa a jikin seat ɗin motar.
Ya sawa motar lock tare da rufe glasses ɗin, ya ƙaro sanyin A.C ya fara jan motar.
"Tun da nake ban taɓa hawa mota me daɗin wannan ba, ko ta Khalil ba ta kai wannan daɗi ba".
"Allah ko?" Ya faÉ—a yana murmushi.
"Wallahi kuwa, kamar in bacci, to wai motar bata da nauyi ne, naga tayi girma da yawa kuma kana tuƙata a haka"
"Ko in sauka in baki wuri ki gwada kiji"
"A' a rufamini Asiri, ina zan iya"
Sai kuma tana ɗan yamutsa fuska ta riƙe cikinta.
Ya kalleta cikin kulawa ya ce "Ya dai?"
"Cikina ne yake ciwo"
"Yunwa kike ji, daga yau idan zaki zo lesson, ki dinga zuwa da Abinci, zan bawa babanki kuÉ—i, ya dinga baki kina sayen Abinci"
A ɗan tsorace ta ce "Taɓ salon ya ce roƙonka nayi, ni bana roƙo, kuma daga yau ba zan sake zuwa wannan lesson ɗin ba, na gaji ai nasara ta Allah ce, ba wannan izayar ce zata sa in ci ba" tayi maganar ranta a ɓace.
Alhaji Ahmad ya ce "Baki san abin da yake tattare da yin nasararki ba, kiyi haƙuri nasara sai an wahala take samuwa, sannan idan mun je gida, za kiyi wa Maman Fadila bayanin abin da ya kai littafinki ɗakin aikin mijinta"
Zaro Amina tayi ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, a can na bar shi kenan? Na shiga uku me zance mata?"
"I don't know" ya faÉ—a yana É—age kafaÉ—a.
"Na shiga uku ni Amina, Daddy kai ka jawo mini, baka gayamata kai kace in kai maka Abinci ba, shikenan wataƙila ta koreni karatuna shikenan, idan kuma tayi mini Afuwa kuma ta zageni ni da Baba" kan ta kai ƙarshen maganar, kuka ya ƙwace mata.
"Ke kuka baya baki wahala ne? Da wasa nake miki na karɓi littafin, na gaya mata ni na saki aiki a ɗakin, littafin yana wurina, meyasa kika ruɗe haka?"
Ajiyar zuciya Amina tayi, tana godewa Allah da ya ƙwaceta, da yau ta san tijarar da zata sha ba ta da iyaka.
Tausayin ta ne ya kama shi, da alama ita ma zata sha gwagwarmayar rayuwa kan ta cinma nasara, ya É—an lumshe idanunsa ya ce "Allah ya rangwanta miki" ya furta a hankali ba tare da Amina ta ji ba.
A ƙofar gida yayi parking ya kalli Amina ya ce "Sauka ki shiga, idan kuma in shiga dake ne, idan ta ganki ki mata bayanin abin da ya kai ki motar mijinta kuma shikenan".
"A'a yi haƙuri bari in sauka, Na gode Allah ya saka da alkhairi".
Bai amsa mata ba, sai binta da yake da kallo.
Baba na ganin Amina ya tareta, yana tambayar ba'asin meye ya faru ta daÉ—e haka?
Amina tayi masa bayani, tare da gaya masa Alhaji Ahmad ne ya É—aukota.
"To ki dai kula Amina, hanklina ya tashi sosai"
"To Baba ka cigaba da yi mini Addu'a"
"Aminatu Addu'a kullum cikinta muke ai"
A falo ta tarar da Hajiya Zainab da Khalil, ta durƙusa ta gaishe su, Khalil ya amsa Hajiya Zainab kuwa ko kallonta ba tayi ba, Amina da ta juya baya a hankali ta ce "kanki ki ka yiwa da baki amsa ba'
Khalil ji yake kamar ya janyo dare, dan yaje ya ga Hafsa, sai wata fara'a yake ta mussaman.
Alhaji Ahmad yayi sallama a falon, suka amsa masa gaba É—aya, ya kalli Khalil ya ce "Kai saukar yaushe?"
Khalil ya amsa da "ÆŠazun nan Daddy"
"Masha Allah, ya aikin?"
"Aiki Alhamdilillah Daddy"
"Masha Allah, Ina Fadila ne?"
Mummy ta ce "Ta dawo tana É—aki tana baccin gajiya"
Ya jinjina kai ya wuce part É—insa.
Fadila kuwa bayan littafinta ta juya, tana kallon rubutun da Yazid yayi, sai mamaki take yadda aka yi ya iya kwaikwayon rubutunta, Yazid yana da abubuwan ban al'ajabi.
Tunowa tayi da maganarsa wai Azumin samari yake yi, kawai tayi murmushi ta rufe littafin.