Sashe 10
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Albarkacin Asabe, ya sanya Alhaji Ahmad ya biya sauran ma'aikatan da ke gidansa kuɗaɗen albashinsu, duk da watan bai mutu ba. Hakan ba ƙaramin daɗi ya yiwa ma'aikatan ba, dan idan baya nan sai sabon wata ya kwan bakwai, matar gidan ba ta biyasu haƙƙoƙinsu ba.
Baba Hassan ji yake ina ma tun kan a rufe jarrabawar su Amina, aka biya albashin nan, da ko duka kuÉ—in ya kama zai bada albashin nasa ta biya jarrabawar.
Da yamma Baba Hassan ya nemi izini, ya tafi tasha in da su Saminu ke lodin can garin su Baba Hassan, Saminu ɗan garinsu ne, shi yake bawa duk wani saƙo da yake kai wa su Amina.
Kamar yadda ya saba yi, ya É—an yi siyayyar kayan Abinci, da sabulun wanka da wanki da su man shafawa, ya É—ora kuÉ—in kashewa ya kaiwa Saminu tasha ya ce ya kai wa su Amina, ace musu yana nan tafe yazo ya gansu da ya samu lokaci.
Amina ta yi murna da ganin Saminu, dan har satar hanya tayi, da ƙafafuwanta ta tafi babbar tasha ta garinsu, tana neman Saminu amma baya nan. Sai gashi katsam ya kawo musu aike daga wurin Baba Hassan.
Bayan gama gaisawa da Inno da Amina, Amina ta gyara zama ta ce "Dan Allah ka kira mana Baba a waya, ina son Magana da shi".
Saminu ya ce "Sai dai wayar tawa babu kuÉ—i sosai, amma bari in jarraba kiransa a waya". Saminu ya kira wayar Baba Hassan, amma shiru ba ta shiga.
Saminu ya ce "Amina wayar ba ta shiga, idan da wani saƙo ne ki bani in kai masa".
Shiru Amina ta yi, tana jin yadda zuciyarta ke wani irin zafi.
Inno ce ta ce "Hmm, ka sanar masa 'yan uwansa za su aurar da Amina ga Malam Rabi'u Jarmai, kuma zasu sayar da gonarsa su yi mata kayan É—aki".
Saminu ya kalli Amina ya ce "Wace irin magana ce haka? Ina laifin su jira ya dawo? Kuma kamar ba su san halin Rabi'u Jarmai ba, karatun nata fa"
Inno ta ce "Kaga kar ka tunzurata, Aure ba laifi bane gallafirin da take a titi da sunan boko sam bai yi ba, amma wanda zasu haÉ—ata da shi É—in ne ba mutumin kirki ba ne"
Saminu ya jinjina kai ya kalli Amina da hawaye suka wanke mata fuska ya girgiza kai ya ce "Kiyi haƙuri Amina, insha Allah zan sanar wa da Baba Hassan ɗin, ki daina kuka".
Amina ta jinjina kai, tana ji a jikinta idan har Baba ya samu labari, wataƙila ya iya taimaka mata ta samu sassauci.
Su kayi sallama da Saminu ya tashi ya tafi.
Tun da Saminu ya tafi, jikin Amina yayi sanyi, tana tunanin ya Baba zai ji idan yaji ana shirin katse cikar burinsa a kanta, da kuma salwantar da 'yar gonar da ta rage ya mallaka.
Bayan tafiyar Saminu, Inno ta shirya ta fita, saura Amina kaÉ—ai a gidan.
"Assalamu alaikum, wai ana sallama da Amina" cewar wani yaro da ya afko ba sallama.
Amina ta ce "Kai kar ka sake shigo mana gida ba sallama, kuma ka koma kace masa ba zan zo ba, ya san in da dare yayi masa"
Amina ta shige ɗaki abin ta, tamkar ba da ita ake sallama ba, sai da yayi kusan aike huɗu amma mirsisi ta ƙi fita. Allah ya taimaketa Inno ba ta nan, balle ta tursasata sai ta fita.
Amina na nan zaune, tana sake duba litattafanta na makarantar boko tana hawaye, ta ƙallafa ranta a kan karatu, ta ɗakko littafin da ake shigar mata da makinta na haddar Alqur'ani a makarantar boko. Ta haɗa kai da gwiwa ta din ga kuka, tana tunanin meye mafita, dan ko a ƙafa a ka ɗaura mata Malam Rabi'u Jarmai, sai ta gutsure ƙafar ta huta, amma ta yaya zata iya daƙile wannan Auren? Tana cikin kukan wani tunani ya faɗo mata, cikin hanzari ta miƙe tsaye. Sai dai murayar da ta jiyo ana kwaɗa sallama ce ta sanya gabanta ya faɗi, ta dafe ƙiji tana faɗin "Innalillahi wa Innalillahi raji'un"!
Domin gyara sharhi ko shawara
08081012143
GABA DA GABANTA
Page 5
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
Litatafaina na AƘIDATA DA RUƊIN ƘURUCIYA duk na kuɗi ne Please.
Ta taga Amina ta leƙa, sarai ta ɗau Muryar su waye, kasa amsa sallamar ta yi dan bata san da wani idon zata kallesu ba.
Yadda suke kwaɗa sallamar ba ƙaƙƙautawa ne ya sanyata amsawa, tare da fitowa daga cikinu ɗakin.
Kallo ɗaya ta yi musu gabanta ya faɗi, dan bata san da wacce suka zo ba, 'ya'yan Malam Rabi'u jarmai ne, wanda ƙawayen ta ne, sai dai su duk sun yi Aure, har da mai yara biyu, Iklima da Shema'u.
Amina ta ɓoye damuwarta ta ce "Shema'au sannunku da zuwa, ku shigo".
Iklima ta ce "Ji munafuka, mu shigo ina, algunguma ki rasa wanda zaki aura a garin nan dan rashin ta ido sai mahaifinmu, Wallahi kin ji kunya Amina".
Shema'u ta karɓa da "Ai zuwa mu ka yi mu ja miki kunne, Wallahi baki isa kiyi kishi da iyayenmu ba, gidanmu kamar kabari ne, Wallahi kika shiga azaba da wahala sai sun koreki da ƙafafuwan ki, gara tun wuri ki san abin yi".
Jiki a sanyaye Amina ta ce "Shema'u ku yi haƙuri, ni kai na ba son Auren nan nake ba Wallahi, kuma har yanzu ban ji a jikina zan iya Auren mahaifinku ba....
"Ba wani nan rufe mana baki, kwaÉ—ayi ne ya sanya zaki auri baban mu ba wani abu ba".
Amina ta ce "Wallahi ba haka bane, ku tambaya ku ji Wallahi ni ba son mahaifinku nake ba".
"Yi mana shiru munafuka, har akwai yarinyar da ta isa ta ce ba ta son babanmu, zaki aure shi dan kwaɗayi, an yi kwantai a gari an ƙare a hanyar boko, ba abin da bokon ta amfana miki, kin gama gantalinki za a liƙawa babanmu, Wallahi ki ka aure shi ƙannenmu sai sun illata ki".
Amina ta ce "Naga ina ta lallaɓa ku kun kasa ganewa, to bari in fito muku a yadda kuke so, ni bana son mahaifinku shine ya nace mini sai ya aure ni, sai wani ihun kwaɗayi kuke yi, meye a gidan naku kuɗin baban naku da ba ci ake ba, tuwo safe rana dare, miyar gidanku kamar ruwan tsarki, kullum a wahala kuke, ya auri wannan ya saki waccan, insha Allah babu abin da zai sa in Auri babanku iyayenku ma fama suke, ta kan su suke yi".
Shema'u ta ce "Kutt, baban namu kike gayawa haka?".
"An gaya masa É—in, yayi zuciya ya daina mayar da 'ya'yan mutane dan yana da kuÉ—i".
"Gara namu uban an san aure yake yi yana saki, wayasan me naki uban yake aikatawa a birni".
"Bakomai tun da ba'a san me yake ba, naku uban kuwa kowa ya san me yake yi, me ake da mutumin da bai san martaba da darajar Aure ba" ganin Amina ta fisu baki ya sanya suka fita suna ƙananun maganganu.
Amina ta koma ɗaki tayi shiruu, tana tunanin mafita, tabbas ta san idan ta auri Malam Rabi'u kashinta ya bushe, dan a gidan nan babu kalar yaran da babu dan wasu daga manyan 'ya'yansa yayyen su Shema'u 'yan daba ne, ga uwar gidansa ita ce babbar masifaffiya, gidansa tuwo kwano uku zuwa biyar ake tuƙawa, idan ranar girkin ki ce ke zaki tuƙa wannan tuwo, sai a kwan uku ana cinsa.
"Kai ba zai yiwu ba, Wallahi ba zan yadda in auri wannan mutumin ba".
"Ke Amina, au zama ki ka yi kina koke-koke, har da surutai ba zaki dangana ba?" Ta jiyo muryar Inno.
Cikin kuka Amina ta ce "Wallahi Inno ba zan auri Malam Rabi'u ba, yanzun nan su Shema'u suka bar gidan nan, ba ki ga cin mutuncin da suka yi mini ba, wai kar in auri babansu ni ce musu nayi ina son babansu, Inno wallahi bana son Mutumin nan ki gaya musu".
"Amina ta yaya zan ce musu ba kya son sa ni a wa? Yanzu haka da na dawo ya tsareni a ƙofar gida, wai sun karɓi kuɗin Aurenki, da kuma kuɗin gonar mahaifinki, wai za'a kawai Jamila dillaliya dubu hamsin a samo miki gado ɗan hannu, a kaiwa Liti kafinta shima wai idan da kujeru na hannu a sai miki, an saka sati uku bikin".
Fashewa Amina ta kuma yi da kuka ta ce "Wallahi ba zan auri wannan mutumin ba, tun yanzu 'yan'yan sa sun fara zuwa suna ci mini mutunci, kuma dan tsabar mugunta an siyar masa gonar babana da arha ya siya, kuma a siya mini kayan É—aki 'yan hannu, dan an mayar da ni mara galihu".
Bakinta Inno ta gwaɓe ta ce "Dan ubanki 'yan uwan mahaifin naki kike gayawa haka, salon su zo su ji suce ni nake ziga ki? Ke a rayiwarki ba ki san tawakalli ba da duk abin da Allah ya tsarawa bawa ba shi da ikon kuskurewa ba, kamar iyaye suke a gurinki fa".
"Ni Wallahi ba iyaye na ba ne, tin da suke son kassara rayuwata, da tozarta mahaifina an cutar da shi an raba shi da gonarsa ba da saninsa ba".
Inno ta bi Amina da kallo, Amina kenan akwai haƙuri wasu lokutan, wasu lokutan kuwa akwai gardama da taurin kai, dan Inno ta fara fagabar yadda Amina ke cigaba da adawa ƙarara da Auren da ake son a yi mata.
*****************