← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 84

Sashe 52

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Azima ta kalli Amminta, Ammi ta jinjina mata kai. Azima ta tashi, ta ta shiga ƙofar, cikin ikon Allah, ta tarar da Amina na ta aikinta.

"H Shanono" Azima ta faɗa da ɗan ƙarfi, Amina na waigowa taga Azima tayi tsalle ta rungumeta tana murna.

"Azima, ya akai kika zo baki gaya mini ba?"

"Ke sauri muke, Ammi na falo muje ku gaisa zamu tafi"

Cikin mamaki Amina ta ce "Dan Allah dagaske har da Ammi kuka zo, muje in ganta"

Tare suka fito falon da Azima, Amina ta ƙarasa gaban Ammi ta durƙusa tana gaisheta.

Cikin fara'a Ammin ta amsa "Lafiya ƙalau Amina, ya karatu Azima ta ce mini makarantarku ta zaɓe ki, a Quiz ɗin su na ƙasa"

"Eh Ammi"

"To a dage ai ta karatu, Allah ya bada sa'a, Azima ce ta nuna mini layn naku, na ce bari in Shigo mu gaisa"

"Amma kuwa naji daÉ—i Ammi, bari in kawo muku ruwa ku sha"

"Babanki ya saya ya ajiye ne?" Cewar Mummy, cike da son ta wulaƙanta Amina a gaban mutane.
Jikin Amina yayi sanyi ta sunkuyar da kai, Azima tayi mamakin abin da Hajiya Zainab ta faɗa, dan bata taɓa sanin irin zaman da Amina take kenan ba, saboda duk surutun Amina bata wannan zancen.

Ammi ta ce "Bakomai Amina, a ƙoshe muke ina da ruwa a mota"
Ta ƙarasa maganar suna miƙewa tsaye, jiki a sanyaye Amina ta ce "Bari in rakaku mota".

"Ke, da kika samu na barki ku ka gaisa, zaki wuce ki cigaba da yi mini aikina ko saina taso kanki?" Har cikinta haka Amina taji ɗacin dizgin da Hajiya Zainab ke mata a gaban baƙi, sai dai ta kasa daurewa sai da hawaye suka zubo mata, cikin ƙoƙarin mayar da hawayen, ta ƙaƙalo murmushi ta ce "Ammi ku gaida gida, Azima sai mun haɗu a school, next week za'a koma insha Allah, Ammi na gode sosai".

Kasancewar Ammi mai matuƙar son 'ya'ya, ya sanya ita ɗa ko ba nata bane yanzu zai shiga ranta, ba ta son biyewa Hajiya Zainab, zasu iya yin babu daɗi, dan ita ta zo gidan, kuma bata san me hakan zai haifarwa da Amina ba, haka suka bar gidan rai a matuƙar ɓace.

Ko da Amina ta koma kitchen, tana aiki tana kuka, kamar wadda babarta ta mutu.

Fadila ta gyara kwanciyarta ta kalli Mummy ta ce "Mum, meyasa ki ka yi haka? A Arziƙin da yake gidan nan, meye dan an bada ruwa?"

"To uwata, ai naji matar tana naniƙa mini yarinyar ne, gara in nuna mata matsayin yarinyar a gidan nan" daga haka Fadila ba ta kuma cewa komai ba.

Wata irin shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin Hafsa da Khalil, duk da baya gari, amma kusan kullum suna tare a waya, gashi a wannan karon ya kasa samun excuse of duty ya koma gida, ko dan ya ga Hafsa, saboda yadda ya dinga komawa gida a kai a kai a baya.
Yanzu yana zaune a ɗakinsa yana video call da Abdul, yana sake labarta masa irin so da shaƙuwar da ke tsakanin sa da Hafsa. Har yake ce masa "Ka san wani abu, ina kuma dawowa gida, zan yi magana a gida a san abin yi, dan ginina na nan Abuja ya kusa kammaluwa.

Abdul ya ce "Mhmm haka ne, to yanzu tsakanin Mummy da Daddy, wa zaka fara sanarwa?" ÆŠan Jimm Khalil ya yi, saboda Abdul ya tuna masa wani abu da yake yawan mantawa, ya san ko Daddy ya amince ida Mummy bata amince ba a isa an yi auren nan ba.

Nan da nan ya yiwa Abdul sallama, ya ajiye wayar ya dulmiya kogon tunani.

Ɓangaren Hafsa ma tun da Allah ya sa Khalil ya sanar da ita very soon zai turo iyayensa, take tunani wurin wa zai tura iyayen nasa? Dangin mahaifinta da basu ɗauke su a bakin komai ba ko kuma wa? Idan kuma dangin mahaifin nata suka mata sharri a wurin iyayen Khalil fa, mussaman idan suka ga suna da rufin asiri fa? Ire-iren wannan tunanin ya hanata sukuni, kuma ta kasa tattauna shi da kowa ciki har da Mama.

Amina tun tana jiran Daddy ya dawo, har ta fara gajiya, dama a falo take zaman jiran nasa, ta kasa karatun sam saboda damuwa da ɓacin rai, ta zubawa TV ido tana kallon wani Film a MBC2 Captain Philips, gaba ɗaya tausayin jarumin ya cika mata zuciya, ji take tamkar ta shiga ta kai masa ɗauki, bayan damuwar da take ciki, ta ƙara da ta film ɗin da take kallo.
Film É—in ne ta samu ya É—auke mata hankali, dan har ta fara tunanin ta ajiye masa Abincin a falo tayi tafiyarta, dan kowa ya kwanta sai ita kaÉ—ai.

Sai wajen goma saura ya shigo Alhaji Ahmad ya shigo falon, ya shigo da sallama, Amina ta É—an kalleshi ta amsa a hankali ta mayar da hankalinta kan tv.
Be kulata ba ya nufi sashinsa, da sauri ta ce "In kawo Abincin?"

"Dama kin ganni?" Ya faÉ—a ba tare da ya waiwayo ba.

"Eh" ta faÉ—a a sanyaye.

"Zan fito in karɓa, ki jirani" ya wuce abinsa.

Kawai Amina ta fashe da kuka, yadda aka mayar da ita kamar wata baiwa, kowa abin da ya ga dama yake mata, banda wulaƙanci wannan wane irin abu ne, bayan wancan jiran da tayi, sai tayi wani again? Ta cigaba da share hawaye, tare da dana sanin zuwanta birni.

Sai goma da rabi, Alhaji Ahmad ya leƙo falon ya ce "Yauwa kawo mini falona, ki haɗo mini da apple guda uku, sannan ki taho da littafinki da biro"
Amina ba ta amsa ba, ta tashi tana cigaba da share hawaye. Alhaji Ahmad ya bita da kallo, da tunanin meye ya sakata kuka.

Ta ɗauko kayan Abincin, ta nufi sashin Daddy, tana ta Addu'a, tare da ƙudurce tana kai masa zata ajiye masa ta fito.

Sai dai da ta shiga taga baya falon, ta tsaya saroro tana bin falon da kallo.
Ta wani corridor ya leƙo, ya yi mata alama da hannu ta zo, gabanta ne ya shiga faɗuwa, tabi bayansa tana waige-waige, dan bata taɓa sanin da wurin ma a cikin gidan ba.

Wani ɗaki ya buɗe ya shiga, Amina ta tsaya daga ƙofar tana leƙa ɗakin, ya haɗu ɗakin, an malaleshi da wani irin lallausan carfet, ga wani irin sanyin Ac da ƙamshin turare da ke tashi, sai kuma computer ta kai goma sha biyu a cikin ɗakin.

"Ƙaraso mana" yayi Maganar yana ƙoƙarin kunna wani socket,kamar sokuwa haka ta ƙarasa shiga, tana waige-waige, ya nuna mata in da zata ajiye masa Abincin. Ta zo ta ajiye, zata juya ta fita, ya ce "Zo ki zauna a nan" ya nuna mata kujerar dake gaban wata Computer. Da ƙyar Amina ta ɗan ɗosana ta zauna, fuskarta duk sauran hawaye.

"Kukan me kike?" Ai kamar ya kuma taɓo mata in da yake mata ƙaiƙayi, ta fashe da kuka.
Be kuma ce mata komai ba, ya zuba Abincin, tare da gyara zaman gilashinsa, ya fara ci, sai da tayi ta gama, yana danna system ya ce "Ina jinki, kukan me kike?"

Ji tayi kamar ta gaya masa abin da Mummy tayi mata, amma ta fasa ta ce "Bacci nake ji, kuma kaƙi ka zo ka karɓi Abincin, duk na gaji"

Murmushin gefen baki yayi ya ce "Ko dai ke da matar gidan ne, kike ƙoƙarin hucewa a kaina?"
Wasa ta shiga yi da hijjabinta, ba tayi magana ba.
Ya miƙa hannu, ya kunna system ɗin gabanta, ya shiga wani video, yadda ake koyar da tips na cin quiz a sauƙaƙe.
A nan ta mayar da hankalinta ta nutsu tana kallo, har tana jotting wasu abubuwan a littafinta, shi kuma ya cigaba da cin abinci.

A haka video ya ƙare, ta ɗago tana kallonsa, sai dai hankalinsa na kan system ɗin gabanshi yana dannawa.

"Kin gama gani?" Ta jinjina masa kai alamar eh.

"To yi mini bayanin me kika fuskanta?"

Nan ta yi masa bayanin abubuwan da ta fuskanta.

"Masha Allah, kina fahimta sosai".

"To zaka tambayar mini Baba zuwa Abujan, kar in ta wahalar banza ina karatu?"

"Zaki je insha Allah"

"Zaka tambayar mini Baban?" Tayi maganar tana sake tattara hankalinta a kansa.

"Insha Allah, akwai abokina a Abuja, idan ma baya son in da za ajiyeki ne, sai ki zauna a can wurin abokina, zuwa a kammala ku dawo"

"To kai a ina kake aiki?"

"Lagos" ya bata amsa

"Amma aka ce a Abuja kake, kuma meyasa baka koma ba?"

"Eh na koma Lagos da aiki, na zo hutun ƙarshen shekara"

"To wannan computocin me kake da su?" Amina tayi maganar tana kallon É—akin.

"Bayanai na, dana aikina ne a ciki"

Amina tayi murmushi ta ce "Aikuwa ina son in iya danna computer Wallahi, ka koya mini aikin da kake nima in dinga danna computer"

Alhaji Ahmad ya lumshe idanunsa ya a buɗe su a kan Amina, duk da baya son yawan surutu, amma abin da yafi buƙata a yanzu da shekarunsa suka fara ja, irin abubuwan ɗebe kewa, da zama ayi hira da shi, Hajiya Zainab kuwa hankalinta a kan kasuwancinta da kuma 'ya'yanta suke, bata fiye biyewa zama da shi ba, balle tayi masa hiraraki, shiyasa ya kan tsinci kansa da jin daɗin yawan tambayoyin Amina, da kuma surutan ta marasa ma'ana wasu lokutan.

"Ba ka ce komai ba"

"Me ma kika ce?"

"Aikin da kake a computer zaka koya mini, nima in dinga taɓawa"

"Sayar da kuÉ—i nake" ya bata amsa yana murmushi.

"Sayar da kuÉ—i kuma, ta yaya za a sayar da kuÉ—i kuma?"

"Ana yi mana, ni ina sayarwa" yayi Maganar yana murmushi.

Amina ta ɗan yi shiru ta ce "Ban taɓa ji ba".

"Yau ai gashi kin ji" ganin tana hamma ne ya sanya ya ce "tashi kije ki kwanta".

Amina ta tashi ta nufi hanyar fita.

"In biyoki da kwanukan ne?" Ya faɗa da ɗan ƙarfi dan ta ji".

Ta waiwayo ta dawo ta kwashi kwanukan tayi waje.

Kashe komai yayi, ya tashi shima ya bar É—akin, sai dai ya bar shi a buÉ—e bai rufe ba ya tafi É—akinsa.

Da safe Alhaji Ahmad ya shirya da wuri, dan yana da wani uzuri na gaggawa.
Chapter 52 · 0% Book details