Sashe 75
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nunata Hajiya Zainab tayi ta ce "Idan ina magana kina saka mini baki, sai na É—auke ki da mari, da ubanki nake magana, na faÉ—a sokwanci, sam bai san aikinsa ba, nace maka ka sallame shi ka samo mana masu gadi na hukuma, wannan ko wani abun ne zai faru ba sai dai ya same mu ba, ba uwar da zai iya tsinana mana ba"
Ga mamakin Amina ta sai ta ji Alhaji Ahmad ya ce "My dear kiyi haƙuri, ki bi komai a hankali, sanin in da Khalil za shi ba alhakinsa bane ba, kuma yana iya ƙoƙarinsa, bai kamata ace kina tada jijiyoyin wuya haka ba"
"Ba dole in tada jijiyoyin wuya ba, ka bar wannan mutumin a shiritarsa É—ana ya bar gida, gaskiya Allah amfana aikin da yayi haka, ya koma in da ya fito, na gaji".
Baba ya risuna ya ce "Dan Allah Hajiya kiyi haƙuri, in Allah ya yadda hakan ba zata sake faruwa ba"
Amina ta zata Alhaji Ahmad zai ɗau wani mataki, amma ya ɓige da lallaɓa Hajiya Zainab a kan tayi haƙuri.
Wani mugun kallo Amina ta yiwa Alhaji Ahmad, idanunta suka cika da hawaye ta É—au ledarta ta wurin Baba kawai ta bar falon, saboda yadda zuciyarta ke mata zafi zata iya zagin Hajiya Zainab.
Alhaji Ahmad ya lura da yadda Amina ta ɗau zafi, amma ba damar yayi wani yinƙuri a lokacin, haka ya dinga rarrashin Hajiya Zainab, ya ce Baba ya koma bakin aikinsa.
Baba kansa ba ya jin daÉ—in yadda Hajiya Zainab ke masa a wasu lokutan, amma ba yadda ya iya idan ya bar aiki makomar karatun Amina da kuma iyalinsa baki É—aya yake tunani.
Kan ya ƙarasa wurin gate ɗin, aka fara horn.
Ya ƙarasa da sauri jikinsa na tsuma, ko Fadila ce ta dawo, kar ya yi wani laifin ya kuma jawa kansa wani cin mutuncin.
Yana buÉ—ewa yaga motar Khalil, É—an tsayawa Baba yayi, yana kallon motar.
Abdul yaje yayi parking É—in motar ya fito ya nufo Baba, Baban ma nufarsa yayi ya ce "Malam Abdul, ya na ganka kai kaÉ—ai ina Khalil É—in?"
Abdul ya ce "Ai Khalil ya koma wurin aiki ne, ya aikin Baba Hassan?"
Baba ya ce "Alhamdilillah"
"Mutanen gidan kuwa suna nan?"
Baba ya ce "Eh ka shiga suna ciki"
Abdul ya nufi cikin gidan.
A falon ya tarar da Hajiya Zainab, tare da Daddy, yana ta aikin rarashinta a kan rashin sanin in da Khalil yake.
Abdul ya shiga da sallama, Daddy ne kawai ya iya amsa masa.
Ita Mummy ma sai yanzu ta tuna da Abdul, ƙila ya san in da Khalil ya tafi, amma ko ya sani ma ita bata da lambarsa balle ta kirashi ta tambaye shi, ko da yake ta san wataƙila Khalil ɗin ɗin yazo nema shima dan da ya san in da yake, ba zai biyo shi gida ba.
Har ƙasa Abdul ya durƙusa ya gaishe su.
Daddy ya amsa masa cikin sakin fusak Daddy ya amsa, ita kuwa Hajiya Mummy ba ta bi ta kan gaisuwarta sa ba.
Abdul ya ce "Dama motar Khalil ce na dawo da ita gida"
"Motar Khalil kuma? Ina shi Khalil É—in ya kex Mummy ta faÉ—a tana zazzaro wa Abdul ido.
Mamakine ya kama Abdul, ganin da alama ba su san ina Khalil É—in ya tafi ba.
"Mummy, wajen ƙarfe shida ya sameni a gida, ya ce in kai shi airport zai koma Abuja, sai in dawo da motarsa gida, naje wurin aiki ne shi ya sa ban dawo da ita ba".
"Amma kai baka da mutunci, har ya haÉ—a baki da kai ya tattara kayansa ya koma aiki, ban san in da yake baka gaya mana ba sai yanzu, kasa hankalinmu duk ya tashi bamu san ina yake ba".
"Wallahi Mummy ni ban san bai gaya muku ba, kawai...
"Dalla rufe mini baki, ai duk wata ƙulla-ƙullar rashin gaskiya kaine kake bashi shawara, na san wataƙila kaine kake hure masa kunne, yaje ya gano wata 'yar talakawa ya maƙale wai ita yake so"
Abdul ya sunkuyar da kai yayi shiru ya gaza cewa komai.
Daddy ya kalli Abdul ya ce "My son, tashi ka tafi Allah yayi maka albarka, ka gaida maman naka"
Abdul ya ce "To Daddy sai anjima"
Sai da Abdul ya fita, sanan Daddy ya ce "Zainab wai meke damunki ne? Dan kawai É—anki ya miki laifi sai ki dinga bin wanda ba su ji ba ba su gani ba da miyagun maganganu da cin mutunci?"
"Au haka kace? Suwaye ma mutanen wa na yiwa ƙarya wancan sakaran tsohon da bai san aiinsa ba ko wannan yaron mai kama da maye ya liƙewa ɗana ya ƙi rabuwa da shi duk wata harkar ƙasƙanci shi ne yake nuna masa"
Ran Daddy ya ɓaci, ya miƙe ya ce "Sai kiyi abin da kika ga dama ki ki cigaba kar ki fasa, idan kika kaini bango kin fi kowa sanin halina"
Bayansa tabi da harara, ta tashi tai nata wuri.
Fadila kuwa tun da taje makaranta, ba ta ga Yazid ba sai lokacin lectures kawai, da an yi yake ficewa daga ajin sai lokacin wata lectures É—in, kuma ko da wasa bai yadda ya kalli in da zai ga Fadila ba, balle a samu kuskure ko ido su haÉ—a.
Ita ma tayi nata ƙoƙari, wurin ganin ba ta ko nuna ta san da zamansa a ajin ba, ta cigaba da harkokint.
Sai dai yin hakan taji ta takura kanta sosai da sosai, ko ba komai Yazid mutumin kirki ne, kuma ya taimaketa sosai a first semester, wanda garin taimakon nata ne har ya rasa wasu marks É—in, amma hakan bai hana shi zama overaller ba!
Bayan Daddy ya dawo daga sallar isha'i, ya tarar da Amina tana shirya Abincin dare, fuskarta babu walwala sam, idanunta duk sun ƙanƙance da alama tayi kuka.
Dining ɗin ya ƙarasa yana murmushi "Meenali me aka dafa ne yau?"
Banza ta yi masa ta cigaba da abin da take yi.
"Ba kya jina ne?"
"To ni me zance" ta faÉ—a bata ko kallon inda yake.
"Amma magana fa nake miki"
Idanunta da suka cika da hawaye ta É—ago tana kallonsa.
"Ka zama mai kulawa da mutuntawa a gareni, ka É—auki lamurana da muhimmanci amma a gabanka matarka take ciwa mahaifina mutunci, idan nayi magana ka ji haushina, ka san yadda nake ji a duk lokacin da iyalinka suka ci zarafin mahaifina a gabana? Kawai dan muna talakawa? Mu muka yiwa kanmu? Duk lalacewar uba uba ne, balle babu lalacewa a iyaye, ni kar ka sake nuna mini wata kulawa, babban abin da za a mini a rayuwata shi ne a girmama mahaifina ya fi mini duk wani tattali da kulawa" ikon Allah Alhaji Ahmad ya tsaya yana kallo, tuni idanunta suka yi jawur hawaye ya wanke mata fuska, ta bar falon ta bar shi a tsaye.
AYSHERCOOL
08081012143
GABA DA GABANTA
BY
AISHA ADAM AYSHERCOOL
PAGE 41
Alhaji Ahmad ya shafi gemunsa, bai zaci Amina zata iya tsayawa ta yi masa tsiwa haka ba, amma ta wani fannin da gaskiyarta, ba bu wanda zai jure a dinga cin mutuncin iyayensa haka kurum, dan kawai talaka ne, amma ai ba shi yayi mata laifin ba.
Amina kuwa ɗaki ta koma, ta zubar da hawaye sosai tayi kuak, ba zata iya ƙirga adadin yadda aka sakata kuka ba a gidan nan, iya cin mutuncin da ake mata baya damunta a kan wanda ake yiwa Baba.
Komawa aiki ya gagari Khalil, daga masallaci sai gida, sai yaji yunwa zata kassara shi, sannan yake order Abinci ya É—an ci kaÉ—an.
Haka nan yaji yana son ya kunna wayar, yayi trying layin Hafsa.
Da saƙonnin Mummy ya fara cin karo rututu, a kan ina ya tafi, bai sanar da ita ba?
Message É—aya ya iya yi mata reply ya ce 'ina wurin aiki'
Ya lalubo lambar Hafsa, ya fara kira, cikin ikon Allah ya ji wayar ta shiga, tashi yayi zaune ya gyara zamansa, yana jiran ya jibta É—aga wayar, amma har wayar ta kaste bata É—aga ba.
Ya kira ya kai sau biyar, amma bata É—aga ba.
Message ya tura mata kamar haka "Dan Allah Hafsa, ba dan ni ba ko sau ɗaya ki ɗaga wayata mana, magana nake so muyi" yana tura nata ya ajiye wayar ya dafe kansa. Mintuna kaɗan ya ji kira ya shigo wayarsa, da sauri ya miƙa hannu ya ɗauko wayar, a zatonsa Hafsa ce amma ya ga sunan Mummy, ya ɗaga wayar ya kai kunnensa tare da yin sallama.
"Sannu Khalil, wato saboda mace ka zama É—an kanka ko? Ka shirya ka koma aiki ban sani ba, saboda bani da amfani a wurinka, sai kawai ka aiko mini da motarka ko?"
"Ba haka bane Mummy, bana jin daÉ—i ne, kuma na riga nayi booking É—in jirgi shiyasa na san at that time babu lallai kin tashi"
"Ai dole kaji babu daÉ—i, tunda na rabaka da waccan yarinyar mana, laila majnun baban soyayya, da ni kake zancen Khalil" ta katse wayarta.
A saɓule ya ajiye wayar ya cigaba da riƙe kansa.
Fadila kuwa zaune take a kan gadonta tayi tsuruu, gaba ɗaya mood ɗin da taga Yazid bai yi mata daɗi ba, haka nan ta ji ta damu, cikin ƙoƙarin kauda tunanin Yazid daga ranta, ya sanya ta ɗau wayarta ta fara game, ita a dole bata damu da Yazid ba.