Sashe 83
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Eh, amma makarantarmu naje na gaida malamaina, ba wani wurin naje ba"
"Kin dai fitan, baki gaya mini ba" ya faÉ—a yana kwance agogon hannunsa.
"Kayi haƙuri, zan dinga tambayarka"
"Well, ya gidan ya kowa da kowa?"
"Kowa lafiya lau, ka san wani abu?"
"A'a, sai kin faÉ—a"
"Jarmai fa na haÉ—u da shi a hanya ya biyoni" É—an tsuke fuska Daddy yayi, amma ya ce "Wow, kin haÉ—u da tsohon zuma kenan?"
"Allah ya kiyaye, ka san yadda na tsani mutumin nan, Allah dai ya taimakeni, bayan tafiyata mata biyu ya aura ya saka"
Daddy ya girgiza kai ya ce "Kashh bai kyauta ba gaskiya, to ke yanzu idan ba kya son Jarmai wa zaki aura?"
"Kai fa kace ba zan yi soyayya Yanzu ba"
Kawai Daddy ya fara dariya, ita ma ta biye masa suna dariyar tare.
"Meenalin Daddy, am missing you gaskiya, da wurin zan tura a dawo mini da ke, ina son ganinki sosai"
"Wallahi Daddy nima ina son in ganka, kuma ka kusa komawa aiki ko?"
"Eh Meenal, hutuna ya kusa ƙarewa"
Ta ɗan langaɓar da kai ta ce "Shikenan idan ka tafi na daina ganinka sai a waya?"
"Will you miss me?" Yayi maganar yana ƙasa da muryarsa.
"Zan yi mana sosai"
"Ai zamu dinga waya, kin san kina dawowa zaku yi tafiyar nan, ki cigaba da karatunki kin ji"
"To Daddy amma daia zaka zo Abujan?".
"Babu tabbas, zan tura Khalil dai lokacin zai yi clashing da time É—in aikina"
Ai sai Amina ta fara kuka tana diddira ƙafa "Daddy ba fa haka muka yi da kai ba, ni dai dan Allah ka zo, ko in fasa zuwan"
Daddy ya É—an buÉ—e baki ya ce "Ki fasa zuwan, da kuwa munyi faÉ—a da ke"
"To dan Allah ka zo" shiru yayi yana sauraren yadda take masa shagwaɓa, ya lumshe idanunsa yana shafa ƙirjinsa, ya ɗan jaa numfashi ya ce "Meenal"
"Na'am"
"Bana son rigima, ki cigaba da karatunki, zan turo a É—aukeki jibi in sha Allah"
"Daddy"
"Shhhhhh, maza kiyi abin da nace"
Ta rausayar da kai ta ce "To shikenan"
Ya ce "Yauwa Meenalina"
"To daddare zaka kirani?"
"Dare lokacin matata ne, sai da safe kuma in Allah ya kaimu" shiru tayi ba tayi magana ba.
"Hello, kina jina?"
"Eh, ina jinka" tayi maganar tana jin haushin amsar da ya bata É—azu.
"Za muyi Video call da safe in sha Allah, ina son in ganki"
"Da safe aiki zan yiwa Inno"
Sai da dariya ta kusa ƙwacewa Daddy, ya ce "Idan kin gama aikin zan kiraki, ki ce ina gaisheta" daga haka ya katse kiran.
Ajiye wayar Amina tayi, tana hararar wayar.
Amina ta sada zumunci sosai a ƙauye, wasu ta burgesu matuƙa da suka ganta, wasu kuma ƙanan maganganu suka cigaba da yi a kanta.
Babu kunya babu tsoron Allah, Jarmai ya cigaba da sintiri a wurin Amina, bayan ba irin cin mutuncin da ƙagen da bai yiwa Aminan ba, bayan barinta ƙauyen.
Kwanan Amina huÉ—u ta fara haÉ—a kayanta, ji take kamar karta tafi, tun ana ya gobe zata tafi, Daddy yake kiranta a waya, yana jadadda mata ta shirya da wuri, zai aiko a tafi da ita.
Ƙarfe sha ɗaya na safe, Amina ta gama shirinta, yaran Baffa Lawan suka shigo gidan wai ga 'yan sanda nan, Amina ta zo.
Inno ta dafe ƙirji ta ce "'yan sanda kuma, meye haɗinmu da 'yan sanda?"
Amina ta ce "Bari in leƙa in gani"
Amina ta saka takalmanta, ta leƙa waje, motoci uku ta gani, da kuma 'yan sanda suna kaiwa suna komowa a ƙofar gidan, yara da matasa suka tsatstsaya suna kallo.
Baƙin glashin wata mota aka sauke, saiga Alhaji Ahmad a ciki a zaun, yana sanye da baƙin glass, da dark blue ɗin shadda ba ƙaramin kyau yayi ba.
BuÉ—e baki Amina tayi da mamaki ta ce "Daddy"
Alama yayi mata da hannu, tazo.
Ƙarasasa Amina tayi gaban motar tana masa murmushi.
"Daddy dama kai zaka zo ka É—aukeni?"
"Eh mana ba gani ba, i hope kin gama shiryawa?"
"Na shirya, amma zaka zo ku gaisa da Inno ko?"
Daddy ya ce "Eh mana, je ki mini iso"
"Amma baka gaya mini zaka zo ba, da na maka girki"
"Kar ki damu, jeki mini iso mu gaisa"
Da sauri Amina ta nufi cikin gidan tana kiran Inno.
"Ke lafiya, meya kawo 'yan sanda?"
Cikin washe baki Amina ta ce "Inno Alhaji Ahmad ne fa, zai zo ku gaisa"
Amina bata tsaya ƙarasa yiwa Inno bayani ba, ta ɗauko uwar tabarma, ta shimfiɗa a tsakar gidan, ta ce "Inno ki sako mayafinki bari in ce ya shigo".
Tare da Amina suka jero suka shigo, ya samu wuri ya zauna a kan tabarma, Inno ta fito suka gaisa, ta shiga jero masa godiya, amma ya ce ba komai karta damu, ya zo tafiya da Amina ne, saboda makaranta.
Inno ta zubo man shanu fal da fura ta bawa Alhaji Ahmad, ya karɓa tare da yi mata godiya.
Amina ta kai Akwatinta mota, Inno ta rakota har ƙofar gida, a nan suka iske su Bala.
Amina ta ce "Daddy, ga 'yan uwan mahaifina nan, ga Baffa Lawan da Baffa Bala" Ta kalli su Bala ta ce "Baffa, ga Alhaji Ahmad, wanda muke zaune a gidansa ni da Baba.
Saboda tsananin kwarjini Alhaji Ahmad, haka suka zube jiki na rasa suka gaishe shi, ya amsa musu yayi musu alheri, sai dai sai da Amina tayi kuka da taga zata tafi ta bar Inno.
A motar da Alhaji Ahmad ya ke Amina ta shiga, yara suka taru suna ɗaga musu hannu suka bar ƙauyen.
"Daddy, wai yana ganka da 'yan sanda kamar zaka kama mai laifi?"
"Saboda tsaro, ai a ƙa'ida ina yawo da su saboda tsaron lafiyata, yanzunma dan doguwar tafiya zan yi ne, amma Allah ne ke karewa ai"
Ta ɗan kalli Daddy ta ce "Mmn kayan nan sun maka kyau, kamar wani ango sai ƙamshin turare kake"
Daddy ya gyara hular kansa ya kalleta ya ce "Kamar wani ango ko? Zaki maimaita a gabanta"
Amina ta tsuke fuska ta ce "Ita wa?"
"Lovely Zeena"
Ta ɗan taɓe baki ta ce "Lovely manya"
"Ke, kin fiye tsaurin ido fa, wai me matata tayi miki ne kike kishi da ita?, gaya mini gaskiya what is in your mind about her husband?" Yayi maganar muryarsa can ƙasa.
Amina ta kalleshi ta ce "Like?"
"Nothing" daga nan yaja bakinsa yayi shiru.
Ko da suka isa cikin garin Kano, maimakon su wuce gida, guest house É—insa suka wuce.
Amina ta kasa yin shiru ta ce "Daddy ya na ganmu a nan kuma, ba gida zamu wuce ba?"
"Eh ba gida zamu wuce ba" yayi maganar ransa a haÉ—e dan kar ta sake yi masa wata tambayar.
Gaba É—aya ba haka ta so ba, da aka yi parking ma bai ce ta sauko ba, dan kanta ta sauko tabi bayansa.
Sai da suka je tsakiyar falon gidan, sannan ya kalleta ya ce "Ki shiga wancan É—akin, kiyi sallolinki, za a kawo miki Abinci ki huta da la'asar Zakiru zai zo ya kai ki gida"
Jiki a sanyaye ta ce to, dan ita duk ba haka ta so ba.
Ta ware mayafinta ta yafa sosai, tayi sallar azahar, tayi adduointa, ta kira Inno ta sanar mata sun sauka, yanzu zasu ƙarasa gida, sun ɗan jima suna waya sannan Amina ta kashe wayar.
Ajiye mayafinta tayi a kan gadon dake ɗakin, ta tafi gaban mudubi tana duba fuskarta, ta kwance ɗan kwalin kanta tana sake gyara shi, kawai aka turo ƙofa, tsayawa yayi a bakin ƙofar yana ƙare mata kallo, gaba ɗaya sai ta ɗan rikice, gashi tayi nesa da mayafinta da ke kan gado.
Lumshe idanunsa yayi ya buɗe, kamar wanda aka yiwa dole ya ce "Zo ki karɓa" yayi maganar yana miƙo mata leda.
Kasa motsi tayi daga in da take tsaye, saboda kunya da ta gama mamayeta.
"Meenal, am talking fa"
Sunkuyar da kanta tayi ƙasa, ta fara tafiya a hankali, tana jin yadda idanunsa ke yawo a jikinta, ta ƙarasa in da yake tsaye ba tare da kalleshi ba.
"Menene? Ya naga kina sunkuyar da kai meyafaru" Yayi maganar tamkar bai san meya sanyata cikin É—ari-É—ari ba.
"Babu komai" ta faÉ—a ba tare da ta kalleshi ba.
"Ga Abinci nan, da kin yi sallar la'asar kije haraba Zakiru na jiranki, ni zan tafi yanzu, zanje wani wuri"
Ta karɓi ledar hannunsa ta ce "Na gode"
Kamar yadda ya gaya mata, bayan sallar la'asar ta tarar da Zakiru a harabar gidan yazo É—aukarta, ita har mamaki ma take yi, Daddy baya tsoron ko Zakirun ya gayawa Hajiya Zainab cewar suna yawo tare, har gidansa ya kai ta.
Zakiru bai nuna mata komai ba, sai tambayarta ya ta baro mutan gida, a haka har suka isa gida.
Baba na ganinsu ya taso da murnarsa zuwa wurin motar, Amina ta fito tana masa murmushi tare da gaishe shi.
Ya amsa mata cikin sakin fuska ya ce "Ya hanya, ya babar taki?"
Amina ta ce "Lafiya lau Baba, kamar kar in dawo gida da daÉ—i"
Baba yayi murmushi ya ce "To ko zaki koma ne?"
"Ai Baba ba dan wannan tafiyar ta makarantar mu ba, da ba zan dawo yanzu ba"
"To shikenan, maza shiga ciki ki samu ki huta"
Amina ta juya ta É—au Akwatinta da Zakiru ya fito mata da ita, Baba sai sannu yake masa, Amina ta ja Akwatinta zuwa cikin gidan.
A falo ta tarar da Hajiya Zainab da ƙawayenta su Turai, sun ci Abinci duk sun bar kwanukan.
Amina ta ce "Ina wuninku?"
A yamutse suka amsa mata, dan Hajiya Zainab bata amsa ba, sai ma kallonta da tayi ta ce "Zo ki kwashe kwanukan nan"
Mamakine ya kama Amina, Hajiya Zainab dai ba makauniya ba ce ba, taga Akwati a hannunta yanzu ta dawo, amma saboda tsabar son ta wulaƙantata wai ta zo ta kwashe kwanuka.