Sashe 18
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amina aiki suke sha a gidan nan kamar ba gobe, kasancewar Amina nai kaifin ƙwaƙwalwa ya sanya nan da nan ta iya abubuwa, ita aikin fa suke ba ya damunta, dan in dai aiki ne ta riga ta saba da shi tun a ƙauye, dan sam ba ya mata wahala, ita wulaƙanci da kallon ƙasƙantattun da ake musu ne yake damunta, shima da tuna ga burinta da yake ranta wanda take sa ran cikawa sai ta yi ƙoƙari ta manta komai.
Dan kusan kullum idan ta je wurin Baba nasihar sa kenan a gareta, ta yi haƙuri.
Amina na ta saka ran ganin wanda zai kaita Makaranta ya dawo, amma shiru ba ta ga ya dawo ba, kuma ba ta ji ana batun dawowar ta sa ba, ta dai yi shiru ta danne abun a ranta, dan abin ya fara damunta, idan aka aiketa ita da Hajara, tana ganin 'yan Makaranta hakan ya tabattar mata da an koma Makaranta.
Yau sun gama aikin su kaf, sun gyara ko ina, wanda ƙarfin aikin ma Amina ce ta yi shi, ta zauna a falo tana kallon TV, sai ga Fadila ta dawo daga makaranta, ta shigo falon ba ko sallama, ta dire jakarta a falon, da mayafinta ta kalli Amina ta ce "Ki kawo mini su ɗaki".
Amina tabi bayan Fadila da kallo ta taɓe baki, a ranta ta ce "Kin shigo ba ki mini sallama ba balle sannu da gida, kuma kin yi dakon jaka da mayafi tun daga makarantar, ƙarasawa da su ɗakin ki shi ne aiki a wurinki, ai kuwa ba zan kai ba' daga haka ta tashi ta bar falon, tayi tafiyarta wurin Baba.
"Uwata, in ce ko dai kin gama duk ayyukan da aka saka ki kan zo nan?"
"Eh Baba, na gama komai".
"Yawwa Uwata ta kaina, banda ganda ko gardama dan Allah, yi nayi bari na bari".
"Insha Allahu Baba, nace yaushe zaka je ƙauye ne? Da na ji kace a wannan satin"
"Eh a wannan satin na so zuwa, amma nafi son in ga yaron nan da zai kai ki Makaranta ya dawo, an kai ki kin fara zuwa sai inje".
"Wallahi Baba kamar ka san abin da ke raina, na yi shiru ne kawai dan kar in takura maka, amma naga an koma Makaranta".
"Mu ƙara haƙuri dai, tun da ya ce za a kai ki, na san za a kai ki insha Allah"
"To shikenan Baba, amma nace mai zai hana idan zaka ƙauyen muje tare ina kewar Inno da yawa".
"So kike muje su sake riƙe ki ko?" Da sauri ta girgizawa Baba kai.
"To idan ba haka ba, ki cire rai da zuwa ƙauye, har sai Allah ya sa kin kammala sakandirenki"
"To Baba Allah ya zaɓa mana abin da ya fi alkhairi".
"Ameen Uwata ta kaina"
Ta shantake abinta, ta cigaba da hira Baba, har sai da aka yi kiran sallar magariba, sannan ta koma ciki.
Kamar yadda Fadila ta bar jakarta da mayafi suna nan a wurin, Amina kuma bata bi ta kan su ba, ta wuce É—akin da take.
Fadila ba ta tashi sanin Amina ba ta kai mata jakarta É—aki ba, sai da ta tashi tafiya makaranta da safe, ta nemi jaka ta rasa, ta duba É—akinta kaf ba ta jaka ba, dan haka ta fito falo tana neman Asabe, dan ta ji in da ta ajiye mata jaka bayan ta gyara mata É—akinta, sai dai tana fitowa ta ga jakarta da mayafinta a in da ta ajiye su, buÉ—e baki ta yi da mamaki, bayan ta tuna taga 'yar mai gadi jiya a falo.
Cikin fushi ta fara ƙwalawa Hajara kira, Hajara da ke kitchen ta jiyo kiran Fadila ta taho da gudu, ta durƙusa.
"Ina wannan yarinyar da ku ke aiki da ita?".
Hajara ta ce "Wai Amina?".
"Ko ma wacece, ki kira mini ita yanzun nan".
"To bari in kirata, naga yau tun da aka yi sallar asuba bata fito ba, kuma ba ta saba hakan ba"
"Ke dalla ɓace mini daga gabana ki je ki kira mini ita, kin tsaya kina mini wasu surutan banza"
Cikin hanzari Hajara ta bar wurin, ta nufi ɗakin Amina, ta tsaya a ƙofa tana ƙwanƙwasawa.
Amina ta na zaune, tana rubutun Alƙur'ani a cikin littafin da ta taho da shi daga ƙauye. Saboda yau ji ta yi tana kewar makarantar Allo, da tana ƙauye da tuni tana nan ta wanke allonta, ta yi rubutu, dan haka yau ta zauna bayan sallar Asubahi ta fara rubutunta.
 Tana jin Hajara na buga ƙofa tana faɗin "Amina ki buɗe ƙofa, Fadila tana nemanki".
Yamutsa fuska Amina ta yi, tare da tura baki, ta cigaba da abin da take yi.
"Amine ki buÉ—e mana"
"Dan Allah Hajara ki ƙyaleni, kullum da wuri nake fitowa, yau wani aiki nake yi, kiyi abin da zaki iya, sauran ayyukan ki bar mini idan na fito zan yi"
"Ke bafa saboda aiki ba, Fadila ce take neman ki".
Tsaki Amina ta yi ta ce "Kwa ci kan ku, ba wanda ya isa ya É—agani daga zaman nan idan ba Allah ba, ko Baba ne ya kirani ba".
Fadila ganin zata makara Hajara ba ta dawo ba, ya sanya ta ɗau jakarta ta fice ranta a ɓace, ta ƙudurce a ranta idan ta dawo sai ta koyawa su duka biyun hankali.
Amina ba ta fito ba sai ƙarfe tara na safe, dan rubutunta ta zauna tai ta yi.
A kitchen ta tarar da Hajara, "Anty Hajaru sannu da aiki".
"Zaki ga Hajaru ganin idonki, yau kin caza mana bala'i, ba yadda ban ba ki fito amma ki ka yi mirsisi ki ka ƙi, ƙarshe sai tafiya ta yi, yau kashin mu ya bushe daga ni har ke idan ta dawo".
Amina ta É—age kafaÉ—a ta ce "Oho, duk masifar 'ya dai na san ba zata É—auki raina ba, sai dai tayi ta ci kanta ita kaÉ—ai".
Buɗe baki Hajara ta yi tare da riƙe haɓa ta ce "Ke Amina dama haka ki ke?".
Amina ta share Hajara, ta nufi ƙofar fita tana cigaba da ƙunƙuni.
Tana fita harabar gidan ta hango Baba, ya shirya cikin wani milk ɗin yadi. Ta ƙarasa ta gaishe shi ta ce "Baba ya naga kamar fita zaka yi?".
"Eh mana, dama ke nake jira in ga fitowarki in yi miki sallama, ƙauye zani".
"Baba da gaske?".
"Ahh ji ja'ira zan miki ƙarya ne?".
"Wayyo Allah, Baba ka gaishe mini da Inno, na so zuwa in ganta, sannan dan Allah ka bata haƙuri, na san na sata a tashin hankali tahowar nan da na yi, bari inje cikin gida in ɗauko maka Abincin karina ka kai mata".
Baba ya ce "A'a ba za ayi haka ba, zan musu tsaraba a hanya".
"Baba dan Allah ka tsaya, yanzu zan dawo".
Amina ta ruga cikin gida. "Hajara, dan Allah bani leda in zubawa Baba Abincin karina ya kaiwa Innota".
"Au yau zai je garin naku?".
Amina ta ce "Eh yau zai je".
Hajara ta ce "Wane irin in baki leda, viva zaki samu, har kayan marmarin nan na cikin firinji da suka kusa lalacewa, duk ki bashi ya kai mata".
"Ahh Hajara sata fa kenan, ba a bani ba".
Hajara ta ce "Dalla bari kiga, idan ki ka tsaya sai sun baki, ba zasu taɓa baki ba, sai dai su ruɓe ki kwashe ki zubar, kuma ai ba ayi mana iyaka a kan Abincin gidan nan ba"
Hajara ta ƙulle soyayyen dankali kaya guda da miyar ƙwai, da manyan magwaro da lemo, ga uwar kankana har da su biscuit. Ita dai Amina taji a ranta duk babu daɗi, tamkar sata suka yi.
Hajara ta rakata suka kai wa Baba, Baba ya duba kayan nan ya ce "Amina wannan kayan fa, kin tambaya ki ka É—akko?"
Hajara ta ce "Baba Hassan, ai ba ayi mana iyaka da Abincin gidan nan ba, kuma idan aka barsu ma a banza za su lalace, su ba su ci ba kuma ba su bayar ba, sai dai mu kwashe mu zubar".
Baba ya karɓa ya kama hanyar tafiya.
Fadila a gaggauce ta shiga ajinsu, kasancewar yau ta makara sosai, sai dai tana shiga ta tarar da lecturer ya na arranging É—alibai, zai yi musu test.
Lecturer da farko ji yayi tamkar ya koreta, saboda ba ta da kunya, amma ya ƙyaleta ya sakata a bencin gaban Yazeed.
Sai wani haÉ—e rai take, tana hura hanci ita a lallai bata so aka ajiyeta a wurin da yake ba.
Nan malamin ya rubuta musu test É—in, tare da sake tuna musu, test É—in maki Ashirin ce, Attendance É—in da yayi kuma maki talatin, zai yi jarrabawar sa maki hamsin. Sannan ya kawo wani lecture yayi invigilating É—in su, shi zai je wani ajin yayi lectures.
A tambayar da ya yi musu ciki har da abinda Yazeed ya koya musu a aji, hakan ba ƙaramin farantawa ɗaliban rai ya yi ba.
Kowa ya duƙufa ya fara rubutu, amma Fadila ta shiga rarraba ido, kamar an kwashewa karya 'ya'ya.
Yazeed yana ta rubutunsa, yayin da malamin ke ta zagawa yana dudduba su.
Yazeed ne ya lura babu abin da Fadila ta rubuta, banda sunanta lambar Admission É—inta da question.
Ya girgiza kai, a gurguje ya ƙarasa nasa, sannan ya waiga ya ga lecturer ba ya kusa da su, ya sanya bironsa ya taɓo Fadila.
"Dalla meye haka?"
"Ya naga ba ki rubuta komai ba?".
"To ina ruwanka da ban rubuta komai ba? Aikin banza É—an sa ido kawai".
"Sorry ba sa miki ido na yi ba, bari in karanto miki".
"Bana so".
"A'a, kar ki manta fa bamu da Attendance ni da ke, kuma ya ce exams É—in ma 50mrks ce, kar a kafe exams a ga kin faÉ—i, za a raina ki. BuÉ—e papern, in dinga karanto miki kina rubutawa".
Ba kunya ta ware paper, ta gyara zamanta, yana karanto mata tana kwashewa a ta ta paper.