← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 84

Sashe 58

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk da Amina ta sha jinin jikinta da irin kallon da Alhaji Ahmad ya yi musu, amma ta maze ta ƙi ko ɗaga kanta, balle ta nuna ta san ita yake yiwa wannan kallon.
Bilal ya gaida Alhaji Ahmad, amma ya amsa masa sama-sama ya fice, Amina na ganin fitar Alhaji Ahmad, ta yiwa Bilal sallama ta shige cikin gida.

Fadila kuwa tun da Kankiya ya Kori Yazid daga ajin, hankalinta yake a tashe, ta rasa meya kamata ta yi, tamkar a kan ƙaya take haka ta dinga jiran Kankiya ya fita ita ma ta fita, ganin ba shi da niyyar fita ne, ya sanya ta tashi ta nemi excuse zata fita, amma Fafur Kankiya ya hanata, ji tayi tamkar ta je ta shaƙe shi ta gwara kansa, wata irin tsanarsa ta ninku zuciyarta.
Sai da yayi kusan awa biyu da wani abu sannan ya bar ajin, yana fita Fadila ta fita, ta dinga duddubawa ko zata ga Yazid, amma babu Yazid babu dalilinsa, duk in da ta san zata ganshi ta duba amma bata ganshi ba, hakan ya sa tayi tunanin gida yayi tafiyarsa, alamar yayi zuciya.
Tunani ta dinga yi, wani irin hukunci yakamata ta yiwa Kankiya, wani mataki yakamata ta É—auka a kansa, amma sai ta yi tunanin kar tayi wani abu a kai, ya kuma cutar da Yazid, haka nan ba tare da ta yanke shawarar komai ba, ta shiga motarta ta tafi gida cike da damuwa.
  A gidanma kasa sukuni tayi, gashi ita ba lambar Yazid ba, balle ta kira shi a waya taji meyafaru bayan fitarsa daga aji ba.
Tana tsaka da wannan tunanin, sai ga kiran Kankiya, ji tayi kamar tayi jifa da wayar, amma tayi yaƙi da zuciyarta ta ɗaga.

"Amincin Allah ya tabatta a gareki amaryata" ji tayi kamar ya watsa mata wuta a zuciyarta, ko muryarsa ba ta ƙaunar ji sam.

"Me ka kirani kayi mini, wai ban maka kashedi a kan kirana ba?"

"Kina fushi da ni dan na kori saurayinki daga aji ko? Ai abinda na gaya miki ne Fadila, muddin ba zai rabu da ke ba, zan ta wahalae da shi ne"

"Wai kai waye ya gaya maka Yazid saurayina ne? Babu wani abu mai Kama da soyayya tsakani na sa Yazid, kuma bari in gaya maka wani abu, wallahi muddin baka kiyaye ni a kan batun soyayyar nan ba, sai na maka abin da har ka mutu ba zaka manta ba*

Yayi dariya ya ce "Ni ma kuma zan yiwa Yazid ba, dan naga a duniya idan ana son ɓacin ranki, to a taɓa Yazid"

Sai kuma yayi ƙasa da murya ya ce "Haba Fadila, duk ke kika saka al'amura suka zama so complicated like this, ni ina da kishi sosai da sosai, shiya sa ba zan iya jure ganinki da wani ba, wallahi idan Yazid ya fita daga harkarki babu ruwana da shi. Yanzu gaya mini yaushe zan zo gidanku?"

"Abudrrasheed Kankiya, banda ina ganin darajar alli da duster, da sai na nuna maka wacece Fadila, na lura rashin sanin wacece ni ya sanya kake mini karan tsaye yadda ka ga dama"

"Hmmm, koma dai menen ai nasan ke mutum ce, kuma duk matsayinki dole zaki aure wataran ƙarƙashin inuwar wani, Fadila mu daina samun wannan saɓanin, in daina wahalar da ɗan mutane, ki fita harkarsa ki bani dama in gwada miki soyayya"

"Shikenan, ni da kai mu zuba mu gani,ka koma ka ƙarewa kanka kallo, sannan ka ƙare mini kallo kasan wacece ni, kan kace kana sona ka san matsayina tukuna, wallahi ka cigaba da takura masa zan nuna maka abin da zan iya yi a kai"

Kankiya ya yi ajiyar zuciya ya ce "Saboda shi Yazid É—in duk kike gaya mini wannan maganganun?"
"An gaya maka ɗin, kayi abin da zaka iya" daha haka ta kashe wayar , tana jin tamkar ta sa a ɗaure Kankiya, ita tausayin Yazid take ji, idan aka ɓata masa career an cuce shi, amma Kankiya na son amfani da wannan damar ya tilasta mata ta so shi, bata taɓa tausayin wani ɗan Adam a rayuwarta ba, kamar yadda take tausayin Yazid. Ita kawai kyawawan halayensa take kallo, sai taga kamar idan aka cutar da shi ba a yi masa adalci ba, yana da halaye masu kyau, ba ya cutar da kowa to shi mai zai saka a dinga cutar da shi.
Ta tuna irin kasadarsa mussaman a É—akin jarrabawa, dan kar wani ya faÉ—i, da tsananin biyyarsa ga malamai, amma hakan bai hana a dinga dizga shi a gaban aji, ba tare da duba halayensa masu kyau ba.
Dafe goshinta tayi, ji tayi kamar kanta ya fashe Saboda rasa mafita.

Ɓangaren Khalil ma yana cikin ɗumbin damuwa, Hafsa ta buɗe what's app a wayar da ya bata, har tayi masa magana ta what's ɗin, sai wani ƙara lallaɓa shi take, tana bashi kulawa ta mussaman, da Adduoi, nasiha gami da kalaman soyayya, wanda hakan ke ƙara masa sonta a ransa. Gaba ɗaya Mummy ta ɗauke masa wuta, ta daina shiga harkarsa, duk dan saboda yana son Hafsa.

Gaba ɗaya fushin da Mummy take yi da shi, bai yi masa daɗi ba, hakan ya sanya, ya kuma ƙoƙarin zuwa ya rarrasheta, sannan yayi mata bayanin halin da su Hafsa ke ciki, ko Allah ya sa ta fahimce shi.
Da sallama ya shiga bedroom ɗin Mummyn, ya tarar da ita a kan gadonta, tana danna Computer, gefenta kuma ga calculator, da alama kuɗi take ƙirgawa.

Tun da ta É—aga kai ta kalleshi sau É—aya, ta mayar da kai ta cigaba da abin da take yi.

"Mummy sannu da aiki"

"Yauwa" ta amsa a daƙile ba tare da ta kalleshi ba.

"Mummy wurinki na zo"

"Ai na ganka, ina kuma jinka"

Khalil ya ɗan gyara zama tare da sosa kai ya ce "Mummy, dama game da Hafsa ne, yarinyar nan da aka ce miki an ganni a wurinta, Mummy yarinyar marainiya ce ne, Da mahaifinta mai abin hannunsa ne, kan ya rasu ya saya mata kadarori, sai dai bayan rasuwarsa dangin mahaifin suka ƙwace komai, shiyasa kika gansu a haka, amma tana da kirki da kuma hali mai kyau, ba ta da wata matsala yarinyar"

Ai tamkar dutse yayi wa wannan dogon jawabin, dan danna calculator kawai take tana shigarwa cikin Computer.

"Mummy ba ki ce komai ba"

"Me kake so in ce maka, ai kai an shanyeka, ni kuwa ba a shanye ni ba a hayyacina nake, nayi mamakin wurin wani malami suka je haka, da har ka iya zuwa ka tunkare ni ni Hajiya Zainab, kake mini wannan maganar banzan, ban sani ba ko orphanage Home ka buɗe, zaka fara rainon marayu da marasa galihu, da har zaka yayi mo min wannan shirgin tsiyar, Khalil banda rashin hankali irin naka, ina kai ina mai suyar Awara a titi, ba bu ilimi mai zurfi, ta gama zaman titi maza sun gama kalleta, in anjima ta ci kwalar namiji, kuma ka ce mini ita ce sirikata,ai kai ma ka san kayi ƙarya"

"Mummy wallahi ba haka Hafsa take ba, tana....

"Dalla rufe mini baki, ina magana kana wani kwantar da murya ce, cece, ni zaka lallaɓa in anince da auren 'yar matsiyata, ka buɗe kunnenka da kyau ka saurare ni, daga yau babu kai babu yarinyar nan, na yanke duk wata alaƙa da take tsakaninka da ita, wallahi na bibiya na tarar ba ka rabu da ita ba, hukuncin da zan yanke maka ba zai maka daɗi ba"

"Mummy dan Allah, ki duba lamarin nan"

"Ni kake cewa in duba lamarin nan, wato sihirin har ya kai ka fifita ta a kaina"

Cikin rauni ya ce "Ba haka bane Mummy, wallahi ba suyi mini asiri ba, suna buƙatar tainako ne Mummy, kuma muna son juna sosai"

Mummy ta jinjina kai ta ce "Da kyau Khalil, suna buƙatar taimako ko, sannu gwamnati kowa naka, tashi ka fita ka bar mini ɗaki" ta nuna masa hanyar fita.

Zai kuma magana, ta sake haɗe rai ta nuna masa hanyar ficewa, haka ya haƙura ya bar mata ɗakin zuciyarsa babu daɗi.

Amina kuwa ba ƙaramin haushin abinda Daddy yayi mata taji ba, haka ta shiga ɗakinta, tayi alwala tayi sallar magariba, ta shiga kitchen ta hau aikin Abincin dare, kasancewar Hajara ce tayi na rana tunda ita tana makaranta.
Gaba ɗaya Amina a gajiye take, tunda kusan wuni tayi aikin da Daddy ya sakata, aikin da a ƙarshe ya sakamata da direta a titi yayi tafiyarsa saboda tayi maganar matarsa.
Ta gama girkin, ta kai dining, ta É—au na Baba ta tafi ta kai masa, ta tarar da Baban a cikin É—akinsa na gadi, yana jin radiyo.

Har zata fita, Baba ya kirawota, ta dawo ta zauna tana kallonsa.
Ya ɗauko wata 'yar jaka ya miƙa mata, ta sa hannu ta karɓa, ta buɗe jakar wani babban kwalin waya ta gani a ciki, ta saka hannu ta ciro wayar tana kallon Baba.
"Baba wannan wayar fa?"

Baba ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Alhaji Ahmad ne ya bani, ya ce in baki, wai saboda ki samu sauƙin karatu, sai dai har ga Allah ni bana son ki mallaki wayar hannu yanzu, amma bana son yi masa jayayya kuma naji ya ce saboda karatunki, ina fatan dai ba roƙonsa ki ka yi ba?"

"Haba Baba, ka san bana roƙo, wallahi ni ban roƙe shi ba"

"To sai kiyi masa godiya, duk da nima nayi masa"

"To, insha Allah zan masa"

Ta tashi tana jujjuya wayar ta bar É—akin Baba.

Har ga Allah tana matuƙar son waya, mussaman duba da yadda ƙawayenta ke da wayar, amma ita ba ta da ita, sai dai da ta tuna da abin da Daddyn ya yi mata, sai haushi ya kamata har ta ce "Mayar masa zan yi, ban so" ta jiye wayar a gefen katifarta tana harar wayar tamkar Alhaji Ahmad ɗin ne a gabanta.
Chapter 58 · 0% Book details