Sashe 15
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta miƙawa mutumin wayarsa, tare da yi masa godiya, ta zauna tana jiran zuwan Saminu.
Mutumin nan ya zauna ya dinga yiwa Amina surutu, amma ko uhmm ba ta ce masa.
Sai bayan la'asar Sannan Saminu ya iso, wata irin ajiyar zuciya Amina ta dinga saukewa tana murmushi.
"Yi haƙuri Amina na barki kina jira, Amina wannan ramar da kika yi fa?"
Maimakon ta bashi amsa sai ta hau kuka, Saminu ya ce "Yi haƙuri, share hawayenki, nayi miki laifi nima dan ban gayawa Mahaifinki da wuri ba, kuma da na gaya masa dama cewa yayi in kai masa ke. Muje maza in kai ki"
Mutumin da ya kirawa Amina Saminu ya ce "To Amina ba sallama?" Shiru ta yi masa tana cigaba da share hawaye.
Saminu ya ɗaukar mata kayanta, ya sa a motarsa ta shiga, ya je ya sayo mata gurasa da nama da lemo ya bata, ta riƙe a hannunta amma ta kasa ci. Suna tafe yana bata labarin yadda gidansu ya hargitse, ita duk tausayin Inno ne yafi damunta.
Ko da suka shiga cikin unguwar tudun Yola, rukunin gidajen da Baba Hassan yake gadi, Amina ta saki baki, tana ganin gidaje tamkar a É—auka a ci.
Da Saminu yayi parking ya ce mata sun zo, nan mamaki ya ƙara baibayeta, gate ɗin gidan ma kawai abin kallo ne.
Saminu ya ƙarasa ya ƙwanƙwasa ƙofar gate ɗin, amma ya ji shiru, ya tura ƙofar suka shiga, lokacin Baba Hassan na fitowa daga ɗakinsa na gadi, a guje Amina ta ruga da gudu ta nufi in da Baba yake ta riƙe hannunsa ta fashe da kuka.
Baba kasa Magana yayi, sai kallon Amina yake yana murmushi, shi dai a duniya ba abin da ya rage masa da yake ƙauna kamar Amina.
Saminu ya ƙaraso yayi masa bayanin komai, Baba Hassan ya dinga yi masa godiya, sannan ya ce dan Allah idan ya koma garinsu, ya haɗa shi da Inno a waya yayi mata bayani, amma bayan ita kar ya gayawa kowa abin da ya faru. Saminu ya tabbatar masa da zai yi hakan, daga nan suka yi sallama ya tafi.
Baba ya zauna Amina ta gaya masa duk abin da ya faru a ƙauye, ya jinjina kai shi kuma ya gaya mata yadda suka yi da Alhaji Ahmad.
Amina ta dinga murna jin batun cigaba da makaranta. Amma Baba ya ja mata kunne a kan yanayin mutanen gidan da halayarsu, A ƙuruciya ta Amina gani tayi ai dan wannan ai mai sauƙi ne.
Baba ya dinga jadadda mata "Sai kin yi haƙuri, rayuwar birni da ta karkara ba ɗaya bace, su mutane ne masu ƙyamar talaka ki iya kan ki, kiyi musu aikinsu su biya miki kuɗin Makaranta".
Amina sai murna take, ashe da rabon burinta zai cika a rayuwa.
Baba ya ce "Muje in gabatar da ke a wurin su".
Amina ta bi bayan Baba da kayanta a bagco, tana ta kalle-kalle, kamar zata faÉ—i.
Ya yin da Baba ke ta Addu'a Allah ya sa Amina ta shigo a sa'a, ta samu ta kammla makarantar Sakandire É—in ta.
Ayshercool
08081012143
GABA DA GABANTA
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
P7
Tuni Amina ta manta da zazzaɓin da take fama da shi, dama na fargaba da damuwa ne, ita wancan Auren da ta baro ya fi komai yi mata daɗi, ga kuma wannan abin farinciki da ta zo ta riska, ba ta taɓa zaton abubuwa za su zo da sauƙi haka ba.
Har sun kai bakin ƙofar da zasu shiga cikin falon gidan, Baba ya tsaya ya kalli Amina ya ce "Uwata ina sake jadadda miki, sai kin yi haƙuri kin kauda kan ki, ki kwantar da hankalinki duk abin da suka ce ki yi, babu musu haka wanda suka ce ki bari, banda shishshigi ki zauna kiyi haƙuri mu samu ki kammala makarantar ki lafiya ƙalau".
Amina ta yi murmushi ta ce "Insha Allah Baba ba zan baka kunya ba, zan yi duk abin da kace" ya jinjina kai sanan ya tura ƙofar ya shiga da sallama.
Alhaji Ahmad ne kawai ya amsa, Hajiya Zainab kuwa na zaune, Fadila na kwance a kan cinyarta, tana kallon T.V.
Baba na gaba Amina na biye da shi, suka ƙarasa cikin falon, Amina ta zube har ƙasa ta gaida Alhaji Ahmad, ya amsa mata cikin mutuntawa.
Ta kalli Hajiya Zainab ita ma ta gaisheta, sai da ta yi mata kallon sama da ƙasa sannan ta ɗauke kanta ta amsa da ƙyar.
Alhaji Ahmad ya ce "wannan ce yarinyar taka?".
Baba ya ce "Eh ranka ya daÉ—e"
Alhaji Ahmad ya kalli Mummy ya ce "Madam, ga yarinyar da na yi miki magana É—azu, 'yar wurin Malam Hassan, dan haka sai ku haÉ—ata da masu aikinku ku nuna mata aikin da zata ringa yi. Sannan yanzu ana hutun makaranta ne, amma da zarar an koma Makaranta za'a kai ta makaranta insha Allah".
Baba ya ce "Na gode Ubangiji Allah ya ƙara Arziƙi".
Amina ma ta ce "Na gode Allah ya saka da alkhairi".
"Ba komai, ki nutsu ki mayar da hankali kiyi karatu da kyau kin ji ko?".
"Tom insha Allah na gode sosai".
Duk wannan abun Mummy da Fadila basu tofa ba, Baba Hassan ya gama godiyar sa ya tashi ya koma bakin gate in da yake aikinsa.
Amina na zaune tana jiran a bata masauki, amma babu wanda ya kuma kulata, sai ma cigaba da hirarsu da suka yi.
Kusan mintuna arba'in tana zaune, ga yunwa tana ji, gurasarta na cikin kayanta, tana so ta keɓe ta samu ta ci, amma ba wanda ya kuma saurararta.
Ba tsammani ta ji muryar Fadila tana kiran "Hajara"
Amina a ranta ta ce "Ji wata murya kamar aljana".
Hajara ta ƙaraso falon hannunta riƙe da duster, ta ce "Gani".
"Dan Allah kai yarinyar nan can wurinku, ta zo ta sanya mutane a gaba da kallo".
Sai yanzu Mama ta ce "Ki kaita É—akin da Asabe ta bari, da safe zan mata orientation"
Hajara ta ce "to" ta kalli in da Amina take, yarinya ɗanya sharaf, tubarkallah baƙa ce mai kyau da ita, sai dai kayan jikinta zai tabattar maka da akwai rangwamen gata.
Hajara ta yi matamurmushi ta ce "Ta so muje ciki".
Amina ta ce "To bari in ɗakko takalmana a bakin ƙofa, kar wani ya samin".
Wani irin kallo Fadila ta yiwa Amina, jin abinda tace, Daddy kuwa murmushi kawai yayi.
Amina ta É—akko takalmanta silifas É—an madina mai zanen yatsu.
Hajara ta ɗaukar mata jakarta suka shiga ciki, Hajara ta buɗe wata ƙofa suka shiga wani falon.
Amina ta ce "Kai, sanyi sosai, naga lokacin bazara ne, amma sanyi sosai nan"
Hajara ta ce "Na'ura ce take sanyaya É—akin ai"
Amina ta ce "Ok ita ce A.C air condition?" Hajara ta kalli Amina jin ta yi turanci ta ce "Eh ita ce".
Ta kai Amina ɗakin da Asabe ta bari, ɗan madaidaici ne da ƙatuwar katifa, akwai mudubi da banɗaki a cikin ɗakin.
Hajara ta ce "Ga É—akin ki nan"
Amina ta zaro ido ta ce "Wannan duk ni kaÉ—ai? Amma tare zamu dinga kwana a É—akin ko?"
"A'a kowa da É—akinsa, ga banÉ—aki nan bari in kawo miki sallaya ko zaki salla, bari in je kitchen in samo miki Abinci"
"To Na gode" bayan fitar Hajara, Amina ta dinga kallon ɗakin, ta leƙa banɗakin tas da shi.
'Allah sarki Inno, da na san haka zan samu komai a wadace da mun taho tare, wannan aljannar duniya haka?"
Ta shiga banɗakin, ta dinga taɓe- taɓe, Dan Amina akwai rawar kai wasu lokutan, hakan ne ya sanya take iya wasu abubuwan.
Ta yi alwala, ta yi sallar magariba, ta janyo kayanta tana ƙoƙarin ɗauko gurasarta ta ci, sai ga Hajara ta shigo da kwanuka, ta ajiye a gaban Amina, sannan ta zauna kusa da Amina ta ce "Ya sunan ki ne?".
"Sunana Amina".
"Masha Allah, ni kuma Hajara"
Nan Hajara ta dinga bawa Amina labarin yanayin mutan gidan, tare da sukar Hajiya Zainab da Fadila, ita kuwa Amina hankalinta sam baya kan Hajari, yana kan daddaɗar doya da miyar ƙwan da Hajara ta kawo mata, lokaci guda kuma tana tunanin Inno.
Daren ranar Amina kasa bacci ta yi, saboda tsoro da rashin sabo, haka ta kwana da fitila a kunne.
*************
Alhamdilillah kwanakin nan Hafsa tana yin ciniki sosai, dan har da dankali take haÉ—awa yanzu bayan awara. Dan har da miya take haÉ—awa idan mutum yana so ya siya da miya.
Wata mota ce tayi parking a ɗan gaban in da Hafsa take suyar awarar ta, mutumin ya sauke glass ya leƙo da kansa, ya kalli Hafsa yayi mata alama da taje.
Kallo É—aya ta yi masa gabanta ya faÉ—i, ta É—auke kanta ta cigaba da abin da take yi irin ba ta ganshi É—in nan bama.
Wani almajiri ne yaje kanta ya tsaya ya ce "Wai ki zo inji mai motar can".
"Kace masa ba zan zo ba"
Almajiri ya koma ya sanarwa mutumin saƙon Hafsa.
Mutumin ya ce "Ka nuno mata ni kace ni nake kiranta".
Ko da yaron ya zo ya kuma sanar mata saƙon mutumin, ta kalli yaron a fusace ta ce "Zaka matsa daga kai na ko sai na kwaɗeka?"
Ba shiri yaron ya matasa ya bar wurin, da Hafsa ta iya tsare gida bata son wargi.
Mutumin ne ya fito daga motar ya ƙaraso kan Hafsa ya tsaya, ya dubeta a wulaƙance ya ce "Ke ni nake miki magana ki ka share ni?"
Ko nuna ta san ƙurar da ta kwaso shi ba ta yi ba, ta cigaba da fifita wutar gabanta.
"Aikin banza wulaƙatancciya, a haka zaki ƙare rayuwarki a wahala, daga ke har mahaifiyar ki haka zaku ƙare, kaɗan ma kuka gani, muddin ina raye sai kun fito titi kuna bara"
Wani murmushi ta yi mai ciwo, ta cigaba da sabgar gabanta.
Ya dinga jifanta da miyagun maganganu, a gaban mutane.
Mai shayin da ke gefen in da Hafsa ke sana'arta ne ya ce "Haba bawan Allah, ta yi shiru ba ta tanka maka ba, sai ci mata mutunci kake a gaban mutane ya haka ne?"
"Kaga saurara mini, ba da kai nake ba, ba ka san meye tsakanin mu ba"