Sashe 66
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hajiya Turai ta ce "Ashe ƙaramar fitsararriya ce, yanzu da na zubar da wannan tsiyar, ai gashi kin bani dukkan hankalinki, dana ɓarar da tsiyar da kuka dogara da ita, ba kece Hafsa ba? Kin samu yaro kin asirce shi, yana muku bauta, 'yar matsiyata ce, ni na zata ma wata haɗaɗiyar yarinya zan gani, kalleki kalli kayan kayan jikinki, Khalil ya miki kama da sa'an Aurenki?"
Sai yanzu Hafsa ta gane ina suka dosa, kuma a kan me suke mata wannan tijarar, da tuni mutane suka fara taruwa suna kallon abin da ke faruwa.
Hajiya Salma ta kalli Hafsa a wulaƙance ta ce "Ɗanmu ba tsarar aurenki bane, ki duba cikin kwararon matalauciyar unguwarku, ba zaki rasa Irinki ki aura ba, ko kuma 'ya'yan kwalta lalatattu irinki, da babu yarinyar kirkin da zata zo bakin titi tana kasa kaya, tana cakuɗeɗeniya da maza, ka ce ta kirki ce, ki nemi irinki daidai ke ki aura, Khalil ba sa'an yinki bane"
Turai ta kalli wasu almajirai ta ce "Kai zo ku ƙarasa zubar mini da wannan kayan ƙazantar, zan biyaku, idan na karya jarin in ga uban da zai ɗorasu, matsiyata gayyar yunwa an samu mai kuɗi ana rawar jikin bin malamai a asirce shi aci dukiya"
Hafsa zuba musu id tayi tana kallon ikon Allah, tana kallon yadda ake cigaba da yi mata watsi da kaya, bayan ta kwashi zagi da cin mutumci a bainar nasi, Hafsa a yau tayi dana sanin sanin Khalil da tayi, dan haka ta yunƙura tayi wani abu wanda daga shi, zata yanke alaƙar ta da Khalil.
Ta ɗauko wayarta ta fara dannawa, zuciyarta na mata wani irin zafi, amma ta dake taƙi yin hawayen, ta shiga neman lambar Khalil.
Hajiya Turai ta yiwa Hajiya Zainab alama da ta fito.
Hajiya Zainab ta buÉ—e motar, ta fito ta nufo in da suke a tsaye da cincirindon mutane.
Gaban Hafsa ya faÉ—i, dan ko ba a gaya mata ba, kammanin matar da ta gani da Khalil ta san mahaifiyarsa ce.
Tuni ta turawa Khalil saƙo kamar haka
"Please man, idan ban takuramaka ba, ka taimaka mini da dubu goma"
Da saƙon ya isa wayar Khalil, yayi mamaki, dan ko da abu mai kamar wasa, bata taɓa roƙonsa abin ficika ba, amma yau tana neman dubu goma
Bai yi tunanin komai ba, ya tura nata dubu talatin.
Mummy ta ƙarewa Hafsa kallo, dan ta gano wani aibun nata, saboda ta ji daɗin cin mutuncinta, amma ba taga alamar wani aibu ba, bayan na talauci.
"Ni ce uwar Khalil, na zo ne nan ne da mutanena, dan in sake ja miki kunne, muddin baki rabu da shi ba, yadda na saka aka watsar da wannan tsiyar da kuke kasawa ku dogar da shi, haka zan saka a rushe mini in da kuke zaune, saina tabattar da kun dauwama cikin tsiya. Wannan gayyar iskar da kike kasawa, da dudu kuɗinsa bai wuce kuɗin ruwan robar da Khalil yake sha a sati ba, da na sa aka watsar, kaɗan nayi miki, kin san waye Khalil kuwa? Kin san waye ubansa a ƙasar nan, kin masa asiri zaki mallake mini shi? To ahir ɗinki wallahi, kuma daga yau na saka almakashi na datse duk wata alaƙa dale tsakaninki da Khalil, saboda ba sa'an Aurenki bane, naji ya ce ke marainiya ce, sai ki jira idan ya buɗe orphanage Home, sai ki requesting ko zaki samu gurbi"
Hajiya Salma ta ce "Talaka kenan, akwai ladabin dole, ga yadda ta sunkuyar da kai kamar ta Allah, irin wannan cinikin ne idan dare yayi suke tara maza su lamube su su basu kuɗi, banda haka ina wata awara zata riƙe mutu"
"Khalil ya biyani kuÉ—in asarar da akayi mini, kuma daga haka insha Allah in dai ni 'yar halak ce, bani ba Khalil har abada, in sha Allah na rabu da shi"
Hajiya Turai ta ce "Kar ma ki rabu da shi, kici ubanki ko ba dan Allah ba, ai karo da karo sai rago"
DOMIN SHIGA VIP GROUP KU TUNTUÆENI TA WANNAN LAMBAR.
AYSHERCOOL
08081012143
GABA DA GABANTA
BY AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
Page37
Hafsa tabi bayan su Hajiya Turai da kallo, da mamakin irin tsanar da ta gani ƙarara a idon Mummy.
Jikinta a sanyaye tabi wurin da aka watsar mata da kaya da kallo, ga sauran mutane da suke tsaye a wurin, Mussaman majalisar mai shayin nan, da wanda suke jin haushinta bata kula su, da wanda take burgesu saboda kamewarta, wasu suka jajanta mata, abin takaicin shi ne yadda har su Hajiya Turai suka yi mata tijara suka gama baby wanda yayi yinƙurin dakatar da su ko basu haƙuri sai son jin ƙwaƙwaf.
Daga irin zage-zagen da suka yi ne, wasu suka gane cewa mahaifiyar Khalil ce da jama'arta.
A gaggauce Hafsa ta durƙusa, ta dinga tsince kayanta da aka baje su a wurin kamar abun banza, zuciyarta na wani irin raɗaɗi da zafi, ta dinga ƙoƙari ta danne hawayenta, mai shayi ya tayata tsince kayan, ya so saka baki, amma ganin su Hajiya Salma sun yi kama da manyan 'yan duniya ya sanya bai iya saka baki ba. Ya tsare mata abin hawa ta shiga, mai shayi ya ce "Ayi ta haƙuri Hafsa, haka rayuwa take"
Ita dai ba ta ce masa komai ba, sai da taga mai Napep É—in nan ya ja baburin, ya bar wurin, sannan ta fashe da wani irin kuka, mai ban tausayi da ratsa zuciya.
"Yaushe zan samu sauƙin rayuwa ni Hafsa, daga wannan sai wannan, Astagfriullah" ta faɗa a hankali tana ƙanƙame jikinta, tana cigaba da raira kukanta, tana jin yadda zuciyarta tayi mata nauyi, shikenan Khalil ɗin da ta saka rai, ta fara samun afuwa a tare da shi, shima zai kauce, zata koma waccan duniyar da yayi ta ƙoƙarin fito da ita daga ciki, mai tarin damuwa da rashin gata.
Kan su kai gida, tuni idanunta sun yi mitsi mitsi, sun yi jawur kamar wadda aka sawa teargas, ta sauko ta sallami mai Napep, ta kwashi kayan da wasu suka yi buɗu- buɗu da ƙasa, ta shigo da su ta ajiye a tsakar gida.
Mama ta kalli kayan ta kalli Hafsa ta ce "Ke lafiya kuwa? Meye ya sameki wanan kayan ya aka yi suka yi kaca-kaca da ƙasa haka?"
Hafsa na ƙoƙarin dannewa, amma ta kasa kawai ta nufi ɗaki da sauri, tana zuwa ta faɗa kan katifar Mama, ta fashe da wani irin kuka, jikinta har rawa yake yi.
Mama ta biyo ta cikin tashin hankali, tana faÉ—in
"Hafsa ki gaya mini, meyafaru wannan wane irin kuka ne kike yi, Ki gaya mini menene" Mama tayia maganar cikin matsananciyar damuwa tana ƙoƙarin ɗago Hafsa.
Hafsa kasa magana tayi, kuma ta kasa yin shiru, nan da nan hankalin Mama ha ninka tashi, cikin rauni ta ce "Dan Allah ki gaya mini maiya faru, ko dai Najib É—in ne dai?" Hafsa ta girgiza kai alamar a'a.
"To Hafsa ki gaya mini menene, har bugun zuciyata ya sauya wallahi, dan Allah ki mini bayani" tayi maganar hawaye na cika idanunta.
A birkice Hafsa ta tashi zaune, tana girgizawa Mama kai ta ce "Mama dan Allah kar kiyi kuka"
"To Hafsa ya zan yi, kin shigo kina wannan uban kukan, ga kayan sana'arki duk ƙasa, dole hankalina ya tashi"
Hafsa ta sunkuyar da kanta, wasu hawayen ma zubowa, ta saka hannunta ta share hawawnta, ta É—an É—ago ta ce "Mama ina ga bani da sa'a a rayuwata"
"Subhanallah, kamar yaya, Meyasa kike faÉ—an haka?"
"Mama Khalil" ta faÉ—a tana sake fashewa da kuka.
Cike da zaƙuwa sa son jin ƙarshen zancen, Mama ta ce "Me Khalil ɗin yayi miki?"
Cikin kuka mai ƙuna zuciya, da dashewar murya, Hafsa ta ce "Mamansa ta zo ita da wasu mata inda nake sana'a, ta ce bani babu ɗanta, wai ni ba sa'ar aurensa ba ce ba, saboda ni talakace, suka ci mini mutunci a gaban mutane, suka zubar mini da kayan sana'ata. Ai kema Mama kin san ai ba dan kuɗinsa nake son sa ba ko?"
Mama tayi shiru, ranta ya ɓaci, idan Hafsa na cikin damuwa, tana iya haɗiyeta taƙi faɗa, amma tabbas tun da ta kasa ɓoyewa Mama, ta faɗa mata kai tsaye, abin ya girmama.
"Yanzu dan kawai kina 'yar talaka shi ne suka je suka yi miki Wannan cin mutuncin?"
Hafsa ta É—aga mata kai tana kuka.
"Shikenan, share hawayenki, Allah ya kawo miki mafi alkhairi, ita kuma Allah ya ganar da ita, in dai Khalil ne ba shine autan maza ba ai"
Hafsa ta faÉ—a jikin mama tana kuka, Mama ta rungumeta sosai tana rarrashinta, ganin Hafsa bata ganinta ya sanya ta lunshe idanunta ita ma, hawaye suka shiga kwararo mata, ita ta matsa Hafsa a kan ta yarda da Khalil, sai da ta yadda da shi tayi nisa a son sa wannan matsalar ta kunno kai, Mama ta share hawayenta ba tare da Hafsa ta gani ba ta ce "Ga ruwan wanka can na dafa miki, na kammla girkin dare, idan an yi sallar magariba, sai kiyi wanka ki zo ki ci Abincin dare.
Hafsa jin Mama kawai take, amma Abincin nan ba ciyuwa zai yi ba a wurinta.
Khalil kuwa ya dinga jerawa Hafsa waya, amma ko ɗaya bata ɗauka ba, ta share wayar, ƙarshe ma ta saka wayar a silent, ta jefata bayan katifarta.
Daddy na zaune a kan kujera 3seater, Fadila na kusa dashi, tana ta 'yan ciye-ciyenta tana masa hira irin ta uba da ɗa. Amina kuma na ƙasa a zaune tana kallon tashar da suke kallo.
Fadila ta ce "Ke ɗan jeki ɗakina, ki ɗauko mini wata leda a kan madubina" Amina ta tsani ke ɗin da Fadila kan kirata da shi, ko ita ko Mummy, amma ba yadda ta iya, haka ta tashi, ta nufi ɗakin Fadilan. Ta je ta ɗauko ledar ta kawo, ta miƙawa Fadila, Daddy ya ɗan ƙure Amina da ido, yana mata murmushi.
Amina dai bata nuna ma ta san ita yake yiwa murmushin ba.
Fadila ta ɗauko turarukan da Yazid ya bata ta ce "Daddy, sansana wannan turaren kaji, da ƙamshi?"
Daddy ya ce "Wow, lailatul sahara, na so turaren nan sosai, ina kika samo shi?"