← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 84

Sashe 3

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amina na zuwa nan a maganarta kawai sai ta fashe da kuka.
Sai kuma jikin Inno ya yi sanyi, ta kalli Amina ta ce "Amina, ta wani fannin ƙannen mahaifinki suna da gaskiya, ba abin da ya dace da 'ya mace, mai shekaru kamar ki sai zaman aure, wannan gararambar da ki ke yi a titi, da sunan karatun boko gaba ɗaya bai dace da ke ba, yanzu da za kiyi aurenki babu me binki gidanki ya ce sai kin zo kin masa wani aiki, amma ki duba maganata".

Amina ba ta ce komai ba, ta cigaba da share hawayen fuskarta, daga bisani ta tashi ta saka hijjabinta, kasancewar babban gidane ɓangare-ɓangare ne a gidan, ta zagaya ɓangaren Baffa Lawan, ƙanin mahaifinta dan kai musu niƙan.

Baba Hassan kuwa ya shiga tsananin damuwa da tunanin yadda zai samo Wannan kuÉ—in da Amina ta tambayeshi, tabbas ya na son Amina ta yi karatu me zurfi, ko bakomai ba za a yi mata gorin Jahilci ba, kamar yadda a kayi masa, har abun ya ke masa ciwo ba. Amma a ina zai samo kuÉ—in? Shi ne babbar damuwar sa.

****************
Kallo ɗaya za ka yi mata kasan a gajiye ta ke, hannunta riƙe da wani ƙaramin bokiti, bayanta kuma wani yaro ne da kaya a kansa ya ke binta a baya.
Ƙofar wani ɗan ƙaramin gida ta tsaya, shi ma yaron ya tsaya, ta sauke masa kayan kan sa, ta buɗe jakarta ta ɗakko masa Naira ɗari ta bashi, sannan ta shiga da kayan cikin gidan.

Sallama ta yi ta shiga cikin tilon É—akin da ke tsakar gidan. Matar da ke zaune akan sallaya daga cikin É—akin ta amsa tare da ce cewa "Sannu da zuwa".

Cikin siririyar muryarta ta ce "Yawwa mama, ya jikin naki?"

"Jiki da sauƙi Hafsa, ya cinikin?"

Ɗan ɓata fuska Hafsan ta yi ta ce "To, Alhamdilillah amma dai yau babu daɗi, dankali be ƙare ba, na dawo da sauran fal".

Matar ta ce "Bakomai, ki kwantar da hankalinki, sai mu ci da ranar nan, sauran sai ayi sadaka da shi".

"To Mama, bari in je in yi wanka in zo in yi salla, in ƙarasa ayyukan gidan".

Mama ta ce "Ai na gama komai ma, kiyi wanka ki ci Abincin".

Hafsa ta ce "Mama, ba ki da lafiya ki kayi aikin, da kin bari na dawo ai".

"A'a babu komai ai, na ji daÉ—in jikina Alhamdilillah".

"To Allah ya ƙara afuwa, bari in yi wankan".

"To shikenan" Mama ta amsa tana ƙoƙarin miƙewa daga kan sallayar.

****************
Kimanin kwanaki huɗu kenan da Amina ta yiwa Baba waya akan kuɗin jarrabawarta, amma shiru bai yi mata aike ba, hakan ya ƙara tabattar mata da ba shi da kuɗin ne, ga wannan 'yan uwan na sa, suna da shi ba basu da shi ba, amma ta san ko giya ta ke sha, ba ta isa ta tunkaresu da wani batu akan makarantar boko ba. Dan sun ɗau karatun bokon 'ya mace kamar wani karatun saɓon Allah, mussaman ita da suka sanyawa ido, suna ganin mahaifinta ya bata goyon baya ta cigaba da yawon boko, ya ƙi yi mata Aure, duk sa'aninta duk sun yi Aure, dan galibi tun a sha uku wasu ake aurar da su. Ita kuwa har yanzu babu ma batun Auren a gabanta, ta ƙi bawa kowa dama balle a nemi Aurenta.
  Misalin ƙarfe biyar na yammaci, Amina tana kan hanyarta ta dawowa gida da ga makarantar allo, ita kanta makarantar Allon duk babu sa'anninta, sai ƙannenta amma hakan bai dameta ba sam, haka ta ke shiryawa ta tafi makarantar allo idan ta dawo daga ta boko, ita ma a makarantar bokon ma ana yi musu ƙarin litattafan addini sosai, hakan ya sa a ilimin addini ma daidai gwargwado ta samu.
   "Kula mana karki faɗi". Da sauri ta dawo da ga duniyar tunanin da ta tafi, ta kalli mutumin da suka kusa yin karo da juna.
"Yi haƙuri"  shine abunda ta furta ta na ƙoƙarin wuce Mutumin.
Mutumin ya yi murmushi ya ce "Aminatu, ba gaisuwa ne?"
"Ina wuni" ta faɗa a daƙile, dan ba ta son doguwar magana, kowani abu da zai haɗata da shi sam.

"Lafiya ƙalau,ya Baban ki ko har yanzu bai shigo gari ba?".

"Eh bai shigo ba".

"Yawwa Amina, ni na gode Allah ma da yasa muka haɗu Yanzu, Amina ya Maganar mu ta kwanaki da na taɓa yi miki ne? Kinga yanzu lokacin kaka ne, da 'yan kuɗaɗena a hannuna, anyi mini girbi amfanin gona yayi kyau sosai, ki bani dama inje in ga babanki ayi Maganar Aurenmu".

Ta kalle shi, fuskarta babu walwala ta ce "Idan ka Aureni kakar kuma ta wuce fa? Da me zaka riƙeni?" Ta yi maganar tana watsa masa wani mugun kallo.

Mutumin ya gyara tsayuwarsa ya ce "Amina, kamar ba ki san waye ni a garin nan ba, ina da tarin gonaki da dabbobi, wanda ke kanki kin san ni ba talaka ba ne, yanzu haka wani daga cikin amfanin gona da na siyar, baki ga kuÉ—in da na sake tarawa ba, noman bana ba abin da zamu ce da Allah sai godiya".

Amina ta yamutse fuska ta ce. "To ina ruwana da kuÉ—inka? KuÉ—in da ba cib
ake yi ba, kamar yadda na gaya maka a baya, yanzu ma zan maimaita maka ne, ni ba zan iya Auren ka ba, ka mini tsufa, duk garin nan ba wanda bai san ka akan auri saki ba, duk shekara lokacin kaka, sai ka yi Aure ka saki wasu, 'ya'ya a gidanka kamar babu me su dan yawa, sunata gararanba a gari, ba kulawa, nima haka ka ke so ka Aureni ka sakeni da 'ya'ya? Dan Allah ka yi haƙuri, ka ga a cikin 'ya'yanka ma akawai ƙawata ai ana barin halak da kunya ma.
Ka dinga duba makomar wadda zaka aura, da tarin 'ya'yanka, sannan ni karatuna shine ya dameni ba aure ba a yanzu, dan haka dan Allah ka ƙyaleni".

Galala ya bi Amina da kallo, be taɓa zaton tana da baki haka ba, duba da ƙarancin shekarunta.

"Ke Yanzu kin gwammace ki tsufa a gari, ba kiyi aure ba? Kuma aike zan kashe miki kuÉ—i sosai, sai gidan da kike so zan sai miki, ba a cikin iyalina zan haÉ—aki ba".

"In dai Auren irin ka ne, da shi gara babu Wallahi, ni ka ga tafiyata ma" ba ta kuma saurarsa ba, ta tafi ta bar shi a gurin a tsaye cike da takaici.

**************
Mummy ce ta fito Falo, cikin wata dakakkiyar shadda ruwan toka, ta sha stone work, wuyanta zuwa hannunta duk gold ne, hannunta riƙe da mayafinta da jakarta.
A falo ta tarar da wata mata da yara guda biyu, kai da ganin matar ka san a wahala take, saboda yadda suke sanye da kaya tamkar tsumma, saboda koÉ—ewa.
A wulaƙance Hajiya Zainab, wato Mummy ta bisu da kallo, ya yin da suka risina suna gaisheta.

Ba ta amsa ba, ta ce "Lafiya daga ina?"

Matar ta risuna ta ce "Hajiya baki gane ni ba? Azumi ce maƙociyarku ta nan bayan layi".

Mummy ta sake ɓata fuska ta ce "Ohhh, sai yanzu na gane ki, ke ɗin ce kullum ƙara lalacewa ki ke kina ƙara muni, lafiya kuwa?"

"Hajiya taimakon nan dai da ki ka saba, shine na sake zuwa yau ma a taimaka, Wallahi marayuna ne yau kwana uku ba abin da na iya ba su suka ci, su masu sickler ga ciwo ya tashi, ga babu Abinci, na buga na buga na rasa yadda zan yi, shine na ce bari in zo don Allah ko ƙanzo ne ki taimaka ki bani in ba su" ta ƙarasa maganar ta na fashewa da kuka.

"Ya isa ni dan Allah yi mini shiru, ku zo ku takurawa mutane, kuna wani kuka kamar ragon mayya ku a dole sai anji tausayinku, ku haifi yara kaɗan ba zaku iya ba, ku daɗi miji su yi ta kwanciya da ku kuna haihuwa, ƙarshe ko su gudu ko su mutu su barku da 'ya 'ya".

Fadila ce ta fito ita kuma cikin wani tsadadden material me kyau, tana faÉ—in "Mummy am ready" tana ganin su Azumi a falo, ta yi turus tare da toshe hanci ta ce "Mummy Warin meye haka?, su kuma wannan mai suke yi mana haka a falo?".

A wulaƙance Hajiya Zainab ta ce "Wai yau ma dawowa ta kuma yi, ta na neman taimako".

"Kuma shi ne za su shigo mana falo, sai warin datti suke yi, mai yasa ba su zauna a waje ba in kin fito kya same su?"

"To ya zan yi? Wannan sakaran mai gadin ya buÉ—e musu sun shigo".

Cike da ƙyama Fadila ta ce "dan Allah ku ɗan jirata a haraba mana, wannan gaba ɗaya kun canza tempreture ɗakin kamar zan yi amai. Ke wa kuke da suna Asabe ki ke kowa? Wata a cikin ku ta zo ta sake mopping ɗin ɗakin nan, a kunna turaren wuta".

Azumi ta ji haushin abun da Fadila ta yi mata, ita da babarta amma babu yadda ta iya, haka ta koma waje ta jira.

Duk wannan wulaƙanci da cin zarafin, dubu biyu kacal Hajiya Zainab ta iya bawa Azumi, wanda sai da Azumin ta durƙusa tana mata godiya.

Suna tafe a mota, Mummy na cigaba da mita, da nuna tsantsar ƙyamarta ga talaka, tare da nuna kamar iyawarta ce ta sa Allah yayi ta a cikin daula.
Chapter 3 · 0% Book details