← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 84

Sashe 64

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khalil ya rasa yadda zai yi da ransa, gashi ya cinye satinsa biyu, amma babu wani daidaito a tsakaninsa da Mummy, balle ya sanya ran zata fahimce shi.
Kusan ƙarfe goma na dare, yana kwance a kan gado, ya rungume pillow, yana ta zuba soyayya a waya shi da Hafsa.

"Baby, ina ga haryanzu Abincin da kika mini, bai gama narkewa a cikina ba, har yanzu bana jin yunwa"

"Ni dai ban yadda ba, idan ulcer ta kama mini kai, sai mun yi faÉ—a"

"Allah Hafsa bana son cin abinci, ga kewar ki ta isheni zan koma wurin aiki"

Ta Kwantar da muryarta ta ce "Eyya,  ai ba komai, ka kwantar da hankalinka, zamu dinga waya".

"Ai ni nafi sonki a kusa da ni Babyna, ginin gidanki ya kusa kammala insha Allah, idan na je zan É—auko miki video ki gani, idan da abin da bai miki ba sai a sauya"

Hafsa ta ce "Wace ni in ce ga abin da bai mini ba, komai kai daidai ne, Allah ya yassare maka halal, ya tabattar mana da alkhairi"

"Ameen my sweet, yadda gari yake da sanyin nan, ace kina kusa da ni, kin dafa mana tea, ina sha ina kallonki cike da so da ƙauna"

Tayi dariya ta ce "Abin da ka hango kenan?"

"Eh mana, da mun yi aure ba ruwaa da bargo, kin isheni"

Ta É—an tura baki ta ce "Zaka fara ko? To sai da safe" ya buÉ—e baki zai yi dariya, yayi tozali da Mummy a tsaye a kansa, wadda ganin bai shigo cin abincin dare ba, duk da faÉ—an da tayi masa ya sanya ta biyo shi É—akinsa, ta zo ta tarar da shi yana waya da Hafsa.

Mugun kallon da ke masa ne ya sanya shi, rikicewa ya katse wayar yana kallonta"

AYSHERCOOL
08081012143
GABA DA GABANTA

BY
AISHA ADAM AYSHERCOOL

PAGE36

Cikin rikicewa da inda-inda Khalil ya ce "Mu..mmm...Mummy dan Allah ki tsaya ki ji"

"Me zan tsaya in ji banda wanda na ji Khalil, ai naji komai ka saurari matakin da ni kuma zan É—auka".

"Innalillahi, Mummy dan Allah kar ki yiwa Hafsa komai, marainiya ce"

"Eh marainiya ce, kai ne baitul mali ai, kai ne mai arziƙin ɗaukar nauyinta a ɗora maka wahala, kana nan kana gina mata gida ko? Sai ta shiga in gani, kaje ta dafa abu tayi barbaɗe barbaɗe ta baka kaci, zaka gamu dani" ta fice fuuu ta bar ɗakin.

A sukwane Khalil ya bita, yana kiran sunanta. Ya cinmata a falo.

"Mummy dan Allah kar a yiwa Hafsa wani abu, ni ki hukuntani, ba zata iya É—aukar hukuncin da zaki mata ba"

"Rufen baki Khalil, ni zaka mayar ƙaramar yarinya, wato har Asirin da suka yi maka ya fara tasiri a kanka ko? Matsa ka bani wuri kan in make ka"

Ya haɗa hannayensa biyu cikin magiya ya ce "Dan Allah Mummy ko sau ɗaya ki saurareni, wallahi mun shaƙu Hafsa bata da wani aibu, dan Allah ko sau ɗaya ki saurareni"

Shareshi tayi ta wuce É—akinta, Khalil ya zauna a kan kujera ya dafe kansa, wani irin gumi ya tsatsafo masa a goshi, duk da a yanayi ake na sanyi.

Amina da ke gefe tana kallon Tv tayi shiru, jikinta yayi sanyi tamkar ita ake yiwa faÉ—an, gaba É—aya taji babu daÉ—i, Saboda Hajiya Zainab ta iya tijara.

Ita Amina abin har mamaki ya bata, ɗanta ma ba ta ƙyaleshi ba, duk dan ya ce yana son 'yar talaka ake wannan dambarwar bala'in.

Jiki a saɓule Khalil ya miƙe, ya bar falon yana tunanin meye mafita, bai taɓa yiwa Mummy turjiya a kan wani abu ba, amma a wannan karon zuciyarsa na raya masa ya tirje, tun da Aurensa da Hafsa bai saɓawa Addini da kuma Al'ada ba, gani yake idan ya fasa aurenta bai mata adalci ba, kuma bai san wani irin hali zata shiga ba kuma bai san hannun wa zata faɗa ba, babban abin daya ƙara tsaya masa shi ne, bai wataƙila idan ya rabu da ita halin da zata shiga na damuwa ya fi na baya, tun da dama shigarsa rayuwarta ne ya bata ƙwarin gwiwa sakewa da rage mata damuwar da take ciki.

Washegari Daddy ya fito falo, ya tarar da Amina a zaune, tana jiran lokaci ya cika ta tafi makaranta "Ina kwana" Amina ta gaishe shi.

"Lafiya ƙalau, yau ban hararekin ba ko?" Murmushi tayi tana sake janyo jakarta jikinta.

"Har kin shirya tafiya makarantar?"

"Eh jira nake lokaci ya cika"

"Ok, school É—in ku sunyi mini waya, a first term za a yi muku registration É—in Jamb da SSCE ko?"

Amina ta ce "Eh haka suka ce mana"

"To ki ƙara dagewa, idan result ɗinki yayi kyau, hope baki manta da sirrinmu ba  ko?"

Cikin murmushi Amina ta ce "Eh, ban manta ba, zan yi karatu sosai in sha Allah"

Daddy ya ce "Good girl" hakan yayi daidai da fitowar Fadila, cikin shirin tafiya makaranta.

Ba ta kawo komai a ranta ba, ta zauna, ta zuba Abinci ta fara ci.

"Ina Mummynku ne?" Daddy ya tambayi Fadila.

"Bacci take, ta ce kar wanda ya dameta"

"Ok, nima fita zan yi yanzu".

"To Daddy a dawo lafiya" Fadila ta faÉ—a tana shan tea.

Da ido ya yiwa Amina alamar, ta biyo bayansa.

Amina ta miƙe ta saɓa jakarta, tabi bayan Daddy.

Sai da suka fito daga falon, sannan ya tsaya Amina ta ƙarasa in da yake, ya dubeta ya ce "Muje in ajiye ki a School ɗin, sai in wuce in da zani"

Amina ta ce "Amma Ba wani wurin zaka ba? Kar ka makara fa, zan hau Napep"

Yadda ya tsareta da ido ne, ya É—an tsuke fuska ya sanya ta yin shiru, yayi gaba ta cigaba da bin bayansa.

"To bari in je in gaida Baba"

"Ki sauri" ya faÉ—a tare da nufar in da motocinsa suke.

Amina ta isa wurin Baba, ta durƙusa har ƙasa ta gaishe shi.

"Lafiya ƙalau Uwata, kin tashi lafiya?"

"Lafiya ƙalau Baba, ya aikin"

"Alhamdilillah, zaki tafin ne?"

Amina ta ce "Eh, amma wai ya ce zai ajiyeni a makarantar"

Cikin rashin fahimta Baba ya ce "Shi wa?"

"Baban su Fadila"

Baba ya ɗan yi shiru, saboda ya lura a 'yan kwanakin nan akwai wani ɓoyayyen abu tsakanin Alhaji Ahmad da Amina, yanzu bata tsoronsa kwata-kwata, ga wata shaƙuwa a tsakanin su. Ga yawan kyautata mata da yake yi, ya yita sayen abubuwa yana bawa Baban ya bata, tuna miyagun fatan da su Bala suka dinga yi a lokacin da ya sanar da su Amina zata taho birni karatu.
Kan Baba ya ce komai, Alhaji Ahmad ya ƙaraso in da Baba yake da mota, ya sauke glashin motar, Baba ya taso da sauri, suka gaisa da Alhaji Ahmad.

Ya ce "Zan sauke Amina a makaranta sannan in wuce"

Baba yana matuƙar jin nauyin Alhaji Ahmad, mussaman duba da irin alfarmar da Ya yi masa a kan Amina, haka ya danne ya ce "To shikenan babu laifi, Allah ya saka maka da alkhairi"

"Ahh kar ka damu babu komai".

Amina ta zaga ta shiga mota, Daddy ya ja motar suka bar gidan.

"Daddy a kashe Ac nan sanyi fa" Amina ta faɗa tana duunƙule jikinta saboda sanyi.

Kwaikwayon muryarta ya yi ya ce "Ba za a kashe ba zafi nake ji"

A ɗan shagwaɓe ta ce "Allah sanyi nake ji, mura zan yi idan baka kashe ba"

"Mayar da ita ɗumi, ai kina kusa da wurin" yayi maganar yana mayar da hankali a kan tuƙinsa.

Ta ce "Ai ban iya ba"

"Ohh Ashe fa 'yar ƙauye ce"

Ta ɗan zumɓura baki, tana kallonsa ta gefen ido.

Miƙa hannunsa ya yi, ya canza zuwa ɗumi, tamkar zai taɓata, hakan yasa ta takure jikinta har da ɗan rintse ido. Yayi murmushi kawai sannan ya ce

"Kin gane kan wayar taki kuwa?"

"Eh na gane, wayar tana da kyau sosai, ga Camera mai kyau, duk nasa lambar ƙawayena da ta Baba a ciki, har what's app aka buɗe mini"

"Waye ya buÉ—e miki?"

'
"Ƙawata Azima"

"Kar ki sake zuwa da wayar makaranta, kuma ban yadda ki saka lambar wani  namiji a ciki ba"

Ta ce "Dama sau É—aya naje da ita makarantar, ba zan sake ba, amma har lambar mazan ajinmu ma ba zan saka ba? Kuma an sani a wani group fa na makarantarmu gaba É—aya".

Daddy ya ce "To daga haka kar a ƙara, idan ba haka ba what's app ɗin ma zan hana"

"Tom na gode sosai, zan kiyaye in sha Allah"

"Kin sa lambar ƙawaye Amma kika kasa ko yi mini flashing a wayar taki, ko kuma da safe ki gaisheni a wayar, bayan har kuɗi na saka a layin, kuma da lambata a ciki"

Amina ta zaro ido ta ce "Haka kurum, in kiraka ta É—aga in ce mata me?"

"Ita wa?"

"Au, ba kowa"

"Saifa kin faÉ—a, ita wa?"

"A'a, haka kurum in faɗa in je ka ajiye ni, a titi" Kawai yayi dariya ya cigaba da tuƙi.

A ƙofar makarantar ya ajiye ta, ya ce "In an tashi zan turo a ɗauko mini ke, ko in zo da kaina"

Amina ta kalleshi ta ce "A É—auko ni a kaini ina? Ina da kuÉ—in mota fa"

Ya haÉ—e rai ya ce "Haka nace"

"To Allah ya baka haƙuri, Allah ya kaimu a tashin" ta ƙarasa maganar tare da buɗe motar ta fice.

Ƙarfe goma da rabi ma safe, sannan Mummy ta tashi daga bacci, tayi wanka ta karya, ta cigaba da tunanin ta ina zata ɓullowa lamarin Khalil, yadda zata rabashi da yarinyar nan.

What's app É—inta ta buÉ—e, ta duba group É—in su, da suke ita da Hajiya Salma da Turai, tayi sallama.
Cikin ikon Allah duk suna online, suka amsa mata, suka gagaisa tare da tambayar junansu yara da kasuwanci, Mummy ta tura musu saƙon Voice message.
"Jama'a ku bani shawara yadda zan ɓullowa lamarin yaron nan, haryanzu fa yaƙi rabuwa da ita, jiya har naje ɗakinsa na tsaya a kansa yana waya da ita, bai san na zo ba, har gaya mata yake, wai zai yi mata video na gidanta na Abuja".

Nan da Nan Hajiya Salma ta haÉ—a group Video call, "Lallai ma Zainab, to wani matakin kika É—auka?"
Chapter 64 · 0% Book details