Sashe 56
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khalil ya lumshe idanunsa yana sauraron bayananta sannan ya furta "Ina sonki Hafsa, dan Allah duk ƙalubalen da zamu fuskanta kar ki rabu dani, na saba da jin daɗin kasancewata da ke, musamman yadda kike kwantar mini da hankali. Kina da haƙuri sosai da hankali, ni dai ina sonki"
"Nima ina sonka, dan kama fini haƙuri, ka kwanta kayi bacci"
"Allah ya tashemu lafiya"
Ta amsa masa da Amin.
Ya ajiye wayar, ya rintse idanunsa yana hango irin halin da zai shiga, idan aka raba shi da Hafsa, ita kanta yana tausaya mata, saboda tana matuƙar son sa, kuma ta saka ran samun afuwar rayuwa ita da mahaifiyarta saboda shigowar sa rayuwarsu.
Hajiya Zainab kuwa har ta kwanata tana mita da banbami, a kan abin kunyar da a ganinta Khalil yake shirin janyo musu, musamman a cikin ƙawayenta, haka ta cigaba da communicating da su Hajiya Turai, suna cigaba da zigata, a kan duk yadda za tayi ta yi ta raba Khalil da yarinyar nan, dan kar ya ja nata abin kunya, kuma kar ayi masa asiri a mallake mata shi.
Amina kuwa ta gama tsinkewa da lamarin Hajiya Zainab, dan bata taɓa zaton al'amarin zai yi zafi haka ba.
Washegari Amina tayi shirinta cikin doguwar rigar da Maman Azima ta bata, ta tafi makaranta, kasancewar lesson ne kawai ba da uniform suke zuwa ba, bada ban Alhaji Ahmad ya rarrasheta a kan ta yi haƙuri, ta cigaba da Zuwa lesson ba, da babu abin da zai sanya ta kuma zuwa, dan gaba ɗaya ta gaji da yawon lesson ɗin nan.
Ta bayan layin gidan tabi, sai dai duk da kasancewar unguwar ta masu hannu da shuni ce, akwai wanda suke masu ƙaramin ƙarfi ne a unguwar, wasu tsirarin mutane ta gano a ƙofar wani gida, ana ta fito da kayan cikin gidan waje, wata mata da tsohon ciki da yara kusan biyar suna gefe sunata kuka, yayin da wani mutum da alama shine mijinta, yake ta rirriƙe wani mutum yana bashi haƙuri tamkar zaiwa mutumin sujjada.
Amina sai ta tsaya tana kallon ikon Allah, wasu tsirarin mutane kasancewar safiya ce, suka tsaya suna taya mutumin bada haƙuri, shi kuma wanda ake bawa haƙurin sai kumfar baki yake yi "Wannan wane irin wulaƙanci ne? Tun yaushe kuɗin nasu ya ƙare, amma ƙaryar yau daban ta gobe daban yaƙi biya, gaskiya ba wani ɗaga ƙafa, akwai mutane a ƙasa suna neman gidan nan, kuma ma sayar da gidan zan yi"
"Dan girman Allah ka taimaka mini, maiɗakina tana watanta na haihuwa, idan Allah ya sauketa lafiya, kan nan na samu kuɗin biyaka, ka san asara na tafka kwanan nan a kasuwa, na gobara da ta ƙona mini kaya"
"Kaga ni fa sayar da gidana zan yi, idan ka samu kuÉ—inka kawai ka kama wani gidan"
Kasa jurewa Amina tayi, kawai ta wuce su ta tafi makaranta, tana tafe tana kuka, tare da tausaya wa mutumin nan da iyalansa, tabbas talauci babu daÉ—i, da ana taimako yadda Yakamata, masu kuÉ—in dake unguwar nan zasu iya sai wa kowane talaka gida, saboda sun ninka talakawan dake unguwar yawa, amma kowa kansa ya sani, sai ranar juma'a zaka ga can gidan ana rabon gurasa can gidan ana rabon alala.
Amina ta dinga jin inama ita wata ce, yadda ta san raɗaɗin talauci, idan Allah ya yi mata arziki ba zata taɓa barin na kusa da ita a wahala ba.
A haka ta ƙarasa makarantar, da tunane tunane daban daban a zuciyarta, tare da fatan Allah ya bata nasara a rayuwa ta zama wata.
Yazid ya nemi afuwar su Amra, na rashin samun damar tsayawa jiya ya koya musu assignment É—in su, sai yau ya tsaya yana koya musu, Fadila na hango shi, amma ba ta nuna tama ganshi ba, balle ta kula shi, sai da ya gama da su sannan ya taho wurinta.
"Dan Allah yau É—aya ki gaishe ni mana, ke kullum sana gaishe ki?"
Ta ce "Ni na saka ka gaishe ni?"
"A'a ni naga yakamata in gaisheki, in ji ya lafiyarki"
Maimakon ta bashi amsa ta ce "Yauwa nace ya ku kayi da Kankiya jiya?"
Yazid ya ce "Jiya har ƙarfe biyar ina school ɗin nan, amma bai dawo ba, yanzu haka ma da wuri na shigo yau, na je ofishin sa, amma sakatarensa ya ce mini baya nan, na zauna na jira shi amma bai zo ba"
"Kaga ka share shi kawai"
"Meyasa zan share shi? Ko wani laifin nayi masa ne dan Allah ki gaya mini?"
Fadila ta kalleshi ta ce "Ni ya za ayi in sani idan ma laifi kayi masa?"
"Saurayinki ne fa, zai iya gaya miki"
Haɗe rai tayi ta ce "Ni nayi maka kama da sa'arsa? Ai zaren ba kalar yadin ne, nafi ƙarfinsa dan haka kar ka sake haɗani da shi". Wani irin sanyi jikin Yazid yayi, lecturer ma fa kenan, ina ga shi karan kaɗa miya, bai ajiye ba, bai bawa wani ajiya ba.
"Meye naga ka wani yi shiru?"
"Bakomai, kawai ina tunanin dalilin da yasa yake kirana ne, ko dai zai ja mini kunne ne akan ki?" Da sauri ta kalleshi ta ce "Me kake nufi?"
"Ina nufin ya ce kar ya ƙara ganin mu tare"
A ranta ta ce 'kai wannan sai kace aljani, ya fiye saurin gane abubuwa'
"Ya kika yi shiru?"
"Ai ni da zai ya kiraka yayi maka warning ɗin, da ya taimaka mini, ka liƙe mini da yawa, na rasa irin wannan abun, kai gashi kome mutum zai maka ba fushi kake ba".
Murmushi yayi, ya sake matsawa kusa da ita, wanda hakan ya fara haddasa mata mutuwar jiki.
"Idan yayi mini haka bai mini adalci ba, kina daga cikin mutanen da zuciyata ta aminta da su shiga rayuwata, daga ranar da kika fara yiwa takalmin ƙafata dariya, zuwa rashin iya turanci na, ban ji ba daɗi a kan yadda kike mini dariya ba, sai wadda sauran 'yan aji suka yi mini, rayuwata da ke maybe temporary ne, da mun gama school shikenan, amma wataƙila in Allah ya ƙaddara ke matarsa ce tare zaku rayu har abada"
Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Dan Allah Fadila, ki bashi haƙuri kar yayi Wani yunƙuri da zai raba abotarmu, let's be friends"
Ta ce "Kai ka gaya masa mana, kuma ina ka taɓa ganin ana abota tsakanin namiji da mace?"
"Ba ayi, amma ina son mu mu fara" yayi maganar muryarsa can ƙasa.
Share shi tayi ta cigaba da danna wayarta.
Gaba ɗaya ya tattara hankalinsa a kanta yana kallonta, ko ƙiftawa baya yi.
"Dan Allah ka daina kallona haka, ni gaskiya ka takurawa rayuwata wallahi" ta faÉ—a a tsiwace tana jujjuya ido.
Ya ce "Kamar bani da zuciya ko?"
"Dama ina ka ganta" murmushi yayi bai ce komai ba, ya tashi tsaye ya bar mata seat É—in.
"In kana da zuciya kar ka sake zuwa wurin da nake, kuma kar ka sake kulani" bai waiwayo ba, yayi gaba yana murmushin da shikaÉ—ai ya san ma'anarsa.
Amina ta na aji ana lesson, ƙarfe sha ɗaya na safe, malaminsu ya shigo ajin, ya kalli Amina a ya ce "Amina ɗauko jakarki ki zo" cikin mamaki ta bi malamin da kallo, ta ga dai lokacin tashi bai yi ba, to ina zata?
Haka ta É—auko jakarta, ta biyo bayansa cikin mamaki.
Ga mamakinta Daddy ta gani a tsaye a ƙarshen barandar ajinsu.
Ƙarasawa ta yi ce "Daddy lafiya kuwa?"
Maimakon ya amsa sai ya ce mata "Ina kwana"
Ɗan sosa kai tayi sannan ta ce "Yi haƙuri, ina kwana?"
"Ai ni na fara gaishe ki, yau bamu haÉ—u ba sai yanzu, kuma na riga gaishe ki"
Amina ta ce "Yi haƙuri"
"Ai ba laifi ki ka yi mini ba, amsawa kawai zaki yi"
"Ai kunya nake ji, ba zan iya amsawa ba" tayi maganar tana sunkuyar da kai.
Dariya yayi ya ce "Zo mu tafi"
Ba musu tabi bayansa, zuwa mota, ya buÉ—e ya ce ta shiga.
Mamaki ya mamaye mata, tana son ta tambayeshi, amma tana tunanin kar tayi wani laifin.
Sai dai kasa jurewa tayi ta ce "Daddy ina zamu je ne?"
"Sayar da ke zan yi" ya bata amsa.
"To ai idan ka sayar da ni ba zan yi tsada ba"
Ya É—an buÉ—e baki ya ce "Inji wa? Tsada za kiyi sosai, har an biyani kuÉ—in ma" dariya Amina tayi tana cigaba da kallon titi, sai dai ga mamakinta, sai taga ba hanyar gida suka nufa ba.
Ta sake kallonsa ta ce "Amma Daddy..
"Shhh" ya katseta.
Haka ta zubawa sarautar Allah ido, sun É—an yi tafiya mai nisa, suka shiga wata unguwa, titunan unguwar kanta sai lokaci lokaci ababen hawa ke wucewa.
Gaban wani ƙaton gate Yayi parking, wani ɗan sanda ya leƙo, sannan ya koma ya buɗe gate ɗin.
'yan sandan sun kai huÉ—u a cikin gidan, suka dinga É—aga masa hannu suna gaishe shi, amma bai kula su ba.
"Daddy suna gaisheka fa" Amina tayi maganar tana waiwayawa.
"Eh na gani"
"To ya baka amsa ba?"
"Kai ke kam tambayoyinki sun yi yawa" bata kuma magana ba tayi shiru.
Yayi parking a ƙatuwar harabar gidan, ya kashe motar ya fice.
Amina zamanta tayi a cikin motar, tana waige waige.
Ya buÉ—e motar ya kalleta ya ce "sauko mana"
A É—an tsorace ta ce "Daddy dan Allah ina ne nan?"
"Wurin wanda ya saye ki na kawo ki"
Gaba É—aya jikinta yayi sanyi, ta bi idonsa da kallo.
"Sauko mana" ya kuma maimaitawa.
Jiki a sanyaye, ta sauko daga motar, tana bin gidan da kallo.
Yayi gaba tabi bayansa, gidan yafi wanda suke ciki girma sosai da sosai, kuma ya tsaru, ya ciro mukulli ya buɗe ƙofar shiga cikin gidan. Wani irin ƙaton falo ne, da sai ka taka steps Sanan zaka isa ga kujerun.
Fuskantar da Amina tayi babu mutane a gidan ne, ya sanya jikinta yayi sanyi, ta É—an tsorata.
"Shigo mana" yayi maganar yana kallonta.
Ƙarara yaga tsoro kwance a fuskarta, hakan ba ƙaramin burge shi yayi ba.