Sashe 23
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana nan zaune a mota, kusan mintuna sha biyar, sai ga Abdul ya dawo, ya buɗe wa Amina motar ya ce "Bismillah zo muje" Amina ta fito daga motar, cike da farinciki tana sake ƙarewa makarantar kallo.
Cikin ofishin shugaban makarantar suka shiga, suka tarar da shi a zaune tare da wasu malamai biyu, sai kuma Khalil.
Har ƙasa Amina ta zube tana gaishe su. Director yayi murmushi ya amsa mata, tare da yi mata umarnin ta zauna.
Ta samu wuri ta zauna, tana cigaba da ƙarewa ofishin kallo, a ranta ta ce "Allah sarki principal ɗinmu, insha Allah sai na gina masa Office irin wannan, mai irin wannan kujerun, shima a dinga sa masa turaruka masu ƙamshi".
Muryar director, ta ji yana tambayarta sunanta da harshen turanci, ta É—ago tare da amsa masa, ya tambayeta sunan makarantarsu, ajinta nawa? Shekarunta nawa? Gaba É—aya cikin harshen turanci, kuma ita ma cikin harshen turanci take mayar masa.
Gaba ɗaya Khalil bai zaci ko Makaranta ta taɓa zuwa ba, dan a haka ya yiwa director bayani.
Nan malaman nan suka fara yiwa Amina interview, sai dai duk ta basu mamaki, saboda kaifin basirarta, gashi duk abin nan cikin harshen turanci suke yi, kuma ko tangarÉ—a babu a bayanan nata da turanci.
Aka yi mata tambayoyi a fannin lissafi, gaba É—aya tayi soliving ba tare da amfani da calculator da aka bata ba.
Director ya ce "Kai Khalil kace gifted ku ka kawo mana? Alhamdilillah na yi farinciki sosai da sosai, yanzu zamu bata aji, ƙarfe biyu muke tashi daga makaranta, na ji daɗi sosai na yaba da ƙwazanta, insha Allah zamu yi ƙoƙarin bata ilimi yadda ya dace, yanzu za'a kaita aji insha Allah".
Amina ta ce "Ai bani da litattafai, littafi É—aya na É—auko".
Director ya ce "Kar ki damu, duk kayan rubutu mu zamu baki, har da jakar Makaranta ma"
Amina ta sake faɗaɗa fara'arta ta risuna ta ce "Na gode, Allah ya saka da alkhairi ya jiƙan magabata".
Suka amsa da Ameen, babban abin da ya ƙara burge su da Amina, shi ne yadda take da tarbiyya da ladabi sosai.
Suka fito daga Office É—in tare da director, da su Khalil.
Abdul ya kalli Amina ya ce "Idan an tashi daga Makaranta, kar ki je ko ina, ki tsaya a wurin da muka ajiye mota yanzu, zamu dawo mu É—auke ki, saboda kinga baki san hanya ba".
"To yaya Na gode, Allah ya biya muku buƙatunku na Alkhairi, ya sa ku gama da duniya lafiya, Allah ya shiga lamarin ku, ya saku farinciki kamar yadda ku ka sani" ta ƙarasa maganar har da hawaye a idonta, dan ba zata iya misalta farincikin da take ciki ba.
Abdul ya yi murmushi ya amsa da "Ameen, ki dage kiyi karatu da kyau Allah ya bada sa'a, ga wannan in an fito break ki sayi wani abun" yayi Maganar yana bata É—ari biyar.
Girgiza masa kai ta yi ta ce "A'a na gode zan iya zama har a tashi ban ci komai ba, a ƙoshe nake" tayi gaba tana ɗaga musu hannu. Wani irin murmushi ne ya suɓucewa Abdul, yarinyar ta burge shi, duk da ɗan karen surutunta, amma acting ɗinta zai tabattar maka da ga gidan tarbiyya take.
Tsakin Khalil ne ya dawo da shi daga tunanin da yake, ya bi bayansa zuwa mota, suna tafe Abdul na yiwa Khalil hirar Amina da yadda ta burge shi. Banza Khalil ya yi masa, dan tun haÉ—uwar sa farko yarinyar ta yi masa tsiwa yake jin haushinta, ga ta da shegen surutu da iyayi kamar jefaffiya.
An samu numfashin Yazeed ya daidaita, sai bacci da yake yi, saboda allurar da aka yi masa, har azahar Fadila ta je ta yi salla ta dawo bai farka ba, tana nan zaune taga ya fara motsawa a hankali, ta zuba masa dukkanin idanunta, dan babban fatanta dama shi ne taga ya tashi ya warware. Captain ya kira Fadila a waya cewar 'yan ajinsu zasu zo duba Yazeed, amma tace ya ware an sallame shi, saboda bata son ƙananan maganganu.
A hankali ya buɗe idanunsa, yana ƙarewa ɗakin kallo, ya kalli hannunsa dake ɗauke da canular anyi hanging ɗin drip.
A hankali ya juya ɗaya ɓangaren, ya yi tozali da fuskar Fadila, sai da gabansa ya faɗi, ƙoƙari yake ya gane, zahiri ne ko mafarki.
"Sannu" ta furta kamar an mata dole.
Ya jinjina mata kai alamar yauwa.
"Ina ne nan?" Ya yi maganar yana kallonta.
"Da ina ya yi maka kama?"
"Yi haƙuri gani na yi ban san environment ɗin ba, dan Allah zan sha ruwa" ya ƙarasa maganar da sigar magiya, tare da tashi zaune ya jingina.
Kamar ya yi mata dole, ta tashi ta buɗe ɗan ƙaramin fridge ɗin ɗakin, ta ɗauko ruwan roba mai sanyi ta miƙa masa. Ruwan sanyi ƙarara dan haka ya karɓa ya ajiye a gefe.
"Ba zaka sha ba ka sa na É—auko?" Ta yi maganar tana tsare shi da ido.
"Yayi mini sanyi da yawa"
Doctor Aliyu ne ya shigo É—akin, ya tarar da Yazeed a zaune "Masha Allah, Alhamdilillah ka farfaÉ—o kenan?" Ganin farar riga a jikin Aliyu ya sanya Yazeed gane cewa likita ne.
"Eh doctor".
"To yaya kake jin jikin yanzu?"
"Alhamdilillah, bana jin ciwon komai, sai rashin ƙwarin jiki".
"Ok, shima insha Allah zai ware, for how long kake da Asma?"
Yazeed ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Gaskiya an jima, da farko pnuemonina ne, sai ya koma asma, to daga baya ya zama chronic, a hankali kuma da na ƙara girma, sai na rage samun attack ɗin, dan har ina aiki a cikin hayaƙi, ƙura idan ba tayi yawa ba ba ta damuna, rabona da ciwon ya tashi nafi shekara huɗu, sai yau na sheƙi hayaƙi da ƙura, na fara tari kuma daga nan ban san abinda ya sake faruwa ba"
Haka kurum Yazeed ya bawa Fadila tausayi, ya sha wahala sosai daga É—azu zuwa yanzu. Nan Aliyu yayi ta bawa Yazeed shawarwari tare da rubuta masa wasu magungunan, ya ce a sayo masa wani abun ya ci.
Fadila ta fita ta bawa security Asibitin kuÉ—i, dan ya siyo wa Yazeed Abinci.
Mamaki ne fal da tambayoyi a cikin ran Yazeed, amma ya san idan ya tambaya ba zai samu gamshashiyar amsa ba, sai ma dai baƙar Magana.
Sallamar Yusra ce ta katse masa tunaninsa, Fadila na ganin Yusra ta miƙe tana faɗin "Beb sai da ki ka zo?"
"Na kasa jurewa ne, na ce gara in zo in ga mai jikin, kuma naga Alhamdilillah shi ne a zaune ko?"
Fadila ta ɗan taɓe baki ta ce "Sannu bawan Allah"
Yazeed ya ce "Yauwa sannu da zuwa"
"Allah ya sa kaffara ne"
Ya amsa da Ameen.
Security ne ya shigo da ledar wani restuarant, ya miƙawa Fadila ta sa hannu ta karɓa ta ciro dubu ɗaya ta bashi, ta fito da takeaway ɗin, ta buɗe dankali da miyar jajjage sai uban yankan naman kaji a kai, ta ajiye wa Yazeed ta ce "Gashi nan kaci, Aliyu ya rubuta maka sallama, in ka gama sai in ajiyeka a gida in wuce gida".
Yazeed ya ƙurawa Abincin ido, amma yaƙi ko motsawa balle ta sa ran zai ci.
"Magana fa nake maka kai mini banza"
"Alhamdilillah na ƙoshi" ya furta yana kaucewa haɗa ido da ita.
"Ban gane ka ƙoshi ba, amma a gabanka ya ce a samo maka Abinci ko?"
Yusra ta ce "Kai kuwa ka daure ka ci mana, ko baka cin irin wannan?".
Yazeed ya ce "Wannan ba cimata bace ta ɗan talaka, ba zan iya cin Abincin nan ba, Na gode sosai da kulawarki a gareni Fadila, ba zan manta ba har abada, amma wannan cimar ku ce ba irin tawa ba, zan ƙarasa gida na samu abin da zan ci a can"
Tsaki Fadila ta yi ta miƙe tsaye, ta kalli Yazeed cike da masifa "Ni zaka rainawa hankali ka gayawa baƙar magana, in wuni a Asibitin nan saboda kai, na san silata ciwonka ya tashi amma ka raina mini hankali, tun safe nake Asibitin nan saboda kai, ko ruwa ban kai cikina saboda zullumi, amma daga tashin ka ka fara ɓata mini rai" ta cillo masa ledar magungunan da aka kawo daga Pharmacy ta ce "Gashi nan, idan ka ga dama ka ɗauka shima idan ba ka ga dama ba ka barshi a wurin aikin banza kawai"
Yusra ta riƙota tana faɗin 'Haba Fadila ba a haka, ai sai ki zobe ladan ki, baki ga ba shi da lafiya ba, ki dinga haƙuri dan Allah"
"Dalla sakar mini hannuna, ba za ai haƙurin ba" ta figi jakarta tayi waje fuuu.
Yazeed kam murmushin gefen baki yayi, ya sauko daga kan gadon a hankali, Yusra tayi ta bashi haƙuri ya ce "Bakomai kar ki damu" sun kai ruwa rana da Yusra kafin ya yarda ya karɓi maganin, shima mutuncin yarinyar ya gani ya karɓa.
Ya shafa aljihunsa ya ji babu komai, dan haka ya sadaƙar jotter sa, da hamsin ɗin jikinsa sun zube, a halin da yake ciki ya fara daɓawa da ƙafafuwan sa dan tafiya gida, ya samu masallaci ya rama sallolin da bai yi ba, daga nan ya wuce gida.
Ƙarfe biyu Abdul ya addabawa Khalil a kan su koma su ɗauko Amina, ko da suka koma tana in da Abdul ya ce ta tsaya, goye da ƙatuwar jakarta ta makaranta.
Tana ganin motarsu ta faɗaɗa fara'arta, ta ƙarasa ta buɗe motar ta shiga, wannan karon Khalil ne yake tuƙi dan a motarsa suka zo, ta gaishe su Abdul ya amsa, amma Khalil ya yi mata banza.
"Amina 'yan makaranta, ya makarantar ya baƙunta?".