← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 84

Sashe 47

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ai ban san kana gida ba, an cinye komai sai dai in wani abun zan dafa maka"

"No, haÉ—o mini coffee kawai, ina da biscuit sai in haÉ—a" yana gama maganar ya juya ya bar wurin.

Mamaki ne ya kamata, babban mutum kamar wannan ya ce zai karya da biscuit.
Kitchen ta nufa, cikin azama ta fara feraye dankali.
Hajara ta shigo kitchen É—in ta sameta tana gyara dankali.
"Amina me kuma zaki da dankali?"

"Babansu Fadila ashe yana gida, hajiya ba ta yi mana bayani ba, ba a yi breakfast da shi ba, shi ne nake haÉ—a masa"
"Yayi" shi ne abin da Hajara ta ce ta bar kitchen É—in.
Nan da nan Amina, ta dafa tea da dankali, ta haÉ—a a tray ta tafi kai masa, sai dai ta shiga tunanin ina zata kai masa?. Ta yanke shawarar kai masa kan dining, taje ta ajiye ta cigaba da sabgoginta, sai kuma ta tuna ba yadda za ayi ya san ta kai masa, idan ba gaya masa tayi ba.

Cike da faÉ—uwar gaba, ta nufi part É—insa, ta shiga da sallama, yana zaune a falonsa yana kallon labarai. Bai waiwayo ba ya amsa mata.
Cikin ladabi ta ce "Ga Abincin can a kan dining".

"Kawo min nan" ya faɗa a taƙaice. Amina ta ɗan yamutsa fuska ta koma falo, tana mitar Alhaji Ahmad ya fiye mulki, sai dai shi baya wulaƙanci kamar matarsa da 'ya'yansa, sai dai miskili ne na gaske.

Da sallama ta koma falon, taje gabansa da tray a hannu ta tsaya, ta kalli kan Centre table ya miƙe ƙafafuwansa a kai, ta wuce Kan dining ɗin dake falon, ta ajiye masa. Har ta juya zata fita a hankali ya ce "Nan zaki kawo mini"
Amina ba ta san lokacin da tura baki ba, ta sake ɗauko trayn ta dawo gabansa, ta kalli ƙafafuwansa dake kan Centre table, in da yakamata ace ta ajiye kayan Abincin.
"To a ina zan ajiye?" Tayi maganar tana satar kallonsa, dan ba ƙaramin kwarjini yake da shi ba.
Shareta yayi, ya cigaba da latsa remote É—insa.
Ta ajiye a saman carfet, ta juya zata fita "Zo nan" ya faÉ—a ba tare da ya kalli in da take ba. Ta dawo ta tsaya.
Ya sauke ƙafafuwansa daga kan Centre table ɗin, yayi mata nuni da ido, a kan a nan zata ajiye masa Abincin.
Kamar Amina ta fasa ihu, dan ta ƙulu sosai, haka ta ɗau tray ɗin ta ajiye a kan table.

"Come back in the next 30minutes" ya faÉ—a yana gyara zamansa.

Amina ta bar falon tana "yau naga tsiya da wasali, da iko da mulkin mulaka'u na masu kuɗi, a haka kamar na Allah ashe shima ya iya tsiya, aikuwa ba zan koma ba" ta leƙa ɗakin Hajara ta ce "Mai gidan nan ya ce kije nan da mintuna talatin"

Hajara ta zare ido, ita a zamanta a gidan nan banda gaisuwa ba abin da yake haÉ—ata da Alhaji Ahmad, ko aiki baya sata, me zai sa ya ce ta je?

"Amina  nayi laifi ne?"

"Nima ban sani ba, ya ce dai kije"

A rikice Hajara ta ce "Na shiga uku Allah ya sa ba korata zai yi ba ni Hajara"

Amina ta koma É—aki abin ta, yayin da Hajara ta tasa agogo tana lissafin mintuna talatin cikin zullumin rashin sanin dalilin kiran da mai gidan yake mata.
Sai da Hajara tayi Addu'oi sosai sannan ta tunkari sashin Alhaji Ahmad.
Tayi sallama ya amsa mata, ta ƙarasa ta shiga falon, ta zube a ƙasa ta ce "Alhaji gani, Amina ta ce kana kirana".
Da mamaki ya kalli Hajara ya ce "Ni kuma?"

"Eh haka ta ce mini, tun É—azu ta ce bayan mintuna talatin kana kirana" ya É—an yi shiru tare da jinjina kai ya kalli Hajara ya ce "Kirawo mini ita" Hajara ta koma ta kirawo Amina, sai dai bata É—akinta, sai da tai ta dubawa ta ganota a É—akin Fadila tana gyara mata.
Nan Hajara ta isar mata da saƙon Alhaji Ahmad na kiranta da ya yi. Sai kuma a lokacin ita ma cikinta ya ɗuri ruwa, sumi-sumi tabi bayan Hajara suka koma falon Alhaji Ahmad. Ya kalli Hajara ya ce "zaki iya tafiya"

Sai a lokacin Amina ta ga tayi wauta, ya mayar da hankali ya cigaba da kallon TV, tamkar bai san da wanzuwar Amina a wurin ba.
Amina tun tana sanya ran zai kulata, har ta sare gashi ta gaji da tsayuwa, ya É—ago ya kalleta, yayi mata alama da ta je gabansa. Ba musu ta je in da yayi mata nuni. "In zauna?" Ta faÉ—a a raunane.

Ya ɗaga manyan idanunsa masu matuƙar haske da kwarjina, ya tsareta da idanunsa ya ce "Na ce ki dawo in the next 30minutes, amma kin turo mini wata, kin kyauta kenan? Ko kuma kin san dalilin kiran?"

Amina ta ɗaga kai ta kalleshi, amma tayi saurin janye idanuwanta ta ce "Dan Allah kayi haƙuri, nima sai da ga baya na ga nayi laifi, kayi haƙuri"

"Kwashe kwanukan nan, kije ki dawo, ko bana falon ki jirani" ta amsa masa da to, ta kwashe kwanukan ta fita sai dai tana zuwa kitchen ta tarar Hajara na tsaye na jiran dawowar ta.

"Amina me ya ce miki? Naga kin daɗe" haɗe rai Amina tayi tana tura baki taƙi kula Hajara, ta lura kwanakin Hajara ta koyi munafunci da sanya ido.
Ko da ta koma Alhaji Ahmad baya falon, dan haka ta zauna a kan carfet tana jiransa, dan bata manta kashedin Hajiya Zainab ba a game da zaman kan kujera ba.

Ta daɗe a zaune, sai ga Alhaji Ahmad ya fito, sanye cikin wani baƙin yadi, ya haska yadin kasancewarsa fari, sai zuba ƙamshi yake yi. Yaje ya buɗe wata drower ya tako in da Amina take, wadda tuni ta miƙe tsaye, ba tare da ya kalleta ba ya ce "Ranar Sunday in Allah ya kaimu, zani wani ɗaurin Aure haɗeja, ƙarfe shida da rabi zan fita, a ɗan sama mini abin da zan ci kan in tafi"
Kamar mara gaskiya Amina ta sunkuyar da kai ta ce "To, insha Allah"

"Karɓi nan" Ya miƙa mata envelope ɗin hannunsa. Ta ɗago ta kalleshi sannan ta kalli envelope ɗin, amma ta kasa karɓa.

"Karɓi mana" yayi Maganar yana sake miƙa mata.
Jiki a sanyaye ta sa hannu ta karɓa, ganin tambarin makarantarsu a jiki ne, ya sanya hankalinta ya ɗan kwanta.

"BuÉ—e da sauri, zan fita" jiki na rawa Amina ta fara kokowa da envelope É—in, tana ganin takarda ta san result ne, aikuwa gabanta ya faÉ—i, hannunta ya hau rawa.

"Ko ba kiyi abin Arziƙi bane, kika tsorata haka?" Bata san lokacin da ta ɗaga masa kai ba alamar eh.

"To ciro mu gani" ya faÉ—a yana cigaba da tsareta da ido.

Ta zaro paper, ta shiga dubawa duk grades ɗinta A ne, First position ta gani a jiki. Wani irin farinciki mara misaltuwa ya ziyarci zuciyarta, ta ɗago ta kalli Alhaji Ahmad fuskarta ɗauke da murmushi, ga hawaye a lokaci guda na farinciki da suka zubo mata a kan fuskarta, a kan gwiwarta ta zube ƙasa tana kallonsa.

"Yadda ka faranta mini, ta hanyar maida ni makaranta, Ubangiji Allah ya faranta maka, ya sa ranar alkiyama ka karɓi littafinka a hannun dama" har cikin kansa addu'a da tayi masa ta tsirga masa.
"Ameen ya Allah, Na gode tashi tsaye"
A hankali ta miƙe tana cigaba da share hawayen fuskarta.

"Makarantarku sun kirani, naje na karɓo result ɗin ki, nayi farinciki sosai da yabon da suke miki, na ƙoƙari da jajircewa, sai dai an ce ba kya jin magana haka ne?" Amina ta sunkuyar da kai alamar a'a.

"Ya zaki ce a'a bayan nima kinyi na gani"

"Dan Allah kayi haƙuri na daina, kar ka gayawa Baba"

"Anyway, an sanar da ni cewar kin ci wannan jarrabawar da suka yi muku, 15th December in Allah ya kaimu, zaku je Abuja, wurin baban Quiz na ƙasa da sauran festival da ake yi na makarantu, zasu fara yi muku lessons na mussaman"
Amina ta ɗan yi jimm, da ta san abu ne mawuyaci Baba ya barta taje Abuja, amma ta dake tayi murmushi ta ce "Allah ya kaimu, na gode sosai Allah ya ƙara buɗi yasa ka fi haka, inje in nunawa Baba result ɗin?" Ya jinjina mata kai. Ta juya da sauri ta bar falon.

A harabar gidan ta tarar da Baba da Zakiru direban Alhaji Ahmad, suna hira, da fara'arta ta tunkaresu, ta miƙawa Baba takardar hannunta.
Ya karɓa tare da kallonta ya ce "Uwata menene wannan?"

"Baba sakamakon jarrabawata ne, ka duba ka gani".

"To ai kin san sai dai ki karanto mini".

"Baba ta É—aya na zo, duk ajinmu na fi kowa maki"

Baba ya faÉ—aÉ—a murmushinsa yana faÉ—in "Alhamdilillah, dama na san uwata ba zata bani kunya ba"
Zakiru ya karɓi result ɗin yan dubawa, ya murmusa ya ce "Baba Hassan lallai wannan 'yar taka ƙwaruwa ce, Allah ya dafa 'yar gidan Babanta"
Amina tayi murmushi ta ce "Amin Malam Zakiru na gode sosai, ka mini alƙawarin cigaba da koya mini karatun addini, amma haryanzu ka ƙi saka lokaci"

Zakiru ya ce "Ba ƙi nayi ba Amina, kinga yanayin aikin namu, wasu lokutan nike kai Alhaji duk in da za shi, idan ba haka ba kuwa gyaran harabar gidan nan kaɗai da aike ta isa ɓata lokaci. Kuma da zarar sun ga muna karatun nan za'a iya tsiro wani abu daban, amma insha Allah zan saka mana lokaci"

"To shikenan, na gode sosai"

Alhaji Ahmad ne ya fito harabar gidan, Zakiru ya nufi in da motarsa take, dan shi zai fita da shi. Baba kuwa ya nufi Alhaji Ahmad, ya cigaba da yi masa Addu'a da godiya.
Alhaji Ahmad ya ce "Ba komai, ai ɗa na kowa ne, naji daɗi sosai kaga zan cigaba da samun ƙwarin gwiwar biyan kuɗin makarantar, tun da tana abin da ake so"
Baba ya ce "Haka ne, Allah Ya ƙara arziƙi"
Ya amsa da Ameen ya nufi mota.
Chapter 47 · 0% Book details