Sashe 45
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Khalil ji yayi kamar ya gayawa Abdul, halin da ake ciki, amma yaji wannan sirrin Hafsa ne, idan ya bayyana bai yi mata adalci ba.
Suka je suka yi salla, Abdul ya ɗau Khalil zuwa wurin da suke zuwa shan fura, dan yaji daɗi, ya bawa Abdul labarin abin da dangin Mahaifin Hafsa suka yi musu, amma ya ɓoye masa batun fyaɗen nan.
Ya ɗora da cewa "Abdul, nayi mamakin jin yadda dangin mahaifinta suka yi musu haka, dangin Daddy nake tunawa, irin karamcinsu da soyayyarsu a garemu, danma Mummy ba ta son alaƙarmu da su".
Abdul ya ce "Khalil, lokaci yayi da yakamta ka cigaba da zumunci da dangin mahaifinka, ko da Mummy ba ta sani ba".
"Ka san wani abu, ina ganin zan shigar da ƙarar yayyane mahaifin Hafsa a ƙwato musu hakkinsu".
Abdul ya ce "A'a Khalil, bakomai ne ake amfani da dukiya ko ƙarfi wurin ƙwatarsa ba, ka mayar da hankali wurin mallakar yarinyar, da kyautata musu, su bar su da Allah kawai, ba abin da dukiyar zata amfana musu, dan ba guminsu bane a banza zasu kaɗar da ita".
"Abdul, ji nake tamkar in nemo yaron nan da ya kai Hafsa wurin 'yan sanda in kashe shi" a razane Abdul ya kalleshi ya ce "Kayi hauka ne kake zancen zaka kashe wani, me yayi maka?"
Taune lips ɗinsa na ƙasa yayi, yana jin yadda zuciyarsa ke wani irin lugude, kansa na sarawa, yayi shiru bai kuma cewa komai ba.
Ba dan Hafsa na gudun kar Mama ta gane wani abu na faruwa ba, da ba zata fita wurin sana'ara ba ma, haka ta fita wurin sana'ar nan sama sama haka take, loka lokaci tana duba wayarta, ko zata ga kiran wayar Khalil ko saƙonsa, amma shiru ba ta gani ba. Hakan ya ƙara jefata cikin damuwa da karaya, ta saddaƙar Khalil ya rabu da ita kenan, ba zai iya ɗaukar ƙaddarar da Allah ya jarabceta ba. Gashi wani irin son Khalil take ji a ranta.
Khalil ya ɗan samu sauƙi, amma sam ya kasa kunna wayarsa, saboda gaba ɗaya kaɗaici yake so baya son damuwa sam, saboda ciwon kai da yake damunsa haryanzu, duk da tunanin Hafsa da tausayinta sune suka haifar masa da halin da ya tsinci kansa a ciki, yana son ya kirata a waya yaji ya take, amma ganin idan ya kirata bai san me zaice mata ba ya sanya ya fasa kiran nata.
Amina ta lura ƙarfe bakwai saura, Daddy ya ke shiryawa ya fita, ko karyawa ba ya yi.
Ƙarfe shida saura tana kitchen tana aiki, taji motsi a falo, dan haka ta fito falon, Daddy ta gani yayi shirin fita, sai zuba ƙamshi yake.
"Daddy ina kwana" ya É—aga idonsa ya kalli Amina, dake tsaye tana kallonsa.
"Lafiya ƙalau" ya amsa mata.
"A kawo breakfast ne? Naga zaka fita baka karya ba".
"No, ina daf da makara, ba saina karya ba".
"Ok, bari in kawo maka mota, sai ka tafi da shi".
"Ok, shikenan" Amina ta koma kitchen, ta haÉ—o Abinci a cikin kwanuka ta saka a kwando, ta kaiwa Daddy mota.
Mama tana banɗaki tana wanka, Hafsa ta saka wayarta a gaba, tana ta gursheƙen kuka, sam ba ta san Mama ta fito daga wanka ba, sai ganin Mama tayi a tsaye a kanta. Da sauri ta wayance ta fara ƙoƙarin goge hawayen.
Mama ta ce "A'a, ai ba sai kin wayance ba, kin san adadin lokacin da na É—auka atsaye a kanki? Ni dama a kwana biyun nan tun da muka dawo daga Asibiti naga kamar kina cikin damuwa, sai dai bana son takura miki ne, saboda ke idan baki ga dama ba mutum in zai mutu, ba zaki faÉ—a masa damuwarki ba. Yanzu gaya mini meye dalilin wannan kukan?".
"Mama bakomai".
"Bakomai Hafsa, ba zaki gaya mini ba kenan, me kike kallo ko kike jira a wayar da kika sata a gaba kina kallo?".
Bata san lokacin da ta sake rushewa da kuka ba, tare da faÉ—in "Mama Khalil".
Mama ta zauna kusa da ita ta ce "Meyafaru da Khalil É—in?".
"Mama na gaya masa, be sake kirana ba, ina ga ba zai iya aurena a haka ba, Mama ba zan taɓa yafewa dangin mahaifina ba, sun mini mugun tabo, ba kowa zai yadda da ni ba"
Jikin Mama yayi sanyi ƙalau, ta rungomo Hafsa a jikinta, ta runtse idanunta hawayen tausayin Hafsa na tsiyaya daga idanunta.
"Taki ƙaddarar kenan Hafsa, a haka Allah zai baki wanda zai so ki a haka, ki daina kukan nan" ƙanƙame Mama Hafsa tayi, ta cigaba da rusa kuka tamkar wadda uwarta ta mutu.
Sai bayan la'asar Sannan Alhaji Ahmad ya dawo gida, da Amina ya fara tozali, tana kunna wa falo turaren wuta, tana sanye da doguwar rigar atamfa, ta É—aura É—ankwalin atamfar.
"Sannu da zuwa" ta faÉ—a cikin girmamawa.
Ya amsa mata da cewa "Yauwa sannu, ga kwanukan ki can a mota, kije ki É—auko na gode sosai".
"To Daddy, bari in gama kunna turaren zan ɗauko" ta cigaba da zaga falon, dan ko ina ya samu ƙamshin turaren, ya nufi sashinsa kai tsaye.
Sai da Khalil ya kwana uku, sannan ya samu ya rabu da wannan matsanancin ciwon kan, ya ɗan ji ƙwarin jikinsa, yaji ba abin da yake buri banda ya ga Hafsa.
Da magariba ya shirya cikin ƙanan kaya, ya sha turare bai ko tsaya yiwa Mummy sallama ba, saboda baya son ta tutsiye shi da tambayar ina za shi?.
Fadila na É—akinta, tana game a waya, Mummy ta shigo tana É—an tsareta da ido.
"Mummy ya dai?"
"Wace maganar na ji doctor Aliyu yana yi É—azu?"
"Wace magana kenan Mummy?"
"Wa kika kai Asibiti?"
Fadila ta ce "Ba wani bane, wannan Yazeed É—in ne da nake baki labari"
"To meye haÉ—inki da shi da zaki kai shi Asibiti? Nifa bana son jaye-jaye me haÉ—in kanwa da kuka?"
"Mummy, bani da wata alaƙa da shi, bani da wani zaɓin da ya wuce in kai shi Asibiti Mummy, na taimaka masa ne saboda..
"Saboda me? Wanene É—inki shi?"
"Mummy matsalata da ke saurin É—aukar zafi, ki tsaya ki saurareni Mummy, da ban yi hakan ba da tuni ina nan ina rama azumi sittin".
Mummy ta ce "Kamar yaya?"
Nan ta warwarewa Mummy abin da ya faru, ta ɗora da cewa "Shi ne saboda son gulma yake wani tambayata a gabanki, ni babu wata alaƙa tsakani na da Yazid".
"To ai shikenan, duk da haka a dai kiyaye, dan ba zan amince a kawaso mini gayyar tsiya cikin zuriya ba".
Fadila tayi murmushi ta ce "Mummy kenan, ki sha kuruminki, ai nima na san ni ba kalar talaka ba ce"
"Ƙwarai kuwa, ai mun tattauna da Hajiya Turai, akwai ƙaninta da ya taɓa ganin hotonki ya ce mata yana sonki, a U.K yake aiki, ina jiran ya dawo ne tukua kan in sanar da ke, sai kuma Allah ya kawo hira na ke gaya miki"
Yamutsa fuska Fadila ta yi, taƙi magana.
"Ya kika yi shiru?"
"To Mummy me zance? Ni dai in bai mini ba, ba ruwana da wata U.K"
"Ke dalla can, zai ma yi miki"
Fadila ta ɗan taɓe baki, sai dai kawai taga fuskar Yazeed na mata gizo. Har Mummy ta ƙarasa surutanta ta fita daga ɗakin, ba wani gane me take faɗa take ba.
Wayarta ta miƙa hannu ta ɗauko, ta ci karo da saƙon Kankiya, da yake addabarta da su. Wani uban tsaki ta ja, ta kashe wayar, maganar Yazeed na ƙoƙarin zamowa gaskiya, Sir Kankiya sonta yake yi.
Æangaren Hafsa kuwa, wunin da tayi koke koke ita ma ya sanya, ciwon kai ya kamata, dan ko wurin sana'ar ba ta fita ba, ta kasa cin abinci sai aikin rarrashi da Mama take yi.
Wayarta ce ta ɗan yi vibrating, ta miƙa hannu ta duba.
 Message ne. "Ina waje"
Da sauri ta tashi zaune ta ce "Mama, Khalil ne wai yana waje"
Mama ta ce "Alhamdilillah" da sauri Hafsa ta tashi zata zari hijjabi.
"Haba ke kuwa, kije ki wanke wannan kumburarriyar fuskar ta ki, ki canza wasu kayan mana"
Cikin azama Hafsa ta je ta wanke fuskarta, jiki na rawa ta fara neman kayan da zata sauya.
Tausayin Hafsa ya kamata, tabbas Hafsa ta kamu da son Khalil sosai.
Ta ɗau dadduma ta nufi hanyar fita har da tuntuɓe.
Yana tsaye a jikin motarsa tana ganinsa ta tsaya cak, tana kallonsa.
"Shi ne kika shanya ni, da juyawa zan yi in koma ai" Kawai ta fashe da kuka.
Khalil ya ce "Subhanallah, Kuka kuma? Me nayi?"
Kuka take sosai, ta kasa cewa komai.
Ya karɓi sallayar hannunta, ya shimfiɗa a kan dakalin gidan, sannan ya zaunar da ita, ya fuskanceta "Am sorry, na tafi ban kuma kiranki ba, bani da lafiya ne, baki ga na rame ba?"
"Na zata ba zaka dawo ba" ta faÉ—a cikin kuka.
"Baby me zai hana ni dawowa?"
Magana take son yi, amma ta kasa.
Khalil ya gyara zamansa ya ƙara matsawa kusa da ita ya ce "Ya isa haka dan Allah, so kike ki kuma sani a damuwa? Ki daina Please" da ƙyar ya samu ta sassauta kukan da take ta ce "Na zata ka daina sona ba zaka dawo ba, saboda abin da na gaya maka, ko kana ganin ƙarya nake yi".