Sashe 37
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hafsa ta É—an yi jimm, sannan ta ce "A'a babu abin da nayi masa".
"Ai maganrki ba abar yadda ba ce wasu lokutan, bana raba ɗaya biyu wani abun ki ka yi masa, ai shikenan kan ki kika yiwa, sai muyi ta jerawa a gida, 'yan unguwa suna mana ƙazafi, Da kin amince wa yaron nan, na tabattar zai riƙe mini ke amana, yaro mai rufin asiri kamar wannan, ya liƙe miki alhalin ke ba kowa ba, ai kuwa Wannan son shine na gaskiya".
 Gaba ɗaya jikin Hafsa ya yi sanyi, ta tuna maganganun da ta gayawa Khalil, kan ya tafi duk da abin arziƙin da yayi mata, wanda ba dan shi ba, da bata san iya wulaƙancin da Najib zai yi mata ba. Ko ya dai na sona ne, tunda ya daɗe haka bai kirani ba? Ta tambayi kanta. 'gara ma ya haƙura ya daina sona, dan ba zai iya aurena ba' ta sake bawa kanta amsa.
 Khalil kuwa daurewa kawai yake yi, amma zuciyarsa na raya masa ya kira Hafsa yaji lafiyarta, kar yaje wani abun ya sake samunta, amma idan ya tuna da shawarwarin Abdul, sai ya haƙura da kiran nata.
Har washegari Amina bata sake ba, tana jin ɗacin abin da aka yi mata a zuciyarta, sai da taje makaranta ne ma, ta ɗan haɗu da ƙawayenta shine ta ɗan sake, amma cikin zuciyarta babu daɗi sam.
SHANONO.
Can garin su Amina kuwa, facalolinta matan su Bala, suka sakota gaba, da zagi da kums habaice habaice, tare da yiwa Innon fatan masifu daban daban, a kanta da kuma Amina da Baba Hassan.
In anjima suma su Lawan É—in da kansu suke zuwa su isketa suyi mata bala'i, suka tattara wani tsohon keken Baba na hawa suka sayar, suka harhaÉ—a dan biyan Jarmai kuÉ—insa, saboda yadda ya sako su a gaba, da fitina da cin mutunci, abu har gaban mai gari ana musu sulhu.
Ƙauye dama tuni ya ɗauka, batun guduwar Amina birni, dan tayi karatun boko, mutan ƙauyen nan suka dinga Allah wadai da abin da Amina da babanta suka aikata.
Yau su Fadila suka kammala jarrabawar wannan zangon karatun, ji take kamar gama makarantar tayi, saboda yadda duk jarrabawar ta takurata.
Sir Abdulmaleek Kankia, wanda suke kira da Sir Kankia, ya zo wucewa ya kalli Fadila da ke tsaye, tana ƙoƙarin kiran waya cikin nishaɗi.
"Fadila Ahmad Dutse" ya kira sunanta. Ta É—aga kai ta kalleshi, shi ne lecturer da ya so ya kori Yazeed a kan littafi ranar, zuba masa ido tayi ba tare da ta ce komai ba.
"Ko ba sunanki bane?".
"Suna na ne mana"
"In ba zaki damu ba, ina son ganinki a office É—ina".
"For what?" Tayi maganar tana kallonsa.
"For something very important to discuss"
"Ka faÉ—a mini a nan mana, meye sai na bika Office?"
"Abu ne da ya shafi jarrabawar ki".
"Jarrabawata kuma?" Ta faÉ—a da mamaki.
Ba tsammani ta É—aga kai, ta hango Yazeed ya zuba mata idanunsa, ta rasa wani irin kallo ne, na tuhuma ne, ko kuma na menene ta kasa ganewa.
Bayan sir Kankiya tabi da kallo, a hankali kuma ta ja jiki ta nufi wurin da Yazeed yake tsaye ya ƙureta da ido.
"Fadila meya ke ce miki ya tsare ki haka?
Fadila ta tsuke fuska ta ce "Meye na tuhumata kuma ina ruwanka?".
"Da ruwana Fadila, ki gaya mini dan Allah".
Ta ce "Cewa yayi wai in je, a kan wani abu ne da ya shafi jarrabawata".
"Meya faru da jarrabawarki?".
"Nima ban sani ba, ko dan mun yi iri É—aya ne da kai" tayi maganar cikin sanyin jiki.
"Ai ba jarrabawarsa ce muka yi iri É—aya ba, amma kije kiji mai zai ce".
"Am scared gaskiya" ta faÉ—a da rauni.
"Meye abin tsoro kuma babbar yarinya, ai babu damuwa ina jiranki, kije ki dawo"
Fadila duk tunaninta a kan jarrabawar su ne, haka ta nufi hanyar da zata tafi office É—in Sir Kankiya.
Ƙwanƙwasa ƙofar Office ɗin yayi, "Yes come in" A hankali ta tura ƙofar Office ɗin, ta shiga. Tun da ta shiga ya zuba mata ido, har ta ƙarasa cikin Office ɗin. Haushi ne ya kama Fadila, saboda ta tsani kallo a rayuwarta.
Zuwa tayi ta tsaya tana kallonsa ta ce "Gani"
Kankiya ya yi murmushi ya ce "Zauna mana".
Ta É—an hura hanci, ta ja kujera ta zauna, tare da basar da Kankiya.
"Fadila Ahmad Dutse" ya kira sunanta.
Ta É—ago fararen idanunta ta kalli Sir Kankiya.
"Ke 'yar garin Dutse ce?" Ya tambayeta yana kallonta.
"Babana ne ɗan garin" ta bashi amsa a daƙile.
"Garin babanku ai garinku ne".
"Sir dan Allah meyasa ka kirani? Meya faru da jarrabawata?".
Sir Kankiya ya ce "Eh to, ba wani abu bane na damuwa da tashin hankali, akwai yiwuwar komai zai daidaita, amma ki rubuta mini lambar wayarki".
"Me yasa zan bada lambar wayata?"
"Saboda idan da buƙatar sake neman ki sai in neme ki kai tsaye"
"To ai ni har yanzu ban san meya faru da jarrabawar tawa ba".
"Zaki sani nan gaba kaÉ—an, ki rubuta mini lambar wayarki" ba tunanin komai, Fadila ta rubuta masa lambarta, sannan ta tashi ta fice daga Office É—in.
A harabar rukunin ofisoshin malaman ta tarar da Yazeed, ta kalleshi da mamaki, ta É—auka tuni ya tafi.
"Yaya aka yi? Meyafaru da jarrabawar?" Ya tamabayeta cikin ƙosawa.
"Nima ban sani ba, bai gaya mini ba, sai dai karɓar lambar wayata yayi, ya ce idan akwai buƙatar a neme ni, za a kirani".
Yazeed ya kalleta da mamaki ya ce "Ya karɓi lambar wayarki?" Ta jinjina masa kai alamar eh.
"Hmm Mutumin nan sonki yake yi, ba wata jarrabawar ki da ta samu matsala".
"What, ka san me kake cewa kuwa?"
"Eh mana, think, idan wani abu ne ya faru da jarrabawarki shi ke da alhakin kiranki, You have all his attendance, kina da Attendance ɗinsa, teses ɗinsa kina da 25mrks, ga exams ɗinsa kin rubuta, meye matsalar kuma?" Ita babban abin da ya bata mamaki, ya a kayi Yazeed ya san makinta na test da kuma Attendance, ita wasu lamuran nasa ma tsoro yake bata. Gashi ya wani haƙiƙance sai masifa ya ke yi.
"Idan ma sona yake ina ruwanka?" Ta faÉ—a cikin tsiwa.
Cikin dakewa da maziya, Yazeed ya ce "Babu ruwana, Allah ya sanya Alkhairi, ya kaimu lokacin aure Mrs Kankiya".
Wani mugun kallo Fadila ta yiwa Yazeed, tare da jan guntun tsaki tayi gaba.
Da sauri ya sha gabanta, ya ce "Am sorry Please, yau fa zamu tafi hutu, Yakamata mu rabu lafiya ko ƙanwata?".
"Ni ka ƙyaleni" tayi maganar a ɗan hasale.
Zuba mata idanunsa tayi, wanda hakan ya sa taji wani abu na yawo a jikinta, da bata san menene ba.
"Fadila me yasa kika tsane ni, me nayi miki, kina gani bana iya sakewa da kowa a makarantar nan, duk da ba kya ƙaunar ganina, amma ni ina jinki tamkar ƙanwata ciki ɗaya, dan Allah ki sassauta tsanar da kike mini, ko nayi miki wani laifin ne?" Shiru Fadila tayi, tana bin Yazeed da kallo, a hankali ta lumshe idanunta.
"Fadila" ya kira sunanta.
Ta ɗago ta kalleshi. "Me nayi miki kika tsane ni ne? Ko dan ni bagidaje ne, ban iya wanka ba, kuma ban iya turanci ba?" Ya ƙarasa Maganar yana kallonta.
Gaba É—aya jikinta yayi sanyi, ta kasa ko motsawa. "Let's be friends" Yazeed ya faÉ—a cikin sigar rarrashi.
Ɗan tura baki tayi tana fici fici da ido, wata irin kasala na cigaba da tsirga mata, tun daga kanta har ƙafafuwanta.
"Talk Fadila" ya faÉ—a yana marairaicewa
"To wai ni me zance?" Ta faÉ—a tana tura baki gaba.
"Be my sister" ya furta saɓanin abin da yake zuciyarsa.
"Kaga, dan Allah ka bani hanya in wuce, gida zan tafi" tayi maganar a shagwaɓe. Babu tsammani, suka ga Kankiya ya ɓullo daga wajen da ofisoshin nasu suke, ya ɗan yi turus yana kallon su. Tunani Fadila ta shiga yi, da gaske mutumin nan sonta yake ya karɓi lambarta, amma da ya rainawa kansa hankali, wannan suka jero ai cewa za'a yi mai aikinta ne, wani sirirn tsaki ta ja ba tare da ta san ya fito ba.
 Wucesu ya yi ba tare da ya ce musu uffan ba, duk suka bishi da kallo, har ya bar wurin.
Fadila ta yi ajiyar zuciya ta ce "Kaga ni na tafi"
"Ok muje, nima tafiyar zan yi" ba wanda ya kuma cewa wani uffan, kowa yana saƙawa da warwarewa a ransa.
Ta buÉ—e motarta ta shiga, Yazeed ya kalleta ya ce "To ayi hutu lafiya, kar a ajiye litattafai a daina karantawa, i will miss you ukty"
Kallon Yazeed tayi, ta É—an yi murmushin gefen baki.
Har motar Fadila ta ɓacewa ganin Yazeed, yana tsaye yana kallonta, yana jin yadda zai yi kewarta.
Da yamma Amina na harabar gidan, wurin Baba, tana ta zuba masa surutu, gabanta ga littafi da biro, tana karatun jarrabawa.
Horn ɗaya aka yi ƙwaƙƙwara, Baba ya miƙe jiki na rawa, yaje ya buɗe gate ɗin, Zakiru direban Alhaji Ahmad, ya silalo da hancin motar, cikin harabar gidan.
Ɗan dakatawa Zakiru yayi da motar, Baba ya ƙarasa Alhaji Ahmad ya sauke glashin motar suka tsaya magana da Baba.
Amina haushinsa take ji yanzu, tun da Allah ya sa 'yar sa taci wa babanta mutunci, kwasar litattafanta tayi, ta bar wurin dan karma ta gaishe shi, ta shige cikin gida, a falo Hajiya Zainab ta dakatar da ita "Ke daga ina haka nake ta nemanki?".
"Ina wurin Baba ne".
"Ke nifa bana son sakarci, idan baban naki kika zo yiwa aiki, sai ki koma can bakin gate wurinsa, idan ya so ya dinga biya miki kuÉ—in Makarantar".
Fadila da ke kwance a kan doguwar kujera, ta ɗan taɓe baki tana kallon yadda Amina ta haɗe rai.
Alhaji Ahmad ne ya yi sallama a falon, zumbur Fadila ta miƙe jin Muryar mahaifinta, da sauri ta ƙarasa in da yake ta rungume shi "Oyoyo Daddy".
"Welcome sweetheart" yayi Maganar cike da kulawa yana sake rungume Fadila.
Hajiya Zainab ta ce "Ashe ka sauka?".
"Wallahi kuwa, kin ganni nan sai yanzu"