← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 84

Sashe 57

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu tsammani taji ya riƙo hannunta cikin nasa, aikuwa ta tsorata, tamkar zata zura da gudu.
Murmushi yayi ya ja hannunta, zuwa wani tangamemen kitchen, sannan ya saki hannunta ya kalleta ya ce "Amina, ke 'ya ta ce, kar ki saka a ranki zan wani abu da zan cutar da ke, amma duk da haka naji daɗin reaction ɗinki akan hakan, kiyi haƙuri na ɗauko ki ba tare da na gaya miki dalilin hakan ba, nan gidana ne galibi ina saukar baƙina a ciki, Abokaina zasu zo garin nan, shi yasa na ɗauko ki ki musu girki dan Allah, bana son yin order na restaurant saboda na yadda da girkin ki, amma idan kinga da takura bakomai, ki bar shi".

Jiki a sanyaye ta ce "Zan yi"

"In kin san na takura miki ki bar shi kawai"

Ta girgiza kai ta ce "A'a, baka takura mini ba, amma me zan girka" tayi maganar tana jin yadda kaÉ—aicewarsu ta takurata.

"Ko me kika girka yayi, zuwa azahar zasu zo insha Allah, na ajiye komai, idan kina buƙatar wani abu sai ki mini magana" ta jinjina masa kai alamar to.

Ya juya ya bar kitchen ɗin, sai da Amina ta tsaya ta gama ƙarewa kitchen ɗin kallo, tana tunanin to ita Hajiya Zainab zaman me take, da mijinta zai yi baƙi amma ba zai kaisu gidanta ba ayi musu girkin a can, sai a nan ba? Ganin bata da amsa, ya sanya ta fara tunanin abin girkawa.

Khalil kuwa jinsa yake tamkar mara lafiya, gaba ɗaya ya rasa abin da yake masa daɗi, sai da yunwa ta ishe shi, sannan ya shiga cikin gidan neman abin da zai ci, sai dai jin Abincin yayi tamkar magani, ya ajiye Abincin ya tashi, shi babbar damuwarsa, kar Mummy ta ce zata yiwa Hafsa wani abu, gashi har ɗakinta ya je ya sameta ya sake bata haƙuri, yayi mata bayani, amma taƙi saurararsa, ta ƙare masa zagi ta koreshi.

Ba zato babu tsammani, Sir Kankiya ya shigo ajin su Fadila, yana muzurai ya fara yi musu bayanin cewa yayi musayan lokacin gabatar da darasi, da malamin da yakamata ya shigo ajin, ya wuce ya ajiye litattafan hannunsa ya fara ƙoƙarin ciro maker daga aljihunsa, yana ɗaga ido, suka yi ido huɗu da Yazid.

"Kai jiya bance maka kaje office É—ina ina son ganinka ba?" Yayi Maganar yana tsare Yazid da ido.

"Naje sir ban sameka a office ba, har kusan biyar ina jiranka"

"You Are very stupid, ni zaka yiwa ƙarya?"

"Ba ƙarya nake ba sir"

"Shut up, tashi ka bar mini aji, kar ka sake attending lectures É—ina, mara É—a'a kawai, and mark you no 75% attendance no exams"
Gaba É—aya Fadila sai ta rasa me ma zata yi ko tace, abubuwan na Kankiya sun wuce misali sun zama hauka.
Ga mamakinta Yazid ko yunƙurin bawa Kankiya haƙuri baiyi ba, ya tashi ya bar ajin.

Kan azahar tayi, Amina ta gama girkin da Daddy ya sakata, duk ta gaji, ta wanke dukkan abin da ta ɓata. Ta bi hanyar da suka shigo ita da Daddy, ta koma ƙaton falon nan, sai dai baya nan, kitchen ta koma tayi alwala ta dawo carfet ɗin falon tayi salla. Bayan ta idar Alhaji Ahmad ya shigo, ya kalleta ya ce "Sannu da aiki"

"Yauwa, na gama, sai in tafi gida ko?" Tayi maganar a ƙagauce.

Yayi murmushi ya ce "Zaki tafi gida, yanzu dai ga É—akin da zaki kai abincin can, zaki jirani, idan sun kammala sun tafi, sai mu koma gida tare.
Amina ji tayi kamar ta fasa ihu, ita gaba ɗaya bata son wannan ƙeɓewar ta su.

Da kansa ya tayata suka shirya komai a ɗakin, ya bubbuɗe kulolin Abincin sai ƙamshi yake yi.

Ya kai Amina wani ɗakin, bayan ya sa ta ɗebi Abincin, ya rufeta a ɗakin. Ya koma taro baƙinsa.

Amina dai gaba ɗaya a tsorace take, wannan gidan sai ayi garkuwa da mutum ma ba wanda ya sani, Amina ta ci Abinci, ta gama amma zaman ya isheta, dan haka ta kwanta a nan ƙasan carfet, wani nannauyan bacci ya kwasheta.

Ya ɗan jima a tsaye a kanta yana kallonta, sannan ya durƙusa daf da ita
"Amina ki tashi kiyi sallar la'asar mu tafi" A hankali ta buÉ—e idonta, firgigit ta tashi zaune, saboda ganin Alhaji Ahmad a tsaye a kanta.

Miƙewa tsaye tayi, tana murza idonta.

"Ni mu tafi kawai"

"Ba zaki sallar ba?" Ta É—aga kai alamar eh.

Ta durƙusa zata ɗau kwanon da taci Abinci ya kalleta ya ce "Bar shi a nan, za a gyara komai insha Allah, muje sai kin yi salla zamu tafi, biyar da rabi fa"

Hankalinta bai kwanta ba sai bayan tayi sallar,  taga sun fita daga gidan sun hau titi sosai, sun fito daga gidan nan.

Suna tafe a hanya Daddy ya ce "Naji daÉ—i sosai, kin fitar da ni kunya, suna ta godiya, Allah yayi miki albarka, Ahmad ya gode sosai"

Ta É—an kalle shi "Waye Ahmad?" Ta tambaya, dan ta manta sunansa ne.

"Baban Fadila da Aminatu" murmushi tayi ta ce "Au na manta sunanka ne"

Ta kashingiÉ—a a jikin seat, tana lumshe ido.

"Kin gaji ko?" Ta É—aga masa kai alamar eh.

"Eyya, sannu to, and please wannan ma sirrinmu ne, kin taimakawa Daddynki, ya fita kunyar abokansa is our secret"

"Tom, ba zan faÉ—awa kowa ba insha Allah" tayi maganar tana murmushi.

Ya zura hannu a aljihunsa, ya zaro kuɗi a envelope ya miƙawa Amina.

Ta kalleshi ta ce "Na menene wannan?"

"KuÉ—i ne na baki, tukuicin abin da kika mini ne, na katse miki karatun ki kin mini aiki"

"Ai dama dai sai ka nuna banbanci duk da kace ni 'yar ka ce" tayi maganar tana tura baki.

"Banbancin me fa?"

"Idan kasa Fadila aiki biyanta kake?"

Mamakin Amina yake, sam yanzu bata shakkarsa, ko shakkar faÉ—a masa magana.

"Eh to, na kan mata tukuici da wani abu, dan na faranta mata rai"

"Ai ni kayi mini abubuwa da dama, kana ciyar dani, ga wurin kwana, ga kuma karatuna, me zai sa sai ka kuma bani wani abu?"

"Wannan ai duk daban"

ÆŠan shiru Amina tayi sai kuma ta ce "Daddy"

"Na'am 'yar Daddy"

"In roƙeka wani abu?"

"Kan ki tsaye makuwa, me kike buƙata?"

Nan ta labarta masa, gidan da ta wuce É—azu da safe, ana fito musu da kaya.

"Yanzu me kike so ayi?"

"Dan Allah ka biya musu, tunda kana da kuÉ—i"

"Waye ya ce miki ina da kuÉ—i?"

"Kai ka gaya mini sayar da kuÉ—i kake, kuma kalli motarka da gidanka, ai dai kana da kuÉ—i sosai"

Murmushi yayi, ya shafi dogon gemunsa, da yake baƙi da fari kaɗan kaɗan a cikinsa.

"Daddy baka ce komai ba"

"Sai na tambayi mata ta, idan ta amince sai a biya musu"

HaÉ—e rai Amina tayi ta ce "Ashe ba za a biya musu ba kuwa"

"Me kike nufi?"

"Ai wannan matar 'yar hana ruwa gudu ce, ba zata taɓa barin ayi abin arziki ba"

Daddy ya haÉ—e rai ya ce "Matar tawa ce 'yar hana ruwa gudu?"

Amina shiru tayi tana É—an kallon gefe dan da zata samu dama, sai ta É—uÉ—É—urawa Hajiya Zainab Ashar dan ta huce.

"Kayi haƙuri, amma wallahi bata da....

"Ke!" Ya daka mata tsawa da sai da ta razana ta kalleshi.

"A gaban nawa zaki zagi uwar 'ya'yana" ji tayi kamar ta ce "Nima a gabana take zagin babana' amma ya koma mata Alhaji Ahmad É—insa, dole ta haÉ—iye maganarta.

Parking ya yi ya kalleta ya ce "Fitar mini daga mota"

"Gida da nisa fa daga nan" ta faÉ—a kamar tayi kuka.

"I don't care, get out" ya faɗa in a serious tone. Buɗe motar tayi a fusace, ta fice ranta a ɓace.
ÆŠan guntun murmushi yayi, ya ja motarsa yayi gaba.

Da ƙafa Amina ta nufi hanyar gida, tana tunanin yadda zata ƙarasa gida a ƙafa.
Ran Amina ba ƙaramin ɓaci yayi da abin da Alhaji Ahmad ya mata ba, yana ta mata kirki, amma dan ta faɗi magana a kan waccan azababbiyar matar ya mata wulaƙanci, duk wahalar da tayi masa, amma bai gani ba, meye ya hana ita 'yar lelen matar tasa tayi masa?.
Haka Amina tayi ta zancen zuci tana mita a ranta.

Horn É—in motar da ta ji yayi mata yawa a kunnuwanta ne, ya sanyata waiwaya.
Murmushi me motar ya sakar mata, gani tayi kamar ta sanshi, ta hau tunanin a in da ta san shi.

"Gida zaki ne?"

"Eh" ta bashi amsa.

"Kamar baki gane ni ba, Bilal ne na nan layinku, muna gaisawa fa idan zaki tafi makaranta" sai yanzu ta tuna shi, yana yawan yi mata adawo lafiya, idan zata tafi makaranta.

"Sannunka ya kake?"

"Lafiya ƙalau Alhamdilillah, taho mu ƙarasa".

Ɗan shiru Amina tayi, yamma tayi liƙis, ta san yanzu haka Baba ya fara tunanin ina ta tsaya, kuma idan ta ce da ƙafa zata ƙarasa kuma, magariba zata rufa mata.
Dan haka bata da zaɓi illa tabi Bilal.
Suna tafe a hanya yana mata hira, ita gaba ɗaya hankalinta baya kansa, fatanta kawai su ƙarasa gida.

Suna zuwa ƙofar gidan, Amina ta fara ƙoƙarin buɗe motar tana masa godiya. Bilal ya ce "Bakomai, muje nima in gaida Baban"

Amina dai ba ta ce masa komai ba, baya son gwaleshi, bayan ya taimaketa.

Tare suka shiga cikin gidan, sai dai Baba baya nan, Dan an fara kiraye kirayen sallar magariba.

Amina ta kalleshi ta ce "Ina ga ya tafi masallaci, na gode sosai".

Bilal ya ce "To ko zaki bani lambar wayarki?"

"A'a ai bani da waya" suna cikin maganar, sai ga Alhaji Ahmad ya fito zai tafi masallaci, tun daga nesa ya fara yi musu wani irin kallo, musamman Amina, Amma Amina ta basar ta mayar da hankalinta kan Bilal.

TOFA ME KUKE TUNANI.
MASU SAN POSTING KULLUM, SU BIYANI IN BUÆŠE MUSU VIP, ZAN DINGA POSTING KULLUM INSHA ALLAH

AYSHERCOOL
08081012143
GABA DA GABANTA

AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

PAGE 32-33
Chapter 57 · 0% Book details