Sashe 2
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Innalillahi, meye wannan? Nice zanci Wannan abun? Mummy kalli abunda ya siyo, ni na taɓa cin wannan abun ne?".
A dirirce yace "hajiya ai shine dankalin".
"Shut up please, ba Irish nace ka siyo mini ba? Banda jahilci i even repeat myself, irish potatoes, kawai sai ka kawo mini wannan abun? Is not late for you, yakamata ko yaƙi da jahilci ka je kayi, ko ka dinga gane abubuwa, kar ka yadda tsufa ya ƙarasa riskarka cikin jahilci. And Carry that rubbish and leave my view, before I open my eyes, ka ɗauka kaje ka ci, wannan abincin yunwa ba zan iya ci ba, ka tashi ka bani guri"
Kalmar Jahilci, ta fi komai ɓatawa Baba Hassan rai, tare da tsaye masa a wuyansa, wani irin zafi da raɗaɗi ya dinga ji a zuciyarsa, duk da kasancewar sa mutum mai haƙuri, amma yau ya ƙulu, tabbas ba dan yana duba wasu abubuwa ba, da tuni ya bar aikin nan, amma maigidan mutum ne mai alkhairi da karamci a gareshi, kuma idan ya bar wannan aikin be san wanne ze yi ba.
Haka nan ya tashi, ya É—au buhun dankalin nan, ya baro falon zuciyarsa a cunkushe, yana jin kamar yayi kuka, amma ya danne, saboda be san me hawayen na sa ka iya haifarwa Fadila a rayuwarta ba.
Fadila kuwa saboda tsabar ɓacin rai, sai da tayi kukan baƙin ciki, saboda yadda tsohon ya ɓata mata lokaci, ga kuma yunwa tana ji, amma ba yadda ta iya.
*******
Tana zaune a ajinsu, wanda galibi 'yan ajin nasu, 'yan wasu ƙauyukan ne, amma daga ƙauyensu su biyu ne suke zuwa Makarantar haryanzu, sauram duk an musu Aure, wasu tun a primary ma.
Abun duniya ya ishi Amina, ta rasa yadda za ta yi ta samu wannan kuÉ—aÉ—en, ta biya kuÉ—in jarrabawar nan.
Ga lokaci yana ta ƙurewa, idan aka riga aka yi jarrabawar nan babu ita, shikenan karatunta ya koma baya.
Duk yadda za tayi ta samu kuɗin nan ta yi, amma ba ta samu ba, gaba ɗaya dabararta ta gama ƙarewa.
"Amina Hassan, ki zo inje Malam Lawan" cewar wata É—aliba da ta zo ta tsaya a kan Amina.
Amina tace "to ina zuwa".
Sannu a hankali ta tashi, ta bar ajin, jikinta duk a sanyaye, damuwa ta hanata sukuni gaba É—aya.
Sallama ta yi a Staff room, ta tarar da Malam Lawan a zaune shika É—ai.
Ta durƙusa ta gaishe shi, ya amsa Sannan yace "Amina, yaya haryanzu shiru ba ki kawo kuɗin jarrabawar ki ba, ga lokaci yana ta ƙurewa, yaya ne?".
Jiki a sanyaye tace "Malam zan kawo insha Allah".
"To ai lokaci ne yake ƙurewa, bana son a rufe baki biya ba".
Amina tace "Insha Allah, zan kawo malam".
"To shikenan, Allah ya dafa".
Ta amsa da Ameen, ta fita ta koma aji, tana cigaba da tunani.
Duk da tsananin zafin ranar da akeyi, ba ta ji, sannu a hankali take tafiya, ita zafin ranaf sam ba ya damunta Kamar yadda biyan kuÉ—in jarrabawar ta ya dameta.
"Aminatuu" aka kira sunanta.
Tsayawa ta yi ta waiwaya, wani dogon matashi ne baƙi a gefen wata bishiya.
Murmushi tayi tace "Laa Saminu, ina wuni".
"Lafiya ƙalau Alhamdilillah, ya Makaranta?"
"Lafiya ƙalau, ashe ka shigo garin namu?"
Saminu yace "eh na shigo jiya, babanki har ya bani saƙo na kaiwa Inno ɗazu da safe".
Amina tace "kashh, ina ta neman yadda zan magana da shi, kafin yayo mana aike, har an biya albashi ne?".
Saminu yace "A'a, ai wata ko rabawa be yi ba, naje gaisheshi ne nace ko yana da saƙo, shine ya bani dankalin Hausa kaya guda yace a kawo muku, da dubu ɗaya".
A ranta tace 'dana san za'a kawo dankalin nan, da siyar da shi a kayi, aka bani kuÉ—in in biya jarrabawa, dan yanzu ko me zanyi, Inno ba za ta bari a saida dankalin nan ba'.
Ta kalli Saminu tace "dan Allah Saminu, ka aramini Salularka, in kira Babanmu, ina son yin magana da shi".
Saminu yace "ba damuwa" ya É—akko wayarsa, ya kira lambar baban Amina ya bata wayar.
Baba Hassan kuwa yana zaune, yau tsawon kwanaki huÉ—u kenan, da cin zarafinsa da Fadila ta yi, amma ya kasa mantawa, ya dinga tuna lokacin da ake binsu za'a kama su a kaisu Makaranta amma iyayensu suka hana, Yanzu ga ranar ilimi.
Wayarsa da ya ji tana ruri, ya É—auka ya kara a kunnensa, tare da yin sallama.
Cikin farinciki Amina tace "Babana".
"Na'am Aminatu na, ya kike?".
"Lafiya ƙalau Baba, munga saƙo mungode Allah ya saka da alkhairi".
"Ameen Aminatu na, kuyi haƙuri ba ayi albashi bane, ya Innar ta ki?".
"Lafiya ƙalau Baba, sai dai....
"Sai dai me?".
"Baba ance mu kai kuɗin jarrabawa, kuma bani da kuɗi, Inno kuma tace ba zata biya mini ba" Amina ta ƙarasa Maganar Kamar za ta yi kuka.
Jiki a sanyaye Baba yace "nawa ne kuÉ—in?".
"Baba dubu huÉ—u ne"
Baba Hassan yai shiru yace "Uwata kinga ba'a daÉ—e da yin wancan albashin ba, ki kai rashin lafiya na turo muku da duk kuÉ—in, kuma yanzu wata ko rabawa be yi ba, amma in Allah ya yadda, zan laluba, sai in bayar a kawo miki".
Amina tace "to Babana, nagode Allah ya saka da alkhairi, Allah ya bani ikon yin karatu, in zama wata ka bar aikin gadin nan".
"Ameen uwata, Allah ya yi miki albarka, ki gaida mini da babar ta ki".
"To Baba sai anjima" ta katse wayar, ta koma gurin Saminu, ta miƙa masa wayar tana murmushi tace "Saminu ga salular, nagode sosai Allah ya saka maka da alkhairi".
Saminu yace "Ameen, ki gaida gida".
Daga haka,ta kuma saɓar hanyar da zata sadata da gidansu.
Ko da taje gidan, ta tarar da Inno ta dafa dankalin da Baba ya aiko da shi daga birni.
Amina tayi murna sosai, ko bakomai yau za su huta da cin tuwo, su ci sakakken Abinci.
Tai shiru da bakinta, ba ta gayawa Inno ta yi waya da mahaifinta, akan zai aiko mata da kuɗin Makaranta ba, dan muddin ta sani, ƙwacewa za ta yi, dan bokon nan da Amina take zuwa, a wuyan Inno take.
Amina na ta dangwalawa da ƙuli tana ci, tana korawa da ruwan randa mai sanyi.
"Salamu Alaikum"
"Wa'alaikum salam" Amina ta amsa.
"Wai inji Babarmu tace ki zo, ki samo musu ruwa zasu É—ora girki". Cewar yaron da yai sallama.
Amina ta kalli yaron tace "ka tambayesu nawa suka sa kuÉ—i suka siyoni a kasuwar bayi? Idan har ba zaku É—ebo musu ruwan ba, to ku mutu da yunwa".
Inno na É—aki tana salla, amma sai wata uwar gyaran murya take yi,kamar ba salla take ba "Eheeem, Mmm, Eheeem" kamar ta kira sunan Amina a sallar nan.
Amina kuwa sai da ta dire ayar zancen da take yi, yaro ya juya ya fice.
Amina tace "Inno, ba fa a irin wannan gyaran muryar a salla, a bokonmu mun karanta a littafin addini, ba'a son wani sauti ya fita idan kana salla, amma kamar za kiyi magana".
"Kyaci ubanki ke da bokon, wato ki kai musu wannan aiken, salon su zo su tayar mana da bala'i a gidan nana da tsakar ranar nan ko? Wai ke meyasa ba kya gudun magana ne?".
Amina tai shiru ba ta tankawa Inno ba,ta cigaba da cin Abincinta.
"Salamu Alaikum, kina ina ja'ira mara kunya, har a aiko kije aike, amma kice ba zaki je ba, har da baƙar magana, 'yar banzar Yarinya da ido kamar bururin gawayi" wani mutum ne ya shigo yana surfa bala'i, yana saɓa babbar riga kamar zai fuka fuki ya tashi saboda masifa.
Amina ta sunkuyar da kai ƙasa, tai shiru, ya dinga zazzaga mata masifa,a ƙarshe yace "Na fuskanci wannan bokon wofin da kike zuwa, ita ce take sawa kina yiwa Mutane rashin mutunci, naga uban da ze sake bari kije bokon, Aure zan miki kan Hassan ɗin ya dawo, tun da dama shine yake goya miki bayan yiwa mutane fitsara, Wallahi ko sadakar ki ne bayarwa zanyi, uban kowama ya huta, algunhuma me suffar munafukai".
Sai da yayi ya gama ya fice, daga Inno jar Amina babu wanda ya tanka masa, sai da Ya fita sannan Inno tace "kinga abunda nake jiye miki ko? Ai gara ai miki Auren, kowama ya huta, ƙila kyayi hankali, ga abunda bakinki ya janyo miki nan"
Amina tace "na fuskanci bokon nan ce tasa duk aka tsaneni, ni kuwa tunda faɗar Annabi ce Sallallahu alaihi Wasallam, yace mu nemi ilimi, ko daga nan zuwa birnin Sin ne, to Wallahi a shirye nake in ɓata da kowa.
Dan kawai ina zuwa boko da na motsa sai zagi, dan me zasu maida ni baiwarsu? Kawai dan banyi Aure ba ina zuwa Makaranta kowane aikin wahala sai ya dawo kaina?, To idan ba'ai mini Aure kan Baba ya dawo ba, ni zan gudu kan ai mini Auren dole, dan Wallahi na zaɓi karatuna akan wannan mutanen".
Inno ta zaro ido tace "ke Amina, ba ki da hankali, ƙannen uban naki?".
"Su ɗin fa, me suka taɓa tsinana mini a rayuwa? Kullum burinsu su ganni a wahala ni da mahaifina, Wallahi aka takurani, zan tattara kayana in koma birni, in ta bulayi har in gano in da Baba yake, muyi aikin gadin tare!.
Domin gyara sharhi, ko shawara
07063065680
GABA DA GABANTA
Page 2
By Aisha Adam (Ayshercool/Jakadiyar Arewa)
(Shin kin karanta littafin DARE DA DUHU?, Wanda yake daga gamayyar alƙaluma uku, daga haziƙan marubuta uku, Zee kumurya, Nimcyluv da kuma Ayshercool, kar ku bari a baku labari, ku mallaki na mu akan Kuɗi Naira 300 kacal. *DARE DA DUHU*
_Allahamdulillah Babu Abinda bright pens za su ce sai godiya a gareku. Kun amshi littafin fiye da kima. Duk cewa Fiction story amma da yawan Labarin abune na da muke fuskanta reality🌚😢_
*DARE DA DUHU*
₦300 NE
Via 0116886423Â Sulaiman Na'ima s union Bank. Idan katin waya ne mtn na 500 idan transfer ne É—ari uku kacal.
Evidence of payment 07063065680 ko 09047871750)