← Book details Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 84

Sashe 43

Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

"Ba dole in ƙi ɗauka ba, Hafsa komai na baki ba zaki karɓa ba, sai kin yi mita da ƙorafi bana son abin da kike mini bana jin daɗi" ya ƙarasa maganar cikin marairaicewa.

Cikin shagwaɓa ta ce "To Shine sai ka daina kirana, kuma daina ɗaga nawa, dan ka sani damuwa"

"Dagaske kin damu kema da bama waya?" Ta jinjina masa kai alamar eh.

"Kina sona kenan?" Yayi Maganar da dukkan nutsuwarsa.

Shiru ta É—an yi, sannan ta kalleshi ta ce "Kana sona da gaske?"

"Ina sonki mana"

"Bari in fara gaya maka waceceni, da ƙaddarar da ta sameni, ban sani ba ko zaka iya cigaba da sona a haka".

Hafsat Usman Dikko, shi ne cikakken sunan Hafsa, mahaifinta haifaffen garin Kano ne, mahaifiyarta ma haka.
Mahaifin Hafsa shikaÉ—ai mahaifiyarsa ta haifa a gidansu ta rasu wurin haihuwa, ya taso a tsakiyar 'yan uba, cikin tsangwama da kyara.
A haka a wahale yayi karatun Addini da na zamani, kasancewar Usman mutumin kirki, mai ladabi ga kowa da kowa ya sanya 'yan unguwarsu kowa yana son sa.
Ya haɗu da mahaifiyar Hafsa, mai suna Safiyya, a nan wani filin ƙwallo da yake zuwa, a nan cikin unguwar gwale. Sai dai itama basu da ƙarfi, dan marainiya ce, yayanta ne yake ɗawainiya da su.
A lokacin da  Usman ya auri Safiyya, ba shi da wata tsayayyiyar sana'a, sai dai mutum ne mai zuciyar nema, sai dai yana da kwalin degree har biyu amma babu aikin yi, gidan da suka tare ma a ciki, gadonsa ne na mahifiyarsa a nan cikin unguwar ɗorayi, wani ɗan ƙaramin gida, haka suke rayuwa.
Kwatsam, Chairman ɗin unguwarsu tsohon abokin mahaifin su Usman ne kan ya rasu, ya bawa Usman offer, a hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa.
Yayi murna ba kaɗan ba, a lokacin 'yan uba suka sake sako shi a gaba, da sharri da jafa'i kala kala dan su cikinsu babu wanda ya yi karatun boko sai shk. Lokaci ɗaya Allah ya ɗaukaka shi a kan harkar aiki, ya mallaki gida da abin hawa, ya mallaki shaguna a nan cikin umgu su, wasu ya bada haya wasu ya zuba kasuwanci ya janyo 'ya'yan 'yan uwansa, amma suka dinga cutarsa. Amma duk da haka Allah bai sa yayi baya ba, kullum gaba yake yi, cikin ikon Allah a nasarorin da ya samu, har da karramawa daga fadar shugaban ƙasa, saboda gaskiyarsa da gudun rashawa.
Gidansa kullum cikin jama'a yake, masu neman taimako, hannunsa a sake yake hakan ya ƙara masa farinjini.
Kusan shekara biyar Safiyya na ɓari, bata haihu ba, sai da aka dage da addu'a da neman magani sannan Allah yasa ta samu cikin jikinta ya zauna, watanni tara Allah ya sa ta haihu, ta haifo ɗa namiji kyakywa mai kama da Usman sak, aka sha shagalin suna aka sanya masa suna Abubakar Sadik, sunan mahaifin Safiyya.
Sadik ya taso cikin gata da kulawa, shekararsa uku a duniya, dangin Usman suka dinga mita a kan Cewar ba a kai musu Sadik, a dinga kaishi saboda ya saba da 'yan uwansa. Ba dan Safiyya ta so ba, aka haɗa kayan Sadik, aka kaishi gidan wan Usman, mai suna Aminu, sai dai kwanan Sadik biyu aka dawo da shi wai bashi da lafiya, duk ya fita hayyacinsa, aka kaishi Asibiti aka yi gwaje-gwaje aka tabattar da wani abu yaci, kwana ɗaya ya rasu, daga Safiyya har Usman sun shiga tashin hankali na gaske, wanda a sanadiyar damuwa da rashin lafiya da Safiyya tai tayi, aka gano tana laulayin wani cikin, a haka ta haifo Hafsa. Lokacin da aka haifi Hafsa, Usman Arziƙi ya ninka na baya, Hafsa ta tashi cikin gata da kulawa. A can wurin aiki, abokan aiki suka sako Usman a gaba saboda cigaba da yake samu, mussaman ta fuskar tsayawa a kan gaskiya, a dangi kuma 'yan uba na ta son ganin bayansa, banda 'yan unguwa da tasu hassadar duk da tarin kyautatawarsa a gare su.
Bayan haihuwar Hafsa, Safiyya tayi ɓari yafi bakwai, wanda sai da likitoci suka bata shawarar, a ɗaure bakin mahaifarta ta haƙura da yinƙurin ɗaukar ciki saboda lafiyarta.
Kasancewar Hafsa ce 'ya ɗaya tilo a wurinsu ya sanya suka ɗora mata duk wata so da ƙauna, Safiyya take ta kulawa da ita, taƙi yarda ta saki jiki ta bawa su Aminu da iyalansu 'yarta.
Shekarar Hafsa goma sha ɗaya, aka yiwa Usman wani ƙarin girma, yaje Abuja aka yi walima, tun da ya dawo ya fara rashin lafiya, aka dinga yawon Asibiti amma babu wani cigaba ba a gano abinda ke damunsa ba, kullum ciwo gaba yake yi, wanda hakan ya yiwa 'yan uwansa daɗi, dan sam basu damu da halin da yake ciki ba, daga matarsa sai mahaifiyarta da wanta ne suke ta ɗawainiya da shi.
Shekara guda yana jinya, Allah ya karɓi abin sa, Safiya ta shiga cikin tsananin tashin hankali da damuwa, tayi kuka kamar babu gobe, mutane aka cika gidan makoki dan an san za a ci a sha, tun kan a share sadakar uku, Aminu da 'yan uwansa Hadi da Ashiru suka fara maganar rabon gado, wani ɗan uwan mahaifinsu ya ce ai sa bari a rufa Arba'in.
Kwanaki Arba'in da ɗaya da rasuwar Usman, suka zo da wani mutum wai shine Alƙali zai yi rabon gado, gaba ɗaya sun sa ran dukiya ta su ce, saboda ba shi da ɗa namiji, Safiyya ta fito da wani rubutu da yayi kan ya rasu, yayi rubutu fiye da rabin dukiyarsa ya sakata a harkar cigaban Addini, manyan kadarorinsa kuwa duk ya saye su da sunan Hafsa, ya mallaka mata su, ɗan abin da ya bari babu yawa sam.
Nan fa suka ce basu yadda ba, ƙarya take ita ta rubuta, ganin suna neman su gwada mata fin ƙarfi, ya sanya ta garzaya kotu, Allah ya taimaketa Alƙali ya tabattar da wasiyyar da Usman ya bari.
Bayan Safiyya ta gama idda, ta dinga samun manema, amma ta ce ita ta gama aure a kan Usman, saboda ta san ba zata samu madadinsa ba.
Mahaifiyarta da ɗan uwanta suka dsge a kan dole tayi wani auren, wani mutum mai suna Musa, shi Safiyya ta tsayar, saboda yana da matuƙar kirki da halaye masu kyau kwatankwacin Usman.
Sai dai su Aminu yayyen Usman na jin batun za tayi aure, suka tada husuma, wai ba za tayi aure ta kai dukiyar marainiya wani wurin a cinye ba, ƙarshe ma suka ce sai dai ta basu Hafsa, ba zata yi agolanci a wani gidan ba, ko kuma ta auri Aminu. Da suka tada masifa da tashin hankali, mahaifiyar Safiyya ta ce tayi haƙuri ta auri Aminu, ko ba komai Hafsa ba zata tashi gidan wasu ba, ba dan Safiyya na so ba ta yiwa mamanta biyayya.
Bayan auren Safiyya da Aminu, yayanta shima ya rasu, ɓarayi suka tare shi a hanya, suka kashe shi, abubuwa suka sake yiwa Safiyya zafi, na rashin da tayi gaba da baya.
Bayan aurenta da Aminu, ya dinga basu kulawa da tattali, duk da a gefe guda iyalansa suna nuna musu tsantsar ƙiyayya da kyara.
A haka ya lallaɓa Safiyya, tayi musu gyaran gida, aka sai motoci biyu a gidan dan amfanin mazauna gidan. Ya dinga lallaɓata da kyautatawa da asiri, ya dinga karɓe dukiyar nan ɗaya bayan ɗaya, dan ba ta iya masa musu a kan komai, da ya ce ta bashi take bashi.
Sai da ya tabattar ya ƙwace komai, ya shiga bushasha shi da 'yan uwansa da iyalinsa, ya fara azabtar da Safiyya da 'yar ta, Hafsa da take 'yar gata gaba da baya, ba ta san wahala ba, amma a tilas aka mayar da ita tamkar baiwa saboda wahala da ita da mahaifiyarta.
Duk wata azabar aikin gidan nan suke yinta, ga hantara da wulaƙanci, Abinci sau ɗaya tal a rana ake basu, kuma Safiyya ba ta isa ta fita daga gidan ba ko wani ya zo in da take ba.
A haka duk wasu alamun girma suka bayyana a tare da Hafsa, kasancewar tana da jiki, duk da wahalar da suke ciki, bai hana surarta fitowa ba.
Nan samarin gidan suka fara kai mata hari, suna nema su keta mata haddi. Ta kasa gayawa Mama, sai dai tai ta kula da kanta, tana koke koke. Duk san Hafsa da makaranta ƙarshe sai da suka rabata da Makaranta.
Saboda yawan kuka da Safiyya take ba ji ba gani, ya Sanya ta haɗu da wani matsanancin ciwon ƙirji, da ya haifar mata da larurar numfashi.
Cikin samarin gidan nan ba wanda yafi uzzura mata, kamar Najib, Najib bashi da mutunci ko ɗa'a, ya samu dukiyar marainiya a wurin mahaifinsa kullum cikin yawo da abokai da shaye-shaye yake, bashi da burin da ya ga Hafsa yayi ƙoƙarin haɗata da jikinsa, ganin taƙi amincewa da hilatarta da yake yi, ya sanya ya fito ya ce Aurenta zai yi, yana sonta.
Babansa ya ce ya bashi, sadaki kawai za'a bayar a É—aura Aure, ai 'yar uwassa ce. Hafsa idan abu na damunta ba ta fiye faÉ—a ba, ita hasali ma bata magana sai ta ga dama, dan haka sai dai tayi ta faman kuka.
Aka aiko wa Mama cewar mahaifiyarta babu lafiya, da ƙyar Aminu ya barta ta je, amma ya ce ba zata tafi da Hafsa ba.
Haka ta rarrashi Hafsa ta shirya ta tafi, sai dai ko da taje gida, ta tarar jikin mahaifiyarta yayi tsananin, da ba zata iya komawa gida ba, ta barta a halin da take ciki ba.
Har dare Mama bata dawo ba, hakan ya jefa Hafsa cikin damuwa, tun tana jiran dawowar Mama, har ta haƙura ta kwanta bacci.
Cikin dare taji mutum  a kanta, tana ƙoƙarin tashi, aka danne ta ana ƙoƙarin rabatabda suturar jikinta, shaƙa mata wani abu aka yi, ba ta shaƙi abin sosai ba, jikinta yayi sanyi ƙalau ta kasa motsawa, sai gani take dishi-dishi, wani abu mai nauyi yana rinjayar kanta. Tabbas ko ba a gaya mata ta gane shi, Najib ne ba wani ba.
Ba ta sake farkawa ba, sai da garin Allah ya waye, gari yayi haske, ta ji saukar ruwa a fuskarta, ta buÉ—e idanunta a hankali, tana kallon Mama da ke kanta a rikice tana kuka tana tambayar Hafsa meyasameta?.
"Mama Najib ne" shi ne kawai abin da ta iya furtawa.
Mama tayi kuka tamkar ranta zai fita ita da Hafsa, ta taimakawa Hafsa ta gyara jikinta, ta kama hannun Hafsa zuwa wurin Aminu, mahaifin Najib, ta gaya masa abin da É—ansa ya aikata. Amma ya hau bala'i, sai da ya janyo hankalin mutanen gidan, uwar Najib ta ce sun yiwa É—anta sharri.
Mama ta ce "Tun da haka ne, wurin 'yan sanda zata kai ƙara" Aminu ya hanata fita, ya cigaba da azabtar da su, kullum Hafsa cikin kuka take ita da Mama, Mama tun bata magana, har Mama ta buɗe baki ta yiwa Aminu Allah ya isa a gaban iyalansa.
Babu tausayi ko imani, ya ware ƙwanji ya dinga dukanta, Hafsa taje cetonta, ya haɗa da ita da Hafsa ya dinga jibgarsu, duka na wulaƙanci kamar dabbobi sannan ya haɗawa Mama da saki uku ba tausayi ba tsoron Allah.
Haka suka koma gidan da mahaifiyar Mama ke jinya, ba Abinci babu mai basu kulawa, ita ma ta zo ta rasu, hakan ya jefa Mama cikin tsananin damuwa ta haÉ—u da larurar hawan jini, da ya haÉ—u da Asma suke addabar rayuwarta tamkar zata rasa ranta.
Duk da haka Najiba bai fasa bibiyar Hafsa ba, saboda rashin Kunya, Mama ta kaisu wurin 'yan sanda shi da mahaifinsa, amma yayi amfani da dukiyarsu ya toshe bakin 'yan sanda, saboda Najib, Mama ta sayar da gidan da suke ciki na mahaifiyarta, suka tashi suka koma É—orayi, gidansu na farko da ta rayu ita da Usman farkon Auren su.
Da kuɗin gidan, ta mayar da Hafsa Makaranta, sai dai Hafsa ta ƙara rasa kuzari da shiga damuwa, tun bayan Najib ya keta mata haddi. Zamansu a gidansu Najib da tashinta cikin tsnagwama da takura, ya ƙara nesanta da farinciki ko cikakkiyar walawala ba ta yi, balle fara'a.
Ƙarshe suka cinye ragowar kuɗin, babu mai basu Abinci, duk da tarin alkhairan mahaifinta ga al'umma, babu wanda ya dube su bayan rasuwar su, da ƙyar Hafsa ta kammala karatun sakandare, daga baya Hafsa ta fara wannan sana'ar ta sayar da awara.
Chapter 43 · 0% Book details