Sashe 5
Gaba Da Gabanta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Baba Hassan ya gyara zamansa ya ce "Amm, dama gurinki na zo Hajiya, Alhaji ne ya aiko ni".
"Ya aiko ka, ya ce me?"
"Dama na kira shi a waya ne, yarinyata zata zana jarrabawa, bani da kuɗi, shine ya ce in zo in karɓa a gurinki".
"Kai kuwa malam Hassan, yakamata ka dinga jin tsoron Allah, yaushe aka baka albashi har da zaka dawo ka ce ga zance ga magana?"
Cikin rauni Baba Hassan ya ce "Dan Allah Hajiya ki taimaka, ni ko rance ne, bana son karatun 'ya ta ya samu naƙasu, idan ya so sai a cire a albashi na".
"Allah wadaran halin talaka, sam ba ku da godiyar Allah, mutum ko naman jikinsa ya ke yanka yana baku ba zaku gode ba. To ni bani da cash a hannuna, sai ka haƙura sai zuwa lokacin da aka ɗakko mini kuɗi a banki".
Ya sake duƙawa ya ce "Hajiya ki taimaka, za su rufe karɓar kuɗin ne".
Fadila a ƙufule ta ce "wai baka ganewa ne? Babu kuɗi a hannunta Yanzu, amma sai magiya ka ke".
Baba Hassan ya ce "to shikenan Hajiya, Na gode" ya tashi jiki a sanyaye ya bar Falon.
********
Zuwa yanzu Amina ta gama fidda rai da samun kuÉ—in da zata biya na jarrabawa, dan yanzu haka tana zuwa makaranta ne kawai, kafin wanÉ—anda suka biya kuÉ—in jarrabawar su fara.
Kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki, haka take tafiyar, tana ƙoƙarin shiga gida ta hangi Kawu Bala, a ƙofar gida yana alwala, kai da ganin alwalar ta sa kasan jahilci ya samu gindin zama a tare da shi, saboda yadda watsa ruwan alwalar nan ko ta ina.
Tana ƙoƙarin durƙusawa ta gaishe shi cikin masifa ya ce "Ke Amina zo nan".
Ba musu ta zo ta durƙusa ta ce "Gani kawu".
"Da ga gidan ubanwa ki ke?".
"Daga makaranta"
"Yawon barbaÉ—a da ta zubar ba?" Kallon Kawu Bala tayi, tare da jin haushin mummunar kalmar ta zubar da ya jinginata da ita.
Ya kalleta ya ce "Ina son sanin dalilin da yasa, Malam Rabi'u ya nuna yana sonki, amma dan iskanci ki ka yi masa rashin mutunci".
Ta É—an yamutsa fuska ta ce "Kawu, ta yaya zan iya Aurensa, mata nawa ya aura ya saka a garin nan? Kalli yadda yaransa suke babu cikakkiyar kulawa, idan na Aureshi yayi yaya dani? Kuma ban fa gama Makaranta ba har yanzu".
"Kinga idan na kuma magana kika yi mini zancen bokon nan, saina karairaya ki, shashasha mara kan gado, na fuskanci akan bokon nan kike wannan iskancin, na fuskanci a can suke hure miki kunne, to ba zai yuwu ba, ubanki ya tsallake ya tafi nasa guri ya bar mu da ke, ke kuma ki ɗakko mana abun kunya ba, saboda wata boko ba, dan haka daga yau na kuma ganin kin je makarantar boko, Wallahi sai na saɓa miki kin ji na gaya miki.
Kuma kiji da kunnenki, zamu karɓi kuɗin Auren Malam Rabi'u, ba zaki cigaba da gandamewa a gida ba, sa'oinki na gidan Aure suna neman aljanna, ke kuma kina tamɓele a titi da uwar jaka da sunan boko, shegiyar bokon da ke ba kuɗi a ke baki ba sai wahala, da wannan wahalar banzar gara in ba zaki yi Auren ba, ki shiga cikin maza a dinga zuwa da ke gona kina noma".
Tuni hawaye ya wankewa Amina fuska ta ce "Dan Allah kawu kayi haƙuri, ku bari in ƙarasa makaranta, ko ina gamawa ne sai in yi Auren, in ya so ku aura mini wanda ku ke so, amma banda Malam Rabi'u dan Allah".
"Au ke zaki faɗi abunda ki ke so ayi?, ai kuwa ba ki isa ba, ko Hassan ubanki bai isa ya ja da maganata ba balle ke, tashi ki bani guri, Allah ya ƙara nuna mini kin fita daga cikin gidan nan da sunan wata makaranta, wuce ki bani guri, da ido kamar gujjiyar mayu".
Cikin kuka Amina ta shiga cikin gida, kai tsaye ɓangarensu ta wuce, ta tarar da Inno tana surfe.
Sakin taɓaryar Inno ta yi, ta nufo in da Amina ta shigo tana kuka, tare da faɗin "Ke Amina lafiya? Waye ya rasu kike wannan kukan?".
Cikin kuka Amina ta ce "Kawu Bala ne wai ya ce kar in sake zuwa makarantar boko, wai Aure za suyi mini".
Tsaki Inno tayi ta ce "Shine za ki shigo kina mini wannan uban ihun, bokon banza da na wofi, matsa daga kusa da ni kar in makeki".
"Haba Inno, kema haka zaki ce? Yanzu kin yarda su aura mini Malam Rabi'u baban su Furera?"
Zaro ido Inno tayi ta ce "Malam Rabi'u kuma? Wannan mara mutuncin?"
"Shi fa, kawu Bala ya ce wai za su karɓi kuɗinsa na Aurena".
Jiki a sanyaye Inno ta ce "To Amina kiyi haƙuri, kin san duk gidan nan babu wanda yake musu da Kawu Bala, ciki kuwa har da mahaifinki, shi yasa na so kafin su farga su yanke makamancin wannan hukuncin, ki fitar da mijin Aure, amma yanzu lokaci ya ƙure Amina, kin san tun da ya waiwaye ki ba wanda ya isa ya sanya shi canza Magana".
Amina ta ɗora hannu a ka, ta zunduma ihu ta durƙusa a gurin ta na faɗin "Wallahi idan aka aura mini mutumin nan an gama da rayuwata, sunana bazawara, dan Allah ku ƙyaleni in yi karatuna".
Inno ta ce ki rufa mana Asiri, kar ki sa su É—auka wani abun ne, ki sa su shigo su yi mana tijara".
Miƙewa Amina tayi ta shige ɗakinsu, tana cigaba da kuka har cikin ranta.
********
Tamkar wasu taɓaɓɓu haka suke ta shewa a falon.
Wata siriyar yarinya ce Kamar Fadila, cikin skirt high west, da wata body hook, sai hula a kanta, ta yi simple make up.
Hatta yanayin rawar kanta da iyayinta irin na Fadila ne. Dama hausawa suka ce, sai hali yazo É—aya ake abota.
Fadila ta kalli ƙawar tata ta ce "Yusra kin ga yadda ki kayi kyau kuwa? Ni kaina na yaba, ina ga shi wanda aka yiwa kwalliyar?".
Yusra ta ce "Girl brother nan naki sai a hankali, Allah ya sa in ishe shi kallo".
Fadila ta ce "dalla kar ki damu, zai yaba haba sai kace ba namiji ba, dole ya ƙyasa, yanzun nan zai shigo, muje ɗakina in ƙara gyara miki kwalliyar nan, a ƙara powder da turare".
Haka kuwa aka yi, suka shiga É—akin Fadila, da yake Fadila gwanace gurin kwalliya da gyaran jikinta, tsaftar muhalli ce komai sai dai ayi mata.
Yusra ta kuma fitowa ta yi ras da Ita, suka dawo falo suka cigaba da hira.
Suna tsaka da hirar ne, suka ji shigowar mota gidan, Fadila ta leƙa ta window, da sauri ta dawo tana faɗin "Girl, gashi nan, shine ya dawo".
Cikin hanzari Yusra ta sake feffesa turare, da sake gyara zama.
Khalil ne ya shigo falon, hannunsa riƙe da wayarsa da makullin mota.
Yana shigowa gaba É—aya Yusra ta rasa nutsuwarta, saboda tsananin kwarjinin da Khalil yake da shi.
"Ina wuni Brother" Yusra ta faÉ—a cikin fargaba.
"Yawwa sannunki" ya amsa yana ƙoƙarin shigewa.
Fadila ta ce "Brother, baka gane ta bane? Yusra ce fa".
Khalil yayi murmushi ya ce "Na ganeta mana, ai nace mata Hi ko?".
Yayi Maganar yana hararar Fadila.
Ba Yusra ba, Fadila kanta ta ji haushin yadda Khalil y nunawa ƙawarta halin ko in kula, duk da wannan tarin hoda da turare da ta saka saboda shi.
Gyara sharhi ko shawara
08081012143
Ayi following account É—ina a Arewabooks@ Ayshercool7724
Da kuma Watpad Ayshercool 7724
Share Please ðŸ™
GABA DA GABANTA
    Page3
      Â
By Aisha Adam (Ayshercool)
(Shin kin karanta littafin DARE DA DUHU?, Wanda yake daga gamayyar alƙaluma uku, daga haziƙan marubuta uku, Zee kumurya, Nimcyluv da kuma Ayshercool, kar ku bari a baku labari, ku mallaki na mu akan Kuɗi Naira 300 kacal. *DARE DA DUHU*
_Allahamdulillah Babu Abinda bright pens za su ce sai godiya a gareku. Kun amshi littafin fiye da kima. Duk cewa Fiction story amma da yawan Labarin abune na da muke fuskanta reality🌚😢_
*DARE DA DUHU*
₦300 NE
Via 0116886423Â Sulaiman Na'ima s union Bank. Idan katin waya ne mtn na 500 idan transfer ne É—ari uku kacal.
Evidence of payment 07063065680 ko 09047871750)
DADICATED TO BRIGHT PENS
Saroro suka yi gaba É—aya suka bi bayan Khalil da kallo.
Yana shiga sashin Mummy ya dawo falo, ya kalli Fadila ya ce "Ke ina Mummy ne?"
Fadila ta tsuke fuska ta ce "Ba ta nan".
Ya ce "ok"
Yusra ba ta gajiya ba ta ce "Yaya a dawo lafiya".
"Ameen thanks" daga haka ya fice.
Fadila ta ja wani uban tsaki, ya yin da Yusra ta yi shiru tana tunani.
Fadila ta ce "Girl, ki yi haƙuri dan Allah, ki kwantar da hankalinki, na miki alƙawari insha Allah sai Brother ya so ki".
Yusra ta ce "Till when dear? Wallahi ba zaki gane yadda nake son Yayan nan naki ba, amma kwata-kwata ya ƙi damuwa dani".
"Kin san me? Kar ki damu, You know he is very classic, shi komai nasa baya son raini, shi yasa amma zamu shawo kansa very soon".
Yusra ta ce "Shikenan, Allah yasa, bari in wuce gida".
Fadila ta ce "Muje in raka ki" suka fito harabar gidan, suna cigaba da tattauna yadda za su ɓullowa lamarin Khalil.
****************
Ta gama shirinta tsaf, cikin dogon hijjabinta, sai dai ta janyo kujerar tsugono ta zauna, ta zubawa kayan gabanta ido.
"Hafsa, ya har yanzu baki tafi ba, ko almajirin da zai taya ki É—aukar kayan ne bai zo ba?".
Hafsa ta ce "Mama, jarin mu ne yayi ƙasa, ana samun ciniki Alhamdilillah, amma kin ga a ciki muke komai, har magungunanki a ciki muke siya, kuma jarin ba ƙaruwa yayi ba, itace ma bashi na karɓa, mai ma kuɗin rabi na bayar aka bani, na cika sauran daga baya idan nayi cinikin yau".